Saboda So da kaunar Buhari wani ya sanyawa jaririnsa suna Buhari

Saboda So da kaunar Buhari wani ya sanyawa jaririnsa suna Buhari

Saboda So da kaunar Buhari wani ya sanyawa jaririnsa suna Buhari; Malam Maiwada ‘Danmallam, ya bada labarin wani mutumi da ya samu haihuwa, ya kuma yi wa shugaban Najeriya takwara da wannan jaririn.

Maiwada ‘Danmallam ya bayyana wannan ne a shafinsa na Fb a yau, Litinin 17 ga watan Junairu, 2021, inda mutane ke ta faman yi wa jaririn addu’o’i.

Legit na ruwaito Kamar yadda ya fada, Danmallam yace wani abokinsa ne ya turo masa sako cewa matarsa ta haihu a ranar Larabar da ta wuce, ya sa wa yaro suna Buhari.

A cewar wannan mutumi da ya samu kyakkyawan yaro, kauna da soyayyar Mai girma shugaban kasa ta sa ya zabi wannan suna watau Muhammadu Buhari.

ALBUM: Keedron Bryant – Keedron [Zip + Mp3] [Lyrics & Video]

download

“Ina kwana mai girma jagorana. Ubangiji ya azurta ni da iyalina da samun jariri namiji a ranar Laraba, 12 ga watan Junairu, 2022.”
“Kuma saboda irin kaunar da nake yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari, na sa wa jaririn sunansa, Muhammadu Buhari.”

“Da mahaifiyar da yaron duk su na lafiya.” – Mai jego.

Me jama’a suke fada?

Mutane su na ta tofa albarkacin bakinsu a sport da wannan karuwa da aka samu. Yayin da wasu suke yi wa iyalin barka, wasu kuma akasin hakan su ke yi.
Allah Ya raya Muhammadu Buhari, Ya albarkaci rayuwarsa – Jafar Jafar

Ina fatan ba za su canza ra’ayi, su canzawa yaron suna daga baya kamar yadda wasu suka yi ba. – Yamai Mohammed

Muhammadu babban suna… Allah Ya raya shi cikin musulunci, Yayi masa albarka. Amin

Muhammad Azare
Masha Allah – Sham Faliya Sharon
Allahumma Aameen. Wasu za su ji haushin wannan abin, babu gaira babu dalili. Sai su yi ta bakin ciki! – Yusuf Muhammad Illo

Amin – SK Usman
Alhamdu lillah Allah yasa masa albarka ya rayashi rayuwar musulunci Allah yasa ya gaji halayen mai sunan gaskiya da rik’on amana.Allah ya kareshi daga sharrin zamani da na shedan a gaida mai jego muna taya ta murna da fatan alheri – Abdulrahman Masanawa

About NgArewa 2782 Articles
Am the pioneer of this web. Am smart, vibrant, and I love to keep the readers informed, and Blogging is my profession and wining is my satisfaction.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*