INDO A BIRNI 2020 – Complete Hausa Novel

[12/31/2019, 11:20 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*IཽNཽDཽOཽ Aཽ BཽIཽRཽNཽIཽ*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*Na*

*Rasheedat Usman*

*(Ummu Nasmah)*

*(MAKAMAR KAINUWA)*👸🏻

📱

*08147537180*

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*

*Nasmah ko Nasirah*

*Sara da Sassaka*

(Baya hana gamji)

Toho

*1 / 1 / 2020*

Tsarabar sabuwar shekara domin ku masoyana.

*Deducated to*

*Aunty Fauza yar Amana*

Uwa mabada mama k’aunar ki dabanne gare ni, domin ke d’in shugaba ce, dake Adalci ga duk na k’asa dake, Allah ya barmu tare Aunty nah.

*بسم الله الرحمن الرحيم*

____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

Alhamdulillahi Ala kulli Halin dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah madaukakin Sarki, salati da d’aukaka da Aminci su tabbata ga cikamakin Annabawa Annabin k’arshe muhammad S’A’W da iyalan gidan sa da sahabban sa har izuwa Ranar Sakamako.

Ina godiya ga Allah daya sake dawo dani lfy, domin sake nishad’antar daku, ina rok’on Allah da yasa yanda na fara lfy ya bani ikon gamawa lfy, Allah ya bamu ikon Amfana da Abunda ke ciki. Ameen 🙏🏻

INDO A BIRNI 2020 - Complete Hausa Novel

*P* 1️⃣ ➡️ 2️⃣

Yara biyu na hango suna cin Uban gudu, yayin da wacce ke gaban take gudun ceton Rai, sosai take gudun Saboda kar wacce ke bin bayan nata ta kamo ta, wani gida naga yarinyar ta fad’a, binta cikin gidan itama yarinyar dake biye da itan tayi, da Gudu ta fad’a wani madaidaicin d’aki, cikin haki.

d’akin da yarinyar ta shiga, itama wacce ta biyo tan take k’ok’arin shiga.

Cikin Sauri wata matashiyar mata ta tare ta tare da cewa.

” Lafiya *INDO* kuke wannan Uban gudu, sannan kuma zaki bita har d’aki, aiko mutuwa ma tana kunyar Idon Uwar d’a, meye *Zainabun* ta Miki?

kika biyo ta har gidan ubanta ba ko kunya.

Huci wacce aka kira da *INDO* take Cikin masifa da bala’i take cewa.

” Sai mutuwa taji kunyar Idon ki, ni kuma *INDO banji taki ba, wlh yau Babu mai hanani cin Uban Zainabu cikin gidan nan, gobe koda kud’i aka Had’a ki baxaki k’ara nema na da tsokana ba, cemin fah tayi *INDO BALA’I* a gidan uban waye aka yanka min suna da *INDO BALA’I* Kinga *Goggo Hali* ki kauce ki bani hanya, kar nayi gefe dake kiga rashin kunya ta, dan wallahi, na ture ki na shige cikin d’akin nan baxai bani tsoro ba, ehe sai dai duk abunda zai faru ya faru, ta k’arasa maganar tana murgud’a baki.

Gam sukaji An rufe k’ofar d’akin tare da dannawa k’ofar sakata, daga rufen zainabu tace

” Baxan fiton ba, kuma na fad’a *INDO BALA’I* ko k’arya nayi ke ba masifaffiyar bace.

Matsawa wacce ta kira da *Goggo Hali* tayi tare da cewa to Kinga ma ta rufe d’akin sai dai idan ni zaki Kama ki daka, tunda ke baki da mutunci, kowa ya miki shaidar tsiya a cikin garin nan.

Cewa *INDO* tayi

” Idan anga dama Amin shaidar Abunda yafi Rashin mutunci ma, kuma wlh yau sai kinga yanda ake tsiya a cikin gidan nan, badai y’ar ki ta rufe d’aki ba, d’aga murya *INDO tayi, tace zainabu kina jina ai idan ba tsoro ba ki fito, mana shegiya y’ar matsorata, kuma wallahi Yau saina huce haushi na akan *UWARKI*.

Juyawa *INDO tayi, karaf kuwa sai idon ta yayi toxali da Randar k’asar Goggo Hali, Wacce take cike fal da Ruwa, Da Gudu tayi madafin Goggo Hali ta d’auko tab’aryar ta, Randar k’asar INDO* ta nufa da Gudu tare da buga tab’aryar akan Randar, fashewa Randar tayi, take kuwa Ruwan ya zube kasa, bokiti na k’arfe dake ajiye gefen Randar k’asar *INDO* ta raruma tare da shek’awa a d’akin mahaifin Zainabu, tsayawa Goggo Hali tayi tana kallon ikon Allah a gun *INDO* domin kuwa Idon ne kawai tsakanin ta da ita, tasan Idan tayi gangancin zuwa ta tare *INDO* to Babu shakka zata iya sauk’e mata tab’aryar a kanta ba damuwar ta bane, domin kuwa tasan Halin INDO tsaf babu wanda ta gyale kaf fad’in kauyen.

Cikin Huci INDO tace.

” Kuma na watsa Ruwan a d’akin Malam Hamxa idan ya dawo shima yasan cewa y’ar sa ta tab’o *INDO* yau,

Bata jira mai Goggo Hali zata ce ba tayi ficewar ta tana rera wak’a.

” Ikon Allah cewar Goggo Hali, yarinya ta Addabi gari, kowa yake Allah wadarai da Halin ki, Yanxu fah ki duba kiga b’arnan da yarinyar tamin, Amma dai wallahi Albasa batayi Halin Ruwa ba dan dai iyayen ki kam, mutanen kirki ne, Su kuma tasu jarabawar kenan, na Samun fitinanniyar yarinya, to Allah dai ya shirye ta.

Jin motsin mutum a bayan ta ne yasa Goggo Hali juyawa, zainabu ta gani tsaye tana sauk’e Ajiyar zuciya, ai kuwa nufar ta Goggo Hali tayi, tare da sauk’e mata rankwashi a kanta, tace.

” Yanxu ke zainabu ki Rasa wa zaki tsokana sai *INDO*, sai kace wacce baki san Halin ta ba, to maxa shiga d’aki ki d’auko min mayafi na, naje wajen Uwar ta wlh sai sun biyani Randa ta, dan baxan yi Asara ba wlh.

D’akin Zainabu ta nufa tana cewa.

” Kije ki wlh Goggo a biyaki Randar ki, tunda y’ar su bata da mutunci.

Ita kuwa INDO fitar ta daga gidan su zainabu, hanyar gidan su ta nufa, tun daga nesa ta hango motar sa, cikin murna da zuwan sa, garin nasu yasa *INDO* kwasa a guje, cikin zumud’i, ta nufi motar, kasancewar Gudu baya bawa *INDO* wahala, kullum a cikin sa, take sam bata da nutsuwa, k’azanta kuma wajen *INDO* subhanallah ba’a magana, domin kuwa k’azama ce ta ajin farko, duk inda ake neman k’azama, to idan aka Samu indo ayi fatiha a tashi, domin kuwa kaf fad’in K’auyen Babu wanda yakai *INDO* k’azanta.

Wannan kenan.

A nutse ya fito daga cikin motar, tare da tsayawa jikin motar yana duba yaran da zasu shigar masa da Kaya cikin gidan, tsohuwa mai ran k’arfe *HAJIYA INNAH* da Gudu INDO ta k’araso wajen nasa tare da yin turus da k’afar ta cikin bak’ar kasa mai k’urar dake shinfid’e a wajen, take kuwa k’asar ta bulewa wannan bawan Allah k’afar sa.

Da sauri ya daga kansa ya dubi *INDO* cikin takaici kuma cikin tsawa yace.

” Wacce irin mahaukaciya ce ke, ki duba kiga yanda Kika bule ni da k’asa, wawiya marar Hankali, Zaki kauce min da gani ko sai na makeki, Useless kawai.

Tura bakin ta INDO tayi, tace

” Wlh yau Kam baxan bar nan ba sai kace kana Sona, shikenan kullum sai ni kad’ai zanta sonka, kai baxaka soni ba, wlh yau sai kace kana Sona, ko kuma kamin Irin Abunda nake gani y’an India suna yiwa y’an matan su, a tibin *Hajiya Innah*, Bari ma na tuno sunan Abun 🤔

Yawwa na tuno kuss, suke cewa, sai kamin sannan zan tafi, turo masa bakinta tayi, tace gashi kamin, kaji mustapha na.

Zaro Idon sa, mustapha Yayi tare da saurin kawar da kansa gefe, jin bugun warin bakin INDO ya bigi hancin sa, wani Irin hucin wari yaji mai tayar da zuciya, cikin k’yank’yamin ta yake cewa.

” Allah ya sauwak’a naso k’azama irin ki, k’azamar k’auye, waima tukunna uban waye zai miki kiss, da wad’annan yellown hak’waren naki, b’ace min da gani kafin na targad’a ki, mahaukaciya kawai, marar lissafi, Amma dai wlh Allah ya isa tsakanina dake, ki rasa waye zakice kina so saini, to wlh Allah ya isa kin cuceni.

Murgud’a masa Baki tayi tace.

” Niba mahaukaciya bace wlh, kuma sai kamin kuss d’in nan, rarumo rigarsa tayi, ta duk’unk’une a ciki.

kasancewar babbar riga yasa, sai buga k’afa take, tana ihu tana cewa.

” *Wayyo Allah na shiga uku wayyo jama’a kuzo ku tayani rok’ar ya mustapha ya min kuss wayyo Allah Jama’a kuxo ni kad’ai nake sonsa shi baya Sona.*

Rasa Yaya mustapha zaiyi da INDO yayi, gashi kuma yana hango wasu dattawa biyu suna, tahowa, ta inda suke,

“Innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un Allahumma ajirni fil musibati, nidai wannan yarinyar ta zamo min masifa wlh, Duk Randa zanzo k’auyen nan, da tsinkewar zuciya nake Zuwa, tunda nasan zan had’u da Bala’i.

da k’arfi mustapha yasa Hanun sa cikin kyamar INDO ya b’anb’aro ta da kyar, tare da hankad’a ta, gefe.

fad’uwa tayi tare da bige kanta jikin bango, wani Irin zafi taji a kanta, Amma duk da haka Bakin *INDO* bai mutu ba, cikin Rashin Kunya, ta taso kamar wacce zata Doki Mustapha, tace.

” Ka ture Allah ya Isa wlh, mungun Azzalumi, kuma wlh Bashi ka d’auka, sai na Rama wlh.

Tana gama fad’in haka ta juya ba tare da ta k’ara Kallon mustapha ba.

Tsuka mustapha yaja, tare da tab’e bakin sa, yace.

” Wawiya kawai marar Hankali da nutsuwa, ai ko d’aura min ke Akayi a kaina, saina sinke ki da k’arfin tsiya, nayi wurgi dake gefe, *K’AZAMAR K’AUYE* kawai.

Yara biyu ya hango, Kira ya k’wala musu, bayan sunxo ne, ya umurce su, da su kwashi kayan sukai masa gidan *Hajiya Innah.*

Tsayawa yayi har suka gama shigar da kayan sannan yasawa motar sa security, yayi gidan, *Hajiya Innah*.

Sauk’ar Ruwa a jikin sa mustapha yaji’ wani Irin shid’ewa Yayi, a gigice ya bud’e Idon sa, karaf suka had’a Ido da *INDO* tsaye da bokitin Ruwa a Hanun ta wanda ta juyewa Mustapha a jikin sa, takaici da haushin ta, shine ya hanasa magana, saima wani mungun kallon daya tsaya yana aika Mata.

Juyawa INDO tayi a guje tana dariyar k’eta tace.

” Na Rama tureni da kayi, daman ai na fad’a maka Bashi kaci, kuma na Rama Yanxu Babu bashi tsakanin mu, masoyina mustapha, *INA SONKA ARADU* tana gudun ne take wannan zancen.

Kad’a kansa mustapha yayi, cikin Jin haushin *INDO* da mamakin ta, yake cewa.

” Anya kuwa wannan yarinyar bata da Aljanu, don ba k’alau take ba, Kam, wai *masoyina mustapha* ko a gidan uban waye na zama masoyin nata, sai Allah, shigewa Yayi cikin gidan, tare da Sallama.

Tana Zaune gefe tana b’arar gyad’a ga kuma tarin kayan da mustapha yasa aka shigo masa dashi, a gefen ta, d’aga kanta tayi tare da cewa

” Lale maraba’ da mutanen Binni, sai Kuma tayi shuru tare da tsurawa jik’ak’k’un kayan jikin sa Ido, cikin mamakin meya jik’a masa Kaya, kasa hakuri *Hajiya Innah* tayi tace.

” Muhammadu dake haka take kiran sa dashi, menene ya jik’a maka kayan ka, kodai ka biya Rafi ne kayi wanka?

Tambayar *Hajiya Innah* ta k’arshe itace ta bawa mustapha Haushi, *wai ko ka biya Rafi ne kayi wanka* sai kace ta tab’a ganin nayi hanyar rafin nasu, cikin gatse ya mayar mata amsa da cewa.

” *A’a ba Rafi Naje ba, tekun Maliya na biya nayi wankan na dawo*.

” To Uban y’an bak’ar magana da zafin Zuciya, Idan da Akwai inda yafi tekun Maliya ruwa ma kaje kayi wankan, aikin banxa kawai daga tambaya sai cibi ya zama k’ari.

Tabe bakin sa yayi tare da d’aga kafad’ar sa, Alamun wannan damuwar kine, shigewar sa Yayi d’akin daya kasance nashi idan yaxo k’auyen.

D’akin fess dashi gwanin ban sha’awa komai a tsare kamar d’akin Mace, kan dressing merron shi kuma kayan shafe shafe ne kalakala masu tsadar gaske na maxa.

Wanka ya shige yayi a ban d’akin Hajiya Inna dake tsakar gidan ta.

Itako Hajiya Inna sai mita take ita d’aya.

” Yaro ace sai shegen Bak’ar Zuciya gare sa, ga rashin hak’urin tsiya, shiyasa nake Allah Allah *Habeebu* ya dawo ya dinga ziyarta ta, sai munfi shiri dashi, fiye da wannan mai Bak’in Ran tsiyar, dan *Habeebu* yaron kirki ne d’an Albarka, na Rasa wani Irin Aiki yake a k’asar wajen Nan, da yak’i dawowa k’asar sa ta haihuwa.

Mustapha daya fito daga ban d’aki ne, yana jin duk mitar da take yi ne, yake ce Mata.

” Kamata yayi ki bisa k’asar wajen ai, ki dawo shi wannan K’auyen da Zama K’arshen K’auna, hakan ne zai tabbatar da kina sonshi, Nima banda k’addara da biyayyar iyaye mai zai kawo ni wannan, Bak’in k’auyen harma wannan jarababbiyar yarinyar ta Addabe ni.

Kuma wlh Hajiya koda wasa naga k’afar yarinyar nan *INDON* cikin gidan nan sai na b’allata.

” Kan Uba cewar Hajiya Innah, to a Bak’in k’auyen aka binne cibiyar Uban ka, kuma baka da wajen daya fi wannan K’auyen tunda shine Asalin Ubanka Haruna.

da kake maganar cewa *INDO* karta shigo cikin gidan Nan, gidan kane koko akwai kud’in ka cikin ginin gidan, to ko ubanka Haruna bai isa ya hana *AISHATU* shigowa cikin gidan Nan ba, bare kuma kai *Karan kad’a Miya* , sai dai Kuma Kai kabar min gidana, badai *INDO* ba Zan Kuma ga Uban da zai hana ta shigowa.

Hararar Hajiya Innah mustapha Yayi, tare da shigewa cikin d’akin nasa ba tare daya k’ara tankawa Hajiya Innah ba.

Itama D’akin ta ta shige tana ci gaba da zagin mustapha, wanda shine gaisuwar da sukayi daga isowar sa. 😄

” Gafaran kudai masu gida cewar Goggo Hali, dake tsaye k’ofar d’akin, Mama mahaifiyar *INDO*.

Fitowa mama tayi, tare da cewa,

“Lale marhaban da Halima, kece yau tafe a gidan nan.

” Eh Nice cewar Goggo Hali, na sameki lfy.

” Lafiya lau Halima ki zauna mana, mu gaisa, naga kin tsaya bayan ga shimfid’ar taburma.

Cewar Umma.

Kad’a kanta Goggo Hali tayi tare da cewa.

” Ba zama bane ya kawo ni Mairo, Y’arki ce tayi min D’ibar Albarka, yau a cikin gidana tare da Kuma b’arna, shine naxo a biya Ni, dan baxan iya Asara ba wlh, tunda ku y’arku tafi k’arfin ku.

Mama taji Zafin maganganun da Goggo Hali ta mata, sai dai Kuma ba laifin ta bane *d’an kuka ne mai jawa uwarsa jifa* da Indo mutum ce mai jin magana da tuni ta daina jawo musu zagi a gari, amma kunnen k’ashi gare ta, sai dai kullum tana mata Addu’a tare da fatan shiriya, ta kintsu ta dawo y’a ta gari wacce kowa zaiyi Alfahari da ita, kuma tasan Allah maji rok’on bawan sa ne, yana jinta yana ganin ta kuma zai Amshi Addu’ar ta.

Bata tsaya tambayan Goggo Hali me Indo tayi mata ba gudun kar taji abunda zai b’ata mata rai, yasa ta cewa goggo hali.

” Kiyi Hkr Halima, *d’an yaune ka haifesa baka haifi halin sa ba* Nawa ne kud’in b’arnan da INDO tayi Miki.

” Randata ta fasa min, sabuwa gal Ranar da naje, garin Sauro na sayo ta, Naira D’ari Uku da hamsin 350.

Kunce bakin zanin ta mama tayi, ta Ciro gudan d’ari biyar ta mik’awa Goggo Hali, tace.

” Gashi Idan kin sanja sai ki Aiko min da d’ari da hamsin.

Karb’a Goggo Hali tayi Babu ko kunya ta fice tare da cewa zan Aiko miki sanjin ki anjuma.

Shuru mama tayi tana tunanin Halin, *INDO* ita tsoron ta ma kar wani ya mata mungun Baki ya kamata, domin kuwa ita kanta Da ta haifi INDO hakuri take da ita, bare Kuma Al’ummar gari.

Tana cikin tunanin ne INDO ta shigo gidan da Gudu tana dariya, tare da zama kusa da Mama tace.

” Mama ina Abinci na, yunwa nake ji wlh, d’azun nan naci Abinci Amma wlh Yanxu ji nake kamar na kwana biyu banci Abinci ba.

Kallon ta Mama tayi, tare da cewa.

” Za kuma yau ki kwana baki ci Abinci ba, domin kuwa kud’in cefenen da Malam ya bani d’ari biyar, na d’auka na biya, Halima kud’in Randar ta, da kika fasa, kinga yau sai mu wuni da *Azumin Dole* d’ari da hamsin ta saura, kuma k’annen ki, zan sayawa garin rogo da suger su Sha.

” Kutumar Uban nan, Goggo Halin ne taxo tace na mata b’arna, ita bata gaya Miki Abunda Zainabu tamin ba.

To wlh Mama sai Goggo Hali ta gwammace Bata karb’i kud’in nan ba, dan wlh sai nayiwa Zainabu mungun dukan da sai sun kashe DUBU a kantin Hassan mai magani.

Gwanb’are bakin ta Mama tayi tare da cewa.

” Ke dai INDO bakya nemawa Rayuwar ki Albarka wlh, yanxu ma sake komawa zakiyi gidan nasu, ki jawo min wani maganar ne, to wlh ko a hanya kika had’u da Zainabu, karki kuskura kisa hanu a jikin ta, Idan Kuma kika sa Hanu jikin ta, to kuwa ranki zai b’aci a wajena shashashar banxa marar kunya.

Tashi INDO tayi tana tura baki tare da maganganu k’asa k’asa, wanda bakin ta ne kawai ke motsi, Sanda taxo daf da k’ofar barin cikin gidan nasu tace.

” Wallahi Mama Babu mai hanani cin Uban Zainabu yau, sai dai Idan bamu had’u ba, gara ma kiyi hakuri kawai.

Tashi Mama tayi na dawo ki samu waje ki zauna INDO yau wuni zakiyi cikin gidan nan tunda Allah ya yoki mai kunnen k’ashi.

INDO bata tsaya sauraron Mama ba ta fice a d’ari tana dariya.

Gidan su k’awar ta Hansai, shigar ta Zauren gidan su hansai ta jiyo muryar Baffah mahaifin Hansai, tsayawa INDO tayi tare da dafe k’irji tace

” Alhamdulillah Allah yaso ban shiga ba, Ashe wannan masifaffun tsohon yana nan.

Kasancewar Baffah mahaifin Hansai ya hanata kula Indo acewar sa zata Lalata masa tarbiyar yarinya.

Juyawa INDO tayi tare da zagawa, ta katangar Ban d’akin su Hansai da nufin ta dirk’a ta ban d’akin yanda zata samu shigewa d’akin Innar su Hansai ba tare da Baffah ya ganta ba.

Kama katangar INDO tayi, kasancewar katangar guntuwa ce, ta dira cikin ban d’akin.

Lami kishiyar mahaifiyar Hansai dake tsugunne Kan shadda tana bayan gari, taji dirowar mutum cikin ban d’akin, cikin tsoro ta fara bin k’afar INDO da kallo, ba tare da ta d’aga kai ta kalli fiskar taba, ihu Lami tasa cikin tsoro, tana cewa.

” Na shiga Uku ni Lami, dan Allah kuyi hkr wlh mantawa nayi, na shigo ba tare da nayi addu’a ba, kuyi dan Allah *ku kuke ganin mu, ba muke ganin kuba ba* wayyo Allah ku kawo min agaji yau Kuma Nayi gamo.

Yayin da fitsari ke bin k’afofin Lami.

Dariya INDO ta shek’e dashi har hawaye na fita cikin idanun ta, ganin yanda Lami ta gigice ta fice hayyacin ta har tana fitsari a jikin ta, yayin da Idon ta, ke rufe gam tak’i bude su.

D’alewa saman katangar INDO tayi ta zauna tana cin dariyar ta, tare da nuna Lami da yatsa.

Nan zan dakata sai naji yanda kuka karb’i book d’in kafin naci gaba da typing.

*Yawan sharhi yawan typing.*

*Share*

*And*

*Comment*

*Alk’alamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah)*

[1/2, 8:05 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽* *A͓̽* *B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*N̸͟͞A̸͟͞*

*R̸͟͞A̸͟͞S̸͟͞H̸͟͞E̸͟͞E̸͟͞D̸͟͞A̸͟͞T̸͟͞* *U̸͟͞S̸͟͞M̸͟͞A̸͟͞N̸͟͞*

*(U̸͟͞m̸͟͞m̸͟͞u̸͟͞ N̸͟͞a̸͟͞s̸͟͞m̸͟͞a̸͟͞h̸͟͞)*

*( ოႩlႩႪႩR kႩiႶႮwႩ)*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*

*Nasmah ko Nasirah*

*Sara da Sassaka*

*(Baya hana gamji)*

*Toho*

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza yar Amana*

Uwa mabada mama k’aunar ki dabanne gare Ni, domin ke d’in shugaba ce dake Adalci ga duk na k’asa dake, Allah ya barmu tare Aunty nah.

*بسم الله الرحمن الرحيم*

____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

*P* 3️⃣ ➡️ 4️⃣

Ilu d’an Lami ne da Baffah sai Innar Hansai sukayo ban d’akin da gudu jin ihun Lami, turus suka tsaya sakamakon ganin *INDO* zaune saman katanga sai washe yellown Hak’waren ta take, tana cin dariya, Salallami Innar Hansai ta d’auka cikin Al’ajabin meya kawo INDO ban d’akin su.

” Ke INDO meya kawo ki nan, yau kuma tsiyar taki cikin gida na kika kawo sa, cewar Baffah.

Jin an Kira INDO ne yasa Lami saurin bud’e idon ta, fes kuwa ta sauk’e su kan INDO dake ta famar dariya ta maida su mahaukata, Cikin Haushin INDO Lami tace.

” Amma dai Allah ya isa tsakanina da ke INDO, tsabar rashin mutunci duk k’ofar gidan nan bai isheki sai kin diro ta ban d’aki, baki sani ba koda mutum koko Babu, ki shigo ki sami mutum a Halin da bai dace ki samesa ba.

Dariya INDO ta sake shek’ewa dashi, cikin dariyar take cewa.

” Kamar dai yanda naxo na same ki kina *Kashi* kai Amma Lami Anyi matsoraciya, duba fah kiga yanda kika jik’e zanin ki da fitsari, sai kuwa ta k’ara shek’ewa da dariyar, *Aradun Allah Lami kashin ki wari gare sa, ni kin gama ma cika min ciki da warin kashin ki*.

Ilu ne zuciyar sa taxo kusa, cikin haushi da hasala yayi kan INDO da gudu, da niyar ya mata dukan da sai anxo an kwashe ta.

Ganin ilu yana nufa ta yasa INDO dirawa daga katangar, ta kwasa a guji, shima ilu rufawa INDO baya yayi, da Gudu,

Babu inda Indo ta nufa sai gidan, *Hajiya Innah* tasan a nan kawai zata tsira daga Hanun Ilu.

Hajiya Innah dake Zaune gindin murhu tana ixa wuta ne taga shigowar INDO da gudu a birkice *Hajiya Innah* itama ta tashi tabi bayan indo da gudu.

Gudu suke sanda suka shiga cikin d’akin Innah, sannan suka tsaya suna haki, Hajiya Innah ce tace

” Ke indo gudun me kike haka, meya faru macijin nan ne, yauma ya k’ara biyo ki.

Dariya indo ta shek’e dashi tana nuna Innah da Hanu, tace.

” Amma dai Inna ke ba k’aramar matsoraciya bace wlh, daga gani na Ina gudu sai ki biyo baya na.

K’ara shek’ewa tayi da dariyar tana nuna Innah yanda taga Innah tayi tsamo a gefe, kamar wanda za’a ce fit ta D’iba da Gudu.

Yanxu ke Innah Idan macijin ne, sai na tsaya harki iso ban rufe ƙofa ba, ai wlh kafin ki ƙaraso na juma da rufe ƙofar nan sai dai Kuma kisan tayi.

” Amma ke dai INDO akwai ja’irar yarinya, yanxu dan baki da mutunci, sai ki rufe ƙofar ki barni a waje, idan ma kasheni macijin zaiyi ke baki damu ba Koh.

” *To me zai dameni Innah, dan kin mutu ai ba Abun damuwa bane, tunda kin mori duniyar, wlh Innah na rufe ƙofar nan baki iso ba shi yafi sauki a wajena.*

Haɗa fiska Hajiya Innah tayi kasancewar ta tsani taji ana kira mata mutuwa muraran, tace.

” *Bari muga idan na mutu a ina zaki dinga samun taliyar turawa mai harɗe ki dinga ci, tunda gani na ne baƙya ƙaunar ganin ina numfashi*.

” Ehhh fah haka ne, kuma Innah, wlh Idan kin mutu Babu inda zan samu taliyar turawan Nan, *to Gaskiya Allah ya Raya min ke Hajiya Innah kodan karna Rasa taliyar turawa,.*

Washe Baki Innah tayi tace.

” Ameen ƴar Albarka shiyasa nake sonki, faɗan mu baya nisa, saboda kin iya farar Addu’a, yanxu……..

Shigowar Ilu yana Banbami ne ya hana Hajiya Innah ƙarasa maganar ta.

” *Lafiya mlm ƙaton gardi da kai zaka shigo min cikin gida, ko sallama Babu, kamar wanda ka shigo gidan Ubanka.*

Nuna INDO Ilu Yayi, yace.

” Ga Wacce na biyo, ki fito INDO wlh idan kika yadda na shigo ɗakin Nan, sai na karya ki.

