JIHAR NASARAWA: Ƴan sanda sun damke Ɗan’Asabe da ya ci zarafin tsohuwa mai shekaru 80 a Lokonga

Handcuffs
Ƴan sanda solar damke Ɗan’Asabe da ya ci zarafin tsohuwa mai shekaru 80 a Lokonga

Ƴan sanda solar damke Ɗan’Asabe da ya ci zarafin tsohuwa mai shekaru 80 a Lokonga

Rundunar ƴan sandan jihar Nasarawa ta damke wani magidanci mai suna Dan’asabe Eddo dake da shekaru 45 da ake zargi da cin zarafin wata Gyatuma mai shekaru 80 a kauyen Kundami dake karamar hukumar Lokonga.

Kakakin rundunar yansandan jihar Ramhan Nansel ya sanar da haka ranar Lahadi a garin Lafia a lokacin da yake zantawa da manema labarai.

Nansel ya ce jami’an tsaro solar samu labarin ta’asar da Eddo ya aikata a kara da aka kawo ofishin ‘yan sanda dake Garaku ranar 14 ga Janairu da karfe 10:30 na dare.

Da Buhari bai zama shugaban Kasa ba da kila babu Najeriya yanzu – Kalu

Ya ce Dan’ Asabe Eddo wanda dan asalin jihar Kaduna ne amma yake zaune a kauyen Kundami jihar, Nasarawa ya bi wannan tsohuwa har cikin gidanta sannan ya kule dakinta inda take kwance tana hutawa ya danne ta yayi abinda ya kai shi.

Nansel ya ce Eddo ya tabbatar wa ‘yan sandan cewa shine ya yi wa tsohuwan fyade amma ya roki a yafe masa saboda ya ce ya hudubar shaidan ne ya bi.

download

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Adesina Soyemi ya ce fannin dake gurfanar da masu aikata laifi irin haka za ta ci gaba da yin bincike akai sannan bayan haka sai a kaishi kotu domin ya fuskanci shari’a.

Adesina ya hori mutane da su rika sa ido domin kare mutuncin tsoffi daga hannun mutane kamar su Eddo a jihar.

About NgArewa 2782 Articles
Am the pioneer of this web. Am smart, vibrant, and I love to keep the readers informed, and Blogging is my profession and wining is my satisfaction.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*