Musu kan kungiyoyin kwallon kafa na Chelsea da Barcelona ya sanya aboki ya kashe abokin shi a Katsina

Musu kan kungiyoyin kwallon kafa na Chelsea da Barcelona ya sanya aboki ya kashe abokin shi a Katsina

An gurfanar da wani dan shekara 18 mai suna Idris Yusif, a gaban babbar kotun majistare ta jihar Katsina, a bisa tuhumar sa da kashe wani Saifullahi Abdullah, a kan musun kwallon kafa.

A cewar jaridar Labarunhausa, Saifullahi mai shekaru 28 ya mutu ne bayan musu da suka yi akan wacce kungiyar kwallon kafa ce tafi wata, tsakanin Chelsea da Barcelona, inda daga baya, wannan musu ya rikide ya koma fada a tsakanin su, a ranar 12 ga watan Disambar shekara ta 2021, cikin karamar hukumar Danja dake jihar Katsina.

Mahaifin Saifullahi ya kai kara

Mahaifin mamacin, ya kai rahoton faruwar lamarin zuwa ga ofishin ‘yan sanda na Danja a ranar 20 ga watan Disambar 2021.

Yusif, wanda aka gurfanar dashi ranar Litinin a gaban babbar kotun majistare, ana tuhumar sa da laifin kisan kai. A karkashin sashi na 190, karamin sashi na(1) kamar yadda kundin tsarin doka na (penal code) ya tanada.

download

Da yake jawabi ga kotu, dan sanda mai gabatar da kara, Bello Lawan yace, Abdullah ya fadi kasa wanwar, a lokacin da suke rigimar tsakanin shi da wanda ake kara.

A asibiti Saifullahi ya rasu

Ya kara da cewa, an garzaya da mamacin asibiti, inda a can rai yayi halinsa.

A cewar rahoton farko:

YoungBoy Never Broke Again Reveals Colors Tracklist

“A ranar 18 ga watan Disambar shekarar 2021, da misalin karfe 3:30 na yamma, Saifullahi Abdullah yayi musu da kai, Idris Yusuf, dan shekara 18. A unguwar Hayan Asibiti dake Danja, akan wacce kungiyar kwallon kafa ce tafi wata karfi da kuma nagarta tsakanin Chelsea da Barcelona wadanda suke a kungiyoyin wasannin nahiyar turai. Wanda a sakamakon haka abin ya rikide ya zama fada wanda shi Saifullahi ya fadi magashiyan.

“Daga baya, aka garzaya da mamacin cibiyar kula da lafiya ta Danja (Danja complete well being centre ) aka kwantar da shi, inda daga baya kuma likita ya tabbatar da mutuwarsa “

Bayan sauraren koken dan sanda mai gabatar da kara, Fadile Dikko, alkalin kotun ta dage karar zuwa 7 ga watan Maris, 2022.

Sannan ta bada umarnin a ci gaba da tsare Yusuf a gidan kaso har zuwa ranar da aka daga shari’ar.

About Da_Great_Niddy K 4285 Articles
Great Technician

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*