” *To Uban ta, Bismillah shiga ɗakin tunda ɗakin Ubanka ne, cewar Hajiya Innah, har wani cewa kake zaka ƙarya ta, to idan ka fasa ƙarya ta ka raina Uwar da ta haife ka.*

Kallon Hajiya Innah ilu yake cikin mamakin ta, yace.

” Hajiya kinsan Abunda ta mana kuwa, kike ƙoƙarin shigar mata faɗa.

” *Ban sani ba kuma bana son Sani, dake ku mutanen garin nan, manyan ku da yaran ku kun tsani INDO, ko wani laifi ku ɗauko, ku ɗaura Mata, to wlh ta Allah ba taku ba, aniyar ku ta biku, har gadan Baccin ku wlh INDO tafi ƙarfin ku*

Hayaniyar da mustapha yaji ne yasa shi fitowa daga ɗakin nasa, yayo wajen Innah, turus ya tsaya yana kallon Innah yanda ta zage, sai zagin Bawan Allah take, ƙarasawa mustapha yayi tare da dafa kafaɗar Ilu yace.

” Abokina lafiya me yake faruwa.

Juyowa ilu yayi, ya fara bawai, mustapha labarin abunda INDO tayiwa mahaifiyar sa, yace wlh da gaske nake, har banɗaki ta faɗa mata.

Shi mustapha baima lura da INDO a wajen ba, sai dai yaji akanta ake Case ɗin tukunna, A zuciyar sa yake cewa, ” wannan yarinyar itace Iblis ɗin wannan ƙauye, yanxu tsabar shaharan yarinyar nan, a fanni Rashin hankali har ki dirƙawa mutane katangar tollet ɗinsu, cewa Ilu yayi.

” Shiga ka jawo ta kaci Uban ta, wannan ɗan iskan bakin nata wanda kullum yake cikin ƙazanta, ka tabbatar kayi rugurugu dashi.

Daga cikin ɗakin Indo tace,

” Nidai wlh ba Uba na ba ehe.

” Zaro Ido mustapha Yayi, yace.

” Sai Uban waye kenan.?

Babu tsoro fiskar INDO ta mayar masa da amsa.

” Sai Uban Wanda ya tsargu.

Kallon ilu yayi yace.

” Ka shiga ka sanja mata kamanni nace maka.

Tare ƙofar Innah tayi tace,

” Naga shegen da zai wuce cikin ɗakin nan, munafiki, idan banda munafurci, meya fito da kai daga ɗakin ka, sai ya fasa mata bakin mu gani.

Jawo Innah mustapha yayi😄 suka hau kokuwa, yayin da ya riƙe mata Hannayen ta gam yana cewa, Ilu ya shiga.

Ganin da INDO tayi da gaske, Ilu zai damƙe ta, yasa ta daka tsalle sai ƙarƙashin gadon Innah, can ƙarshe.

Neman Indo Ilu yayi sama da ƙasa ya Rasa, ko motsin ta, baiji ba cikin ɗakin, fitowa Yayi cikin Huci yace, ta fah ɓace babu ita cikin ɗakin nan.

” Babu ita kamar Yaya cewar Mustapha, Yanxu na hango yarinya, kace bata nan ta ɓace sai kace Aljana.

” Wlh Babu ita, kaxo ka duba ka gani.

Sake Innah mustapha yayi, yasa kansa Cikin ɗakin, bai ganta, dube dube ya hau yi Amma Babu INDO sama da ƙasa, ko a ransa bai kawo INDO zata shige ƙarƙashin gado ba.

” Haba ai daman *Biri yayi Kama da Mutum* yanda yarinyar nan, take dole tana Aiki da Aljanu ne, Idan ba Aljani ba waye zai ɓace ɓat lokaci ɗaya.

Kallon sa ya mayar kan Ilu yace kaje kayi hkr, kawai ka barta da Allah dan yarinyar nan tafi ƙarfin mutum sai dai Aljani.

Shigewa Ilu yayi yana cewa wlh ido na Idon INDO, sai na mata shegen Duka.

” Kama kashe ta idan kaga dama, cewar Hajiya Innah kuma zanje har wajen Ubanka naji idan shiya turo ka gidan nan kamin rashin mutunci.

Ficewa waje shima mustapha yayi ba tare daya kalli Hajiya Innah ba.

Ɗakin ta shiga, tace.

” To fito ja’ira marar Kunya nasan ai kina cikin ɗakin, ashe daman Bala’i kika nemo shiyasa kika shigo a guje, har nima kika Sani gudu, yau da sun kamaki sai dai wani bake ba wlh, daman haushin ki, suke ji.

Fitowa INDO tayi tana dariya, tace

” To ya suka iya dani Innah, ni ɗin tsayuwa zanyi su jibge ni, ni dai yanxu Innah ki bani taliyar turawan Nan, naje gida na tafasa, dan baxan tsaya gidan nan ba, ya mustapha yaxo ya ritsani.

” Ai kuwa kinga ɗauki wannan, kwalin ki kaiwa Uwar taki ta tafasa muku keda ƙannen ki.

Ɗauka Indo tayi tana cewa, shiyasa nake sonki Innah, kodan wannan taliyar, ficewa tayi tana waige waige kar Ilu ko mustapha su riƙota, cikin sa’a kuwa har ta shiga cikin gidan bata haɗu da suba.

Zaune mlm sa’idu mahaifin Hansai yake gaban mai gari, yayin daya kawo ƙarar INDO kan Abunda ta shiga cikin gidan sa ta masa.

Nisawa mai gari yayi tare da cewa.

” Ita Indon ce tayi wannan ɗanyen Aiki, umurtan Dogari yayi akan cewa yaje yaxo masa da Mlm Musa mahaifin INDO.

Da sauri dogari ya tafi aiken da mai gari ya masa.

Sallama Dogari ke kwalawa a ƙofar gidan su indo, Yayan Indo Tanimu shine ya fito, jin sallama da ake yi, Dogari ya gani tsaye.

” Lafiya kuwa Dogari, cewar Tanimu.

” Lafiya lau mlm Musa Nake nema, mai gari ke kiran sa, yanzu a fada.

” Me gari kuma, Allah dai yasa lfy.

” Koma menene idan yaxo yaji, ka shiga kamin Sallama dashi.

” Baya nan Amma bari naje kasuwar na kira sa, zaizo yanzu insha Allah.

” Shikenan bari na koma, ka tabbatar yaxo yanzu.

” Insha Allah zaizo.

Tanimu bai koma cikin gida ba, ya shige, kasuwa wajen, mlm Musa, yana zaune bakin shagon nasa na tireda, yana jin rediyo, yaga Tanimu ya masa Sallama.

Amsa Sallamar yayi yace.

” Tanimu kaine cikin shagon nawa, yaushe ka dawo daga wajen Raken naka.

” Yanzu na dawo Baba bamma daɗe da dawowa ba, naji sallamar dogari, shine yace min mai gari na son ganin ka yanzu.

Mlm Musa baiyi mamakin jin kiran mai gari ba, yasan *Tatsuniyar Gizo bata wuce ta Ƙoƙi* wannan kiran da mai gari ya masa bazai wuce wata maganar Indo ta jawo masa a gari ba, tashi yayi ya kulle shagon nasa ya cewa, Tanimu muje.

An taro fadar mai gari, ana jiran isowar mlm Musa, sai Kuma ga shi ya iso, zama yayi tare da gaishe da mai gari, sannan mai gari ya dubi, mlm Sa’idu yace

” Maimaita masa Abinda ke tafe dakai.

Duban mlm Musa, mlm Sa’idu yayi tare da fara jero masa tijarar da, Indo ta masa cikin gida.

Ya ƙarasa zancen da cewa, na gaji kawai mai gari ya min tsakani da Indo da Kuma ƴata, babu mu Babu ita, ko a hanya taga Hansai, karta ƙara koda kallon ta.

“Allah ya huci Zuciyar ka, mlm Sa’idu, duk Abinda kace Indo tayi banda musu ko ja akan haka, fiye da haka ma zata aikata, Kuma insha Allah daga yau na maka Alƙawarin cewa, Indo ko ƙofar gidan ka, bazata ƙara kallo ba, duban sa ya mayar kan mai gari, yace yallaɓoi dan Allah Ayi hkr insha Allah hakan bata ƙara kasancewa ba.

Nisawa mai gari yayi yace,

” To mlm Sa’idu kaji bayanin mlm Musa, nima ina ƙara baka hkr, tabbas kam yarinya bata kyauta ba, kayi hkr, gaba idan ta sake zamu ɗauki ƙwaƙwaran mataki a kanta.

” Shikenan mai gari, Nayi hkr, Allah ya yafe mana duka.

Godiya mlm Musa yayiwa mlm Sa’idu da mai gari, sannan yacewa Tanimu ya tashi su tafi.

Tanimu Allah Allah yake, ya isa gida ya samu Indo, wlh yau kam mai ƙwacen Indo a hanun sa Sai Allah.

Cikin Sa’a kuwa Tanimu suna shiga shiga cikin gidan itama Indo tana shigowa, da kwalin Indomie ɗinta a kayi, karɓar kwalin Tanimu yayi ya ajiye a gefe sannan yaja Indo har ɗakin da Mama ke kiwon tumaki, rufe ƙyauran Tanimu yayi, Mlm Musa na ganin haka, yayi murmurshi tare da shigewa cikin ɗakin sa, dan yasan yau Indo ta shiga Uku hanun Tanimu.

Kallon Tanimu Indo tayi tace.

” Me zamuyi Anan ɗin yaya, naga ka rufe ƙyaure, kayi sauri ni zanje na dafa taliya tace.

Tanimu bai tanka Indo ba, sai ma sunkuyawa da yayi ya ɗauki bulala, ya hau zabgawa Indo, ihu Indo take tana ƙoƙarin riƙe bulalar Amma Tanimu bai bari ta riƙe bulalar ba, sosai Tanimu yake dukan, Indo, ita kuwa sai cewa take.

” Allah ya isa zai kasheni mungu, azzalumi, wayyo Mama, yaya zaiyi kisan kai cikin gidan nan, ka sakeni shege mugun banxa.

A jiye bulalar Tanimu yayi ya daki bakin Indo da ƙarfi sanda ya kawo jini, take kuwa bakin ya kunbura suntum, sannan ya buɗe ƙyauren ya fice, yabar Indo tana birgima tare da ihu, Mama da Mlm Musa ya sanar da ita abunda ya faru, ko kollon inda Indo take Mama bata kalla ba saima, ɗage kwalin Indomie da tayi ta mayar gefe, tasan baxai wuce Hajiya innah bace ta bata taliyar.

Har dare Indo tana zaune ɗakin tumakin nan taƙi fitowa, zagi kuwa Babu irin wanda Tanimu baisha ba, Jauɗo kuwa ƙaninta daya leƙa da duwatsu ta jefe sa.

Babu wanda yace mata fito, kowa harkar gabansa yake, koda Mama ta gama abincin dare ma Indo ƙinci tayi, mama dai mayar da abincin ta tayi cikin madafi, cikin dare kuwa da yunwa ta Addabi Indo Babu wanda ya sani ta zaga ta ɗauki Abincin taci.

Washe gari da safe Mustapha ya fito cikin shirin shi na komawa cikin dutse dake Garin Jigawa, Hajiya Innah ya samu tana cin ɗumamen tuwon ta, zama yayi gefen ta, tare da Gaishe ta, Amsawa tare, dace.

” Muhammadu har ka fito baxaka bari kayi karin kumallo ba.

” A’a innah idan na koma gida na karya, kuɗi ya ciro dubu ashirin ya ajiyewa innah, tare da mata sallama.

” Allah ya kiyaye hanya ta masa ka gaishe da iyayen naka, habibu kam wannan karon baka haɗamu munyi magana ba, tare da basa su daddawa kuka harda kuɓewa bushashiya tace gashi ka kaiwa uwar taka sayi Amfani dashi.

Karɓa yayi yace innah kwana biyu wayar Habeeb idan na kira bata tafiya, ina ga babu network ne cikin garin naku.

” Shikenan to sai Allah ya ƙara dawo dakai ka haɗamu.

Har zauren gidan ta rakosa sannan ta koma.

Mustapha ya buɗe motar sa da niyar shiga kenan yaji Muryar Indo na cewa.

” Masoyina komawa zakayi kuma, ni dai wlh ban gaji da ganin kaba ka bari sai gobe ka koma, kafin nan zan maka kafi tsire sai ka kai tsaraba gidan ku.

Juyowa Mustapha yayi a fusace da niyar make Indo, sai kuma yayi tozali da bakin Indo dake kumbure sun tum harya sanja mata kammani, dariya ce ta kwacewa Mustapha yana nuna Indo, yace yau kuma waye ya iya jada Aljana.

Gaskiya ku ƙara yawan sharhi ko na ajiye Alƙalamina, domin bakwai sharhi mai tsawo.

*Share*

*And*

*Comments*

*Alƙalamin Rasheedat Usman*✍🏻

*(Ummu Nasmah)*

[1/3, 8:05 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*

*Nasmah ko Nasirah*

*Sara da Sassaka*

*D̸͟͞E̸͟͞D̸͟͞I̸͟͞C̸͟͞A̸͟͞T̸͟͞E̸͟͞D̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty Fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gare Ni, domin ke ɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake, Allah ya barmu tare Aunty nah.

*بسم الله الرحمن الرحيم*

____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

*P* 5️⃣ ➡️ 6️⃣

Taɓa bakin ta indo tayi tace.

” Oh wannan Azzalumin ne ya Tanimu, yamin haka da baki, Kuma wlh na rantse da Allah sai na bawa tumakin sa maganin ɓera sunci sun mutu, badai shi azzalumi ba.

Wlh saiya gwammace bai taɓa ni ba.

Zaro idon sa, Mustapha yayi, Yace.

” Ke mahaukaciya, ke yanzu idan aka barki sai ki kashe masa tumaki, dake kema tinkiyar ce, hankalin ku ɗaya da tumakin, amma dai Allah ya Kawo Miki shiriya, dan wlh iyayen ki suna fama da ɓakin cikin ki, sai dai Allah ya basu hkrn zama dake, iya gama faɗin haka ya buɗe motar sa da niyar shiga, indo tayi carap tace.

” Dan Allah ya Mustapha karka tafi wlh ban gaji da ganin ka ba.

Tsuka Mustapha yaja tare da shigewa motar sa, yaja da ƙarfi, duk ya bule Indo da ƙura, bin motar Indo tayi da gudu tana.

” Ya Mustapha ka tsaya dan Allah na manta bance maka, *kifiyar Sonka ta soke ni a ƙirji na, Wlh ina Sonka sosai har cikin ƙahon Zuciyata*.

Shi kam Mustapha baima san tana yiba, dan tuni yayi gaba Abinsa, juyawa Indo tayi Ranta a haɗe, cikin takaicin tafiyar Mustapha, gashi wannan zuwan da yayi basu wani haɗu sosai ba, dawa Allah zai haɗa Indo idan ba Zainabu ba, can ta hango Zainabu tsaye ita da, Hansai suna zance, lallaɓawa Indo tayi yanda Zainabu baxata ganta ba, bare ta gudu, ita ko Zainabu sam bata wani lura da Indo ba sai ji tayi an tsakomo ta.

Ware idonta Hansai tayi cikin jin tausayin Zainabu.

” Uban waye na kama dan kutumar ubanki, ƴar durun uwa, da kin zata kin tsokaneni a banxa ne, to wlh yau na lahira saiya fiki jin daɗi.

Ƙoƙarin kwacewa Zainabu take hanun Indo sai dai ina Indo tafi ƙarfin ta, dukan Zainabu Indo take tsakanin ta da Allah, yayin da ta wurgar ta kasa, ta ɗane ruwan cikin ta, sai dukan bakin ta take tana cewa.

” Dan ubanki akanki zan huce haushi na yau, gobe Uwar ki Hali zata ƙara zuwa gidan mu kai ƙarata, na kuma ƙara tareki naci ubanki, karku fasa karna fasa, muga nida ku waye zai gaji.

Sannan ta sauƙa da ruwan cikin Zainabu.

Harara ta zabgawa Hansai tace.

” Ke kuma matsa ki bani waje, kema kinyi Sa’a, Wlh da Mai Gari ya kama Baba na, da kema naci naki uban.

Ita dai Hansai bata kula Indo, ba har tayi tafiyar ta.

Hansai ce tace

” Ki tashi kiyi hkr, kema Zainabu meya kaiki tsokanar Indo, kinsan dai Indo tafi ƙarfin ki, maza ma yaya suka ƙare da ita bare kuma ke.

Kuka Zainabu tasa, cikin jin haushin dukan da Indo tayi mata,

Rabuwa sukayi da Hansai kowa ya kama hanyar gidan su.

Da kuka Zainabu ta ƙarasa wajen Goggo Hali.

” Lfy Zainabu meya same ki, zaki shigo min gida da kuka, cewar goggo Hali.

” Ba Inda bace, ta kama ni da duka, wai gobe ma ki ƙara kai ƙaranta gidan su, itama ta ƙara kamani da duka.

Sallallami Goggo Hali ta ɗauka, sannan tace.

” Kinga Zainabu ki haƙura ki bar Indo da Allah domin kuwa Indo shaiɗaniya ce, Babu mai iyawa da ita sai ALLAH.

Tura baki Zainabu tayi tace.

” To Allah ya isa na Wlh.

” Shikenan zai kuma isar Miki.

Misalin ƙarfe Uku na Rana Mustapha ya shigo cikin dutse, Shango Estate na gani Rubuce a mashigar Inda zai shigan, gidaje ne da yawa cikin Estate ɗin, wani gida mai shegen kyau naga Mustapha ya shiga, yara biyu ya samu a compaunt ɗin gidan suna ƙwallo, da gudu yaran suka taho wajen sa, suna Oyoyo yaya Mustapha, parking ɗinsa ya gyara, sannan ya fito yana dariya, ɗaya bayan ɗaya Mustapha ya ɗaga su yana cewa.

” Autan Momy, yau Babu islamiyya ne, na ganku a gida.

Sharif ne yace.

” Babu yaya, malamin namu baban sa ya mutu, wai sai anyi Uku mu dawo.

” Ayya Allah ya jiƙansa da rahama, ina Momy?

Ishaq ne yace,

” Tana ciki yaya, Aunty *RAUDA* ma taxo jiya take tambayan ka, Momy tace, ka tafi ƙauye wajen *Hajiya Innah*.

” Sannun ta da zuwa to,

Tare suka ƙarasa makeken falon, wanda ya tsaru da Adon pink da purple, falon yayi kyau sosai, idan ka ɗaga kanka sama kuma, tozali zakayi da wani ƙaton Elagement, Kama ce tsantsan tsakanin su kamar a raba ruwa biyu, haka suke, basu da wani banbanci, koda ta yatsa ne, gefe ɗaya anyi Rubutu da manyan baƙi, *MUHAMMAD MUSTAPHA AND MUHAMMAD HABEEB*, sai kuma gefe duka Family ɗin gidan, wata kyakkyawar mata na gani fara sol daga ganin ta kasan bafulatanar Asali ce, sai wani Dattijo shima kyakkyawa wankan tarwaɗa, sai kuma wata yarinya ƙarama, da kuma ƴan biyun ta Hudu Habeeb Mustapha sai Sharif da Ishaq.

Muryar Momy yaji a bayan sa tana cewa.

” Mustapha yaushe ka shigo.

Murmurshi yayi yace.

” Yanxun nan shigowa ta, na same ku lfy.

” Lfy lau yasu Hajiyan ka barta.

” Tana lfy sai darun tsufa ni wlh Momy na gaji da zuwa wannan ƙauyen gaskiya, Daddy ya daina tura ni, kullum naje ƙauyen nan da ciwon kai nake dawowa.

Murmurshi Momy tayi tace.

” Mustapha idan bakaje ba waye zaije, kasan dai *Sharifa* baxata iya zuwa ita kaɗai, haka kuma Sharif da Ishaq sunyi ƙanƙanta, Habeeb kuma baya ƙasar ma gaba ɗaya, tunda kaine babba, ai dole kuma kaje ka.

*RAUDA* ce ta fito daga kitchen ɗin Momy hanun ta riƙe da cooler, dariya tayi tare da cewa yaya Mustapha sannu da dawowa, Haɗa Ransa Mustapha yayi, yace

” Yawwa sannu, tare da kawar da kansa gefe.

Jikin *RAUDA* ne yayi sanyi ganin irin amsar da Mustapha ya bata cikin hadewar fuska, gashi ita kuma Allah ya ɗaura mata jarabawar soyayyar sa, amma sam Mustapha baya sake mata fiska Asali ma idan tana waje bai cika zama ba, ta rasa Meye aibun ta da Mustapha ke gudun ta.

Shigewa tayi, daining ta ajiye, foodplast ɗin dake hanun ta, ta ƙara komawa kitchen ɗin domin kwaso sauran Abincin.

Shigewa ɗakin sa yayi, ba tare daya ƙara wata magana ba.

Ran Momy sam baiyi daɗi ba, domin kuwa bata jin daɗin abunda Mustapha ke yiwa RAUDA, gashi ita kuma tana da burin ganin sun haɗa kansu kodan ƙudirin dake ranta na Son haɗa su, Aure.

RAUDA jikin ta a sanyaye tace Momy na haɗa komai a daining bari na shiga ɗakin ya Mustapha, na share masa.

To Momy tace mata sannan ta haura sama ita kuma RAUDA tayi ɗakin Mustapha.

Fitowar shi kenan daga tollet, ɗaure da towel, a ƙugun sa, yaga mutum Zaune gefen gadon sa, ta ƙurawa pic ɗinsu shida Habeeb ido.

Tsuka yaja mai ƙarfi wanda ya dawo da RAUDA cikin hankalin ta.

” Me kike nema a nan? ya jefo mata tambaya.

” Babu komai, daman ɗakin zan gyara maka sannan na sanar da kai, Food is ready.

” Na gode to, amma sharar bana buƙata, abinci kuma na ƙoshi, kina iya tafiya.

” But amma ya Mustapha.

Da katar da ita Mustapha yayi ta hanyar cewa, sorry Please leave me alone, kaina ciwo yake ina buƙatar hutu.

Cikowa idon RAUDA yayi da hawaye Cikin tausayin kanta na *Son Maso wani*

🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻

Afwan Fan’s wlh yau na wuni a makaranta ban samu na muku typing mai yawa ba, ku biyo ni next page gobe.

*Yawan comments yawan typing*

*Share*

*And*

*Comment*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah)*

[1/5, 2:39 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*

*Nasmah ko Nasirah*

*Sara da Sassaka*

*D̸͟͞E̸͟͞D̸͟͞I̸͟͞C̸͟͞A̸͟͞T̸͟͞E̸͟͞D̸͟͞ T̸͟͞o̸͟͞*

*Ä̤ṳ̈n̤̈ẗ̤ÿ̤ F̤̈ä̤ṳ̈z̤̈ä̤ ÿ̤ä̤r̤̈ ä̤m̤̈ä̤n̤̈ä̤*

ṳ̈ẅ̤ä̤ m̤̈ä̤b̤̈ä̤d̤̈ä̤ m̤̈ä̤m̤̈ä̤

k̤̈ä̤ṳ̈n̤̈ä̤r̤̈ k̤̈ï̤ d̤̈ä̤b̤̈ä̤n̤̈ ẗ̤ä̤k̤̈ë̤ g̤̈ä̤r̤̈ë̤n̤̈ï̤, d̤̈ö̤m̤̈ï̤n̤̈ k̤̈ë̤d̤̈ï̤n̤̈ s̤̈ḧ̤ṳ̈g̤̈ä̤b̤̈ä̤ c̤̈ë̤ d̤̈ä̤k̤̈ë̤ ä̤d̤̈ä̤l̤̈c̤̈ï̤ g̤̈ä̤ d̤̈ṳ̈k̤̈ n̤̈ä̤ k̤̈ä̤s̤̈ä̤ d̤̈ä̤k̤̈ë̤.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

Aunty Hauwa Maman Uswan, ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya🙏🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*

____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

*Godiya*

Gareku masoyana, a gaskiya banda bakin da zan muku godiya domin kuwa kun nunawa wannan book ɗin nawa ƙauna fiye da tunani na.

Allah ya bar ƙauna, ina muku godiya a duk inda kuke, da wanda nasan su da wanda bansan suba.

*P* 7️⃣ to 8️⃣

Mai ya shafawa jikin sa, sannan ya zura jallabiya, wayar sa ya ɗaga, ganin kiran ɗan uwan sa, Habeeb.

” Mutanen India, kwana biyu kun manta da mu fah.

Dariya Habeeb yayi cikin zolaya yace.

Ni waye na isa da mantawa da ɗan uwana na haihuwa, kasan dai kaima hakan baxata kasance ba, rai ya mata da rai.

” Ba wani nan cika min baki kake yi kwana biyu ka jini shuru ai zaka neme ni meya faru.

” Nafa nemi layin ka naji unable to connection, na kira Momy take cemin, ai ka tafi ƙauyen dasina, wajen *Tsohuwa mai Ran Ƙarfe Hajiya Innah*, Gaskiya nayi missing ɗin tsohuwar nan, kasan rabo na da ita, 8yrs.

” Ƙauyen Dasina ko ƙauyen masifa, kullum naje wannan ƙauye sai na dawo da ciwon kan wannan mahaukaciyar Aljanar yarinyar.

Dariya mai sauti, Habeeb yayi, yace.

” Gaskiya zanso ganin wannan, Aljanar taka, da kullum nake shan labarin ta, *umm Waya ga Musty Angon Aljana INDO* zanso ganin Ranar da zaka cewa INDO *I love You*

” Amma dai Allah ya isa tsakanina da kai Habeeb, ashe kuwa zaka mutu baka ga wannan Ranar ba, Allah ya kiyashe ni, ɗiban yayi, kaga ma sai Anjuma naga Alamu, yau da baƙar Fata ka tashi, kafin bakin ka yayi tasiri kaina gara na kashe waya ta.

Dariya ce sosai Habeeb yake tun yana kan kujera saida ya sauƙo ƙasa, yanda Mustapha ya hasala kai kace, ance gobe za’a ɗaura masa Aure da INDO, duba wayan yayi yaga harma ya kashe wayar.

” Mustapha Sarkin Zafin Zuciya, gaskiya duk matar da ta Aure ka, zata sha wahala kafin ta gane halin ka, domin sanin Halin ka sai wanda yayi dogon Zama da kai.

Tashi yayi daga ma daidaicin falon da yake ya shige bedroom ɗinsa tare da turawa Mustapha saƙo kamar haka 👇🏻

Allah ya huci Zuciyar ka ɗan uwana, sannan ka shirya tarbata gobe ina hanya insha Allah, zanzo hutu.

Murmurshi mustapha yayi bayan ya karanta saƙon Habeeb, tura masa yayi da cewa.

Kai amma gaskiya naji daɗi sosai Allah ya kaimu goben da rai da lafiya, bari ma naje na fara yiwa Momy Albishir.

*DASINA*

Kwanan Mustapha Uku da tafiya, Indo dai tsiyar tata da sauƙi, domin kuwa yau har ruwa Mama ta samu Indo ta jido mata, Bayan ta gama ɗibawa mahaifiyar tata Ruwan ne, cikin girma da Arziki tace Mama na tafi gidan Innah.

A dawo lfy Mama ta mata, sannan Indo ta fice daga gidan zuwa na Innah, a hanya ta gamu da Baffah mahaifin, Hansai, har ƙasa Indo ta sunkuya ta gaishe shi, mamaki ne ya cika, Baffah ganin Indo a nutse, har mutuncin gaisuwa ya samu, Amsawa yayi ta shige, abunta gidan Innah.

