JIGAWA: Rundunar ‘yan sanda ta saurari kararrakin fyade 35 a cikin watanni hudu

JIGAWA: Rundunar 'yan sanda ta saurari kararrakin fyade 35 a cikin watanni hudu

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta bayyana cewa ta saurari kararrakin fyade 35 a cikin watanni hudu a jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Usman Gomna, ya sanar da haka wa manema labarai ranar Laraba a garin Dutse.

TSADAR RAYUWA: Tsawon watanni 11 farashin kayan abinci ya na hauhawa bai sauka ba – FAO

Gonna ya ce rundunar ta saurari kararrakin fyade fiye da sauran laifuffuka kamar su garkuwa da mutane da kai wa mutane hari.

” A cikin watanni hudu da suka gabata jihar ta samu raguwar wadanda aka yi garkuwa da su zuwa mutum 10 a cikin watanni hudu.

Gomna ya yi kira ga iyaye da su rika sanya wa ‘ya’yansu ido da kula da zirga-zirgan su, musamman yara kanana da ake dora musu talla suna gararamba a tituna suna talla.

Subhannallah Kalli Abin Bakin Ciki Yanzu Ma’aurata Abinda Suka Komayi Kafin Aure Suna Fakewa Da Wani Wa’azee

” A Mafi yawan lokutta an fi yi wa yara kanana saboda gararamba da suke yi ba tare da kulan Iyayen su ba.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya gwamnatin jihar ta kafa dokar yanke wa masu fyade a jihar hukuncin kisa.

Dokar ya kuma ce za a biya wadanda aka yi wa fyaden naira 500,000.

About Daniel olakunle 97 Articles
Am the pioneer of this web. Am smart, vibrant, and I love to keep the readers informed, and Blogging is my profession and wining is my satisfaction.

Be the first to comment

We Love Comments