RASHIN TSARO: Na fallasa wa Buhari gaggan masu hana ruwa gudu a Zamfara – Matawalle

ZAMFARA FOR BUHARI

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya bayyana cewa lallai ya sanar wa shugaban kasa Muhammadu Buhari gaggan masu hana ruwa gudu recreation da matsalar tsaro a jihar Zamfara.

Matawalle ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa ranar Litini.

” Na taho fadar gwamnati ne domin in sanar da shugaban Kasa abubuwan da suke faruwa a jihar Zamfara musamman a wadannan kwanaki wanda aka yi kisar mutane da dama a wasu kananan hukumomin jihar.

Bayan haka Matawalle ya karyata rahotannin da ake yadawa wai an kashe mutane sama da 200 a wannan hari da suka kai.

” Ni da kai na na ziyarci Bukuyyum da Anka, kuma sarakunan wadannan garuru solar sanar dani ainihin mutanen da aka kashe. kuma duka ba su wuce mutum 58 ba. Amma wasu na ta yada karerayi wai mutanen da aka kashe solar fi dubu.

download

” Wadannan wasu ‘yan siyasa ne da basu da kishin jihar suke ruruta wutar rashin zaman lafiya. Su kira ‘yan jarida su gaya musu maganganun da ba gaskiya bane. Na kuma sanar da shugaban kasa na kuma gaya mishi ko su waye.

Bayan haka ya yi karin haske recreation da shirin sulhu da gwamnati ta yi a baya yana mai cewa ” A lokacin da muka yi wannan tsari ya yi aiki. sai da aka yi watanni 9 babu kisa ko hari da aka kai a ko’ina a fadin jihar. Amma wasu da ba su son nasarorin da aka samu a lokacin wadanda ke jin dadin abinda ke faruwa suka koma suka rika zuga ‘yan bindiga su koma su ci gaba da aiyukan ta’addancin su.

MUTAN ZAMFARA SUN BANI: ‘Yan bindiga sun aika wasiku kauyuka 9 su biya Harajin miliyoyin naira ko su kwankwadi ruwan azaba

Ban ga alaman za a kawo karshen hare-haren ta’addanci a Zamfara nan kusa ba – Matawalle

” Bisa ga irin mutanen da muke da su a jihar Zamfara, ban ga alamar za a kawo karshen ayyukan ta’addanci ‘yan bindiga a nan kusa ba. Domin akwai wasu gaggan mutane da suke cikin sa tsundum suna amfana da shi. Kuma burin su shin su nuna wa gwamnatin tarayya cewa gwamnatin tarayya da na jihar solar gaza domin suna tare da ‘yan bindiga.

Matawalle ya ce ya ziyarci kasar Nijar domin ya tattauna da gwamnatin kasar recreation da yadda za a dakile shige da ficen ‘yan bindiga da bakin haure.

A karshe ya ce mutanen Zamfara za su ga canji tun daga cikin wannan mako da ake ciki.

About NgArewa 2780 Articles
Am the pioneer of this web. Am smart, vibrant, and I love to keep the readers informed, and Blogging is my profession and wining is my satisfaction.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*