Baffah ne yace,

” Allah dai yasa *ba nutsuwar kwantan ɓauna tayi ba*

Indo ta samu Innah sai shan Baccin ta takeyi hankali kwance, bata tashe ta ba, saima tsintsiya da ta ɗauka ta sharewa Innah gidan ta tsaf, tare da wanke mata kwanukan ta, sannan ta hura wuta, ta dafa taliyar ta, sanda taci ta ƙoshi tayi gyatsa sannan tace

” Alhamdulillah, to bari na lissafa aikin ladan da nayi yau, na farko dai, nayiwa Mama ɗiban ruwa, na gaishe da Baba, na kuma gaishe da Baffah, yawwa sai yanzu da nayiwa Hajiya Innah aiki, wataƙil zan iya samun, lada, guda *ɗari da tamanin* ko haka na tsaya a cikin satin nan na samu, yawwa to yanzu bari na tashi Innah ta bani Naira hamsin na tafi shagon ɗan tasi na sayo maganin ɓera, dariya tayi tace, ya Tanimu nida kai shege ka fasa cikin wannan ƙauyen, tashi Innah ta hau yi, da salati a bakin ta, Innah ta farka, washe baki Innah tayi tace.

” Kaji ƴar Albarka ina mafarkin ki, sai kuma gaki.

Naɗe kafar ta Indo tayi tace dan Allah Innah gaya min me kika ganni inayi cikin mafarkin.

Dariya Innah tayi tace,

” Ganin ki nayi, a Makeken gidan da Muhammadu Mustapha ya gina, kina zaune hakince, komai sai dai kisa amiki, ga kayan ciye ciye kala kala, ke harda fah ƴarinya na ganki wai harkin haihuwa.

Rufe idon ta Indo tayi wai ita a dole taji kunya, ance an ganta da yarinya ta haihu, cigaba da cewa Innah tayi.

” Kinga wasu maka makan kujeru dake cikin ɗakin ki, harda wani ƙaton tebi.

Dariya Indo tasa tace.

” *Wayyo Allah, Allah ya Kai damo ga harawa ko baici ba yayi ɓarna chap Innah waya ga INDO A BIRNI, za’a ga tsiya Aradun Allah, dan zan tsula ciyata son Raina, kinsan Innah, nifa Idan na Auri ya Mustapha ya daina fita kenan, karma wata shegiya ta gansa tace tana sonsa*.

dariya Innah tayi tace.

” Idan kin hanasa fita naga shegen da zai nemo muku abinci kuci, bare ma kekam mai cin tsiya, nifah nama fi sonki da Habibu, domin kuwa yafi wannan mai zafin ran tsiya, sauƙin kai.

Tura baki Indo tayi tace.

“Kinga Innah Idan kina son mu zauna lfy ki daina zagin ya Mustapha, waye ma habibu, sunan ma ko daɗi Babu, wai *HABIBU* nidai ya Mustapha nake so.

Kama bakin ta Innah tayi, tace

” Ikon Allah, wai damma ba kyale ki yake yiba kullum yana cikin Hantarar ki, da tsangwama.

” Naji nidai yanxu bani Hamsin, tunda sharar da nayi miki ma baxaki gode min ba, sai ki bani ladar shara na da wanke wanke, dan nayi ne domin ki biyani.

Sai lokacin Innah ta lura da sharar da Indo tayi mata, fes ta share gidan ya fita, dariya Innah tayi, tace.

” Sannu ƴar Arziki Irin Albarka, ai ɗari ma zan baki ba hamsin ba, laritarta Innah ta buɗe ta ɗauko gudan Ɗari ta bawa Indo.

Aiko kuɗin nan na shiga Hanun Indo ta tashi a guje, sai shagon ɗan tasi, maganin ɓera tace ya bata na hamsin, karɓar kuɗin ɗan tasi yayi, tare da danƙa mata maganin ɓerar.

A hankali Indo ta shigo cikin gidan nasu tana leƙen, gidan domin bata son kowa yasan ta shigo gidan, cikin Sa’a kuwa Babu kowa tsakar gidan, ɗakin tumakin ta shiga, suna ɗaure sunfi goma, dusar dake gaban su ta zazzagewa maganin ɓerar, sannan ta dama shi sosai, kallon tumakin tayi tace.

” Kuyi hkr fah tumaki ba da son raina ba zaku mutu, wanda ya ɗaure ku shine ya jawo muku dan haka sai ku ɗauki hkr, wuf tayi ta fice tabar gidan kafin kowa ya ganta, a dakalin ƙofar gidan nasu ta zauna, zuwa azhar kafin ta shiga cikin gidan nasu.

Fitowar Mama daga ɗakin ta, zatayi madafi ne, sai taji tumaki na wani irin gurnani, leƙa ɗakin tayi, sai tagan su gabaki ɗaya kwance, bakin su kuwa sai fitar da kunfa yakeyi, zaro ido Mama tayi, da sauri tayi ɗakin Tanimu ta kira sa tare suka fito duka harda Baba, Salati Baba ya ɗauka, cikin mamaki yake cewa

” ikon Allah dobbobi kamar wanda suka ci guba, maxa Tanimu, tafi ka kira idi mahauci yaxo ya siyi dabbobin nan dan Wlh mutuwa zasu yi.

Da gudu Tanimu ya fice daga gidan, a gigice, INDO dake zaune taga ficewar Tanimu, Dariya tayi, tace.

” Lallai magani ya fara aikin sa.

Tare Tanimu suka dawo da idi mahauci, ko Kafin su iso ma tuni tumaki kam sun mutu, gaba ɗaya ko ɗaya bai tsira ba, shuru Tanimu yayi tare da zamewa ya zauna a ƙasa, sai Kuma hawaye ya fara bin idanun sa, Mama ma taji tausayin sa ainun, domin kuwa ko wani rago ɗaya zaiyi dubu Arba’in, Baba kuwa, Haƙuri ya fara bawa Tanimu da cewa ya ɗauki ƙaddara.

INDO da ta shigo cikin gidan ne, ta samu Tanimu na zaune sai famar kuka yake, salati ta ɗauka tare da cewa.

” *Subhanallah me zan gani haka, GARDI da kuka, sai kuma tasa dariya, Allah sarki daɗi na da gobe saurin zuwa, haka Nima jiya iwar haka, ka Sani kuka, sai gashi nima yanxu Allah ya saka min.*

Jin furucin INDO yasa Mama, zargin kodai Indo ce tasawa dabbobin nan wani Abu suka mutu.

” Zo nan Indo cewar Mama.

” Naxo kuma Mama me zanyi ni Kuma?

” Kixo nace ko, idan kuma baxaki zoba, sai ki faɗa min.

Tahowa Indo tayi, kusa da mama, tace

” Gani nan tana tura baki tayi maganar.

” INDO kece kika kashe dabbobin nan koh?

Saurin ɗago kansa Tanimu yayi jin abinda Mama ke furtawa.

Cikin rashin tsoro, Indo tace.

” Ni kuma Mama, akan me zan kashe masa dabbobin sa?, nikam bani bace.

Murmurshi Mama tayi kasancewar tasan Halin Indo, indai kin haɗa ta da Allah to zata faɗa miki gaskiya, sannan tace.

” Dan Allah dan Annabi na roƙeki da Allah ki faɗa min idan kece kika kashe dabbobin nan?

” Shikenan tunda kince Allah, ai kin gama magana, dole zan gaya miki gaskiya.

Har ga Allah Mama ganin da nayi Ya Tanimu haka kawai jiya yata jibgata akan wata banxa lami, Babu wanda ya hanasa cikin gidan daga ke har Baba, shiyasa ganin da nayi bani da gata cikin gidan nan, ba’a sona yasa ni ƙwatawa kaina ƴanci ta hanyar, zuwa gidan Innah nace ta bani hamsin, tana bani kuwa nayi shagon ɗan tasi na sayo maganin ɓera, kuna cikin uwar ɗaka, na shiga na juye maganin ɓarar cikin Abincin dabbobin, Amma fah Kafin na saka musu saida nace dabbobin su yafe Min ai.

A fusace Tanimu ya tashi zai rufe Indo da duka.

Dakatar dashi Baba yayi ta hanyar cewa tsaya Tanimu.

Kallon Indo yayi yace.

” Haba yanzu dan Allah akan ɗan dukan, da ɗan uwan ki, ya miki jiya shine shine zaki masa wannan mungun Aikin, kisan Asarar da kika masa kuwa, haba Indo meyasa bakya jin magana ne, innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un, yanxu Indo, tsiyar taki, harmu ma baki barmu ba, to wa zaki bari, iyayen kima baki kyale ba, bare Kuma Wasu, kiji tsoron Allah Indo ki gyara alaƙar ki da al’umma.

” Haba Baba wacce nasiha zaka tsaya yiwa wannan shaiɗaniyar, Ka kyale ni kawai yau na koya mata hankali cikin gidan nan na karya ta, ta zauna kowa ma ya huta da bala’in ta, dan Indo masifa ce.

Mamace tace.

“Subhanallah, haba Tanimu, ƴar uwar taka kake kira da masifa, baxaka nema mata sauƙi ba, sai kake binta da mungun baki, to karna sake jin ka kirata da masifa, da kake cewa a barka ka koya mata hankali, jiyan da ka doke tan, meya jawo maka yanzu, Bayan Asarar da tayi maka, a yanzu ni kaina Uwar Indo lamarin ta ya fara bani tsoro, idan kace ma dukan ta zakayi, gobe sai ta maimaita maka abinda yafi na yau, addu’a kawai ya dace mu bita dashi, Allah daya bamu ita, shi zamu roƙa ya shirya mana ita.

Baba ne yace.

” Tabbas Maganar mahaifiyar ku gaskiya ce, addu’a shine mafita tsakanin mu, da Indo.

Kallon ta Mama tayi tace.

” Kinyi sallar Azhar ne?

” Banyi ba cewar Indo tana haɗa rai tare da hararar Tanimu.

” Jeki ki ɗauki buta maza kiyi Alwala, kiyi Sallah.

*Ni fah Mama ba yanxu nake yin Sallah ta ba, sai da isha’i nake haɗa Asuba magriba Azhar da kuma isha’i.*

Kuyi hkr da rashin jina jiya da bakuyi ba, hakan ta faru ne ta sanadin bana typing Ranar Asabar, fans ɗina dake group ɗin Sara da Sassaqa sun san hakan.

*Share*

*And*

*Comments*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah)*

[1/6, 4:33 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*

*Nasmah ko Nasirah*

*Sara da Sassaka*

*D̸͟͞E̸͟͞D̸͟͞I̸͟͞C̸͟͞A̸͟͞T̸͟͞E̸͟͞D̸͟͞ T̸͟͞O̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni, domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga na ƙasa dake.

Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

Aunty Hauwa Maman Uswan ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya.🙏🏻

😄😄😄😄 Sara da Sassaqa fan’s kuyi hkr wlh ban manta daku ba, ina nan ina typing ɗinsa, za kuma kuga posting, gobe insha Allah.

*بسم الله الرحمن الرحيم*

____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

*P*•••••••9️⃣ ➡️ 1️⃣0️⃣

Tsawa Mama ta dakawa INDO tace,

” Maza ɗauki buta kije kiyi Alwala kiyi Sallah maxa, sannan ki ɗauko uniform ɗinki, na boko ki wanke gobe Litinin kuna da makaranta, Anjuma kuma zakije makarantar Allo.

” Nifa Mama Babu wani wanki da zanyi, haka zansa uniform ɗin, ni bokon ma ba wani damuna tayi ba.

Tanimu dake jifan Indo da mungun kallo ne ya tashi ya fice daga cikin gidan, domin Wlh ji yake kamar ya shaƙe wuyan ta, sai dai babu damar yin hakan sakamakon hanasa da Mama tayi.

INDO tana haɗa rai haka ta ɗauki buta tayi alwala, bayan tayi sallar ne, ta ɗebo uniform ɗin bokon nata, ta wanke su, tas kuwa ta wanke, domin Indo badai iya wanki ba, sai idan bata ga dama ba, tayi jiƙa jiƙa.

Jummalo ce ƙanwar INDO ta shigo cikin gidan hanun ta ɗauke da ledar shinkafar da Mama ta aike ta, ta siyo mata shagon ɗan tasi, da Sallama jummalo ta shigo, amsawa Indo tayi, tare da cewa.

” Zona aikeki jummalo ɗakin Mama ki ɗauko min ɗankwalin uniform ɗin nan.

Babu musu jummalo ta shige ɗakin Mama, tana sallah ta same ta, ajiye ledar tayi tare da duba cikin kayan wankin Indo, da ƙyar jummalo ta samo ɗan kwalin, ficewa tayi ta miƙa mata, cikin neman faɗa Indo ta fara cewa jummalo.

” Wato ke kuma jummalo tsabar baƙar mugunta, shine jiya kika wanke uniform ɗinki ko ki haɗa da nawa ki wanke, kinyi Asara ai ke kam, *mai shegen wariyar Launin fata*,

To gashi ai na wanke yanxu banga abunda ys ya cinye ni ba.

” Kiyi hkr na duba uniform ɗin naki ne ban gani ba shine yasa na wanke nawa kaɗai, Amma ai kinsan kullum nice nake wanke mana uniform koh.

” Kuma haka ne, kinsan nifa idan ana min abu kullum Rana ɗaya banga ammin ba, ji nake kamar ba’a taɓa min ba, shikenan jeki, nima na gama gari zan shiga dan wlh ba xanje makarantar Arabbi ba yau.

Ita dai jummalo shigewar ta tayi ɗakin Mama ba tare da ta tankawa INDO ba.

Washe gari da safe jummalo tayi shirin makarantar ta, kunu da ƙosai taci, sannan tayiwa Mama sallama ta tafi, ita ko Indo bata da Alamar, zata makarantar ma, dan ko karin kumallon ma batayi ba, tana zaune, kawai tayi shiru.

Mamace ta dube ta tace.

” INDO baxaki makarantar bane, jummalo har ta juma da tafiya, takwas fah yanxu, ko karin kumallo baki yiba.

” Zani mana, nafi son sai sun gama wannan tsayuwar tukunna, mema yake da suna, asandabilyu, ko Assambly, oho sai sun gama tukunna.

” Tashi maxa kisa uniform ɗinki, kixo kici abinci, ki shige makaranta, bana son shashancin banxa, ko dan kinga ina kyale ki, shine kike min abunda kika ga dama dan ubanki, ki tashi nace, cikin tsawa Mama take maganar.

Tashi Indo tayi tana ƙunƙuni tasa uniform ɗin, ko karin kumallon ma ƙinyi tayi, ta fice daga gidan.

” Allah ya shirya ki Indo cewar Mama.

A hanya Indo ta ɓelɓelce, ba ita ta shiga cikin makarantar tasu ba, sai ƙarfe tara na safe.

Taxo daidai bakin window na ajin nasu taji for master nasu yana kiran sunan ta.

” *Ashatu Musa*

Daga jikin window INDO ta amsa da ƙarfi.

” *Labbaika Present Sir Naxo, gani nan ma a nan*.

Gabaki ɗaya Ajin juyo da kallon su sukayi zuwa ga Indo, yayin da Mlm Sani ke cin dariya, suma Ajin dariyar suka ɗauka.

Cikin dariyar ne, Mlm Sani yace.

” Sannun ki da zuwa to, sai ki samu damar ƙarasowa koh.

Shigowa Indo tayi ba tare da tsoron lattin da tayi ba, tsayawa tayi gaban mlm Sani tace.

” Mlm gani.

” Meyasa kika zo a latti? Me kuma yasa kika amsa min sunan ki daga waje?

Wa kuma yace kin amsa sunan ki sau biyar?

Mlm Sani ya jefo mata tambaya tare da ƙara gyara zaman bulalar sa, a hanun sa.

Haɗa fuska tayi, tana kallon bulalar hanun sa, kafin tace.

” Mlm duka wannan tambayar zan amsa ni kaɗai.

Ɗago bulalar Mlm Sani yayi, tare da cewa zaki amsa min koh saina lillisaki tukunna.

” Zan baka ta fada masa tana turo bakin ta gaba.

” Ina jinki, tell me.

” Mlm to ka fassara min Abunda kace na ƙarshen, toll ma, meye ne shi da Hausa.

” Murmurshi Mlm Sani yayi kasancewar yasan Indo tana da ƙoƙari, indai akayi darasi bata fahimta, ba, to fah sai tayi tambaya, kuma dags wannan lokacin ta riƙe kenan a kwakwalwar ta, gaskiya Indo badai brench ba.

” Tell me, yana nufin cewa faɗa min.

Kin gane.

Kaɗa kanta INDO tayi alamun ehh ta gane sannan tace.

” Mlm Abunda yasa nayi latti tsakani da Allah bana son tsayuwar asandabilyu ne, na biyu kuma, na amsa ne saboda bana son ka samin banxo ba, sai na Uku kuma, da nace *Labbaika* wai dai Mlm na maka *Larabci ne* dan kasan na iya, *Present Sir* kuma wai na amsa maka ne da yaren turanci, sai kuma *Naxo* da Hausa na maka.

Kaga Mlm ai nayi ƙoƙari dana iya Yaren Uku koh.

Kaɗa kansa Mlm sani yayi tare da jinjina shirme irin na Indo, da yarinta, wato dai Kowa da irin tasa yarintar, duban ta yayi yace.

” Dan Allah INDO daga yau duk ranar monday ki dinga zuwa kina halartar Asembly yana da amfani sosai, sannan daga yau ki daina amsa suna daga waje, ki bari sai kin shigo class tukunna, sannan daga yau idan an kira sunan ki, ki amsa da Present kawai kinji.

” Naji Mlm kuma baxan sake ba in Allah ya yarda.

Muga farcen hannu ki, da kuma kitson ki, uniform dai naga kin wanke.

Miƙo masa hanun Indo tayi, wayyo Allah, farcen Indo sunyi zaƙo zaƙo sai kace wacce bata taɓa yankan farce ba, tunda uwar ta, ta haife ta, kayin ta kuwa da ta buɗe Babu abunda yake tashi sai tsamin datti, kitson ta kuwa tsabar daɗewa har ba’a ganin tsagun.

” Subhanallah cewar Mlm Sani, meye haka INDO, wani irin ƙazanta ne wannan, ki dubi farcen ki, da kayin ki babu ko daɗin gani, haba Indo kike tsafta dan Allah.

Kinji, kinga yanda kike babbar yarinya haɗaɗɗiya, da zaki ke tsafta haba wa, karki ga kyan da zakiyi.

Su Indo Mlm Sani ya fasa mata kai, cikin dariya tace

” Allah Mlm ni kyakkyawa ce.

Dariya Mlm Sani shima yayi domin a iya zaman sa da Indo ya gane idan zaka bita a hankali tana da sauƙin kai, za kuma ka ribance ta, idan kuma da faɗa kake binta, baxata taɓa gyarawa ba.

” Sosai ma kuwa, a wani fitowar kyan naki ma, sai kin yanke farcen ki, kin tsefe kanki kin wanke, kije kiyi kitso, ai Babu mai gane ki Indo tsabar kyan ds da zakiyi.

Ƙara washe yellown hakwaren ta Indo tayi, tace

” Wlh Mlm yau zanyi kitso, na yanke farce na, har ƙunshi sai nayi, Allah sarki ashe ni kyakkyawa ce, nake ɓoye kyawuna.

Murmurshi Mlm Sani yayi cikin jinjinawa yarinta irin na Indo yace.

” To Allah ya kaimu jeki zauna maxa zamu fara lesson.

Rasa wajen zama Indo tayi sakamakon cika teburin zaman da akayi, sai dai ta zauna a ƙasa, hango Zainabu Indo tayi zaune ita da su Hansai, wajen nasu ta nufa, cikin gadara da bata rai, tace, ke Zainabu tashi ki bani waje na zauna.

Saurin tashi Zainabu tayi, kasancewar tana tsoron taƙi, tashi, Indo taci uban ta.

Ta koma ƙasa ta zauna.

Girgiza kanta Hansai tayi ganin fin ƙarfin da Indo tayiwa Zainabu.

*ⓓⓤⓣⓢⓔ*

Dariya sosai RAUDA keyi, har tana riƙe ciki, tace.

” Wlh ya Habeeb ka bani dariya, wai yaushe zaka gane ka girma ne, wai camma, London ɗin haka kake musu irin wannan calikancin.

Dariya shima Habeeb yayi tare da cewa.

” Zan girma amma sai randa nayi Aure dan har yanzu a matsayin Yaro nake.

Momy dake sauƙowa daga step ne take cewa.

” Kai kam baxaka girma ba, tunda har yanxu ka gagara yin hankali, kullum wasa shine cinka da shan ka.

Murmurshi Habeeb yayi, yace

” Kai Momy kema abunda zakice kenan, Momy ai rayuwa saida wasa da Dariya, har yaushe kullum mutum zai zauna cikin haɗe fuska, gaskiya ni baxan iya wannan rayuwar ba.

RAUDA ce tace.

” Shiyasa Rayuwar ka take burgeni ya Habeeb, kana komai cikin sauƙin kai saɓanin ya Mustapha da baya sakewa da kowa, daga Momy sai kai.

Dariya sosai Habeeb yayi yace.

” Bros sai a hankali haka yake tun tashin mu, bai cika sakewa akan komai ba, so kar wannan ya dameki, domin *A JININ SA YAKE*.

Momy ce ta nisa tare da cewa.

” Abinda nake faɗi mata kenan, ta daina damuwa da Halin mustapha, Amma ta kasa ganewa wataƙil idan ka faɗa mata, sai ta gane naka.

” Hmm RAUDA Amaryar mustapha, tun yanxu kin tsoron sa, ina kuma ga anyi Auren, ya faɗa mata tare da kanne mata ido😉.

Murmurshi RAUDA tayi tare da cewa.

” Ya Habeeb kaima dai da tsokana kake, nine muke soyayya da ya Mustapha, lallai zolayar ka bata baka dai dai ba.

Dariya Habeeb yayi yace.

” Shikenan *Abar Kaza cikin gashin ta*

Amma nidai nasan abinda ke wakana.

Jin motsin mutum ne yasa Habeeb juyawa, Mustapha ya hango yana sauƙowa daga step, cikin haɗewar fuska, dariya Habeeb yayi ganin kallon da Mustapha ke aikawa RAUDA, kallon wulaƙanci.

Sanda ya zauna kusa da Habeeb sannan yace

” Sannu da hutawa Momy.

” Yawwa sannu sai yanxu ka fito, Tun ɗazu ɗan uwan ka ke jiran ka, kuma kasan dai Daddyn ku, yace by four ku samesa kasuwa.

” Sorry Momy wlh bacci ne ya danne Ni, amma yanxu ma bata ɓaci ba, zamu tafi, kallon Habeeb yayi yace, muje bros.

” Muje ina ai idan kaga na tashi anan sai Momy ta mana Shari’a, Momy gani ga Barrister mustapha, ki mana Shari’a.

” Ina sauraron ku kaji iyayen faɗa badai ku haɗu ba sai kunyi cece kuce tsakanin ku, cewar Momy.

Dariya Habeeb yayi Yace.

” Momy cewa fah nayi gobe muje ya rakani DASINA wajen Hajiya Innah, amma bawan Allah nan yace baxai jeshi ba.

Murmurshi Momy tayi tace.

” Yana da gaskiya Habeeb, kwata kwata kwanan sa uku da dawowa, kuma gashi ya koma bakin Aikin sa, kaga kuwa kai kaɗai zakayi tafiyar ka.

Dariya mustapha yasa tare da cewa.

” Yes Momy daɗi na dake Adalci, Mlm Habibu Angon Hajiya Innah, tafiya DASINA ya kamaka kai ɗaya, sai ka tashi mu dangana zuwa ga Daddy.

RAUDA ko Babu abunda take sai kallon mustapha Kamar wacce zata haɗiye sa, shiko suna haɗa ido zai maka mata harara.

*Share*

*And*

*Comments*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah)*

[1/7, 5:31 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*

*Nasmah ko Nasirah*

*Sara da Sassaka*

*D̸͟͞E̸͟͞D̸͟͞I̸͟͞C̸͟͞A̸͟͞T̸͟͞E̸͟͞D̸͟͞ T̸͟͞O̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar amana*

Uwa mabada mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.

Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

Aunty Hauwa Maman Uswan, ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya🙏🏻.

*بسم الله الرحمن الرحيم*

____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

___________________________________

Masoyana bani da bakin da zan muku godiya, na gode na gode sosai, da ƙaunar ku gare Ni, yanda kuke Son book ɗin *INDO A BIRNI* abun ba’a cewa komai, waɗanda suka min magana ta privet cewa na sasu a group ɗin *INDO A BIRNI* suyi hkr dan Allah wlh group ɗin ya cika, ku nema a wani group nasan baxaku rasa ba.🙏🏻

*P*••••••1️⃣1️⃣ ➡️ 1️⃣2️⃣

Kauda kanta RAUDA tayi cikin ƙunar rai, ta rasa menene ya gaxa a jikin ta da mustapha yake mata wannan wulaƙancin, gashi Dai Mamy tace mata malamin ta, ya tabbatar mata cewa Mustapha zaiso ta, amma har yanzu shuru, sai ma uban wulaƙanci da take fuskanta a wajen sa, yau dai ta ƙudurce a ranta, dole sai ta koma gida, kodan Mamy tasan halin da ake ciki, domin kuwa baxata iya Rayuwa Babu mustapha ba, shine numfashin ta, taya to rayuwa zata kasance Babu numfashi, dole ma sai ka soni mustapha, dole ne.

Maganar da Habeeb ke mata shine ya dawo da ita daga duniyar tunanin data faɗa.

” Dan Allah Sis RAUDA anjuma ki haɗa min Abinci, mai kyau, ai kinsa abubuwan da nafi buƙata.

” Ba komai ya Habeeb zan haɗa maka insha Allah, adawo lfy.

” Habeeb ne kawai ya amsa da Ameen shikan mustapha, kallo ma bata isheshi ba, bare kuma ya amsa sai ya dawon ta.

Sallama sukayi wa Momy sannan suka wuce wajen daddy kasuwa.

RAUDA kallon ta, ta mayar wajen Momy tace.

” Momy bari na haura sama na ɗan miƙe, kafin Anjuma na sauƙo na ɗaurawa ya Habeeb girki.

A fito lfy ta mata, sannan ta haura sama.

Kwanciya RAUDA tayi akan gadonta tare da ɗaukar wayan ta ta dannawa mamyn ta Kira.

Da sallama Mamy ta Amsa, tace RAUDA lfy naji Muryar ki kamar wacce taci kuka.

” A’a Mamy ba kuka nayi ba, kawai raina ne yake ɓace, Mamy na shiga Uku, ya Mustapha baya sona, Mamy ko kallo na, baya sonyi, ya zanyi Momy, ta ƙarasa maganar cikin kuka mai tsuma Zuciya.

” Ya isa Haka RAUDA, ki daina kuka, domin kuwa muddun ina numfashi dole sai Mustapha ya durƙusa a gaban ki da gwiwwowinsa yana roƙarsa soyayyar ki, Dani yake zancen, tunda shi butulu ne, baisan Alkairi ba, ai yana da tarihin Halaccin da mahaifin ki yayiwa ubansa, ki kwantar da hankalin ki, zai shigo hanu, sai kin juyasa kamar wainar tanda.

Cikin farin ciki RAUDA tace.

” Promise Mamy, wlh ina son ya Mustapha, fiye da yanda nake son kaina, jiya ma ya Habeeb yake cemin, zasuxo Anjuma su gaishe ki.

” Okey Allah ya kawo su lfy.

Da Ameen RAUDA ta amsa sannan sukaci gaba da zancen Duniya.

Menene Asalin Mustapha?

Menene alaƙarsu da RAUDA?

Menene Dangantakar su da ƙauyen su Indo?

