MUTAN ZAMFARA SUN BANI: ‘Yan bindiga sun aika wasiku kauyuka 9 su biya Harajin miliyoyin naira ko su kwankwadi ruwan azaba

Wasikar Bandits

A wasu wasiku da suka bayyana rabar Litinin a wasu kauyuka dake Zamfara, mahara solar gargadi mazauna wadanna kauyuka su gaggauta biyan su kudin tara na haraji cikin gaggawa ko kuma su sha ruwan azaba daga wurin su.

Wadannan wasiku wanda ya kunshi harda lambar waya solar gargadi mutanen kauyukan Yargalma, Wawan Iccen Ibrahim, Wawan Iccen Salihu Gaude Galle da Tungar Gebe. Sannan kuma akwai Nannarki da Ruwan Kura.

Wani gogarman ‘yan bindiga mai suna Dogon Sabi na Auwali Wanzam ne ya rattaba hannu bisa wadannan wasiku.

Ga yadda suka kasafta kudaden da kowacce kauye za ta biya: Yargalma N5,000,000, Wawan Iccen Ibrahim N4,000,000, Wawan Iccen Salihu N1,000,000, Gaude N1,000,000, Galle N1,000,000, Tungar Gebe N500,000. Nannarki da Ruwan Kura N5,000,000

Hakimin Zugu dake karamar hukumar Bukuyyum, shine ya tabbarwa PREMIUM TIMES yana mai cewa duka wasikun an aiko su garin Zugu ne.

download

Ya kara da cewa wasu da ‘yan bindigan suka saki ne suka zo musu da wasikun domin rabawa kauyukan.

Wani shugaban matasa a yankin ya bayyana wa wakilin mu cewa wasu da ‘yan bindigan suka saki ne bayan solar biya kudin fansa suka taho da wadannan wasiku.

ZAZZABIN LASSA: Mutum 48 sun kamu, mutum biyu sun mutu a Najeriya a cikin makon jiya

Ya kara da cewa tuni har mazauna kauyukan solar fara hada kudade domin biyan iyayen gidan su wato ‘yanbindigan domin gudun afkawa bala’in su.

Idan ba a manta ba Arewanmu Ta buga labarin yadda mazauna garin Nahuche suka yai tattaki zuwa fadar gwamnatin jihari domin rokon gwamnati ta kawo musu dauki saboda bala’in ‘yan bindiga da suka addabe a garin.

About NgArewa 2782 Articles
Am the pioneer of this web. Am smart, vibrant, and I love to keep the readers informed, and Blogging is my profession and wining is my satisfaction.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*