Malejin tsadar rayuwa ya ƙara yi wa ƙugun ‘yan Najeriya ɗaurin kalangu, bayan sassaucin watanni takwas

IMG 20210907 144559 HDR2 scaled

Awon mizanin malejin tsadar rayuwa ta tsawon shekara ɗaya a Najeriya, ya ƙara cillawa sama, bayan sassaucin tsawon watanni da aka samu a jere.

Tsadar rayuwa ta ƙaru da kashi 15.63 a cikin watan Disamba, 2021 idan aka kwatanta ko aka auna ta watan Nuwamba mai kashi 15.40.

Wannan bayani ya fito daga Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa, wadda mallakin Gwamnantin Tarayya ce, a ranar Litinin.

Hukumar, wato NBS ta ce farashin kayan abinci da ayyukan biyan buƙatun dole da na yau da kullum, solar ƙaru da kashi 15.63 cikin Nuwamba, 2021, idan aka auna na watan Disamba 2021, shekara ɗaya baya kenan.

Jigawa ta zama dandalin Ƴan ciranin Siyasa, Daga Ahmed Ilallah

download

Sannan NBS ta ce idan aka auna canjin farashin kayayyaki tsakanin watan Disamba 2020 da Nuwamba 2021, za a ga cewa farashin ya ƙaru da kashi 1.82 cikin Disamba 2021, alhali adadin ƙarin a cikin Nuwamba 20210, bai wuce kashi 1.08 ba.

Tashin alƙaluman ƙididdigar ya faru ne saboda ƙarin tsadar kayan abinci da aka riƙa samu.

NBS ta ƙara da cewa tsadar kayan abinci ta yi sama zuwa kashi 17.37 bisa 100 a cikin Disamba, 2021.Amma idan aka kwatanta da Disamba 2021, za a ga cewa ƙasa ya yi da kashi 19.56.

About NgArewa 2781 Articles
Am the pioneer of this web. Am smart, vibrant, and I love to keep the readers informed, and Blogging is my profession and wining is my satisfaction.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*