KATSINA: ‘Yan bindiga sun kashe dan jarida, sun yi garkuwa da mutane bayan sun kwace hanyar Jibia zuwa Zurmi

KATSINA: 'Yan bindiga sun kashe dan jarida, sun yi garkuwa da mutane bayan sun kwace hanyar Jibia zuwa Zurmi

‘Yan bindiga sun bindige wani dan jarida mai suna Ibrahim Dankabo yayin da ya kai gudummawar kururuwar yunkurin sace wata mata a Kukar Babangida, cikin Karamar Hukumar Jibia.

Bayan kisan Dankabo, sun arce da matar wadda mahaifiyar wani basarake ce da ke cikin Jamhuriyar Nijar.

KANJAMAU: Najeriya ce kasar da ta fi yawan jarirai dake dauke da kwayoyin cutar a duniya

Wani mazaunin yankin mai suna Gide Suleiman ya shaida wa AREWANMU cewa maharan sun kuma tare hanyar Katsina zuwa Jibia, sun kwashi matafiya masu yawa, wadanda duk mazauna garin Magamar Jibia ne.

“Mu na zaune cikin wani mawuyacin hali, saboda jami’an tsaro da kan su sun ce a daina bi hanyar Gurbi daga Zurmi daga Jihar Zamfara zuwa Jibia a Jihar Katsina.

download

“A wannan hanya duk abin da ‘yan bindiga ke yi babu mai iya yi masu magana. Akwai jami’an tsaro a Jibia har mota biyu. Amma motocin sun kakare ba su iya motsawa tsawon watanni biyu da su ka gabata zuwa yau.” Inji majiyar AREWANMU.

Ya ce ko an yi wa jami’an tsaron kiran gaggawa, ba su kai dauki.

Jihar Katsina na daya daga cikin jihohin da ‘yan bindiga ke cin karen su babu babbaka a Arewa maso Yamma.

ROKON BUHARI GA ‘YAN BINDIGA: ‘Ku wa Allah ku sako sauran daliban Jami’ar Greenfield’

Wannan kisa da samamen kama matafiya ya faru a ranar Litinin. Dama kuma wani mazaunin garin Rumah ta cikin Karamar Hukumar Batsari, ya shaida wa AREWANMU ta wayar tarho cewa hankalin mazauna kauyuka a tashe ya ke.

“Tabarbarewar tsaro ta kai lalacewar da ‘yan bindiga na bin kauyuka kamar ‘yan tashe. Su dira wannan kauye su kwashe dukiya da dabbobi, sannan kuma su nausa wani kauye.

“Gida-gida su ke shiga. Ba su duka ba su zagi. Amma da ka yi masu tsaurin ido za su bindige ka.”

About NgArewa 2667 Articles
Am the pioneer of this web. Am smart, vibrant, and I love to keep the readers informed, and Blogging is my profession and wining is my satisfaction.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*