🤔🤔🤔🤔🤔

*Dangantakar su*

Alhaji Mamman babban limami ne, a cikin ƙauyen *DASINA* mutum ne mai karancin da mutunci, ana girmama sa, sosai cikin wannan garin, Yana da matar sa ɗaya mai suna Harira yaran ta suna kiran ta da INNAH, yaransa biyu, Haruna shine babba, sai Hindu wacce ake kiran ta da Hinde a cikin ƙauyen, Mlm Mamman takaka ne sosai, wani sa’in abincin da zasu Ci ma gagarar su yake, kasancewar ya samu matar rufin Asiri, bata taɓa nuna gajiyawar ta akan Rashin Abincin gidan Mlm Mamman ba, haka zata san dabarar da zatayi, yaran ta, su sami Abinda zasu Ci, maƙocin Mlm Mamman, Mlm Hadi mutum ne, mai kyautatawa maƙoncin sa, duk da shima bawai yana dashi bane sai dai rufin Asiri, amma yawanci idan yayi cefenen gidan sa, to sai yayiwa, Mlm Mamman, zumunci ne mai ƙarfi tsakanin su, matan Mlm Hadi, Safiya, da Rabi, suna zumunci sosai da INNAH, musamman Rabi, kusan zaka iya kiransu ƙawaye da INNAH, Rabi tana da ɗanta ɗaya mai suna Musa, Musa da Haruna ɗan Innah kusan komai tare suke yinsa, shaƙuwace mai ƙarfi, tsakanin su.

Tafiya suke suna, zance, dawowar su kenan daga, makarantar Allo, Haruna ne yake cewa Musa.

” Musa ina ganin fah xan tafi birni neman kuɗi, dan kaga mun gama Secondary School, Bamu da Halin da zamuje gaba da Secondary, Kuma gaskiya ni, ina da burin cigaba da karatu, kodan na taimaki rayuwar iyaye na, da ƙanwata.

Shiyasa na yanke wannan shawarar, idan kaima kana da wannan burin, sai mu haɗa hanya.

Shuru musa yayi kafin yace.

” Gaskiya Haruna ni bani da burin cigaba da karatun Boko, iya Secondary ɗin ma, da nayi ya isheni, gara na nemi sana’a na fara, tunda kai kayi niya, kaje ka, Allah ya baka Sa’a yasa ka shiga, birni a Sa’a.

” Shikenan Musa na gode sosai, kuma baxan taɓa manta Addu’ar ka gare niba, Haka Abotar ma baxata taɓa yankewa ba.

Har suka iso gida tattaunawa suke kan tafiyar Haruna birni, da la’asar Haruna da musa suka sami iyayen su, a majalisar su, na dattawa da maganar tafiyar, Haruna birni, domin neman kuɗin da zaici gaba da karatunsa, da farko Mlm Mamman yaƙi, yarda, da tafiyar Haruna birni, sai da Mlm Hadi yasa baki tukunna, nan ma daƙyar mlm Mamman ya Yadda, bayan ya amince masa ne, suka nufi wajen Innah, domin sanar da ita, dan shi Haruna a niyarsa gobe yaƙe son wucewa, birni.

A zaune suka sami Innah bakin murhu tana iza wuta, tsugunnawa sukayi, tare da mata barka da gida.

Kallon su Innah tayi tace.

” Musa kune tafe yanxu, ya Rabin take.

” Lafiyar ta ƙalau Innah, tace ma na gaida ki.

“Ayya Ina amsawa, Haruna ka shiga ɗaki na akwai abinci rufe ku ɗauka kuci koh.

Da to Haruna ya Amsa tare da cewa

” Innah idan kin gama, muna son zamuyi magana ne, dake.

” Ba damuwa kuje kuci abincin ina zuwa nima.

Bayan sun gama cin abincin ne Innah ta shigo cikin ɗakin, tare da zama.

Musa ne ya dube ta, tare da sanar da ita ƙudirin Haruna, na son zuwa burni neman kuɗi, ya kuma sanar da ita yanda sukayi da Mlm Mamman.

Innah bata wani hanasa ba, illa ma cewa da tayi.

” Tunda har Mlm ya yarje maka, ni babu abinda zance, sai dai a duk inda kake Haruna ka kasance mutum mai ruƙe amana tare da haƙuri, ka kuma ji tsoron Allah, ka zauna da duk mutanen da kayi tarayya dasu, Allah ya baka Sa’a yasa ka sami Abinda kaje nema, kake zayartar mu, duk lokacin daka samu zama, hakanne zai nuna mana kana lfy.

Haruna yaji daɗin addu’ar mahaifiyar sa sosai, cikin farin ciki da murna suka fice daga cikin gidan.

Washe gari da safe Haruna ya ɗauki dangwalin sa, tare da yiwa ƴan uwa da abokan Arziki sallama, har bakin gari, Musa ya raka Haruna da ƙyar suka iya rabuwa cikin kewar juna, kafin musa ya dawo cikin ƙauyen shi kuma, Haruna ya kama hanyar tashar mota domin hawa motar da zata kaisa birni.

Cikin sa’a kuwa Haruna ya shiga birni da farko ya fara sana’ar sharan shago ne a kasuwa, a biyasa ɗari hamsin, a wuni yana samun Dubu biyu kullum, na sharar shagon, akwai Ranar da Haruna yake yiwa Wani Alhaji sharan shago, sai tsinci kuɗi, wajen dubu goma rafar su, komawa Haruna yayi ya kawowa Alhajin kuɗin yace gashi tsinta yayi, yana masa shara, shiko Alhajin ashe da sanin sa, ya ajiye kuɗin domin ya gwada amanar Haruna, kasancewar yana son ɗaukar sa yaron shago,

Alhaji muktar yaji daɗin samun, Haruna daga cikin masu Amana, daga nanne fah ya ɗauki, Haruna, yaron shago suna saida Atampopi, akwai ɗan Alhaji muktar, Bello, zai ɗan girmi Haruna kaɗan sanshi a lokacin ma yana da mata, muktar da Haruna, jinin su ya haɗu sosai, shaƙuwace mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu, inda kullum suke tare.

Akwana a tashi Babu wuya wajen Ubangiji, Alhaji muktar ya yadda da amanar Haruna sosai, inda hakan tasa ya ɗauke sa ya kaisa gidan sa da zama, tare da sashi, kawo takaddun sa, ya nema masa University.

Alhamdulillah Rayuwar birni tayiwa Haruna daɗi, tunda gashi, yana sana’ar sa, kuma yana zuwa makaranta, haka ƙauyen suma yana kaimu musu ziyara sa’i da lokaci, bai Kuma manta da abokin sa, Musa ba, inda yakan yawan nasa Alkairi.

Haruna cikin nasara ya gama karatunsa inda ya fito da good result, wato first class, Babu ƙyashi Alhaji muktar ya basa Aron kuɗi kimanin, 20 millions yace ya buɗe shagon sa na kansa, idan yaso yake biyansa kuɗin sa da kaɗan kaɗan, Haruna yaji daɗin alkairin da Uban gidan nasa ya masa.

Cikin ikon Allah, kasuwa rake jawa Haruna inda ya samu ninkin kuɗin da Alhaji muktar ya basa aro a cikin shekara ɗaya.

Fili Haruna ya saya tare da fara ginawa, ya kuma fara neman, Auren A’ishah wacce suka haɗu da ita taxo siyan zani shagon nasa, soyayyah mai ƙarfi ne ta shiga tsakaninsu.

Cikin ikon Allah kuma yayi nasarar samun Auren, A’ishah, inda Alhaji muktar shine ya karɓi Auren bisa umarnin Mlm Mamman, ƴan ƙauyen Dasina suka zo Aure.

Harda Musa ma ya sami Halartar Taron ɗaurin Auren.

Bayan shekara Uku.

A’ishah matar Haruna ta haifi yaranta, maza kyawawan gaske, Hatta Hajiya Innah ta halarci wannan sunan, inda yara sukaci sunan, Muhammad Mustapha, da Muhammad Habeeb.

A lokacin ne kuma Musa Nasa Auren ya tashi, Haruna kusan shine yayi hidimar bikin, Musa, Tare sukaxo da matar sa A’ishah, da ƴan biyun sa, sunan matar da Musa ya Aura Maryam itama ƴar cikin ƙauyen nasu ne, bayan bikin ne Haruna suka koma cikin Birni, da matarsa A’ishah.

Inda ya buɗewa Musa shagon sai da kayan tireda.

Acikin wannan shekarar ne, Allah ya ɗauki Rayuwar mahaifin su Haruna da mahaifin musa tsakanin su sati ɗaya ne kacal, sunji zafin mutuwar sosai, Innah kuwa tasha kukan ta, har ta godewa Allah.

Haruna ya ɗauki kanwar sa, Hindu ya koma da ita birni yaso ya tafi da Innah, amma Innah taƙi, tace Babu inda zata, a barta anan ƙauye har mutuwar ta.

Bayan shekara biyu da mutuwar mahaifin Haruna, ya biya musu kujerar hajji, dashi da Innah da kuma matarsa A’ishah, suka sauƙe falari, a cikin shekarar.

Ƙanin Alhaji muktar, Usman shine ya auri Hindu, inda ya tafi da ita birnin Istanbul kasancewar acan yake aiki.

Shekaru sunja rayuwa sai tafiya take, yanxu ƴaƴan A’ishah biyar bayan ƴan biyun ta na farko, ta sake haihuwar Mace mai suna Sharifa sai kuma ta sake yin wasu ƴan biyun, ishaq da Sharif, inda zumuncin Haruna da Bello tayi ƙarfi sosai, har ta kai ga Bello yakan ɗauko ƴarsa RAUDA ya kawo ta weekend, gidan Alhaji Haruna, Inda ita kuma RAUDA ta taso da tsantsan ƙaunar Mustapha, wanda shi yake ɗaukar hakan a matsayin, Hauka take yi.

A lokacin su mustapha sun gama karantunsu a ƙasar London, har sun kama aikin su, inda Mustapha ya karanci Lawyer shi Kuma Habeeb ya karanci medical doctor, Hospital ɗin da Habeeb yayi practical, suka ɗauke sa. Aiki

Shima Musa yanxu yana da yaran sa, biyar, Tanimu, INDO, jummalo, Abubakar sai kuma Haruna mai sunan Abokin nasa.

Haruna da iyalansa suna ziyartar mahaifiyar sa, sosai wacce yanxu suke kira da Hajiya Innah.

Wannan shine tushen labarin su.

Ku biyo Alƙalami na gobe insha Allah domin komawa cikin labarin *INDO A BIRNI*.

*Share*

*And*

*Comment*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah)*

[1/8, 5:26 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*

*Nasmah ko Nasirah*

*Sara da Sassaka*

*D̸͟͞E̸͟͞D̸͟͞I̸͟͞C̸͟͞A̸͟͞T̸͟͞E̸͟͞D̸͟͞ T̸͟͞O̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.

Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya.🙏🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*

____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

🙏🏻🙏🏻🙏🏻😩😩😩😩

Ya Ubangiji ina roƙo gareka daka sa *Farisa* ƴar sister Ladingo marubuciyar matar GwamnaTana hanu na gari, Allah ka kareta a duk inda take, ka Bayyana ta cikin gaggawa.

Ameen 🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻

*P*•••••••1️⃣3️⃣ ➡️ 1️⃣4️⃣

*Mu Dawo cikin labarin mu* 🏃🏻‍♀

Yau Indo tun dawowar ta daga makaranta, ta nemi Ruwa a baho da dutsin goge kaushi, ta jiƙa ƙafarta, yayin da kuma reza ke riƙe a hanun ta tana yanke farcen ta, ita dai Mama tana tsaye gefe tana kallon ikon Allah, ɓarawo da bacci, wai yau Indo ce ke yanke, farce harda gugar ƙafa, yarinyar da ko zaka mutu kana cewa Indo wanke ƙafarki baxata wanke ba, sai dai ki mutun, bare kuma gugar ƙafa, yau kuma sai gashi ita ɗayan ta, tanayi ba tare da kowa ya sata ba, bayan ta gama yanke farcen Hanun nata ne, sai Kuma tahau gugar ƙafa, cikin mamaki Mama ke kallon ƙafar Indo, yanda ta fita fes, Babu wani alamar kaushi, ashe daman datti ne, yasa kafar Indo fita hayyacinta, yanke farcen ƙafarta, tayi, sannan ta dubi Mama tace.

” Mama tsammin Omo na wanke kayina dan Allah, ina son zanje gidan Laure ne, kitso Anjuma.

Zaro ido Mama tayi tace.

” Me kika ce, zaki kitso gidan Laure, ke ɗin kuma yau Indo, kece zakiyi kitso.

Dariya Indo ta kwashe dashi tace.

” Eh wlh Mama, Mlm Sani yace idan na yanke farce na, nayi kitso, ba ƙaramin kyau zanyi ba, sai nafi duka ƴan matan garin nan kyau, tana fari da Ido take yiwa Mama maganar, kuma yace gani ƴar ɗagwas ɗagwas kyakkyawa son kowa ƙin wanda yarasa,.

Dariya ce ta suɓucewa Mama ganin yanda Indo ta dage, wai a dole ita kyakkyawa ce, haba ai daman wannan tsaftar bata Allah da Annabi bace, dole da biyu, cikin dariyar Mama ta nunawa Indo gun wanke wanken ta, tace

” Jeki ki ɗauko gashi can kixo na wanke miki kayin, tsifar ma ni sai nayi miki, Mlm Indo kyakkyawar garin nan, Mama ta faɗa tana cin dariya.

Indo dai bata Wani damu da dariyar da Mama ke mata ba, ta shige ta ɗauko Omon, tas Mama ta wanke mata kayin tana zolayar ta, tsifa Mama tahau yi mata, gashin Indo yana da masifar tsayi, ga yawa, kuma yana da ɗan tauri kaɗan, runtse idon ta, take, tana jin zafin yanda mama ke figar gashin nata, cikin fara gajiya da jin zafin tace

” Mama ki daina min da mugunta Mana, wannan ai mugunta ce, sai jamin kike da ƙarfi.

” Nice kuma nake miki muguntar Indo, cewar Mama.

” Yo to Mama, gani nayi sai jamin gashi kike da ƙarfi, dole nace munguta mana, ai sai kimin a hankali, Allah kika cigaba da jamin gashi zan fasa kitson ma, sai nabar gashin a haka.

” Wannan shegen taurin gashin naki, daya kusan wata biyar baiga kitso ba, ai dole aja shi da ƙarfi, idan kuma bakya so to sai na ƙyale ki, adunga miki kallon ƙazama, mummuna, kinga yanxu ma yanda kika fito fes dake ƴar ɗagwas ɗagwas kyakkyawa.

Ta ƙara zugata.

Washe baki Indo tayi tace.

” Wasa fah nake miki Mama, kedai ita jan gashin zanyi hkr, kuma wlh Mama yau har ƙunshi zanyi, a gidan Hajiya Innah ma zan kwana nayi ƙunshi na, mai shegen kyau, bari ma jummalo ta shigo na aiketa gidan su Zainabu ta siyo min gam ɗan yanka, ina zaki bani kuɗin koh Mama harda na kitson ma.

” Dole na mah kuwa, ai yau komai kike so zan baki shi cikin gidan nan, Hajiyar kyau.

Jummalo da ta shigo gidan ne, ta ga Indo anyi fes, sai faman tsifa suke yi, dariya ne yaso ƙwace mata, amma sanin Halin Indo da tayi kamar yunwar cikin ta yasata maida dariyar ta ciki, tasan tana dariyar nan, to yau kuma ta shiga Uku mai kwatarta hanun Indo sai Allah, ƙara sowa tayi wajen nasu tare da cewa.

” Ganan aiken naki nan, Mama wai inji innar talatun kuma, ki aiko da kuɗin dashen naki, harda na wancan satin.

” Kinga jummalo shiga ɗaki, cikin samira ta, na ukun nan akwai kuɗi ciki, ki ɗauko dubu ɗaya, ki kawai innar talatun, kixo ga ashirin ki karɓowa, Indo gam a wajen Goggo Hali.

Cikin mamaki Jummalo tace,

” Gam kuma Mama, me Indo kuma zatayi da gam, chap Abun mamaki, wai da gaske ƙunshin nan zakiyi ne.

Ko kafin Mama ta bawa jummalo Amsa Indo ta mayar mata da cewa.

” *Ubanki zanyi da Gam, kinji shegiya dai, har wani tambaya ta kike mai zanyi da gam har da wani mamakin ki, to kyau zan fuki dan uban………….*

Buge bakin Indo da Mama tayi ne ya hanata karasa maganar tata.

” Wai Indo me yasa baxa kiyi hankali bane, yanxu uban naku kike zagi dake ke baki da mutunci, kedai ba’a zama dake lfy wlh, sai kin nemo masifa, yanxu dan ta tambaye ki, shikenan sai ya zama laifi.

Tura baki Indo tayi tace.

” Tambayar Rainin wayo fah tamin, kuma na rantse da Allah, sai na yiwa jummalo shegen duka yau cikin gidan nan, badai kin daki baki na akanta ba.

Sake mata kai Mama tayi,tare da cewa.

” Tashi kije ki kashe ta, baki dake ta, ba tunda ke baki da mutunci, kuma naga wanda zai biya miki kuɗin gam ɗin dana kitson, marar mutunci.

Cikin Rau Rau da baki Indo tace.

” Idan kin hanani sai me, *ko a kwalar Rigata tunda Innah tana duniya ai dai baxan ga baƙin ciki ba, ehe*

Kan jummalo tayi da gudu yayin da itama jummalo tayi waje da gudu, Rufa mata baya Indo tayi, kira Mama take ƙwala musu, amma basu ma san tanayi ba.

A kofar gidan, Ɗan Birija, Indo ta ritsa jummalo da duka, sai kokuwa suke yayin da yara suka cika suna musu waƙa.

Jin hayaniya da Ɗan Birija yayi ne, ƙofar gidan sa, ya sashi fitowa, Indo ya gani tasa JUMMALO gaba sai duka take, kamar wacce ta samu jaka, kasancewar ƙarfin su ba ɗaya ba, ya indo tafi ƙarfin jummalo.

Da ƙyar Ɗan Birija ya ɓanɓare Jummalo daga hanun INDO, huci Indo take tana cewa.

” *Ko yanxu kinji A jikin ki, harda dukan Asarar kuɗin da Mama zata bani, kika min bakin ciki na miki, gobe ma ki sake shiga safga ta*.

Juyawa jummalo tayi tana zabgar kuka, ta koma gida, yayin da ita kuma Indo tayi hanyar gidan Hajiya Innah tana zagin ɗan birija ƙasa ƙasa, ya jita sarai amma ya ƙyaleta saboda yasan ba kunya gareta ba, ta basa Kunya cikin mutane ba abu bane mai wahala wajen ta.

” Innah !! Innah !! Innah !! Innah dai wai ina kika shiga, ina kiran ki, kinyi shuru, idan baxaki amsa ba, sai nayi tafiyata Wlh.

Innah da ta fito daga banɗaki ne, tace.

” To Uwar ƴan marassa hakuri, saboda ina tsoron ki, Uwata karki tsine min na shiga duniya, sai na taka dokar Ubangiji na amsa miki ina daga cikin banɗaki, Uwar ƴan mita.

” Mtss, wannan kuma matsalar kice, ni yanxu kuɗi zaki bani na tafi kitso gidan Laure kinga na yanke farce na, Idan na dawo daga kitson kuma zaki bani Lalle na ƙunsa.

” Muje ɗaki na baki, yau kuma aljanun tsafta ne, kenan suke kusa.

” Kinga Innah idan zaki bani ki bani, idan baxaki bani ba, shikenan, sai na haƙura, basai kin tsaya kina jero min magana ba.

“Muje nace ai na baki ko, Uwar marassa Kunya.

Tura baki Indo tayi, suka shiga, Innah ta bata ɗari ɗaya.

Ficewa Indo tayi tana cewa Innah sai na dawo.

Adawo lfy Innah ta mata, bayan fitar indon ne Innah tace.

” Ikon Allah yau kuma

A indon ta take, to Allah dai ya raba yaran gari da shiga gonar ki, dan Wlh yau duk Wanda ya shiga gonar ki yau baxai fito lfy ba.

*Dutse local government*

Sai wajen ƙarfe tara na dare, su mustapha suka shigo cikin gidan, tare da mahaifin nasu Alhaji Haruna.

Zubewa mustapha yayi saman kujera tare da cewa.

” Wash Allah Wlh yau na gaji Momy, kaina ke ciwo.

” Momy gaskiya Rayuwar ɗanki akwai gyara cikin ta, ace mutum shi a rayuwarsa baya ƙaunar Hayaniya, tun ɗaxu yake mita, cikin kasuwar nan.

Cewar Habeeb.

Daddy ne yayi murmurshi cikin ƙaunar yaran nasa, yace.

” A’a Habeeb bana son takura, kasan dai kowa da yanayin sa, dan haka karka takura min Yaro.

Dariya Mustapha yayi tare da cewa,

” Yawwa daddy gaya masa dai ko zai gane, tunda ya kasa fahimta ta, har yanzu.

Tsumewa Habeeb yayi, tare da tura baki yace.

” Na dai gane cikin gidan nan, ba’a sona anfi son mustapha, RAUDA kawai ke kulawa dani cikin gidan nan.

Dariya RAUDA tayi tana satar kallon Mustapha tace.

” Sannu da dawowa Daddy.

” Yawwa sannu RAUDA, ya kike jin zaman gidan namu, ina fatan dai baki da wata matsala, idan akwai kuma kiyi gaggawar sanar dani, domin magance miki shi.

Shuru RAUDA tayi tare da duban mustapha tana jin a cikin zuciyarta kamar ta sanar da daddy buƙatar ta, na son Auren Mustapha, sai dai kuma tana jin nauyin Daddy baxata iya sanar dashi wannan zancen ba.

” Babu wata matsala daddy, ina jin daɗin zaman cikin gidan nan sosai.

Alhamdulillah daddy yace, haka ake buƙata.

Kallon Momy yayi yace.

” A’ishah muje ki haɗa ruwan wanka ina son zan kwanta da wuri, bacci nake ji, kai kuma Habeeb, karka wuce DASINA ba tare da mun haɗu ba, saboda akwai saƙon da zan baka.

Da to Habeeb ya amsa sannan daddy suka haura sama shida Momy.

RAUDA ce tace.

” Ya Habeeb ganan abincin naka yana daining.

” Yawwa RAUDA na gode sosai bari na cika tunbi na kafin na haura sama, wannan bawan Allahn kan sunci abinci da Momy ta aika kasuwa, ya nuna Mustapha da hanu.

Taɓe bakin sa Mustapha yayi tare da cije lips ɗinsa, ya tashi yana ƙoƙarin haurawa sama, sai idon sa ya hango masa Sharifa tana zaune tasa, su ishaq da Sharif gaba sai buga games suke, tsawa ya daka masu.

” Keeeeeeee.

A gigice su Sharifa suka ɗago idon su, jin muryar Dodon nasu Mustapha, Uban ƴan takura, cewar Sharifa.

” Uban me kuke Anan, yanxu.

Shuru sukayi, suka kasa ce masa game suke yi.

Tsawa ya ƙara daka musu a karo na biyu.

” Ba magana nake muku bane kunyi min shuru.

Cikin rawar murya Sharifa tace.

” Game muke yi.

” Game kuke yi, ya maimaita maganar, amma me nace muku kuke yi daidai wannan lokaci?

” Karatun ƙur’ani ta mayar masa da Amsa.

” Okey shine saboda kun Raina ni, shine kuke Game koh.

” A’a yaya kayi hkr zamu ɗauko littafin yanxu muyi karatun baxamu sake ba.

Shigewa yayi yana cewa.

” Kuma sake kuga matakin da zan ɗauka a kanku cikin gidan nan.

Ajiyar Zuciya Sharifa ta sauke ganin sunsha, dariyar Habeeb taji a daining yana cewa.

” Barrister Mustapha babban yaya, Ango na RAUDA.

Murmurshi RAUDA tayi jin daɗin sunan da Habeeb ya kira, *ANGON RAUDA* Allah ya tabbatar da bakin ka, RAUDA ta ayyana a Zuciyarta.

Wayyo Allah sister’s kuyi hkr da wannan, Wlh naso nayi muku typing yafi haka yawa, sai dai uzuri sunyi min yawa yau akaina.

🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻ya Ubangiji ina roƙo gareka daka bayyana ƴar gidan Ladingo, wato Farisa, Allah kasa tana hanun na gari, ba mungu ba, Allah ka bayyana ta cikin gaggawa.

🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻

*Vote*

*Share*

*And*

*Comments*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah)*

[1/11, 3:49 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*

*Nasmah ko Nasirah*

*Sara da Sassaka*

*D̸͟͞E̸͟͞D̸͟͞I̸͟͞C̸͟͞A̸͟͞T̸͟͞E̸͟͞D̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty Fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba dake Adalci ga duk na ƙasa dake.

Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya🙏🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*

____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

*Ina ƙaunar ku masoyana*

Na gode sosai da ƙaunar ku gareni, kwana biyu kawai da banyi typing ba, kun damu sosai, har ta privet masoya ke min magana, wasu kam ma bansan group ɗinsu ba, gaskiya na gode sosai, hakan ya nuna min yanda kuke ƙaunar wannan book ɗin.

*P*•••••1️⃣5️⃣ ➡️ 1️⃣6️⃣

Yana shiga ɗakin nasa wanka ya faɗa, Bayan ya fito daga tollet ɗinne ya mulke fatar jikin sa, da mai da turare, sannan yasa gajeren wando Wato 3cutter da best sannan ne ya faɗa saman gadon sa, tare da jawo system ɗinsa, ya buɗe, yana jin shigowar, Habeeb bai ɗago kansa ba, shima dai Habeeb bai kulasa ba, saima shigewa wanka da yayi, bayan ya shirya ne, ya dawo saman gadon nasu ya faɗa, tare da rufewa, mustapha system ɗinsa, sai a lokacin mustapha ya ɗago ya kalle sa, yace.

” Ya haka Malam, da rufe min system?

” Saboda Magana nake so muyi dakai.

” Okey ina sauraron ka, Allah yasa mai amfani ce, nasan Halin ka, da zolaya, domin itace ɗabi’ar ka.

Murmurshi Habeeb yayi, tare da cewa.

” Wannan maganar mai muhimmanci ce, mustapha.

“Okey ina sauraron ka.

” meyasa kake nunawa kamar baka san RAUDA na Sonka ba? Wannan yarinyar fah tayi nisa a cikin Sonka, amma kai nunawa kake bakasan tanayi ba, Bayan kuma nasan Kasan tana Sonka, ka sani fah walaƙanta ɗan adam baida amfani duk mai Sonka yafi maƙiyin ka, ko yaya yake, komai kuma muninsa, bare kuma RAUDA bata da wani muni daga fuska har dirin jikin ta.

Why mustapha, Please Answer my Questions?

Cije lips ɗinsa yayi, wanda ya zama masa jiki a rayuwarsa, yana son cije lips ɗinsa, magana ya fara.

” Saboda bana sonta, bata min ba, nifa kaga RAUDA bata daga cikin kalar matar da nake bukatar aura, sannan kuma bata da aji tunda har zata iya furtawa namiji cewar, tana sonsa, mace mai aji neman ta, ake ace ana sonta ba, ita bace zata nema tace tana son.

Da kake maganar diri, koka manta da cewa shi so Babu ruwan sa, da kyau ko muni, idan kana son mutum baka ganin munin sa dan haka ni kyan mace ko munin ta, baya daga cikin ra’ayina nafi son mace mai kamun kai da nutsuwa tare da ilimin zamani dana Addini, idan har na samu mace mai wannan suffar komin munin ta, zan iya Auren ta, idan har ina sonta, sai amsar tambayar ka, ta ƙarshe itace, bani nace ta soni ba, bare kuma har tayi zurfi cikin soyayya ta, wannan damuwar tace ba tawa ba, idan kana tausayin ts mai zai hana kai ka Taimake ta, ka Aure ta, ai ina ga kamar Babu banbanci tsakanin mustapha da Habeeb, dukan su Abu ɗaya ne, kaga kuwa duk wanda yaso mustapha dole zaiso Habeeb, kodan tsantsar kaman dake tsakanin mu.

