SIYASA ROMON JAƁA: Mashawarcin Buhari ya ce ba zai goyi bayan Tinubu a zaɓen 2023 ba

Mashawarcin Buhari ya ce ba zai goyi bayan Tinubu a zaɓen 2023 ba

Yayin da aka fara kaɗa gangar zaɓen 2023, kuma har wasu jiga-jigai solar fara karkarwa su na kirari, ɗaya daga cikin wanda ya nuna maitar neman tsayawa takara a ƙarƙashin APC, shi ne jagoran jam’iyyar Bola Tinubu.

To sai dai tun tafiya ba ta ma kai ga batun fitowa yankan tikitin takara ba, Tinubu ya fara haɗuwa da cikas.

Wasu da aka riƙa danganta su da Tinubu solar riƙa fitowa su na ƙaryatawa, musamman Ƙungiyar Yarabawa Zalla (OPC), Dele Mamudu da wasu daban.

A jiya kuma Mashawarcin Shugaba Muhammadu Buhari a kan Al’amurran Siyasa, Babafemi Ojudu, ya fito ya bayyana cewa ba zai goyi bayan kamfen ɗin ubangidan sa Bola Tinubu ya zama shugaban ƙasa ba.

Ojudu wanda yaron Bola Tinubu ne a baya, ya ce amma fa kada jama’a su ka matsayar da ya ɗauka a matsayin cin amana.

download

Cikin Wata sanarwar da ya fitar a shafin sa na Fb a ranar Talata, Ojudu wanda ya ce shi da Tinubu solar daɗe su na tafiya tare, “to amma a gaskiya mutunci na da tunanin da zuciya ta ke nuna min, ba daidai ba ne na goyi bayan Tinubu ya zama shugaban ƙasa.”

Ojudu da Tinubu solar fara shaƙuwar siyasa tun farkon 1990, inda tsohon gwamnan Lagos ɗin da kuma ɗan jarida Ojudu, wanda ya koma ɗan siyasa ya zama sanata.

ARCEWAR ƊAURARRU 5,238 DAGA KURKUKU: Ku kashe masu kai hari kurkuku har lahira – Umarnin Aregbesola ga Jami’an tsar

Tinubu ya narka kuɗi a mujallar TheNews, wadda mallakin Ojudu da wasu abokan sa ce a lokacin.

Sai dai kuma a cikin 2016, Buhari ya naɗa Ojudu Mashawarcin Shuagab Ƙasa a Harkokin Siyasa, kuma ya umarce shi da ya yi aiki tare da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo.

Duk da cewa Tinubu ne tsanin da aka taka aka ɗora Osinbajo kan kujerar Mataimakin Shugaban Ƙasa, tun tafiyar ba ta yi nisa ba su ka raba hanya, babu jituwa a tsakanin su.

Ana ganin dai a yanzu Ojudu ya ɗauki hanyar goyon bayan takarar Osinbajo, kuma ya fara tallar sa a zahiri da baɗini.

A cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata, tsohon sanatan ya ce har an fara yi masa barazana, kuma iyalin sa ma ana yi masu bsrazana, saboda kawai matsayar da ya ɗauka ta ƙin mara wa Tinubu baya.

“Kada ma wani ya yi tunanin cewa zai iya tirsasa ni yin abin ca mutunci na da zuciya ta ba su amince min na yi ba.” Inji Ojudu.

“Masu yawan kiran waya ta su na yi min barazanar banza da wofi da masu neman su kunyata iyali na, su daina haka nan.

“Na san Tinubu. Ina girmama shi. Da yawan waɗanda ke goyon bayan sa a yanzu, ba su ma san wane ne Tinubu ba. Da solar san wane ne Tinubu da ba su tsaya su na tayar da jijiyar wuya a kan sa, har su na neman ci min mutunci ko kai min hari ba.

“Lokacin da Tinubu ya ƙi goyon bayan takarar Obasanjo a 2003, ba a kira shi maci amanar jinsin Yarabawa ba ko maci amanar Afenifere.

ZARGIN KWARTANCI: ‘Yan sanda sun wanke sanata Akwashiki, sun ce yi kazafi aka yi masa bayan bincike da suka yi

“Ya zaɓi abin da ran sa ya biya masa a lokacin, kuma tarihi ya yi masa hukunci da alƙalanci. To ni ma ina so tarihi ya yi min hukunci da alƙalanci.

“Kuma lokacin da Tinubu ya goyi bayan Olu Falae maimakon jagoran mu Bola Ige, ai babu wanda ya kira shi Tinubu ɗin maci amana.

“Ku kuma ƙananan ‘yan iskan da ke ta aiko min da saƙonnin waya ku na yi min barazana, ni da iyali na, kuma ku na surfa min zagi don na ƙi goyon bayan Tinubu, ku sani hakan ba dimokraɗiyya ba ce.

“Na shafe shekarun tasowa ta a rayuwa ina yaƙi da danniya da masu danniya da masu mulkin soja. To har yanzu a shirye na ke, kuma ba zan saki abin da zuciya ta ta fi kwantawa da shi ba, ko da kuwa za a ɗauki rai na.”

About NgArewa 2725 Articles
Am the pioneer of this web. Am smart, vibrant, and I love to keep the readers informed, and Blogging is my profession and wining is my satisfaction.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*