Kotu ta bada belin saurayin da ya dirka wa ciki ya waske ya barta cikin wahala kan naira 100,000

images 54

A kotun majistare dake Ota jihar Ogun ne aka gurfanar da Korode Yusuf mai shekara 24 saboda kin kula da budurwar da ya dirka wa ciki.
Yusuf wanda ke zama a layi na 6 na Kajola Okuwa a Isale Ariya dake kasuwan Ota ya aikata haka ne a ranar 1 ga Maris 2021.

Lauyan da ya shigar da karan E. O. Adaraloye ya ce Yusuf ya bar budurwarsa dake dauke da tsohon ciki da yunwa sannan ya ki biyan sauran bukatunta duk da cewa suna zama tare.

Adaraloye ya ce rashin kula da budurwarsa dake da ciki da Yusuf ya yi ka iya cutar da rayuwar yarinyar da dan dake cikinta.

Shi kuwa Yusuf ya musanta duk abin da lauyan ya fada a kansa yana mai cewa yana iya kokarinsa wajen biyan bukatun budurwarsa amma rainawa take yi.

ZARGIN KWARTANCI: ‘Yan sanda sun wanke sanata Akwashiki, sun ce yi kazafi aka yi masa bayan bincike da suka yi

download

Alkalin kotun A. O. Adeyemi ta bada belin Yusuf akan Naira 100,000 tare da gabatar da shidu biyu dake aiki kuma suke biyan gwamnatin jihar haraji.

Adeyemi ta ce Yusuf ya tabbatar cewa shaidun da zai gabatar na zama a wurin da kotun dake da Iko.

Za a ci gaba da shari’a ranar 21 ga Janairu.

About NgArewa 2676 Articles
Am the pioneer of this web. Am smart, vibrant, and I love to keep the readers informed, and Blogging is my profession and wining is my satisfaction.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*