Murmurshi Habeeb yayi cikin jinjina tsatstsauran ra’ayi Irin na, Mustapha, shi wlh yana mungun tausayin RAUDA, domin kuwa yasan ba ƙaramin so take yiwa mustapha ba.

” Kai take so ba Habeeb ba, kamar muce kawai ɗaya, amma halayyar mu, ta banbanta, wata ƙil badan kyan fuskar ka take sonka ba, wata ƙil tana sonka dan wani abu dake tattare dakai may be yanayin kane yake burgeta, kokuma Halin ka, ko kuma haka kawai take sonka, amma tunda kace, Allah ya zaɓa muku Abunda yafi Alkairi.

Ameen Mustapha yace tare da jawo system ɗinsa ya buɗe, yana cewa Habeeb.

” Shiyasa fah jiya da kace muje gidan su, ka gaida Mamy nace maka baxan jeba, Saboda wannan shegiyar ƙanwar Tata mai shegen bakin tsiya, kana zuwa zata fara tambayar ka, ya soyayyar ka da RAUDA kamar ni nace mata ina soyayya da RAUDA.

Dariya Habeeb yayi yace.

” Ni kam ai zanje na gaishe ta, dole na, kodan yawan kira na da take a waya, tace min idan ta kira ka, baka dagawa sai kaga dama.

Dariya shima mustapha yayi, tare da cewa.

” Haka tace maka kenan, Duk kiran da zata min akan damuwar ƴarta ne, shiyasa ban damu da ɗaga kiran ta ba.

” Allah sarki Habeeb yace, tana taya ƴarta neman soyayyar kane, shiyasa, kasan uwa da tausayin ɗanta.

Ni ya maganar case ɗin khabeer da uwarsa Momy sarah ne, naji SADIQ yana cewa court ɗinku zai kai su?

Danni rabona da khabeer tun sanda yaje London kamo wani Alhaji.

Ɗago kansa Mustapha yayi, ya kalli Habeeb kafin yace.

” Wlh banda masaniya dan gaskiya na daɗe, rabona da khabeer, tun randa mukaje gaishe sa, daya kwanta rashin lfy, wajen shekara ɗaya kenan.

” Daman can ba shiri kuke ba, kaga bari na kwanta, dan mun daɗe muna hira har 12.

” Allah ya tashe mu, lfy nikam ba yanzu ba, sai na gama aiki na, akwai wani bincike da nake yi.

Itako RAUDA ta kwanta tayi lamo akan gado, ta rasa meke yiwa rayuwar ta daɗi, pic ɗin mustapha ta zubawa ido wanda ta tura a wayar Habeeb, ta daura kan wayar ta, wannan wacce irin soyayya ce nake maka Mustapha, soyayyar ka ta zama cuta ce a gare Ni, why !! why !! why baka sona, menene bandashi menene Aibu na, daka tsaneni haka, Allah ka sassauta min soyayyar mustapha cikin zuciyarta, ko zan samu sauƙin ciwon dake damuna cikin ƙirji na.

Ahaka bacci ɓarawo yayi nasarar capke RAUDA, cikin damuwar da take ciki na tsanar da mustapha ke gwada mata, inji ta da faɗa.

Washe gari da safe, momy ta riga kowa tashi kasancewar zata yiwa Daddy breakfast, zai fita kasuwa da wuri, a kitchen ɗin RAUDA da Sharifa suka taradda Momy, gaishe da Momy sukayi ta amsa tare da cewa.

” Sai yanxu kuka tashi kenan, dana biye ku, yau da saidai Daddyn ku, ya tafi kasuwa ba tare da yayi breakfast ba.

Murmushi RAUDA tayi tace.

” Ehh Wlh Momy, bayan nayi sallar Asuba ne bacci ya ɗauke Ni, kije ki zamu ƙarasa aikin, fita Momy tayi tana ce musu.

” Kudai yi da jikin ku, dan daddyn ku zai fita kasuwa yau da wuri.

Wajen wanke wanke Sharifa ta shige yayin da RAUDA ta tsaya kan girkin. Cikin 30 minute suka haɗa komai suka jera saman daining, Mustapha da Habeeb tare suka sauƙo, kafin Momy da daddy su fito suma.

Gabaki ɗayan su, a daining suka haɗu yayin da RAUDA tayi seving ɗin su, kafin RAUDA ta iso kan Mustapha, yayi saurin cewa, Sharifa tayi seving ɗinsa, ɗago kanta RAUDA tayi cikin jinjina irin ƙiyayyar da mustapha ke gwada mata, wato tsabar tsana, abincin ma, bazan zuba masa ba, duk motsin Mustapha akan idon RAUDA ne, yayin da shi kuma ko inda take bai kalla ba, bayan sun gama breakfast ɗin ne, RAUDA tacewa daddy,

” Daddy ina son Anjuma zan koma gidan mu.

Kafin Daddy yayi magana Momy ta rigasa ta hanyar Cewa.

” Zaki koma gida kuma RAUDA, keda kikace zakiyi mana sati biyu, kwatakwata fah kwanan ki biyar ne, shine kike zancen komawa gida, kodai akwai Abunda muke miki ne, idan akwai ki faɗa mana.

Cikowa idon RAUDA yayi da hawaye, ita har ga Allah babu wani Abunda suka mata, kawai gajiya tayi da kallon tsana da wulaƙanci da Mustapha ke mata, gara kawai ta koma gidan su, ko zata samu mafita wajen mahaifiyar ta.

” Babu Abunda aka mini Momy kawai dai zan koma gida ne.

” Kin tabbata Babu Abunda aka miki RAUDA, cewar daddy.

” Wlh Babu komai daddy kawai so nake na koma gida.

Ɗago kansa Habeeb yayi yana kallon RAUDA cikin tuhuma, kasancewar yasan dalilin daya sa, zata koma gida, sunkuyar da kanta ƙasa RAUDA tayi, ta ɗauke idon ta, daga na Habeeb, shi Kuma Mustapha yana jinsu, bai ɗago kansa ya kalle su ba, bare ma susa ran zaiyi magana, tashi yayi tare da cewa su Momy.

” Ni zan shige office, Habeeb ka gaida Hajiya Innah idan kaje, sai Allah yayi dawowar ka.

” Okey Babu damuwa zataji. Cewar Habeeb, amma baxaka tsaya mu fita tare ba.

” A’a hanyar mu ba ɗaya ba, kawai Allah ya kiyaye hanya.

Daddy ne, ya tsayar da mustapha ta hanyar cewa.

” Ka tsaya RAUDA ta shirya sai ka sauƙe ta, a gidan su, kafin ka shige office ɗin.

Ɓata ransa mustapha yayi, yace.

” Daddy ni na riga na shirya, zan shige office kuma sauri nake yi, tunda ga Habeeb zai fita bai shirya ba, idan yaso saita jirasa ya sauƙe ta.

Momy ce tace.

” Habeeb baxai sauƙe ta ba, kaiɗin kaine zaka sauƙe ta, ka zauna ka jira ta har ta shirya, sai ku fita tare.

” But amma Momy……

Ɗaga masa hanu Daddy yayi tare da cewa

” Ya isa ka zauna ka jirata, ke kuma RAUDA jeki shirya maza karki ɓata masa lokaci.

Tashi RAUDA tayi tare da haurawa sama yayin da Mustapha ya bita da kallon ƙiyayya, da kuma harara.

Ran Mustapha idan yayi dubu toya ɓaci, akan me za’a zaunar dashi ace dole saiya jira wannan abar, shiya kawota gidan ne, koko zaman sa take cikin gidan, Habeeb ne, yazo daidai kunnen sa ya sunkuya, tare da cewa.

” Ka zauna kayi jiran Amarya yaro, don naga alama momy na sonka da RAUDA, sai kayi hkr, ka zauna jira.

Yana gama fadar haka ya ɗaga kansa tare da haurawa sama, yana yiwa Mustapha dariyar mugunta, harara mustapha ya bi Habeeb dashi ba tare daya tanka masa ba.

Har Habeeb ya fito, Daddy ya basa saƙo wajen Mlm Musa da Hajiya Innah, tare suka fice da daddy suka bar Mustapha Zaune yana jiran RAUDA.

Momy ce ta tashi tare da cewa, bari na haura sama naga maiya tsayar da RAUDA haka tun ɗaxu.

Shidai Mustapha baice komai ba, yana Zaune cikin haɗa fuska, yana ganin RAUDA da Momy suna sauƙowa, ya ɗauko baƙin glass ya manna a idon sa, tare da ficewa waje, cikin motar ya shiga ya zauna jiran ta, har bakin motar Momy ta rako RAUDA, tana cewa.

” To RAUDA ki gaishe da Hajiya Turai ɗin kice Mata, ina zuwa nima insha Allah, Allah ya kiyaye hanya mun gode sosai.

” Zataji RAUDA tacewa Momy, sannan ta buɗe gaban motar ta shiga, jan motar mustapha yayi ba tare daya kalleta ba.

Ƙira’ar malam Ibrahim Abdulrasheed Mustapha ya kunna cikin wayar yana bi a hankali.

Muryar RAUDA yaji tana cewa.

” Ya mustapha meyasa baka sona, menene Aibuna, kasan irin soyayyar da nake maka kuwa…….?

” Enough RAUDA, bana buƙatar jin muryar ki, cikin motar nan.

” Saboda ka tsaneni baka sona koh, dole ai kace nayi shuru, wani irin tsanane wannan, kodan nace ina sonka shine kake wulakanta Ni.

Dariyar takaici Mustapha yayi, tare da yin wani wawan burki, cikin tsawa yace,

” Fita min daga cikin mota, ki fita min nace daga cikin mota, sau nawa zan faɗa miki cewa bana sonki, ko ana soyayyar dole ce, fice min daga cikin mota.

Murmurshi mai ciwo RAUDA tayi tare da sa hannun ta, ta buɗe motar ta fice, cikin tsanar Zuciyarta data ke son Mustapha.

Tsuka mai ƙarfi Mustapha yayi, sannan yaja motar sa, tare da bule RAUDA da ƙura, yayi gaba abunda.

Share guntun hawayen daya cika mata Ido tayi, tare da tare mai adaidaita sahu.

*DASINA*

A hankali INDO take tafiya, ita a dole tasha gayu, ansha lalle da kitso harda, wanka aka sha, tafiya take a hankali, wai zatayi tafiyar ƴan gayu, wani yaro ne ya taho da bokitin ƙullin koko, a kayin sa, sanda yazo daf da INDO cikin tsautsayi, yayi tuntuɓe da ƙaton dutse, sheƙowa ƙullin kokon yayi gaba ɗaya jikin Indo ya wanke mata jiki, tun daga kayi har ƙafifin ta.

” *Kutumar Uba* dan ubanka tsinanne, shine zaka min wanka da ƙullin koko, tsabar kana baƙin cikin nayi wanka, to wlh yau sai naci kutumar ubanka, shaƙo wuyan sa, Indo tayi, haba wa, sai kokuwa, dakuwa suke sosai yayin da yara suka taru a kansu suna rera musu waƙa

” *Ku tasu arna ku tasu ku tasu ba mai raba ku, kai mu raba ace munyi zamba, ku tasu arna, ku tasu dai ba mai raba ku*

Aiko kamar zuga Indo suke yi, ta dage sai jibgar juna suke.

Habeeb da shigowar sa kenan, cikin ƙauyen ya hango yara cike sai zabgar kokuwa ake, parking yayi, tare da fitowa daga cikin motar ya nufo wajen nasu.

” Kai baku da Hankali ne, kuke kokuwa.

Juyowa Indo tayi cikin masifa da rashin Kunya, wa zata gani idan ba Mustaphan ta ba, fit tayi shuru tare da sake yaron tana dariya, tace

” *Tafi abunka kaci albarkacin masoyina mustapha jeka na tafe maka ya Mustapha yaushe ka zoka sannu da zuwa kaga yanxun nan Innah ta shiga cikin gidan mu bari na kira maka ita*.

Zaro ido Habeeb yayi jin ta kirasa da mustapha, kuma masoyina, daga bayan sa yaji yara na cewa lallai yau tasi’u Allah ya ƙwace sa a hanun Indo.

” *INDO Habeeb ya furta sai kuma ya kwashe da dariya tuno labarin Indo da mustapha yake basa, Ashe Itace ALJANAR MUSTAPHA LALLAI BARRISTER MAI ƳAN MATA KALA KALA*.

__________________________

Bana typing Ranar asabar yauma ganin da nayi kwana biyu banyi typing ba, yasa na daure nayi muku🙏🏻

*Vote*

*Share*

*And*

*Comments*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah)*

[1/13, 3:29 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*

*Nasmah ko Nasirah*

*Sara da Sassaka*

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take a gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.

Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya🙏🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*

____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

*P*••••••1️⃣7️⃣ ➡️ 1️⃣8️⃣

Cikin dariya Habeeb yace wa Indo.

” To jeki kira Hajiyan, idan kin kirata sai ki wanke jikin ki koh, dan kin Zama dodo.

Sake baki Indo tayi tana kallon Habeeb cikin mamaki wai yau mustapha ne yake mata magana cikin sakewar fuska, mutumin da baya dariya, kullum cikin faɗa yake, ƙara leƙa fuskar tasa ta Indo tayi.

” Lafiya kike leƙen fuska ta, cewar Habeeb.

Wangale yellown hakwaren ta Indo tayi, tace wa Habeeb, gani nake kamar ba kai bane ya Mustapha, shifa ya Mustapha yana da faɗa kuma kullum cikin haɗewar rai yake, kai kuma naga kana dariya kuma baka faɗa.

Dariya Habeeb yayi Yace.

” Nine mana na sanja miki ne, Hajiya Indo.

” *Aradun Allah ya mustapha ka sauya kodai ka fara sona ne, yanda kake min murmurshin nan dafe ƙirjin ta Indo tayi tace har ji nake wasu kifiyoyin sonka na harbi na, a ƙirji na, Wayyo Allah Wlh ya Mustapha sonka yamin ɗaurin huhun goro ina sonka ya Mustapha na dan Allah kaima kace kana sona ko zanji daɗi*

Dariya sosai Indo ta bawa Habeeb dariya yake sosai, domin shi Wlh yarinyar ma, comedy ɗinta burgesa yake.

Cikin dariyar yace.

” Jeki ki kira Hajiyan ni na wuce, gidan nata idan mun sake haɗuwa zan gaya miki, motarsa ya koma yaja shi zuwa ƙofar gidan Innah.

Da gudu Indo ta shigo cikin gidan har tana tuntuɓe.

” Hajiya Innah !! Hajiya Innah.

Innah da suke zaune da Mama suna firar duniya, tace.

” Lafiya Indo kike min wannan kira kamar wacce kike bina bashi.

Mamace tace.

” Hajiya ai kinsan Halin Indo babu hankali sam a tare da ita, kullum cikin shashanci take, bata da nutsuwa sam.

Tura baki Indo tayi tare da ɗaukar bokiti, tayi wajen randa tana cewa.

” Ya mustapha ne, yaxo, shine yace na mishi kiran sa, idan kinga zaki iya zuwa kije idan kuma bazaki iya ba, Sai ki zauna ni dai wanka na zanyi naje *musha fira da masoyina*.

Salati Mama ta ɗauka tana cewa.

” Lallai Indo rashin kunyar taki ta shahara yanxu gaban mu kike kiran masoyi, Allah ya shirya ki, to waima ke a hakan za’a soki baki da hankali da nutsuwa, ga rashin mutunci, da fitsara, babu wanda baki iya ba, ciki, Babu mai sonki a haka.

Dariya Hajiya Innah tayi tana cewa.

” A’a maryama aiko INDO sai tafi ƴan matan garin nan farin jinin Samari kinga indodo na maza jeki kiyi wankan ki, rabu da maryama.

” Ai nima Innah yau banda lokacin ta, bare naji haushin zancen ta tunda ya Mustapha yamin dariya Kuma yace naxo zaice min yana sona.

Zaro ido Innah tayi tace mustaphan, ne yace miki haka, wannan ɗan bakin Halin tsiyar, ikon Allah, naga wata sabuwar yaudara gurin Muhammadu, anya ma kuwa mustapha ne, yaxo garin nan, gani nayi kwatakwata satin sa ɗaya da zuwa, amma ban sani ba ko ubansa Haruna ne ya aiko sa, maryama bari naje gidan na gani.

” To Innah na gode a huta gajiya.

Cewar Mama.

INDO kuwa wankan ta, ta shige tabar Mama zaune tsakar gida.

Da sallama Innah ta shiga cikin gidan Habeeb ta hango Zaune bakin ƙofar ɗakin ta, daga nesa itama INNAH tayi zaton mustapha ne, sanda ta ƙaraso daf dashi, taji Habeeb ya sureta yana hajijiya da ita, domin tasan shi kaɗai ne, mai mata wannan yahudancin, rufe idonta Innah tayi gam, tana zagin Habeeb.

” Ka sauƙe ni dan ubanka Haruna, kaji ɗan iskan Yaro zai ƙarasa ni.

Cikin dariya Habeeb ya sauƙe Innah tare da cewa.

” Missing ɗinki nayi fah Amarya ta, an juma ba’a haɗuba, yanxu na ganki kuma ai dole na juyaki.

Dariya Innah tayi tace.

” Ja’iri Habibu aini nasan babu mai min wannan iya shegen sai kai, yaushe ka dawo ƙasar, kullum saina tambayi Muhammadu, kai sai yace min ai baka da Ranar zuwa ɗan albarka Ashe kaine kake tafe, ni fah nayi mamaki da naji Indo tace min Muhammadu ne yaxo.

Dariya Habeeb yayi yace.

” Nine nan Innah nayi nayi mustapha mu taho tare wlh wannan bawan Allah yaƙi, wai ba yanxu ba, ko dai kina basa ciwon kaine Innah.

” Toni ina ruwa na, dashi idan yana soma karya ƙara zuwa waje na, daga nan har abada, dan ubansa.

Dariya Habeeb yayi Yace.

” Ni Babu ruwana a tsakanin ku, kunfi kusa, nine bare tsakanin ku, bari naje nayi wanka, akwai kaya cikin but ɗin mota, bari nayi wanka saina nemo yara su kwashe, yace akwai wanda za’a kai gidan Mlm Musa.

To saika fito cewar Innah, ɗakin da mustapha yake sauƙa inda yaxo garin shima Habeeb nan ya sauƙa.

Wanka Habeeb yayi tare da kwantawa baccin gajiya.

Wanka Indo tasha fes da ita, ta taho gidan Innah, Innah tana zaune tsakar ɗakinta Indo ta shigo tana leke leƙen ta ina zata ga mustapha, ɗakin Innah taxo ta zauna tare da cewa Innah, ina yaya Mustapha yake.

Dariya Innah tayi, tace.

” To shasha wannan ba Muhammadun bane, Habibu ne, ɗan uwan haihuwar sa, kamace kawai suke, sai banbancin hali da suke dashi.

” *Haba haba daman dai akwai walakin goro a miya, nidai nasan mustapha bai taɓa min dariya ba, wannan kuwa yana dariya, harma da kula mutum, kallon jikin ta, tayi yanda tasha wanka harda ɗige ɗige da tasha a fuskar ta, sai kuma tasa kuka 😩 tace yanxu kenan nayi wankan banxa, wlh danasani banyi wannan wankan ba*.

Dariya sosai Innah tayi tace.

” Yanxu ke INDO baza kiyi wanka danjin daɗin jikin kiba, sai dan wani, amma dai kinji kunya Wlh.

Ƙara sautin kukan ta Indo tayi, tsakanin ta da Allah take kuka tana yiwa Innah masifa, cikin ɗaga murya.

” *Ni ki ƙyaleni nayi kuka na, Wlh banyi niyan ƙara wanka ba, sai wani sati Ranar juma’a shine ya cuceni yasani nayi, har yasa naji kifiyar Son ya Mustapha ta sokeni ashe ba shi bane, Kuma wlh wankan Allah ya isa nayi, tunda banyi niya ba, kuma Innah kiga fah yanda na zage nayiwa fuska ta kwalliya, duk dan ya Mustapha yace nayi kyau*.

Habeeb da tun sanda yaji hayaniyar Indo ta hanasa bacci ya fito, ya tsaya gefe yana kallon shirmen Indo, shi Wlh burgesa take idan tana wasu abubuwan.

” To kukan ya isa haka.

Taji Muryar Habeeb daga bayan su.

Tsale Indo tayi ta diro gaban Habeeb tana ƙara sautin kukan ta, tana cewa.

” *Baxan yi shuru ba Wlh yau wuni zanyi ina kuka, kuma Na wuni ina zan Allah ya isa, dan ancuce ni Wlh.*

” 😆 Ikon Allah yau ni Habeeb ina ganin ikon Allah, to naji, idan kin wuni kina kuka ai kanki ma wuni zaiyi yana miki ciwo, to wai Allah ya isan wa kika jawa shi?.

” *Kai kai na jawa Wlh, tunda kaine kayi kama da ya Mustapha na, shine harda cemin kaine ya Mustapha, ashe ƙarya kake min, KUMA NA JAMAKA YASIN DOGUWA, MAI JAN WANDO KUMA BULLUƘUTU BAƘAR MUTUWA TSAKANINA DAKAI ARADUN ALLAH BAN YAFE BA*.

kaɗa kansa Habeeb yayi cikin jinjina yarintar Indo, Yace.

” Badai akan mustapha kike jamin Allah ya isa ba, to zo na miki hoto saina kai masa gida yaga wankan naki, ba shikenan ba.

Shuru Indo tayi tace.

” A shagon waye zamuyi photon shagon salisu zamuje.

” A’a a wayata zan ɗauke ki, wayar ya ciro daga cikin aljihun wandon sa, tare da cewa kin gani, fito waje na miki.

Tana washe bakin ta, Indo, Indo ta fito, Innah kuwa haɓa ta riƙe tana kallon rashin mutunci da Indo ke tsulawa, Habeeb ya yiwa indo pictures wajen kala Uku kafin ya mata da Innah, sai kuma sukayi sulfie shida INDO, suka zo sukayi su Uku harda Innah.

Cikin son zolayar mustapha Habeeb ya cewa Indo zo mamana, na miki video, ki faɗi saƙon ki, wajen masoyin naki, yana gani motsin bakin ki.

Zaro ido Indo tayi tace.

” Nice mamanka ƴar mitsitsiya dani, kai kuma ƙatoto dakai, nidai ka kira ni da indo na.

Dariya Habeeb yayi Yace.

” Nikam baxan kira sunan kiba, Saboda sunan mamana ke gare ki, idan kuma kince baxan kira ki da mamana ba, to na fasa miki video.

” Shikenan to na yadda, ka shirya na fara.

Dariya Habeeb yayi tare da saita Indo da wayarsa yana cewa ehh na shirya.

Gyaran murya Indo tayi sannan ta fara jero kalamai.

” *Assalamu alaikum yaya Mustapha ina kwana ya birni, da kuma mutanen cikin ta, yaya Mustapha yaushe zaka zo, Wlh nayi kewar ka, kuma gashi kullum kibiyar sonka harbi na, yake, ina sonka da yawa da yawa yaya Mustapha na, kaga wannan kwalliyar ma, kaine nayiwa, tana maganar tana fari da ido tare da washe haƙwara*

Dariya sosai Habeeb yasa sanda yake kallon videon, kafin ya bude data ya turawa mustapha su.

A wunin Ranar sabone sosai ya shiga tsakanin Indo da Habeeb.

Kusan tare suka wuni Habeeb na cin dariyar indo, tana basa labarin soyayyar da takewa mustapha, sam Habeeb bai nunawa INDO ƙyama ba, yanda kika san ƙanwar sa ta jini haka suke mu’amala da indo.

*Dutse local Government*

Da gudu RAUDA ta shigo cikin gidan nasu, shige Mamy tayi a falo tayi ɗakin ta, a saman gadon ta, ta zube tare da sakin wani marayan kuka, mai tsuma Zuciya.

Tana kukan mamy ta shigo cikin ɗakin, cikin tashin hankali, kusa da RAUDA ta zauna tare da ɗago kanta ta ɗaura bisa cinyar ta, tace

” RAUDA menene meya faru, wani Abu aka miki, kika shigo min gida haka.

Cikin matsanancin kuka, harda majina RAUDA tace.

” Ya mustapha ne, Mamy ya Mustapha baya sona, ya tsaneni mamy ƙirjina nauyi yake min, soyayyar ya Mustapha zata kasheni Mamy, ki taimake ni Mamy, Wlh idan ban Auri ya Mustapha ba mutuwa zanyi Mamy.

” Tsuka mai ƙarfi Mamy taja, tare da cewa.

” Haba RAUDA ke baki da wani aiki sai Mustapha Mustapha kullum ke kenan wannan sunan ne a bakin ki, waye ma mustapha me yake dashi da kika liƙe masa yana wulaƙanta ki, ga samarin da suka fi mustapha suna zuwa miki amma kinƙi sauraron su, meya fiki dashi da zai ke wulaƙanta ki, *kyau ya fiki Asali ko gata, ba komai ba laifin ki bane laifin wannan shegiyar Zuciyar taki ce, mai nacin tsiya, zanje na nemo miki soyayyar mustapha koda kuwa komai nawa zai ƙare, dole zanbi shawarar Habiba, zanje Niger wajen malamin nan, mustapha sai yayi dana sanin wulaƙanta ki a cikin rayuwar sa, Mu zuba mu gani, nida kai shege ka fasa, domin kuwa karen bana shike maganin zomon bana*

Kiyi hkr ki share hawayen ki, bari na ɗauki gyale na, naje gidan Hajiya Habiba mu tattauna.

Ɗagawa mamy kai kawai RAUDA tayi, Mamy na ficewa daga ɗakin RAUDA ta tashi taje gaban babban ilajimen ɗin mustapha dake maƙale a bangon ɗakin, ta tsaya tana magana kamar wacce take gaban sa.

” *Why mustapha why baka sona menene Aibuna, meyasa ka tsaneni, shin laifi ne danna soka, ko kuwa haramun ne, idan na soka,? tabbas nasan kasan zafin soyayyah, bai kamata ka Azabtar dani ba, kaji tausayi na, dan Allah ya Mustapha, ta ƙarasa maganar cikin kuka tare durƙushewa a wajen tana kukan hade da ajiyar zuciya*.

Shiko mustapha yana zaune cikin office ɗinsa hankali kwance yake harkokin sa, yama manta da wata RAUDA cikin rayuwar sa, zama yayi tare da kunna ƙira’ar Mlm Ibrahim Abdulrasheed, yana sauraro tare da bin karatun, cikin suratul Muminun.

Kamar wanda akace ya kunna datar sa, yana kunnawa saƙon Habeeb na shigowa.

Buɗe wa yayi, sai kuwa yaga pictures ɗin Indo guda Uku tare da video, da kamar bazai buɗe ba, sai kuma wata Zuciyar ta sashi buɗewa.

Duk tsare gidan mustapha da haɗe ransa sanda video nan ya basa dariya, sanda ya gama dariyar sa, sannan Yace.

” *Wannan kece mahaukaciyar kam cikakkiya ma, Habeeb kuma an haɗu da indo, lallai Innah kema kin shiga Uku da shiririta, HABEEB HABEEB mutum ya girma amma har yanzu baisan ya girma ba, ita kuma shasha, waini tayiwa kwalliya, koda yake ance idan baka da hankali ka aikata komai.*…………..

*YAWAN SHARHI YAWAN TYPING*

*Vote*

*Share*

*And*

*Comments*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah)*

[1/14, 3:19 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*

*Nasmah ko Nasirah*

*Sara da Sassaka*

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.

Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*

____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

*BANSO YIN MAGANA BA, AMMA DOLE SAI NAYI MAGANA, HABA ƳAN UWANA YA KAMATA KUKE YIWA WRITERS UZURI, IDAN HAR KIN BIYO WRITERS PRIVET KINCE TA TURO MIKI BOOK, BATA KULAKI BA KAMATA YAYI KI MATA UXIRI HAR ZUWA WASHE GARI, KIGA IDAN BATA KULAKI BA, BAREMA IRINA DA YAU DUK SAƘONNI NA A WAITING MESSAGE SUKA ZO MIN KAƊAN NE WANDA SUKA ZOMIN A BUƊE, KU DAINA KIRAN CEWA WANE NADA GIRMAN KAI DAN ALLAH.*

*DUK DA DAI BANI AKA ZAGA BA, AMMA DAI ƳAR UWATA CE WRITERS, KUMA ABUN YAMIN ZAFI, TAYA BAƘYA COMMENTS CIKIN GROUP ƊINTA, DAN TA CIREKI SAI YA ZAMA LAIFI ITA BATAJI GANDAN MIKI TYPING BA SAI KENE ZAKIJI GANDAN MATA COMMENT, TA CIREKI KUMA KIN BIYOTA PRIVET DA ZAGI, HAR KINA KIRAN CEWA, IDAN KINGA DAMA SAIKI MATA MUGUNTA KI ƁATA MATA SUNA.*

*KIJI TSORON ALLAH DOMIN KUWA BABU ABUNDA ZAKI IYA MATA, SAI DAI IDAN UBANGIJIN TANE YA ƘADDARA MATA DOMIN IDAN UBANGIJIN TA BAI YADDA BA BABU ABUNDA KE KIKA ISA KI MATA.*

*DUK WACCE NA ƁATAWA RAI SANADIN WANNAN MAGANA YAYI HKR 🙏🏻 NI DAI NA FAƊA NE DOMIN WACCE TAYI MAGANAR TASAN CEWA BABU MAI ƘADDARAWA MUTUM ABU SAI UBANGIJIN SA YA SO*

*P*••••••1️⃣9️⃣ ➡️ 2️⃣0️⃣

Hanun sa yasa da niyar goge video da pictures ɗin sai kuma yaji kira a wayar tasa.

daga kiran yayi tare da amsa Sallama.

Ya daɗe yana wayan kafin daga ƙarshe naji yana cewa, shikenan Abdul Babu damuwa sai kazo goben, yana gama wayar.

tana mutuwa Babu chage, tsuka yaja tare da tattara, kayan sa, ya kulle office ɗin, ya nufi motar sa, kasancewar lokacin tashin sa daga aikin yayi.

” Kinga sharifa tashi ki ajiye wannan wayar da tun ɗazu kika sata gaba kin kasa min Aikin komai, tunda shi girkin nayi, aikuma dai zaki samu ki min gyaran kitchen ɗin koh.

Ajiye wayar Sharifa tayi tana haɗa rai ta nufi kitchen ɗin, wayar ta Momy ta ɗaga tare da dannawa RAUDA kira, ringine ɗaya RAUDA ta ɗauka tare da cewa, barka da yamma Momy.

” Yawwa RAUDA Barka dai, ya naji Muryar ki, kamar wacce kikayi kuka.

Goge guntun hawayen ta RAUDA tayi tace.

” A’a Momy ba kuka nake ba, ina ga ko network ne yake rawa, dan nima haka nake jin muryar ki.

” Ayyah cewar Momy, ai network ɗin mtn sai a hankali, daman na kira naji kin koma gida lafiya ne.

Murmurshi RAUDA tayi cikin jin daɗin yanda Momy take sonta tace.

” Na koma lfy lau Momy, yanxu ma haka aiki nakewa Mamy ta fice unguwa.

” Ayyah to bari na ƙyaleki kiyi aikin ki, kya gaida Mamyn naku idan ta dawo.

” Zataji RAUDA tace tare da kashe wayar, sai kuma ta ƙara goge hawayen daya gangaro mata, sannan ta kira raihana ƴar aikin su, domin taya ta haɗa abinci a daining.

Har Mamy ta dawo babu walwala a fuskar RAUDA.

Dafa kafaɗar RAUDA Mamy tayi, tace

‘ ki kwantar da hankalin ki, insha Allah kin kusa samun mustapha a tafin hanun ki, munyi magana da Hajiya Habiba, tace bama sai naje ba, ita zataje mana chan Niger ɗin wajen malamin.

Gyaɗa kanta RAUDA tayi tace.

” Allah ya jiyar damu Alkairi, Mamy maganar kuɗin, wayar da nayiwa Abba har yanzu shuru yace zai baki ki bani, kuma naji shuru har yanzu.

” Cap kin ganni da shiririta ko, ya bani kuɗin nan fah, dubu ɗari, suna cikin dressing mirror na, kije ki ɗauka, ina gama wataƙil abban naku gobe ya dawo.

” Allah ya dawo dashi lfy, Sallah RAUDA ta shiga yi, yayin da itama Mamy tayi nata ɗakin.

Sanda ya tsaya yayi sallar magriba kafin ya shigo cikin gidan nasu, a falo ya taradda duka family na gidan har Daddy.

Gaishe dasu Daddyn yayi tare da ƙoƙarin haurawa sama, yaji Muryar Daddy ya kirasa.

Dawowa yayi tare da zama ƙasa gefen ƙafar Daddyn.

” Mustapha waiko ka manta da cewa kun girma ne, har yanzu banji kun fara maganar Aure ba, ya kamata kuma, yanxu haka kuna tare da iyalan ku fah, yanxu fah kuna da shekara 30 me kuke jira?

Shuru mustapha yayi kasancewar shi harga Allah yanxu Babu maganar Aure a gaban sa, baya kuma neman ƴar Kowa, bai kuma shiryawa aure ba yanxu.

Jin shurun yayi yawa ne yasa daddy cewa,

” Ya naji kayi shuru, ko bada kai nake magana bane.?

” Daddy kayi hkr, a yanxu kam gaskiya bana neman Aure, a ɗan ƙara mana lokaci, insha Allah ZAMU nema.

” Allahu yasha, dan ya kamata ku fara nema tun wuri, tashi Allah ya maka albarka.

” Ameen Daddy na gode.

Kallon Daddy Momy tayi tace,

” Alhaji ni Kuma ga wani shawara, me zai hana mu haɗa Auren yaron nan mustapha da RAUDA, kaga yarinyar tana da hankali, shikenan sai muyi tuwo na maina, hankali kwance, koya ka gani?.

” To A’ishah baxan ce miki a’a ba, amma gaskiya da hakan zata kasance sai nafi kowa farin ciki, sai dai kuma karki manta da cewa su yaran yanxu ba’a musu dole cikin al’amuran su, mu barsu idan akwai rabon Aure tsakanin su, Allah ya haɗa su, ni bana son takurawa yaro cikin lamarin sa.

Ɓata rai Momy tayi domin kuwa bata so haka ba, taso ne Daddy yabi bayan ta, sai kuma ya mata tozon raƙumi ya yasar da zancen ta gefe, shuru tayi bata ƙara cewa komai ba, domin kuwa tasan daddy kaifi ɗaya ne, baya magana biyu.

Ƙarfe takwas daidai mustapha ya sauƙo suka ci abinci bai wani juma ba ya koma ɗaki kasancewar yanda yake jin marar sa, na famar ƙulle masa, kwanciya yayi tare da yin shuru, tun marar tasa na masa kaɗan kaɗan har ta dawo tana masa ciwo sosai, muƙurƙuso kawai mustapha keyi saman gadon sa, domin yasan Halin ciwon nasa, Babu Abunda ke sasa wannan shegen ciwon sai munguwar sha’awar da yake da Ita, gashi yanxu ya kai matakin da bazai iya tashi ya ɗauko tablet ɗin dayake amfani dashi ba, riƙe marar yayi sosoi, yana jin wani mungun felling na taso masa babu Abunda yake buƙata yanxu irin yaji mace kusa dashi, gashi shi Allah yayi shi da kyankyamin tsiya, bazai iya kusantar matar da batasa ba, yana cikin wannan Halin Allah ya jefo Ishaq cikin ɗakin, da hanu mustapha ya masa alamar yaxo, tahowa Ishaq yayi da sauri wajen yayan nasa, a hankali Mustapha yake masa magana cewa ya buɗe drower akwai tablet yellow ya kawo masa tare da ruwa a prich.

Ɗaukowa Ishaq yayi ya basa, da ƙyar mustapha ya miƙe yasha maganin sannan ya koma ya kwanta, aikuwa bai juma da shan maganin ba, wani irin gumi ya yanko masa, duk jikin sa ya sake, a haka bacci ya ɗauke sa.

*DASINA*

Yau kwanan Habeeb huɗu a ƙauye dasina, sosai Kuma yake jin daɗin zaman garin, Zaune suke Shida Indo cikin gidan Hajiya Innah, tashi Habeeb yayi tare da nufar bishiyar maina dake tsakiyar gidan, hawa bishiyar yayi Yayin da Innah da indo suka zuba masa Ido, ƙaryo mainar yayi, sannan ya sauko yana gyara ta, sanda ya gyara ta, tsaf sannan ya kalli Indo yace.

” Ungo karbi.

Kallon sa, Indo tayi tace.

” Bangane ungo ba, me zanyi dashi kuma.

” Yawwa tambaya mai kyau, kinga dai na farko kince kina son Mustapha koh?

Gyaɗa kanta Indo tayi alamar ehh, harda ɗan murmurshin ta.

” Yawwa to kinga shi kuma mustapha yana son mace wacce haƙwaran ta, suke fari tas, kamar dai nawan nan, kinga ke Kuma naki hakwaren kin barsu sun ɓaci da datti, to shine naga cewa mai zai hana tunda nida ke, mun zama ƙawaye, na taimake ki, na taya ki, neman soyayyar mustapha, kuma ta yanda zamu fara dole sai mun fara da gyara ki tukunna, ki dinga wanka kina wanki kina goge haƙwaran ki, idan mustapha ya ganki fes, dole zai soki, kinga shi mace mai tsafta yake so, shiyasa ma, na ɓallo miki wannan iccen mainar dan ki fara goge bakin ki, kuma ba iya yau kawai zakiyi ba, kullum sai kinyi, ni Kuma na ɗau alƙawarin duk sanda na koma birni zan turo miki maclean da brush, wanda zaki dinga wanke haƙwaran ki dasu.

Kin yadda?

“Na yadda ai nasan kai kana sona baxaka cuceni ba, na yadda da kai fiye da yanda na yadda da Innah.

Harara Innah ta dokawa Indo tace.

” Kuji ja’irar yarinya, yo to ni ina ruwana dake, balle kuma yardar ki, shima Habibun wuyar sa, kukai Anjuma ne, sai an jiku a rana.

Dariya Habeeb yayi tare da cewa.

“Kinga rabu da Hajiya karɓi, ki fara goge bakin, ki goge fah sosai.

Karɓa Indo tayi ta tauna sannan ta fara dirjan bakin ta, dashi, sosai ta dage take goge haƙwaran ta, har jini suke tana goge, sanda ta fara jin zafi tayi wurgi da magogin gefe tace.

” *Kan bala’i Wlh ya Habibu kai mungu ne, kaji yanda bakina ke min zafi, kuma kasan yana zafin tsabar baƙar mugunta shine zaka bani kace na goge baki, to aradu baxan goge ba*.

Haɗa Ransa Habeeb yayi sannan yace.

” Nine mungun koh, shikenan na gode, daga yau kuma Babu ruwana dake, baxan ƙara taimakon kiba akan mustapha, daman akwai wacce take sonshi a can birni, kinga shikenan idan yaga ta fiki gaye da haɗuwa, mai fararen haƙware, tas tas dasu, sai ya sota, shikenan ke kuma kin tashi a *TUTAR BABU YA MANTA DA WATA INDO MA A DUNIYA, NI KUMA INA CAN INA WAJEN AIKINA BAZAMA KI GANNI BA, BARE MA KICE NA TAIMAKA MIKI* .

Zabura Indo tayi cikin masifa da bala’i ta miƙe tsaye tayo kan Habeeb tana cewa.

” *Ita yarinyar taci ubanta, kaji shegiya wai ya Mustapha take so, to Wlh ƙarya take ya Mustapha ƙwalelenta, yafi ƙarfin ta ya Mustapha na Indo ce, ita ɗaya, YASIN NASHA RUWAN ARADU DUK SANDA ALLAH YA HAƊANI DA ITA SAI NACI KUTUMAR UBANTA, SAITA GWAMMACE KIƊA DA KARATU, KAIMA HAR WANI MAIMATA WA KAKE KAMAR WANDA KA FAƊI ABUN ARZIKI, TO YASIN NA HAƊU DA ITA SAINA SANJA MATA KAMMANI, KAN UBAN CAN WAI YAYA MUSTAPHA NA, TAKE SO, LALLAI KAM, SANNU SARAN MAI BAƘAR TA KASHI GATA BULU GATA JAJA, SHEGIYA, KAWAI*.

Sunkuyawa tayi ta ɗauko magogin tace, badai kan goge baki bane, *TO YASIN INDAN NA FARA GOGE BAKI NA, SAI YAFI NAKA HASKE, TA ƘARASA MAGANAR DA HARARAR HABEEB TAYI ƊAKIN INNAH TANA GOGE BAKIN*.

Dariya ce ta kwacewa Habeeb ganin yanda Indo ta taso kansa da Bala’i kamar shine yace yana son Mustaphan.

Kallon Innah yayi yace Hajiya.

” Lallai kuna fama da indo cikin garin nan.

Dariya Innah tayi tace.

” Wai damma kwanan nan bata ɗebo magana, amma ai Indo Rana ɗaɗɗaya ne, bata jawowa iyayen magana da zagi a cikin gari, amma naga kai yanxu kana iyawa da Ita.

Dariya Habeeb keyi, yaji wayar sa, na ringine, Bros ya gani manne a jikin screen ɗin wayar dariya Habeeb yayi ya ɗaga tare da cewa.

” Allah ya taimaki Barrister sai yau aka ga sakon nawa ne.

Murmurshi Mustapha yayi daga can Yace.

” Badai kaje ka zaune wajen Hajiya ka manta da muba, kodai mu biyoka da sauran kayan kane.

Dariya Habeeb yayi tare da cewa.

“A’a kuyi hkr ba sai kun biyoni dashi ba zan dawo, jiya da daddare munyi waya ai da daddy, har ya bawa Momy wayar.

Sai yanxu mustapha yayi dariya yace.

” Ya sanar dakai kenan.

” Meya sanar dani, ni babu wani Abunda ya sanar dani, taɗin duniya kawai mukayi ya kashe wayar sa.

” Cewa yayi ya fara gajiya da mu, ya kamata mu nemo matan Aure.

Dariya sosai Habeeb yayi sannan Yace.

” Nine dai ya kamata na nemo matar aure ba kai ba, kai kam ai kana dasu, ko baka zaɓi sauran ba, ya kamata ka zaɓa cikin *RAUDA DA INDO, kaga daman kullum cikin felling kake, shikenan saika huta da shan tablet*.

Tsuka Mustapha yaja tare da cewa.

Daɗi na dakai kenan ba’a maganar arziki dakai, kaika sansu har kake tunawa dasu cikin rayuwar ka, kaga ni sai Anjuma ma.

Dariya Habeeb keyi yace.

” Allah ya huci Zuciyar ka, ga Innah zakuyi magana.

Da gudu ya ƙarasa ɗakin Innah ya ɗaura wayar kunnen Indo, cikin raɗa yanda mustapha bazai jiba, yace kiyi magana mustapha ne.

Cikin ɗoki da murna indo ta ƙankame wayar tare da cewa……………..

*Vote*

*Share*

*And*

*Comments*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah)*

[1/17, 6:16 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*

*Nasmah ko Nasirah*

*Sara da Sassaka*

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.

Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*

____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

*P*•••••••2️⃣1️⃣ ➡️ 2️⃣2️⃣

” *Wayyo Allah daɗi kashe ni, ya Mustapha na, Aradun Allah ina sonka, kibiyar sonka ta soke ni, kaji wani irin daɗin da naji kuwa da ya Habibu yace ga mustapha na*.

Jin shurun da tayi ne, yasata kallon Habeeb tace.

Ya Habibu banji yayi magana ba, fah.

Mustapha bai kashe wayar ba, shuru yayi yana jin su, domin kuwa yana jin sanda Habeeb yake, cewa Indo gashi mustapha ne kiyi Magana, shiyasa yayi shuru ba tare daya kashe wayar ba, yana jiran Habeeb ne ya karɓi wayar ya masa rashin mutunci.

Karɓar wayar Habeeb yayi tare da dubawa, cikin mamakin ganin mustapha bai kashe wayar ba, kuma bayan yaji Muryar Indo, sa wayar yayi a kunnen sa, tare da cewa.

” Bros ya kuma kayi shuru kana jin masoyiyar ka, tana sanar dakai yanda kifiyar sonka yake sukan ta kayi mata banxa.

Murmurshi mustapha Yayi cikin jin takaicin yawan wasan Habeeb, shi dai komai zai iya yiwa mutum wasa akansa, koda kuwa mutum yana cikin Halin da baya buƙatar wasa.

” Hmm to Uban ƴan neman magana, naji sai kuma akayi yaya, Sarkin ƴan neman magana na duniya, Kuma bari kaji na sanar dakai daga yau baxan ƙara neman ka a waya ba, har sai kabar wannan ƙauyen, Kuma karka Ƙara nema na, dan ko ka kira baxan ɗaga ba, tunda kaima kana son biye wannan shashashar ku zama iri ɗaya.

Murmurshi Habeeb yayi, cikin serious ya cewa mustapha.

” Bros naji abunda ka faɗa min kuma na ƴarda, sai dai ina son kasan Wani Abu guda ɗaya, kallon Indo yayi da ta mayar da hankalin ta wajen sa, ficewa yayi daga ɗakin Innah yayi nasa yana cewa.

*Duk yanda mutum yake, bai kamata ka wulaƙanta shiba, domin kuwa, gobe baka san mai zai zama ba, sannan aini a tunanina, shi mai Sonka yafi maƙiyin ka, kuma bai cancanci wulaƙanci daga gare kaba, Amma kai Bros……..*

” Enough Habeeb bana buƙatar wani magana daga gare ka, cikin tsawa yace, *akan me zaka bawa wannan shashashar Iblis ɗin wayata, yarinyar data gagari Uban kowa cikin wannan ƙauyen, ƙazama marar Hankali da lissafi, idan har kaima ka koma shashasha, toni ban koma ba, da nawa hankalin a jiki na*

Yana gama faɗin haka ya kashe wayar.

Zuciyar Habeeb idan tayi dubu to, ta ɓaci domin kuwa yaji zafin maganar da mustapha ya faɗa masa, duk da yasan halin zafin zuciyar mustapha, zai iya yiwa kowa ihu idan ranshi ya ɓaci, sai dai baiyi tunanin, dan ya bawa Indo waya, ranshi zai ɓaci haka ba.

Shigowar Indo ne, ya katse masa maganar zucin daya ke yi.

” Ya Habibu ya kuma ka tafi baka bani wayar munyi magana da shiba, kuma har nasa raina zanji Muryar yaya Mustapha na, tana maganar ne tana tura baki.

Murmurshi Habeeb yayi tare da cewa.

” Babu network ne, shiyasa wayar ta tsinke, Amma ki bari sai gobe, idan ya sake kira sai na haɗaa ku.

Tsumewa Indo tayi, tana murguɗe murguɗen baki, tace.

” Nidai Wlh ya Habibu ban yadda ba, ai naji kuna magana dashi yanxu, shine ka gudo nan dan karka bani muyi magana, toni ban yadda ba, sai dai ka kira min shi yanxu ko Kuma kayi min video Irin na ranan sai ka kai masa tunda kace gobe zaka koma birni, idan kuma kaƙi min to Wlh *ALLAH YA ISA BAN YAFE BA JAMIN RAI DA KAYI*.

Haɗa Ransa Habeeb yayi, ya gallawa ya Indo harara, tare da cewa.

” Wato dai ke Indo baki da kunya, ni kika jawa Allah ya isa koh, ban girme ki bane da zaki jamin Allah ya isa, kamar wani sa’an ki, dan kinga ina kulaki koh, shine zaki zageni, Babu laifi nane da nake kulaki, shi mustapha ai da Baya kulaki baki zagesa ba sai Ni, ya karasa maganar cikin, haɗa fuska.

Duk tsiyar Indo da iya shegen ta, sanda taji jikin ta, yayi sanyi, karo na farko da taji tayiwa wani rashin kyautawa, har taji tayi danasani, shuru tayi tare da cewa.

” *KAYI HKR DAN ALLAH BAZAN SAKE BA*.

Ƙin kulata Habeeb yayi, ya kuma kawar da kansa gefe, yace.

” Ki tashi ki fita ki bar min ɗaki na.

Zama Indo tayi daɓas gaban Habeeb tana masa magiya kan yayi hkr, amma ina Habeeb ko kallon ta baiyi ba, bare tasa ran zai kulata.

To fah Indo ta fara ƙula, ganin yanda take bawa Habeeb hkr amma yaƙi kulata, cikin jin haushi tace.

” *Shikenan to, tunda baza kayi hkr ba, inata baka hkr kaki kulani dan ma ka samu na baka hkr, Aradun Allah ban taɓa bawa Kowa hkr ba, har Mama, sai kai Kuma kace baxa kayi hkr ba, sai Kuma ta fashe da kuka tana Cewa, shikenan tunda kaƙi kulani kuma wlh baxan bar nan ba, ina Zaune har sai kace kayi hkr, da makarantar Allo zan tafi, Kuma na fasa zuwa tunda baxa kayi hakuri ba, tana kukan ne take wannan maganar*.

Dariya Habeeb yayi cikin jinjina yarintar Indo, yama rasa dame zai fassara, wannan hali na Indo, da yarintar zai kirasa ko kuma da me zai kira, tunda dai yanxu Indo zatayi shekara goma a duniya, kamar dai ta wuce a kira shi da yarinta, ya kuma fuskanci yarinyar tana da sauƙin kai, idan zaka bita a hankali, tana kuma da fahimta, ya fuskanci Indo tana son mai kulawa da lamarin ta, tunda gashi yanxu har hkr take basa, da ace ni mazaunin kasar nan ne, to tabbas zan iya sauyawa Indo halayyar ta, kuma yarinyar da zata gyaru cikakkiyar mace za’a tayar, murmurshi Habeeb yayi, sannan yaci gaba da maganar zucin sa, zan nemi transfer daga London zuwa ƙasata ta Nigeria, duk wani weekend zan dinga yinsa cikin wannan ƙauyen, domin ganin na inganta rayuwar wannan yarinyar da ake ganin tafi ƙarfin kowa, domin kuwa *BABU GAGARARRE SAI BARARRE DA KUMA WANNAN YARINYAR INDO ZAN NUNAWA MUSTAPHA KUSKUREN SA NA RAINA ƊAN ADAM* .

READ:   Matar Lameer - Complete Hausa Novel

Kallon sa ya mayar kan Indo yace.

” To tashi nayi hkr, maza kije ki tafi makaranta, idan kin dawo sai muyi video koh.

Mai kuka ce, ta dawo dariya, tashi tayi tana dariya tace.

” Yauwa yaya Habibu ko kai fah, a dai afuwa yana da daɗi, ni videon ma na fasa, bari naje na dawo ka kunna min kallo nayi a wayar ka.

Dariya Habeeb yayi sannan yace.

” Amma dai kije kiyi wanka tukunna, kuma kinga wannan aswakin, ki barsa a bakin ki, kina gogewa har ki dawo.

” *Na shiga Uku ya Habibu wanka Kuma, Ranar da kaxo fah nayi, nidai gaskiya baxanyi wanka ba sai Ranar juma’a*.

” Innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un yanxu Indo wankan ne, kike yinsa sati sati, Haba, ashe dai gaskiyar mustapha ne, da yace min, abunda yasa baya sonki ke ƙazama ce, kuma bakya jin magana, ashe da gaske yake, tunda yanxu maganar sa, ta zamo gaskiya, kinga Babu ruwana baxan ƙara cewa ya Aure kiba, tunda kinga ita wacce na gaya miki tana sonsa ƴar gaye ne, Kuma kullum sau biyu take wanka, to kinga mai zaiyi dake, mai wanka sati sati, ga mai yin wanka biyu kullum.

Haɗa ranta tamau Indo tayi, shi kansa Habeeb haushin sa, take ji, idan taji ya ambaci sunan wata tana son mustapha, cikin jin haushi tace.

” *YA HABIBU DAN ALLAH NA ROƘE KA*.

Kunshe dariyar sa Habeeb yayi domin kuwa ya harbo jirgin Indo, indai kana son tayi abu cikin gaggawa to kace mata budurwar mustapha ta birni nayi, to yanxu zatace sai tayi wanda yafi nata, kuma daman dan tayi wankan ya mata haka.

” Umhum ina jinki roke ni.

” *DAN GIRMAN ALLAH DAN ANNABI MUHAMMAD (SAW) KA DAINA CEWA WATA TANA SON YA MUSTAPHA, KAGA KAIMA FAH HAR KASA NAJI HAUSHIN KA, SAURA MA KAƊAN NACE MAKA ALLAH YA ISA HAUSHIN DA KASA NAJI, KUMA SAI NA FASA CE MAKA ALLAH YA ISAN, AMMA YANXU ZANJE NAYI WANKAN INA DAI SHIKENAN KOH MAGANA TA ƘARE*

” Dariya Habeeb yayi yace to karya nayi baida budurwar ne, ke dai kawai ki dage, ki fita wanka da wanke baki, ko zamu samu mustapha ya soki.

Magana Indo zatayi Habeeb ya yace Mata.

” Shit maza jeki kiyi shirin makaranta, kar lokaci ya ƙure.

Shigewa Indo tayi, sanda taxo daf da Innah ta sunkuya gaban ta, tare da cewa.

” Allah ya turo miki da malakul maut, ya ɗauke ki mu huta, ni yanxu na gaji da ganin ki, ni bani ashirin nayi kuɗin tara.

Tashi Innah tayi tare da ɗaukar Salati.

” Innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un yanxu Indo mena tare miki cikin wannan Duniyar, da kike neman Rayuwata, shikenan ni kuma yau baxanyi bacci ba, yarinyar nan tamin baki, nama isa na sake baki ina bacci na jini cikin barzahu, shegiyar yarinya, ja’ira, to bazan mutu ba, yanxu dan ubanki Musa sai naga mutuwar iyayen ki, naga taki naga ta jikokin ki, shegiya mai mungun baki.

Habeeb jin mitar Innah daya sashi fitowa ne, ya tsaya yana cin dariyar ta, Innah da tsoron mutuwar ta.

Ita kuwa Indo, dariya tayi tace.

” Hajiya Innah ina ma zaki ga ƴaƴana bare kuma jikokina, ai kafin nan kin daɗe a lahira, ni ki bani kuɗin na tafi, kar kisa nayi latti.

” Bazan bayar ba, kixo ki ƙwata dan uwarki, a hakan zan baki kuɗina kina neman Rayuwata, to bazan bayar ba.

Ganin da Habeeb yayi, Indo da Innah zasu iya kaiwa magaruba, suna wannan faɗan bai damesu ba, yasa Habeeb Ciro kuɗi Naira dubu dubu ce,a jikin sa, ɗaya ya ɗauko ya cewa, Indo gashi karɓi maza kije kiyi sanji ki ɗauki, hamsin ki dawo min da sanji na, karfa ki hallaka kuɗin nan duka.

Zuwa Indo tayi ta karɓa tare da cewa, yanxu ma zan kawo maka sanjin ka, kafin na wuce makarantar.

Kallon Innah tayi tace, ke Kuma, yau ki jira zuwan malakul maut, dan sai kin mutu mutum ya tsufa ya tsofe amma bai son mutuwa, kuma mutuwa dole ce a kanki, .

