Lambar Shaidar Dan Kasa (NIN) za ta taya mu fallasa batagari, mabarnata da ‘yan iska – Buhari

0
15

Lambar Shaidar Dan Kasa (NIN) za ta taya mu fallasa batagari, mabarnata da 'yan iska -Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Rajistar Lambar Shaidar Dan Kasa (NIN) da kuma hada ta da lambar waya zai taimaka wajen yaki da matsalar tsaro a kasar nan.

Cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai Femi Adesina ya fitar bayan taron kaddamarwa a ranar Alhamis, Buhari ya ce da zarar an hada kowace lambar waya da lambar shaidar dan kasa, to babu sauran wurin buya ga batagari, mabarnata da ‘yan iska.

Buhari ya yi wannan bayanin a lokacin kaddamar da Shirin Karfafa Amfani da Kayyyakin Sadarwa na Gida da Sabon Tsarin Rajistar Katin Dan Kasa da Lambar Waya.

Ya ce idan aka taskace dukkan ‘yan Najeriya da mazauna kasar nan a rumbun tattara bayanai wuri daya, zai karfafa tsaro da sa-ido wajen hana aikata manya da kananan laifuka.

READ:   ROKON BUHARI GA 'YAN BINDIGA: 'Ku wa Allah ku sako sauran daliban Jami'ar Greenfield'

“Tsarin NIN zai magance daya daga cikin bangaren da mu ke da sakaci wajen tsaro. Amma yanzu za mu iya gane kowa a Najeriya. Za mu iya tantance mutum nan da nan, har da batagari da ‘yan iska.” Inji Buhari.

Cikin shekarar 2020 aka fara aikin hada lambar shaidar dan kasa da lambar waya, aka ce za a kulle cikin Disamba.

Sai dai an rika dagawa har sau biyar, saboda dalilan rashin saurin da aikin ba ya yi.

Zuwa yanzu dai an hada lambobin waya miliyan 190 ga lambar katin shaidar dan kasa miliyan 54.

Buhari ya shawarci dukkan ‘yan Najeriya su gaggauta yin rajistar hada lambar waya da katin dan kasa.

READ:   Yadda Istimna'i (Zinar Hannu) ke Zama babbar barazana ga Sabbin ma'aurata

“A shekarun baya an yi wannan kokarin, amma ba a yi nasara ba saboda wasu dalilan da su ka hada har da yi wa shirin makarkashiya. Amma a yanzu wannan gwamnatin ta tabbatar da shirin ya yi nasara.”

Ministan Sadarwa Isa Pantami ya ce an yi wa mutum miliyan 54 rajistar lambar katin shaidar dan kasa tare da hada lambobin wayoyin su da lambar shaidar NIN din su.

Ya ce ya na da yakinin za a yi wa kashi 99.9 na ‘yan Najeriya da mazauna kasar nan rajistar NIN da ta lambar waya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here