ROKON BUHARI GA ‘YAN BINDIGA: ‘Ku wa Allah ku sako sauran daliban Jami’ar Greenfield’

0
12

ROKON BUHARI GA 'YAN BINDIGA: 'Ku wa Allah ku sako sauran daliban Jami'ar Greenfield'

Shugaba Muhammadu Buhari ya roki ‘yan bindiga sako sauran daliban Jami’ar Greenfield ta Kaduna da har yanzu ke tsare a hannun su.

Ya kuma yi rokon su a sako duk wani da aka yi garkuwa da shi a fadin kasar nan.

MATSALAR TSARO: Majalisar Dattawa na ganawar sirri da Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya

Wannan roko na cikin wata sanarwar taya daliban Babbar Kwalejin Aikin Gona kubuta da su ka yi daga hannun ‘yan bindiga, bayan sun shafe sama da kwanaki 50 a tsare.

Cikin bayanin da Kakakin Yada Labarai na Shugaban Kasa, Garba Shehu ya fitar a ranar Laraba, Buhari ya taya daliban na ‘Federal College of Foresty Mechanizarion, Afaka su 27 murnar kubuta daga hannun ‘yan bindiga.

READ:   Jerin Tsofaffin Jaruman Kannywood Mata Da Sukaga Jiya Kuma Sukaga Yau

Bidiyo: Aminu Saira Ya Sake Karin Bayani Akan LABARINA S3 Da Kuma Wata Sanarwa Mai Mahimmanci

Ya kuma taya iyayen su da gwamnatin jihar Kaduna murnar ganin karshen wannan kakuduba.

“Mu na kuma godiya ga dukkan wadanda su ka sa hannu su ka taimaka wajen kawo karshen wannan matsala, musamman jami’an tsaro, jami’an Ma’aikatar Muhalli da kuma Gwamnatin Jihar Kaduna. Kuma mu na godiya ga ‘yan Najeriya dangane da addu’o’in da su ka rika yi.”

Sai dai Buhari ya nuna damuwa kan masu amfani da siyasa su na kara rura wutar matsalar tsaro a kasar nan.

Sannan kuma ya jaddada kokarin sa wajen tabbatar da cewa ‘yan Najeriya sun rika samun walwala da zirga-zirgar zuwa ko’ina a fadin kasar nan, ba tare da tsoron masu garkuwa ko ‘yan bindiga ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here