” Sai kixo ki kasheni ai dan uwarki, sai kici kanki ai mayya kawai.

Dariya Habeeb yayi, kawai tare da shigewa ɗakin sa.

Daddare hira sosai Indo da Habeeb suka sha, dan tun zuwan Habeeb mutanen gari suka samu sauƙi wajen Indo, wani sa’in wuni guda zatayi bata fito waje ba, tana maƙale gidan Innah tare da Habeeb.

Innah kuwa yau taki kula Indo, haka itama Indo bata kula Innah ba.

Tsakar dare gari yayi shuru, kowa yayi bacci babu Abunda akeji sai kukan tsuntsaye, Indo dake kwance ɗakin Innah ta tashi tare da ɗauko farin yadin da ta sayo da kuɗin da Habeeb ya bata, dan ƙin kai masa sanji Indo tayi, shima kuma ya manta da ya bata kuɗin, ware yadin Indo tayi tare da rufawa a jikin ta, tayi wajen gadon Innah, sanja Murya Indo tare da taɓa Innah, tashi Innah tayi, haba wa Innah tana buɗe Ido taci karo da mutum lulluɓe da farin yaji, baya Innah taja tare da cewa.

” Waye ne?

Wata irin murya Indo tayi tace.

” Nine mala’ikan mutuwa naxo ne na ɗauki ranki, cikin Aminci, dan haka ki kwantar da hankalin ki.

Rawa jikin Innah ya fara, ja da baya take tana magana da karfi tana cewa.

” Wallahi bani bace wacce zaku ɗauki ranta, wayyo Allah, dan Allah mala’ika ka barni na ɗan kara kwanaki a duniya.

Duk ta gigice ta fita hankalin ta.

Habeeb dake kwance ne yaji ihun Innah ya fito da gudu, cikin tsoron ko wani abune ya sami Innah.

Yana shiga ɗakin yaga Innah takure a gefe sai rawa jikin ta, keyi, haskawa Habeeb yayi da wayar sa, daga ƙafifin ta, ya gane Indo ce, baiyi magana ba, cikin tsabar haushin Indo, saima ɗauketa da wasu tagwayen maruka da yayi tare da nuna ta da yatsa yace

Kuyi haƙuri da wannan wlh naso nayi muku typing yafi haka, sai dai kuma yau muna biki ne, na sister na, kuma wlh bawai ina jin daɗin jiki na bane, mu haɗu daku next page, Ranar Lahadi, in Allah ya kaimu, dan gaskiya bana typing Ranar Asabar.

Gashi yau naso na dawo har cikin dutse, domin ganin halin dasu RAUDA suke ciki, amma ba damuwa mu haɗu next page, tunda Indo ta cinye wannan page d’in ita kaɗai.😄😄😄😄

*Vote*

*Share*

*And*

*Comments*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻

*(Ummu Nasmah ce)*

[1/20, 4:14 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*

*Nasmah ko Nasirah*

*Sara da Sassaka*

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.

Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*

____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

*P*•••••2️⃣3️⃣ ➡️ 2️⃣4️⃣

“kin san me kika aikata kuwa, ki duba kiga yanda jikin wannan baiwar Allah ke rawa, ko kin manta da cewa tana da Hawan jini, so kike ki kasheta, idan mala’ikan bai kasheta ba, aike zaki kasheta, wani irin haline dake wannan, da baki san Wanda ke miki Alkairi ba, tsuka yaja tare da juyawa yayi kan Innah, gani yayi jikin Innah ya sake, da sauri ya kai kunnen sa kan ƙirjin Innah, ajiyar zuciya ya sauƙe jin suma tayi, juyowa yayi ya finciko Indo gaban Innah, Yace, gashi kin kasheta ai kin huta, shikenan Hankalin ki ya kwanta.

Zaro ido Indo tayi, sai kuma ta fashe da kuka, tana Cewa.

” Innah ki tashi dan Allah karki mutu, Wlh wasa nake miki, ya Habibu ka tashe ta dan Allah, wayyo Allah na shiga Uku na kashe Innah, shikenan yau kuma ni Indo na shiga Uku, sai kuma ta zauna daɓas a ƙasa, tana cewa,

*Shikenan Babu ni Babu cin taliyar turawa tunda Innah ta mutu, Babu mai bani kuɗin kashewa na jawa kaina Asara, ni Wlh da akwai mai maye mini gurbin Innah bazan yi wannan kukan ba, wayyo Allah na, taliya ta kam shik………*

Tsawa Habeeb ya daka mata tare da cewa.

” Rufe min baki, dallah dame zanji da ita Innah zanji koda masifar kukan ki, na banxa.

Shuru Indo tayi tare da gallawa Habeeb harara, sai kuma ta tashi ta koma gefe ta zauna, tare da tsurawa Habeeb ido daya ɗauki ruwa yayi kan Innah.

Yayyafawa Innah ruwa Habeeb yayi, kafin Innah taja numfashi mai nauyi, a firgice ta farka tana kalle kalle.

Tausayi Innah ta bawa Habeeb gani yanda take leƙe leƙen cikin ɗakin, cikin taushin murya Habeeb yake ce mata.

” Ki kwantar da hankalin ki, Innah mafarki fa kikayi, ba wani mala’ikan mutuwa daya zo cikin ɗakin nan, ki daina razana dan Allah.

Cikin rawar murya Innah ke cewa.

” Wlh Habibu ba mafarki nake ba, na ganshi cikin ɗakin nan, yace raina zai ɗauka, kuma Wlh bana son na mutu yanxu, ka tashi kawai Habibu mubar gidan nan, nikam na yafe zaman gidan nan.

Ikon Allah cewar Habeeb.

” Haba Innah nace miki mafarki kikayi ko, ga car INDO ki tambaye ta, kiji, itama ihun da kike cikin Bacci ya sata tashi, kinganta can kinsa itama ta kasa bacci kiyi addu’a ki kwanta ta ɓangaren daman ki, babu wani mafarki da zaki ƙara yi.

Saurin kallon Habeeb Indo tayi ganin ya ɓoyewa Innah cewa itace ta mata wannan aikin, sai kuma ta sunkuyar da kanta, ƙasa tuno yanda jikin Innah yake rawa, tana kokarin maida dariyar ta, cikin ta, kar Habeeb ya ƙara jin haushin ta.

” Shikenan Habibu, Indo kixo mu kwanta, amma dai nasan Baccin yau kam na rasashi dan ba iyawa zanyi ba, karna kwanta na ƙara wannan mungun mafarkin.

” Yawwa to ko kefa Innah, kwanta itama Indo zata zo ta kwanta yanxu.

Bayan Innah ta kwanta ne, Habeeb yayi, wajen Indo tare da sunkuyawa daidai kunnen ta, yace.

” Na rantse da Allah kika ƙara tsorata tsohuwar nan, Wlh !! Wlh !! Wlh, kema yau tsakar gida zan wurga ki, na rufewa Innah ƙofar ɗakin ta, naga keda ita wa zai fara mutuwa yau ko kuma naga wanda zaifi wani jikkatuwa tsakanin ku, tunda ke, baki da mutunci.

Tashi kije ku kwanta.

Tura bakin ta Indo tayi ba tare data maidawa Habeeb Amsa ba tana hararar sa ta ƙasan ido, gadon Innah tayi tare da cewa.

” Matsamin na kwanta kuma wlh karki matseni, kuma banda gwarti, dan kina hanani bacci ehe.

Ita dai Innah bata tankawa Indo ba, dan yanxu bata da lokacin faɗa da indo a halin da take ciki, haka suka kwana har gari ya waye ba tare da Innah ta runtsa ba, idonta biyu har garin Allah ya waye.

Da safe Innah ta aika Indo gidan talatu mai ƙosai siyo musu na karin kumallo, karɓa Indo tayi tana kallon Innah tana dariya ta fice daga cikin gidan.

Ita dai Innah taƙi biyewa Indo yau, bare suyi ɗan Halin da suka saba.

Gidan ƙosan cike yake da yara, kowa na jiran layi, itama Indo ajiye kwanon layin tayi, tare da samun gefe ɗaya ta zauna, kokuwa ne ya tirke tsakanin mariya da Garba, yayin da garba yafi jibgar mariya, anko rabasu garba yaƙi rabuwa, shiga mai taurin kan tsiya, haushin yanda garba ke dukan mariya ne, ya kama Indo, ta tashi taje tsakiyar su, tace.

” Kai garba na sayi faɗan, rabu da ita mu gwabza dani naga jarumtar taka, ɗan mai taurin kan tsiya ka dage sai jibgar ta, kake dan kaga kafi ƙarfin ta.

Sakin mariya Garba yayi yana kallon Indo cikin dariya yace.

” Wanda suka fiki ma na gwabza dasu basu share ba bare kuma ke, idan kin shirya shigo mu fara kiga yanda zanyi dake, idan kina dukan wasu ki share to yau kam kin shigo hanuna, za kuma kiga yanda zaki sha wahala.

” *Dariya Indo tayi tare da sunkuyawa ƙasa ta ɗebo ƙasa, a duka tafukan hannun ta, ta buɗewa Garba tace, ƊAUKI ƊAYA, GANA MASIFA GANA BALA’I, ZAƁI DA WANNE ZAMU GWABZA*.

Na bala’in garba ya ture, ai kuwa take kokuwa ya kaure tsakanin Garba da indo, inda faɗa ya juya salo, ya zamana yanxu Indo ce, ke jibgar Garba, saɓanin ɗazu da garba ke jibgar mariya.

Kokuwa suke sosai, inda garba yaji jiki sosai amma tsabar taurin kai irin na, garba yaƙi haƙura yabar faɗan itama kuwa Indo cewa tayi muddun garba bai haƙura ba, sai dai su wuni suna faɗan, da gyar da suɗin goshi aka raba garba da indo, ɗauko kwanon Indo talatu tayi ba tare da layin Indon yaxo ba, sa mata ƙosan da koko tayi tace gashi ki tafi.

Karɓa Indo tayi tana cewa Garba.

” *Ko wani shege ma waje ya samu, ka dage sai dukan ƴar mutane kake, ɗan iska ƙaton banxa, girman biredi tashin kofin shayi, gobe ka bawa wani labarin Indo*.

Sanda Garba ya tabbatar da indo ta juya tana tafiya, ya taho da gudu ba tare da Indo ta ankara ba, ya ture ta, faɗuwa ƙasa Indo tayi daga ita har koko da ƙosan, shigewa da gudu Garba yayi yana cewa

” Na rama kiji kema idan da daɗi.

” Ihu ne, kawai Indo ba tayi ba, ganin Abunda Garba ya mata, Gashi Kuma ya tsere mata bazata iya kamo sa ba, tashi tayi cikin ƙwafa tare da cewa.

” *Zamu gamu wata rana sai ka gwammace kiɗa da karatu, in kere na yawo zabo na yawa wata rana za’a haɗu*

Ɗaukar kwanon nata tayi, ta koma gidan Innah.

Ganin mutum Innah tayi a kanta, da kwano riƙe hanun nata, duk tayi futufutu da jikin ta, kallon ta Innah tayi tace.

” Aya na ganki haka kamar an koroki, wai wanka kikayi da ƙasa ne, duba kiga yanda kika yi wata kala duk kin ɓata jikin da datti.

” Tura bakin ta Indo tayi wanda ya zamo mata sana’a tace.

” Faɗa mukayi da Garba, na masa shegen duka, shine da yaji haushi, ban ankara ba ya ture min koko da ƙosan ya zube ƙasa ko kaɗan bai saura ba.

Habeeb ne daya fito cikin shirin sa, na komawa, cikin dutse ya girgiza kansa, yana jin Ikon Allah wajen Indo, wato ita duk Inda taje sai ta saida hali, Allah ya kyauta ya kuma shirye ki,.

Cikin masifa Innah ke cewa.

” Kan bala’i wato shi garban ne, ya zubar min da koko da ƙosan nawa da ubansa, to kuwa tashi zanyi naje har wajen shi uban nashi naji idan shine ya turo sa, tashi muje ki raka ni Indo.

Murmurshi Habeeb yayi tare da cewa.

” Haba yanxu ke idan an barki sai kije, kinsan Abunda ita indon ta masa ne, kuma idan banda Indo da rashin hankali kina mace ina ke ina faɗa da namiji, Babu kyauma ai, hararar Indo yayi yace, kindai ji jiki Wlh, tunda ke baza kiyi Hankali ba.

Tashi Innah tayi tana cewa.

” to Uban ƴan iya magana, a ina akace mace baza tayi faɗa da namiji ba, to tayi faɗan ke Indo, daga yau cikin garin nan, duk Uban da ya miki ki takasa ko ubanwaye ne, kuwa.

Murmurshi Habeeb yayi tare da cewa.

” Allah ya baki hkr Innah nikam ba baƙon zafi bane, tafiya ma zanyi yanxu, kallon Indo yayi Yace, muje ki rakani gidan ku, na gaisa da Mama da baba na wuce ina son shiga cikin dutse da wuri, ke kuma Innah shigewa zanyi daga can baxan dawo ba.

” Bazaka tsaya kayi karin kumallo ba, zaka wuce da wuri haka.

Dariya Habeeb yayi yace.

” Dame zanyi karin kumallon Innah, bayan anyi tanbola da koko da ƙosan.

Shikenan to ka gaishe da iyayen naka, ka cewa wannan ɗan baƙin Halin, ya aiko min da saƙona dan ubansa.

Dariya Habeeb yayi cikin zolaya yace.

” Babu ruwana tsakanin ki da mustapha sai Allah dan haka bazan shiga tsakanin kuba.

” Karka shiga tsakanin namu, yanxu nasan idan ka tafi sai kuma tsawon rai kafin na ƙara ganin ka Habibu, sai kuma tasa kuka, Habibu Allah dai ya ƙaddara saduwar mu.

Murmurshi Habeeb yayi tare da cewa.

” Bazan dade ba, Innah idan na koma can wajen aikin nawa ma, bazan daɗe ba, zan ajiye musu Aikin su, na dawo gida na cigaba da aiki na, so bazan fi wata Uku ko huɗu ba, zan dawo insha Allah.

Shikenan Habibu Allah ya kiyaye hanya ya tsare, ya sanyawa Rayuwar ku, albarka.

Ita kuwa Indo haɗa fuska tayi jin ance Habeeb zai tafi, dariya Habeeb yayi tare da cewa.

” Haba indodo na, meye na haɗa fuskar kuma bayan baxan daɗe ba, zan dawo.

” Ya Habibu bana son ka tafi, amma tunda kace bazaka juma ba, shikenan, idan kaje ka cewa ya mustapha ina gaishe shi, kace masa ina sonsa kullum da sonsa nake kwana nake tashi.

Murmurshi Habeeb yayi yace.

” Insha Allah kuma zan isar miki da saƙon ki, Indo ki daure kike zuwa makaranta kinji, ki rage yawan rashin ji sannan kullum kike wanke bakinki kina gogewa kinji indona.

” Ya Habibu xan rage, koda ƙaɗanne, zan kuma ke zuwa makaranta kullum, kuma kullum zanke wanke baki na.

Bayan Habeeb sun shiga cikin gidan su Indo, ya gaishe da iyayen ta, duk da ma bai samu Baba ba, dubu ashirin ya ajiyewa Mama tana godiya tare da cewa ya gaishe da Hajiya A’ishah.

Cikin jimami da bacin rai Habeeb da INDO suka rabu, yana ɗaga mata hanu tana daga masa, har yayi mata nisa, juyawa Indo tayi gidan su da niyar taje ta tafi makarantar Boko.

*DUTSE LOCAL GOVERNMENT*

Zaune suke sun gama breakfast kasancewar yau Daddy na gida bazai fita kasuwa ba, kallon Mustapha dake zaune yana game a wayar sa Daddy yayi tare da kiran sunan sa, amsawa yayi tare da kallon Daddy.

” Mustapha ka shirya kaje gidan Alhaji ka karɓo min saƙo, kuɗi zai baka, idan ka karɓa ka shige bank ka ajiye min su cikin account ɗina, zai baka 20millions.

Amsawa mustapha yayi da to, amma bawai zuciyarsa na ƙaunar zuwa gidan su RAUDA ba.

Momy ce tace.

” Yawwa bari na baka saƙo ka kaiwa RAUDA, daman akwai sarƙar da na saya mata, tunda zakaje saika tafi mata dashi koh.

Haɗa Ransa Mustapha yayi Yace.

Ki ajiye kawai Momy duk sanda taxo kya bata, karna manta ta cikin motata.

” Bazan ajiye sai taxo ba, kai mata zakayi yanxu, ka manta kuma mu gani, sarkar ce, zaka manta, inbanda baka son kaimata ne

Tashi mustapha yayi, cikin jin haushin aikan da Momy ta masa wajen RAUDA ya haura sama, yana mita cikin ransa, tare da jin haushin RAUDA, shidai har ga Allah haka kawai baya ƙaunar RAUDA cikin rayuwar sa, kuma bawai tana da wani Aibu bane ko wani mungun hali, a’a bata da ko ɗaya, shi kansa yasan RAUDA macece mai nutsuwa tare da biyayya ga duk na sama da ita, tana da kyawun ta dai-dai gwargwado, a fili yace.

” Ajine kawai bata dashi,

Tunda har zata iya furtawa namiji cewa tana sonsa, ai macen da takai mace, ita ake zuwa ace ana so, ba itace zata ke bin namiji ba, ko ita wannan INDOn da take cemin tana sona, daman can ita ba nutsuwa gareta ba, bare kuma a samu Class tare da, ita, ita ɗayan ta, ma Aljana ce, ita za’a iya mata uxirin rashin Hankali da rashin lafiya na aljanu da take fama dashi, amma ke RAUDA kina mace mai Class, har kin kai 3 Hundred level a JSU kixo kina zubar da ajinki wajen maza, banza jarababbiya kawai, tsuka yaja tare da shigewa tollet.

Ita kuwa Momy da gangan ta aiki mustapha wajen RAUDA, duk neman yanda zata haɗa kansu, har shakuwa ta shiga tsakanin su, yanda zata samu sauƙi wajen haɗa su, aure.

Sharifa Momy ta daga tace ta shigar da kwanuka kitchen, sannan ita kuma ta tashi domin zuwa gyarawa Daddy ɗakin sa, kasancewar shi Daddy yace baya buƙatar ƴar aiki cikin gidan sa.

Cikin shirin sa, Mustapha ya fito, yana sanye da ƙananan kaya, Baƙin wandon jeans, da Red colourn riga, gashin kanshi kuwa kwance kasancewar mustapha ba ma’abocin Aski bane, sai Uban gyara da kuma mayuka da yake amfani dasu, wa kansa, toshe idanun sa, yayi da baƙin glass, ɗakin Momy ya nufa, bata ciki, fitowa yayi ya shiga na Daddy, tana gyaran ɗakin ya sameta, ki bani aiken naki Momy zan wuce.

Murmurshi Momy tayi sannan, ta fito daga ɗakin Daddyn nasu, shi kuma mustapha na biye da ita har cikin ɗakin ta, bakin gadon ta ya zauna kafin, Momy ta ɗauko sarƙar tare da Zama kusa da mustapha.

” Ga saƙon dan Allah ka tabbatar ka bata hanu da hanu, ka shiga har cikin falon nasu, ka gaishe da mamyn nasu, koh.

Karɓa yayi tare da ce mata insha Allah zan shiga, sannan ya tashi ya fice Momy na masa a dawo lfy, tare da fatan Allah ya haɗa kansu da RAUDA, dan ta fahimci kamar akwai ƙiyayyar RAUDA cikin Zuciyar mustapha.

A falo ma, a dawo lfy Daddy yayiwa mustapha, sannan ya fice daga cikin gidan.

Hajiya Turai mahaifiyar RAUDA, suna zaune tare da Hajiya Hindatu, ta kawo mata saƙonta, na Niger, dariya Hajiya Turai tayi tare da cewa.

” Amma dai Hindatu na gode sosai, Wlh ai daman nasan harkar ki Babu wasa cikin sa, kinsan yanda nake jin tausayin yarinyar nan, na rasa wani irin soyayya take yiwa wannan yaro, bata sauraron ko wani Saurayi ita dai kullum mustapha shine a bakinta, shiko ya maida ita shasha baya ma sauraron ta.

Dariya Hajiya Hindatu tayi tare da cewa.

‘ to yanxu kam ya shigo hanu, dan wlh muddun kunyi amfani da wannan magani dai-dai to tabbas sai Mustapha ya shigo hanun ku, kunyi yanda kuke so dashi, na gaya miki, wannan cikin abinci za’a sa masa ku tabbatar yaci abincin, wannan kuma ƙofar ɗakin sa, zaku barbaɗa, shima ku tabbatar ya, tsallaka, sai wannan turaren kuma, RAUDA ta tabbatar ta shafa shi duk sanda zasu haɗu dashi.

Idan kuka bi wannan dokokin dana lissafa muku, to kun sami mustapha kun gama, ina ita RAUDA take, taxo na ja mata kunne sosai ma tukunna.

” Bata Nan ai Hajiya ta tafi makaranta, amma insha Allah yau tana dawowa, a gidan su zata kwana, domin ganin ta gabatar mana da wannan aikin.

Yawwa da dai zaifi, bari na koma gida Hajiya, nabar sakina kwance zazzaɓi na damunta.

” Ayyya Allah ya bata lfy, na gode sosai Hajiya Insha Allah zaki ganni duk abunda ke faruwa zakiji.

Allah yasa muji Alkairi cewar Hajiya Hindatu.

Har compaunt ɗin gidan Mamy ta rakata, Hajiya Hindatu na fita mustapha na shigo da hancin motar sa cikin gidan.

Salim ƙanin RAUDA dake buga boll tsakar gidan Mamy ta shige zuwa cikin falon ta.

Parking mustapha yayi ya ɗan juma kafin ya fito daga cikin motar, kiran salim yayi, da gudu salim ya ƙaraso.

Tambayar sa Mustapha yayi ko Abban su nanan.

” Ya mustapha yana nan, ka shiga yana nan ɗakin da suke ganawa da baƙi, yana tare dasu.

Ɗakin Mustapha ya nufa, yana riƙe da hanun salim suka shiga.

Mustapha bai daɗe da shiga ɗakin baƙin Abban nasu ba, itama RAUDA ta shigo cikin gidan, dawowar ta kenan daga school………

Kuyi manage da wannan🙏🏻🙏🏻🙏🏻

*Vote*

*Share*

*And*

*Comments*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah ce)*

[1/24, 10:06 AM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*

*Nasmah ko Nasirah*

*Sara da Sassaka*

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.

Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*

____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

Kuyi hkr masoyan Indo a birni na rashin jina kwana biyu da bakwayi, hakan ta faru ne, sakamakon tafiya da nayi zuwa garin Jigawa, gashi muna hidimar bikin, sister na, Please kumin afuwa zuwa ranar talata idan Allah ya dawo dani Gombe lafiya, sai mu ɗaura daga inda muka tsaya, karku gaji da jira na, abunda yasa kuma nake ɗan yin typing ɗin Sara da sassaqa, Saboda shi book ɗin na kusa gamasa ne, Please kumin afuwa, tare da addu’ar Allah ya dawo dani gida lfy.

Please ku taya ni share ɗinsa domin ya samu ya isa zuwa ga masoyana.

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah ce)*[1/29, 11:53 AM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*

*Nasmah ko Nasirah*

*Sara da Sassaka*

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.

Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya 🙏🏻

_________________________

*Masha Allah my ƙawalliya ƙawar Arziki Zarahn Abdul, momyn Ahlan, ina tayaki murnar kammala wannan shahararren book ɗin naki wato (Shuhuda) Allah ya bamu ikon amfani da darusan dake cikin sa, Abunda kikayi kuskure kuma Allah ya yafe miki, congratulation momyn Ahlan🤝🏻*

_________________________

*Alhamdulillah fan’s gani na faso dole na daure nayi muku typing yau saboda ƙaunar da kuke yiwa wannan book, waɗanda suka kira ni, suka min murnar kammala book ɗina na Sara da sassaqa baya hana gamji toho da kuma waɗanda suka turo min text har zuwa kan waɗanda suka min murna ta online tare da fatan Alkairi, na gode sosai da ƙaunar ku gareni.*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

*P*•••••••2️⃣5️⃣ ➡️ 2️⃣6️⃣

Cikin gajiya RAUDA ta shiga cikin falon nasu, a saman kujera ta faɗa tare da cewa.

” Wash Wlh Mamy yau na gaji sosai, wani text mukayi mai zafi kaina ciwo yake ina gani ma, wanka zan shiga nayi na kwanta.

” Amma dai ke RAUDA akwai malalaciya, yanxu kin dawo bazaki zauna kici abinci ba, sai kije kiyi wankan, idan yaso saiki kwantan, waya sani ciwon kan ma kona, yunwa ne.

” Bafa yunwa bane Mamy, kawai text ɗinda mukayi ne, ya samin wannan ciwon kan.

Shigowar Salim da gudu ne ya hana Mamy yin maganar da tayi niya, tace.

” Lafiya ka shigowa mutane ɗaki da gudu salim cewar Mamy.

” Mamy daman zan faɗawa Aunty RAUDA ne, ya mustapha yaxo yana ɗakin ganawar Abba yanxu haka.

Murmurshi Mamy tayi domin kuwa mustapha yaxo mata a dai-dai, wannan shine first tagget ɗina akanka, daga yanxu zan fara wannan maganin, duk cikin Zuciyarta take wannan zancen, kallon salim tayi tace.

” Naji koma wasan ka, manga na, ta masa maganar cikin sigar rarrashi, fita yayi abunsa, sannan Mamy ta dubi RAUDA tace, maza jeki ɗaki ki kwaskware fuskar ki, turaren da Hajiya hindatu ta bata wanda zata shafa a fuska, Mamy ta miƙo mata, tace maza ki shafa yanxu Hajiya hindatu ta kawo sa, tace indai kin shafa mustapha ya kalle ki, anwuce wajen, domin kuwa dole ya soki.

Aiko cikin murna da zumuɗi RAUDA ta karɓi turaren tare da shigewa bedroom ɗinta da gudu, murmurshi Mamy tayi tare da yin kitchen domin yiwa Mustapha barbaɗe barbaɗe cikin ruwa da abinci, kasancewar tasan indai mustapha yaxo gidan Abba yana nan, dole saiya ci abinci, kafin ya tafi.

Mustapha kuwa shigar sa, part ɗin bakin Abban ya samu saura mutum ɗaya ne, har ƙasa mustapha ya sunkuya ya gaishe su, kafin Abba ya masa nuni da gefen sa, yace yaxo ya zauna.

Bayan Abba ya sallami bakon nasa ne, ya dubi mustapha Yace.

” Muhammad Mustapha ne, ko Muhammad Habeeb, kasan bana gane ku, idan kuka haɗu waje ɗaya, gashi kuma Alhaji Haroun yace min shima Habeeb ya shigo ƙasar.

Murmurshi Mustapha yayi yace.

” Nine mustapha Abba, daman Daddy ne, yace naxo na karɓi sako wajen ka.

” Ayyya Muhammad Mustapha, tashi mu shiga ciki to, sai kaci abinci, kafin na baka saƙon koh.

Mustapha bai yiwa Abba musu ba, ya tashi ya bisa cikin gidan, a daining suka tarar da Mamy ta shirya abinci, gaishe da Mamy mustapha Yayi ta amsa cikin sakin fuska tana tambayar sa, mahaifiyar sa, tana lafiya yace mata, kafin Abba ya umurce shi da cewa ya zauna a daining ɗin, zaman kuwa sukayi, Mamy itace tayi seving ɗinsu, yayin da ta zubawa mustapha mai maganin, basu Kuma juma da zama ba, itama RAUDA ta fito cikin kwalliya, ta zauna kujerar dake kallon ta mustapha, wanda yana ɗaga idanun sa, ita zai kalla, tunda RAUDA ta zauna mustapha bai ɗago idanun sa, ba bare su haɗa da RAUDA, yadai ji Muryar ta, Abba ne ya kalli mustapha Yace.

