ZARGIN KWARTANCI: ‘Yan sanda sun wanke sanata Akwashiki, sun ce yi kazafi aka yi masa bayan bincike da suka yi

Yan sanda sun wanke sanata Akwashiki, sun ce yi kazafi aka yi masa bayan bincike da suka yi

Idan ba a manta ba an rika watsa bidiyo da hotunan Mataimakin Kakakin Majalisar Jihar Nasarawa, Godiya Akwashiki, a soshiyal midiya wadanda aka yi masa zigidir, bayan zargin kama shi da kokarin neman wata mata wa tana Maris din 2019.

A wancan lokaci an watsa cewa an kama Godiya Akwashiki ne ya na kokarin kwanciya da matar tsohon sakataren Hukumar Kula da Shari’a ta Kasa, Danladi Halilu, da aka sani da ‘Envuluanza.’

A cikin bidoyon, an ga yadda zababben sanatan ke ta rokon a ba shi ruwa ya sha. Can daga sama kuma ana jin wata murya wadda aka tabbatar da cewa ta Danladi din ce.

Bayan haka sai Akwashiki ya garzaya ofishin ‘yan sanda bayan karyata zargin da aka yi masa cewa siyasa ce kawai da bita da kulli.

PREMIUM TIMES ta nemin kwafin wanke Akwashiki da ‘yan sanda suka yi domin tabbatar da abin da yayi.

download

Sabuwar wakar Hamisu Breaker ‘Dan Dako’ data girgiza Kannywood a shekarar 2022

A takardar ‘yan sandan, an gani karara cewa tabbas mai zargi Danladi Envulanza bai bada kwararan shaidu ba kan cewa lallai Akwashiki ya nemi ya yi zina da matarsa wanda dalilin haka ne ya sa aka yi masa zindir a bainar jama’a.

‘Yan sanda solar ce binciken su duk ya nuna kazafi a ka yi masa da kuma gobarar gabar siyasa da ta nemi ta babbake shi tsakanin sa da wani, amma babu inda aka ga wai ya nemi ya yi lalata da matar abokin hamayyarasa a siyasar Nasarawa, Danladi.

Bayan haka shi da kansa Akwashiki ya bayyana cewa bayan wannan wulakanci da aka yi masa, manyan jihar hadi da gwamnan jihar, sarakuna da masu fadi aji na yankin su solar yi zama da shi solar ce ya janye karar a kotu su yi sulhu a tsakanin su wanda hakan yayi.

” Na ji kiran da manya suka yi mini shi yasa na rubuta wa yan sanda su dakatar da binciken da suke yi wanda shine ya kawo kara gaban su cewa solar yi sulhu a tsakanin sa da mijin wanda ake zargi ya nemi matar sa, wato Danladi Envulanza.

About NgArewa 2773 Articles
Am the pioneer of this web. Am smart, vibrant, and I love to keep the readers informed, and Blogging is my profession and wining is my satisfaction.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*