Jigawa ta zama dandalin Ƴan ciranin Siyasa, Daga Ahmed Ilallah

Badaru Campaign

Babu wata al’umar da mulkin dimokaradiyya zai mata amfani ta hanyar raya kasa da kuma ci gaban al’umma sai suna sanya masu jagorancin su, walau ta hanyar zabe ko bada mukami daga cikin mutanen da suke cikin su kuma alal akalla da suke da wadannan dabi’u.

Na farko masu kishin su, wayanda za su iya sadaukar da kawunan su don gina al’umar su da jahar su. Mutum ba zai zama mai kishin al’umar sa ba, sai ya kasance a cikin ta dadi da kari, ya san matsalolinsu, kuma tun kafin yakai wani matsayi ana gwagarmayar magance matsalolin al’ummar su da shi.

Na biyu, ya kamata ya zamanto mai ilimin garin su, jahar su da karkarar su, ba wai sani na suna ba, a a sani na zahiri, ta yadda yasan karfin su da gazawar su ta kowane fanni daga tattalin arziki, zamantakewa, ilimi, matsaloli da ma siyasar su, sannan ya kasan masanin al’adun su, addinin su da kuma ilimin zamani da gogewar siyasa da iya mu’amala da mutane.

Na uku, ya kamata ya kasance mai amana da mutunci da kuma kyakkyawar niyyar taimakon al’umar sa baya wai neman biyan bukata ta samun mulki ba, ko sanayya ko tara abin duniya ba.

Shin ba zai zame mana aya ba, irin mutanen da ke zuwa su ribbaci siyasar yankunan mu ko jahar mu, yayin da suke cikin mu, kullum suna tare da mu, in har kasuwa ta watse sai mu daina ganin su, ko jaje ko gaisuwar mutuwa basa zuwa mana balantana su taya mu biki yayin da muke cikin anashuwa?

download

Bai kamata talauchi ko kwadayin neman abin duniya ba, mutane suna sayar da yancin su da bayar da damar su ga wasu mutane da suka kasance yan fataucin siyasa domin kawai a kwai wata alaka, wanda da ga baya kwalliya taki biyan kudin sabulu.

Kamar yadda a kan yi gudu hijira don bido abin duniya, mafi akasarin yan gudun hijira, su kanje garin da suke da dangantaka, watakila dangantakar ta kusace ko ta nesa, musamman yayin da aka hango za a iya samun abin da ake nema ko kuma bukata za ta iya biya.

Duk da kasancewar dalilai da dama kan sa mutane su kauracewa garin su watakila dalilin hijira, don fatuci ko neman sana’a ko a zamanance yin aiki, musamman irin na gwamnati kan sanaya mutane barin garuruwasu na ainihi, sabon ko dadewar zama kan sa wasu ma su mance da garuruwan su, amma yaya da jikoki kan rike garuruwan su na ainihi a zuciyar su, yaya ko jikoki kan dawo garuruwan iyayen su da kakannin su, don neman biyan wata bukata, musamman ma in har anga bukatar zata iya biya.

Duk lokacin da aka buga gangar siyasa, mutanen Jigawa kan bakin yan ciranin siyasa daga kowane bangare suna tururuwa cewa suma ai yan jahar, saboda kakanin su anan a ka haifesu, wani lokacin har suyi uwa da makarbiya akan harkar siyasa, su zamanto suke jan akala saboda wasu dalilai, har ya kasance a kan fifita su fiye da kwararrun da ke cikin jahar mu, a basu damar da ba abawa yan siyasar mu ba duk da sunfi wanan bakin kwarewa wajen sanin matsalolin mu da yadda za a iya magance su.

Duk mai zuwa farauta baya fita ya dufafi daji kai tsaye, sai yayi karatun dajin, ya fidda dabarun da zai yi nasara a farautar sa, to haka zalika dan cirani, dan ciranin siyasa yafi kowa wayo bai dawo wa gari ko jahar da zai yi siyasa, sai yayi nasa karatun.

Duk da kasancewar ana ganin jahohi irin su Jigawa suna ciki jerin jahohin da suke koma baya a harkar siyasa, ilimi da ma wayewa, dadi da kari ana ganin tana cikin jahohin da talauchi yayiwa kakagida, wannan ya bawa jikoki da tattaba kunnin Jigawa damar zuwa ciranin siyasa, har ma su sami dauri gindi a wajen kartikan siyasar jahar.

A wani bangaren su kansu jagoraorin siyasar yan kanzagin su wato kartukan siyar kan bada gudunmawa ta wajen dagushe yan siyasar da suke tare da su yau da gobe ta wajen hana su dama ta yin takara da wakilci, ta yadda suke bawa irin wadannan bakin wannan damar, akawai misalai masu dama daga karamar hukumar Kiri-Kasamma zuwa gwaram da ga Babura zuwa Kiyawa.

JIHAR ZAMFARA: Ka wa Allah ka sa baki ‘yan bindiga su dawo mana da ‘yan uwan mu da suka sace – Mutanen garin N

A yanzu ma da aka soma buga gangar zaben 2023, mun wayi gari da gannin irin wadannan bakin na tururuwar shigowa, wasu solar shigowa da kungiyoyin su ko gidauniyoyin su don tallafawa mutane, wasu solar yi gyaran ido a wurare daban daban, musamman ma a wurin da ake neman bukata, kai kace babu makafi da Nijeriya sai a Jigawa, wasu solar dan yi rabo na kudi da kayan masarufi da sunan tallafawa, wasu kuma solar shiga kafafen watsa labarai nada dana zamani ta hanyoyin dillalansu, suna suna tunawa mutane matsayin kakannun su da iyayen su a garuruwan su dama Jigawa. Sannan kuma allunan hutunan su a manyan biranen mu, don muzabe su.

Koma menene lokaci yayi da za mu fuskanci matsalolin da ke damun jahar mu ta wajen neman jajirtattu masu kishin mu domin yi mana jagoranci, mu yarda muna da matsala wajen ci gaban ilimi, lafiya rashin sana’a ga matasan mu, talauchi da ya addabi al’umomin mu musamman ma na karkara.

Kuma kawai wadanda suka son matsalolin mu ne, kawai za su iya fidda mu a cikin wannan yanayin, su ka dai ne za su iya jagoranta da nusar da matasan mu masu tasowa don zama shugabannin mu na gobe. Amma bako mai zuwa yatafi, kawai ya kanyi siyasa ne don kashin kansa da gina kansa da iyalensa. Wannan ya sanya har yanzu wakilcin mu musamman a majalissar Abuja ya kasa yin ingancin da zai taimakawa jahar mu. Wakilcin mu a majalissar jaha ma ya zama tamkar dandalin shan shakatawa a kasa haifar da dimokadiyya mai yanci.

Duk da ya zama dole mu kaunacin Yan uwan mu a ko ina suke, kuma mu bawa kowa damar bada gudunmawarsa wajen gina Jaharmu dama damar yancin kowa a matsayin na da Jaharmu, amma sai anyi takatsantsan.

alhajilallah@gmail.com

About NgArewa 2725 Articles
Am the pioneer of this web. Am smart, vibrant, and I love to keep the readers informed, and Blogging is my profession and wining is my satisfaction.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*