Tirƙashi Ankama wani magidanci zai saida ƴaƴansa mata biyu a Jihar Akwa Ibom

Tirƙashi Ankama wani magidanci zai saida ƴaƴansa mata biyu a Jihar Akwa Ibom.

Jami’an Hukumar Tsaro ta Civil Defence a Jihar Akwa Ibom sun cafke wani mutum yana kokarin sayar da ƴaƴansa biyu saboda bashi da ya yi masa yawa.

A safiyar yaune muka tsinkayi wani saban rahoto daga jihar Akwai Ibom.

Duba da irin ta laucin da muke fama da shi a cikin kasarmu Nigeria haƙiƙa wannan abun yana mutuƙar ɗaga hankula jama’a jama’ar ƙasar baki ɗaya.

Baya da haka a na zargin mutumin da hada baki da matarsa wajen sayar da ƴaƴansu guda biyu biyu mata a kan Naira 700,000 domin ya biya bashin da ake binsa.

Tirkashi: Bidiyon jarumi Sadiq Sani Sadiq yana rawar rashin daraja da wata

READ:   Jerin Fitattun Jaruman Kannywood Da Suke Da Muni Kafin Su Girma

Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Umana Ukeme ya fitar a ranar Laraba ta ce mutumin ya shiga hannu ne a garin Uyo babban birnin Jihar Akwa Ibom wanda jami an tsaron sukayi ram dashi.

Umana Ukeme ya ce mutumin wanda yake rayuwa a Kasar Kamaru ya shiga hannu ne tare da mai dakinsa a ranar 15 ga watan Nuwamba bayan bincike sirri ya bankado yunkurinsa na sayar da yaran mata biyu.

Jami’in na hukumar NSCDC ya ce daya daga ƴaƴan mutumin akwai mai shekarun haihuwa shida sai kuma karamar mai shekaru hudu.

Sanarwar ta ambato mutumin mai shekara 40 da ake zargi yana cewa ya yi niyyar sayar da ƴaƴansu ne saboda tsananin talaucin da yake fama da shi.

READ:   Mustapha Nabruska Yayiwa Afakallah Wankin Babban Bargo Akan

To jama’a zamuso mukarɓi ra ayoyin Ku akan aukuwar wannan lamari don jin tabakinku zamuso kubiyomu kaitsaye ta sahinmu na tsokaci.

Kada ku manta ku danna mana alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar mungode.

Source: Dalatopnews

About Arewanmu 609 Articles
24/7 Hausa Hip Hop Music, Music Videos, Wakokin Hausa, Labarai, Kannywood, Naija Music, Addini, Fadakarwa, Wasanni, in indigenous language✅✅✅

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*