Yadda Maimartaba Tsohon Sarkin Kano Ya Fitar Da Mutum Sittin Daga Gidan Kurkurku

A yau din nan majiyarmu ta samu wani labari wanda toshon mai martaba sanusi lamido sanusi na II ‘yanta fursunoni mutum goma sha hudu kamar yadda wannan hakizin marubuci ya sanar mai suna Indabawa Aliyu Imam inda ya wallafa a shafinsa kamar haka.

A yau Laraba, Maimartaba Sarkin Kano na goma sha hudu kuma Khalifan Tijjaniya Malam Muhammadu Sunusi ya fitar da mutum sittin daga gidan kurkuku.

Mutum goma sha hudu ne suka shaki iskar ‘yanci a gidan gyaran hali na Kurmawa sakamakon biyan bashin kudaden da suka yi sanadin shigarsu gidan na Kurmawa wanda Maimartaba ya yi, wanda aka biya Niara Miliyan Sha Hudu da Dari Bakwai Da Sabain da Tara N14, 779,000:00.

Kalli Katafaren Sabon Gidan Musa Mai Sana Ya Girgiza Matan Kannywood

Daga nan kuma, an rankaya gidan gyara hali na goron dutse, inda mutum arba’in da hudu suka shaki iskar ‘yanci wadanda suka hada maza ishirin da hudu da mata ishirin, an biya miliyan goma sha bakwai da dubu dari takwas da hamsin da shida.

Da yawan wadanda aka fitar bashi ne ya sabbaba zuwansu gidan na gyaran hali, sai wadanda aka saka musu tara suka kasa biya.

Fiye da shekaru masu yawa Maimartaba tsohon Sarki yake wannan alkhairin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here