” Muhammad Mustapha, kaci abinci mana, an zuba maka Kuma.

Sai a lokacin RAUDA tace.

” Sannu da zuwa ya mustapha ina wuni.

A dakile Mustapha yace.

Lfy tare da ɗaukar spoon.

Daga Mamy har RAUDA murna suke mustapha zaici abincin domin kuwa sunsan yana ci yaxo hanu.

Ɗebo abincin mustapha yayi, har zai kai bakinsa sai yaji Ringtone din wayar sa, maida spoon ɗin yayi ya fasa kaiwa bakin nasa, tare da ɗaga wayarsa, ji nayi yace.

” Ka samu bayanan, to tsaya dai-dai roat block ɗin gani nan zuwa yanzu, tashi mustapha yayi yacewa Abba.

” Amin afuwa Abba, wlh wani sako zan karba mai mahimmanci, gun wani, gashi kuma baƙo ne, hanyace ta biyo dashi tanan garin zai shige, idan zai yiwu da an bani sakon saina samu na shige.

Murmurshi Abba yayi yace.

” Babu damuwa Muhammad Mustapha ai kana cin abinci cikin gidan nan, ke Turai jeki ɗauko masa wannan karamar jakar dana shigo dashi.

Daga Mamy har RAUDA ji sukayi kamar an soka musu mashi cikin ƙirjin su, da mustapha ya tsallake wannan tarkon nasu, sunji mungun bakin ciki, haka dole Mamy ta shige ta ɗaukowa mustapha sakon ta basa, ƙarɓa yayi tare da yiwa Abba sallama, ya fice da sauri, tashi RAUDA tayi itama cikin sauri tabi bayan sa, tana cewa.

” Ya mustapha baka jiba.

Tsayawa mustapha Yayi daga buɗe murfin motar tasa, ya ɗago kansa, carap kuwa sukayi ido biyu da RAUDA, wani irin tsinkewa zuciyar mustapha yayi, kansa kuwa neman juye masa yake.

” Subhanallah ya furta da ƙarfi tare da ambaton, innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un, la’ilah ha’illah anta subhanaka inni kuntu minnazalimin, tare da zama cikin motar da sauri yana dafe da kansa, yafi 15 minute yana Zaune yana ambaton Ubangiji, Kafin yaji komai ya dawo masa normal, har lokacin kuma RAUDA na tsaye wajen, bai ƙara ɗago kai ya kalleta ba, saima wani tsawa daya daka mata.

” Wai RAUDA me kike nema dani ne, kin dameni kin dami rayuwata, RAUDA duk wani take taken ki, na sani, Sona kike, to dan Allah zan roƙeki, ki ƙyale Ni, nikam bakya cikin matan da nake burin Aura, baki min ba, dan haka, ki sawa zuciyar ki, salama ki daina wahalar da kanki, iya gama faɗa mata haka, yasa hanun sa, ya dauko sarkar da Momy tace ya bata, ya wurgo mata tare da cewa idan kinga dama ki ɗauka Momy ce tace na kawo miki, sannan yaja motarsa da ƙarfi yabar wajen.

Tsabar takaici RAUDA ta kasa motsi daga inda take, tsaye, hawaye kuwa ya wanke mata fuskar ta, sunkuyawa tayi ta ɗauki sarƙar sannan ta shige cikin falon nasu, tsayawa tayi ta goge hawayen ta, kafin ta shige su Mamy tayi bedroom ɗinta, Abba ne, ya kalli Mamy yace.

“Turai Kamar akwai Abunda ke damun RAUDA koh naga yanayin ta, kamar ya sauya?.

” Meka gani abban RAUDA, cewar Mamy.

” Haka dai na gani kamar mood ɗinta ya sauya ba kamar yanda ta fita ɗazu ba.

” To gaskiya ban sani ba dan ban lura da shigewar ta ba amma dai gaskiya Babu Abunda ke damunta.

” Okey shikenan tunda haka kikace, bari na shige bedroom ɗina, ki samu kisa a gyara part ɗin baƙin nan.

” Shikenan Abban RAUDA, za’a gyara.

Bayan Abba ya shige bedroom ɗinsa ne, Mamy tayi bedroom ɗin RAUDA, tana kwance tayi rup da ciki sai kuka take mai tsuma Zuciya, hawaye kuwa harda majina, girgiza kanta Mamy tayi, tare da zama, ta fuskanci RAUDA tace.

” Shikenan ke yanzu haka zaki zauna kullum kina yiwa namijin kuka, yanxu ke bazaki dage a matsayinki na mace ba, ki jawo hankalin mustapha, sai kace wacce kika fito daga ƙauye, ki tashi ki wanke fuskar ki, ki shirya zaki koma gidan su, mustapha da Zama har sai buƙatar mu ta biya, zan miki bayanin duk yanda zakiyi amfani da maganin, zamuyi nasara akansa insha Allah.

Cikin kuka RAUDA take cewa.

” Mamy na haƙura da ya mustapha domin ya faɗa cewa baya sona, Kuma mun haɗa ido shi, wannan maganin ƙarya ne Mamy, tunda Bayan mun haɗa ido dashi ne ya furta min cewa baya sona, na haƙura Mamy nasan mutuwa zanyi, domin soyayyar ya mustapha bazata barni nayi nisan kwana b……..

Toshe mata baki Mamy tayi tace.

” Ki daina furta waɗannan mugayen kalaman, dole ma mustapha ya soki kota Halin yaya, magani kuma yana da kyau, ki tashi nace kibi umurni na, ki shirya ki tafi, karkiyi zuciya akan abunda zuciyar ki, bazata ita haƙuri dashi ba.

Tashi RAUDA tayi ba tare da ta kara cewa Mamy komai ba, tayi tollet.

Shiko mustapha yana fita darect, wajen mutumin da sukayi waya yaje, wasu takaddu ya basa sannan sukayi Sallama ya wuce bank ya ajiyewa Daddy kuɗin sa, sannan ya dawo gida, a falo ya samu Habeeb Zaune yana danna waya suna game shida Sharif, ware idonsa mustapha yayi tare da cewa.

” Yaushe ka dawo kai kuma.

Murmurshi Habeeb yayi tare da cewa.

” Tun ɗazu nakai 2 hours da dawowa.

Zama mustapha yayi yana cewa.

” Kace yau kabar Innah da kewa, ni nayi zaton ma ai sai mun bika da kayan kane.

Dariya Habeeb yayi tare da cewa.

” Wlh ƙauyen ne, yamin daɗi, mussaman dana samu Indo, gaskiya yarinyar tayi a rayuwa.

Taɓe bakin sa Mustapha yayi, tare da cewa dake shashancin ku ɗaya ba, amma inbanda haka meye abun burgewa wajen, wannan taɓaɓɓiyar wacce ta addabi al’ummar garin, ni kaga bari na shige inada abunyi cikin ɗaki, tunda naga kaima baka da abun faɗa.

Murmurshi Habeeb yayi tare da cewa.

” A fito lfy daman ai nima bance ka zauna ba,.

Shidai Mustapha bai tankawa Habeeb ba ya haura sama.

Sharif ne ya cewa Habeeb.

” Ya Habeeb, ya mustapha ya cika masifa, kullum yana cikin faɗa, ni tsoronsa ma nake ji wlh, kuma fah ya Habeeb ance duk mai faɗa mungu ne.

Haɗa ransa Habeeb yayi tare da cewa.

” Kul na ƙara jin wannan maganar a bakin ka, yayan naka ne, yake masifa, har kike cewa mungu, to wlh idan ya jika, wlh saina lahira yafika jin dadi kadai san halinsa.

Tura bakin sa Sharif yayi tare da cewa.

” Kayi haƙuri ya Habeeb bazan sake ba.

Murmurshi Habeeb yayi yace.

” Ya wuce Autan Momy, game ɗin suka cigaba dayi, sallama RAUDA tayi hanun ta janye da akwati.

Amsawa Habeeb yayi cikin fara’a yace.

” A’a baƙuwar muce ta dawo, kinga mun dawo a dai-dai kuwa, nima ban juma da shigowa, ba.

Murmurshi RAUDA tayi kafin ta ƙaraso, tace Lallai munyi anko, kenan nima yanxu ina zaune naji kawai ina son dawowa, Sharif ne ya amshi akwatin nata, yana ƙoƙarin haurawa dashi, ita kuma ta zauna kusa da Habeeb suka cigaba da magana.

Mustapha daya fito da key a hanun sane, yayi turus sakamakon ganin RAUDA Zaune yarinyar daya bari yanxu cikin gidan su, tsuka yaja tare da cewa.

” Mayyah kawai, sannan yasa kansa ya fice ba tare daya kallesu ba.

Girgiza kansa Habeeb yayi, cikin takaicin mungun hali irin na mustapha, da nunawa mutum ƙiyayya a fili.

*DASINA*

Tafe take riƙe da kara a hanun ta, tana raira waƙarta.

” Ayya raye ayye ayye, ayyya raye ayye dije, zaman gidan wani tilas ne, ba’a kanki ne aka fara ba, ba’a kanki ne za’a ƙare ba, ƴar tsohuwa mai lallen zo yaki nan, kunsa mata amaryar nan n……..

Maganar da malam Yakubu makaho ya mata shine ya katse mata waƙar tata, cikin murna tana dariya tace.

” Lah Baba Yakubu kaine, Aradu ban lura dakai ba, ina zakaje da sassafen nan haka.

” Yo Indo ina zanje kuwa idan ba Bara ba, bara zan fita mu sami na cefenen gida.

” Kai Baba Yakubu yanxu yanda kake da tiƙeƙen ƙaton Yaron nan, Sani bazai je yayi sana’a ya kawo muku na cefenen ba, har sai kai da kake makaho kaje kayi bara ka Kawo kuma yaci, to aradu ni a gidan ya Tanimu shine yake bada kuɗin cefene, gashi kuma baban mu yana da idanunsa, amma dai Aradun Allah Sani yayi Asara.

Dariya Mlm Yakubu yayi, domin kuwa yasan duk haukar Indo, yaudai maganar data faɗa tana kan hanyar gaskiya, sannan Yace.

” To ya za’ayi Indo tunda shi bazai nema ba, aini dole na nema, kodan ƙananan yara.

Kallon dubu ɗayan da Mama ta aiketa siyo kwanon shinkafa da rabin mudun wake tayi, sai kuma ta kalli Mlm Yakubu, ta sake kallon dubun kai tsaye tace.

” kaga Baba Yakubu karka je barar nan, dan wlh na tsani barar nan, gashi kai Kuma ba ɗan jagora kake dashi ba, badai kuɗin cefene kake nema ba, ta gashi wannan dubu ɗayan kaje kayi cefene ba shikenan ba.

” Ina kika samo dubun indodo, da zaki bani?, ya tambaye ta cikin mamaki.

Ƙarya Indo ta zafgawa domin tasan idan tace masa kuɗin aika ne bazai karɓa ba, domin kuwa jinin Indo da Mlm Yakubu yaxo ɗaya sosai suke shiri, sannan tace.

” Tsintarta nayi ɗaxo daman zan kaiwa Mama ne nace nayi tsintuwa, kaga tunda yanxu kai kana buƙata, saika karɓa.

Karɓa Mlm Yakubu yayi yana shiwa rayuwar Indo albarka, kama sandar tasa Indo tayi tace muje Baba Yakubu na rakaka gida, sai ni kuma na wuce gida.

Tafiya sukayi Indo ta raka Mlm Yakubu har ƙofar gidan sa, sannan ta ruga da gudu tayi gidan su.

Mama na Zaune ta ɗaura ruwa a murhu tana zaman jiran Indo ta kawo mata shinkafa ta tsince ta saka cikin tukunyar, sai ganin Indo tayi ta shigo mata hanu ziƙau babu komai, tsayawa tayi akan Mama tayi shiru ba tare da tayi magana ba.

Kallon ta Mama tayi sannan tace.

” Ya kika tsaya a kaina ne, yiwa zaki bani magani ina aiken dana miki.

Kai tsaye Indo tace.

” shagon ɗan tasin a

rufe ne.

” Arufe kuma cewar mama, to bani kuɗin na aika jummalo gidan su, Hadiza ta sayo min.

Kallon mama tayi tana turo baki gaba tace.

” *Nayi miki sadaka da kuɗin*

” Kinyi min sadaka da kuɗin, mama ta tanbaya, ban gane kinyi sadaka da kuɗi ba.

” *Mama Baba Yakubu makaho ne, na haɗu dashi yanxu a gangare, zai tafi bara, shine yamin magana, yace zaije Bara ne, ya samo kuɗin cefene, shine ni kuma ya bani tausayi, na basa sadakar dubun taki, tunda ke kina da mai baki, ya Tanimu, shi kuma bashi da wanda zai basa, Sani ma shege ne, baya basa*.

Kallon takaici Mama ke bin Indo dashi, domin kuwa yanxu ta fara tsoron lamarin Indo, kodai tana da aljanune a kanta, cikin haushi Mama tace.

” Shikenan kin raya gidan wasu ke kuma kin kashe naku gidan, yau wasu zasu ƙoshi mu kuma zamu wuni da yunwa, yanxu Indo idan banda sakarci Irin naki kin taɓa ganin inda mutum yayi kyauta da abunda ba nasa ba, to Kuma Wlh yau sai kinsan kinyi kyauta da dubu, danko yau Babu mai hanani cin ubanki cikin gidan nan.

Danƙo Indo Mama tayi, ta rufeta da duka, ihu Indo take tsakanin ta da Allah kamar wacce mama take yanka ta, Baba saude maƙwabciyar su, da taji ihun Indo yayi yawa ne, yasa ta, zagowa cikin gidan, daƙyar ta ƙwaci Indo hanun Mama tana cewa.

” Haba mero yanxu wannan dukan da kike yiwa yarinyar nan ai yayi yawa, babu kyau fah yawan duka.

” Ki barni mero na daki yarinyar nan yau ko zan huce, wlh na gaji da halin Indo, kullum da Abunda yarinyar nan take jawo min, masifar yau daban ta gobe daban, yanxu dan Allah Saude ki duba ki gani, tun da hantsi na ɗaura sanwar abinci, na aiki yarinyar nan Indo taje ta siyomin shinkafa na bata gudan dubu, jummalo na kwance bata da lfy, kinga har yanzu ƙarfe 1:00 na azahar ta dawo min, babu aiken dana mata, wai take cemin tayi sadaka da dubu ɗayan, sai kace ƴar gidan wani babban attajiri, da zakiyi kyautar dubu.

” Ashsha haba yanxu ke Saboda baki da hankali, ki ɗauki kuɗin abincin ku, ki kyautar, baki kyauta ba, Indo dan Allah mero kiyi hkr, kibar maganar ta shige yaran yanxu ne saida hkr, duk yawanci haka suke.

” Zan haƙura Saude sai wlh yau baxan bawa Indo abinci cikin gidan nan ba, sai daita kwana da yunwa, kallon Indo Mama tayi tace, zaki fice minne da gani kosai na taka miki wuya, shashasha marar lissafi.

Ihu Indo ta ɗauko ta zunduma, sai kuma tayi waje da gudu tana ihu, girgiza kanta Baba Saude tayi, sannan ta kara bawa Mama hakuri ta koma cikin gidan ta.

Tashin jummalo Mama tayi ta dauki ɗari biyar tace taje ta sayo musu shinkafa.

Da gudu ta shiga gidan Innah tana ihu.

” *Wayyo Allah na shiga Uku na lalace wayyo Allah Mama zata kasheni, wayyo Allah bayana ya kare*

Jin ihun Indo yasa Innah fitowa da gudu rike da zani a hanu, tana cewa.

” Subhanallah wani shegen ne, zai kashe ki?

” Innah Mama zata kashe ni, ta karya min bayana, tamin duka saura kaɗan ma ta jefani wuta Allah ya kawo Baba Saude ta ƙwaceni kuma tace wlh yau bata bani abinci ba.

” Ita mairon ce, tace haka, cewar Innah, me kika mata to, nasan dai ruwa baya tsami banxa.

Tura bakinta Indo tayi tace.

” Wai dan kawai ta aikeni da dubu, shine na haɗu da Mlm Yakubu, zashi bara, wai basu da kuɗin cefene, shine fah na mata sadaka da kuɗin nace yaje yayi cefene.

Salati Innah ta ɗauka tare da cewa.

” Yanxu daman akan ɗan wannan abun mairo ta miki wannan mungun dukan, dan kawai kin mata sadaka kin nema mata lada a wajen Ubangijin ta, to muje gidan naku naji dalilin da ta miki wannan dukan.

Mayafinta Innah ta ɗauka tasa Indo a gaba tana mita har gaban Mama.

Ganin Innah da Mama tayi ta tashi da sauri ta ɗauko mata taburma tana Cewa.

” Sannu da zuwa Innah lale maraba.

Cikin masifa Innah tacewa Mama.

” Bana son sannu da zuwan ki, ki riƙeta, yanxu mairo kan dubu shegiya kika yiwa indo wannan dukan, saboda kawai ta nemo miki lada wajen Ubangijin ki, kunce bakin zanin ta, Innah tayi, ta ɗauko gudan dubu ta wurgawa Mama tace, ga kuɗin ki, ladan sadakar kuma Allah ya bawa Indo, duka kuma da kika mata kin daki Allah ya Isa.

Murmurshin takaici Mama tayi sannan tace.

” Kiyi hkr Innah, ki karɓi kuɗin ki, nikan bazan riƙe kuɗinki ba, Allah ya huci Zuciyar ki, kiyi hkr dan Allah.

Harar Mama Innah tayi tace.

” baxanyi hakurin ba, abinci Kuma kar Allah yasa ki bata, muje Indo kici abinci harki kyautar.

Shigewa Indo tayi tana yiwa mama dariya harda gwalo, tabi Innah suka tafi, gidan ta.

Girgiza kanta Mama tayi cikin jinjina ƙarfin hali irin na Innah, ita daya kamata tayiwa Indo faɗa wai itace take ɗaure mata gindi, ya Allah ka shirya min Indo cewar mama.

A hanya Innah da indo suka bi wajen mahauta Innah ta saya musu nama, sanna suka dawo gida, zama sukayi Innah ta dubi Indo tace.

” Ki saurareni da kyau kiji Abunda zan faɗa miki, duk cikin ƙauyen nan duk wanda ya miki ki masa karki bari, aci kashi a kanki, domin kuwa naga an fara samiki ido cikin garin nan.

Dariya Indo tayi tace.

” Innah yo dama wa zan ƙyale, yanxu ma jira nake Allah ya haɗani da garba naci ubansa la’ada waje zaisan yamin Asarar ƙosai da koko na, dan uwarsa.

*Yawan sharhi yawan typing idan kunyi sharhi kaɗan nima kujini shuru sai bayan sati biyu, idan Kuma kunyi sharhi mai yawa kujini kullum tare da typing mai yawa*.

*Vote*

*Share*

*And*

*Comments*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah ce)*

[1/30, 1:00 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*

*Nasmah ko Nasirah*

*Sara da Sassaka*

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.

Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya 🙏🏻

TALLAH TALLAH TALLAH

Ina kuke makaranta littattafan Hausa ku matso kusa ga dama ta samu, ni ɗinnan dai *(UMMU NASMAH)* na shirya tsaf domin gabatar muku da sabon Novel ɗina, wanda zai nishaɗantar daku ya faɗakar daku, yasa ku cikin tunanin, mai taken *(RUƊANIN ZUCIYAH BIYU)* Wannan littafin yasha banban da sauran littattafan dana saba gabatar muku, labarin yana tafe da Soyayyah mai ban tausayi, ƙiyayya ƙyama tsangwama, tausayi, littafin zai ruɗa tunanin ku, kudai ku cigaba da biyoni domin karku bari a baku labari da abaku gara ku bayar, karku manta da sunan sa *(RUƊANIN ZUCIYAH BIYU)*

Nice taku mai son farin cikin ku a koda yaushe, *UMMU NASMAH CE*✍🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*

____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

*P*•••••••2️⃣7️⃣ ➡️ 2️⃣8️⃣

” Kinga Indo tashi maza ki hura wutar nan, yau shinkafa zamuci da jar miya.

Tashi Indo tayi, ta fara kici-kicin hura wuta, domin kuwa Indo babu laifi akwai ƙoƙarin zama tayi girki amma idan taga dama, fah.

Suna aikin su suna taɗi har suka gama, cin abincin sukayi, saida akayi la’asar sannan Indo ta koma gidan su, siɗi siɗi ta shige ta ɗauki allonta tayi makaranta, tun biyar da rabi aka tashe su, tafe Indo take ita da Hansai, suna zance, Hansai ne tace.

” Indo ɗazu da zan tafi makaranta naga lami ta dawo daga tafiyar da tayi, har take cemin Anjuma zata shiga gidan ku.

Tsale Indo ta daka, cikin murna tace.

” Tsakani da Allah Hansai da gaske kike lami ta dawo.

” Wlh da gaske nake, ta dawo na ganta, da idanuna.

“Wayyo Allah daɗi, aminiyata ta dawo, rugawa Indo tayi da gudu tare da mikawa Hansai allonta tace ki kaimin gida.

Lami aminiyar indo ce ita da Hansai, itama lami hatsabibiyace sai dai bata kai Indo ba, shiyasa sukafi shiri da Indo fiye da Hansai.

Aiko Indo kiciɓis sukayi da Lami a ƙofar gidan su, cikin murna suka ɗane juna, Lami tace.

” Ƙawas andaɗe fa ba’a haɗuba, tun ɗazu naje gidan ku, Mama tace kinje makaranta, har gidan Innah naje tace bakya nan.

” Kedai Lami bari Wlh bana jin daɗin garin nan da bakya nan, ayyya Lami ya mustapha na dai har yanzu baixo ba sai sau ɗaya kawai nanma bai daɗe ba ya tafi, amma inaga zan lallaɓa Innah muje Birnin nan, Allah indai har naje baxan dawo ba.

Labarin Habeeb Indo ta dinga bawa Lami, har pictures ɗin da sukayi, ta karasa maganar da cewa.

” Kinga wata shegiyar kama kuwa da suke yi, gashi yana da kirki, sosai ba irin ya mustapha ba, kullum yana cikin haɗiye rai.

Shewa Lami tasa tare da cewa,

” Ke ƙawata, kwantar da hankalin ki, ba sai kinje ba, tunda Innah tana cikin garin nan dole zaizo shi, dan haka sa ranki a inuwa, amma gaskiya naso haɗuwa da wannan Habibun, yanxu dai ba wannan ba, ina zamuje neman magana kinsan an daɗe ba’ayi ba.

Shuru Indo tayi tana tunani, sai can tace.

” Muje shagon Mlm Ibrahim ko zamu samu Garba, muci ubansa daman ina da cikin sa.

” Muje Lami tace tare da kama Hanun Indo suka tafi.

Aiko Garba dake zaune yana jirawa babansa shago, ya hango su Indo suna, zuwa, tashi Garba yayi ya ruga da gudu domin kuwa yasan muddun ya shiga hanun su Indo ya shiga Uku, rufa masa baya suma sukayi da gudu, amma ina kafin su iso Garba ya tsere musu.

Haushi ne ya kama Indo cikin takaici, ta dubi Lami tace.

” Shege ya gudu, Ranar mafah haka yamin ya tsere Min.

Kallon shagon su Garba Lami tayi tace.

” Kinga Abunda zamuyi kawai mu ɗebi, biskit da minti muyi gaba, shi kuma shikenan, ki barsa.

Haka kuwa akayi suka shiga shagon suka ɗebi biskit da minti, sukayi tafiyar su, Indo kam a hanya, ta rabawa yara wanda ta ɗiba ko ɗaya bata ciba.

Lami ce ta kalleta tace.

” Ya kika rabar da naki baki ciba, bakya sone.

” Ina so mana kawai dai bazan ciba ne, nasan yau sai baban garba ya kaimu ƙara wajen mai gari, akan kayansa, kinga basu da hujjar da zasuce na biyasu kayan su, sai suje su nemi yaran dana bawa su karbi Kayan su a hanun su.

” Amma dai ke Indo akwai shasha, yo su kuma yara ina ruwan su, aida kici da karki ci, akan kene kika ci, garama kici idan yaso a miki hukunci da tushe.

” Kan Uba cewar Indo, uban waye ya isa ya hukunta ni akan abunda banci ba, to wlh ba’a isa ba, *Uwar kuturu ma tayi kaɗan balle na makaho* idan kuma akace za’a hukunta ni to wlh shima kansa mai garin saiya gane kurensa.

” Mtss matsalata dake Indo rashin wayo sai kitayi ni wlh saina ci, sai dai duk abunda zai faru ya faru.

” Na Yadda banda wayon kuma wlh karkici kema ki rabawa yara, kamar yanda nayi idan kuma kikaci to wlh duk hukuncin da mai gari ya yanke mana, akanki ne ke ɗaya, dan wlh *Banci kaza ba baxanyi aman gashi ba*

” Mtss sai kuma kiyi, tafiyar ta, Lami tayi tabar Indo tsaye a wajen.

Itama Indo tsukar tayi, ta tafi tana zagin Lami cikin ranta.

Gidan su, ta shige Mama ta samu zaune tana talge, kusa da jummalo ta zauna dake zaune tana, karkarwar zazzaɓi, sai hawaye dake zuba cikin idanunta, kallon jummalo tayi tace.

” Sannu jummalo ya jikin naki.

Hawaye ne, ya gangaro fiskar jummalo tace.

” Mutuwa zanyi Indo, dan Allah ki nutsu ki daina ɓatawa Mama rai kinga ni zan tafi na barki da Mama, dan Allah ki daina ɓata mata rai.

Kallon ta Indo tayi, sai kuma ta tuntsire da dariya, tace.

” Kai jummalo duk zafin ciwon ne, haka, wlh yau da Innah kika faɗawa Maganar nan da kinsha zagi.

Tana maganar ne, sai kuma taga Idon jummalo yana juyewa, sai kuma ta fara wani irin nishi, tsoro da Indo tajini yasata kwalawa mama dake madafi kira.

” Mun shiga Uku mama kixo jummalo zata mutu, wai daman da gaske kike mutuwar, zakiyi, wayyo Allah.

Da gudu Mama ta fito daga madafi, tayo kan jummalo tana girgiza ta, himar dinta mama ta dauko, tasa Indo ta kama mata, jummalo suka fito da niyar zuwa chemist amma ina kafin su ƙarasa fita daga gidan jummalo rai yayi halinsu, kallon Indo Mama tayi taga ita bata sanma jummalo ta rasu ba, cikin dauriya da ƙarfin hali tace.

” Mu koma Indo mu ajiye ta, tayi bacci jikinta yayi sauƙi.

Juyawa sukayi suka kwantar da jummalo, Mama tacewa Indo taje ta mata kiran Innah.

INDO na fita Mama ta fashe da kuka, tare da rungumo jummalo a jikinta tana mata addu’a.

Indo bata wani juma ba, suka shigo tare da Innah, da sauri Innah ta ƙaraso gaban Mama ganinta tana kuka tace.

” Mairo lfy meya faru, kike wannan ajiyar Zuciya haka.

” Innah jummalo ta rasu, ta tafi ta barni Innah.

Daɓas Innah ta zauna a ƙasa tare da sakin kukan itama, sai aka rasa waye zai bawa wani hakuri tsakanin su.

Allah sarki Indo, wato duk inda dan uwa yake yana son ɗan Uwansa, kasa kuka Indo tayi, ta zauna itama kusa da jummalo, sai kuma ta tashi ta fice da gudu, ashe Baba ta kira, tare suka dawo Baba yaxo ya same su sai sharbar kuka suke.

” Haƙuri Baba ya basu tare da musu nuni da cewa, jummalo yanxu bata buƙatar kuka a garesu, addu’a take bukata, Allah sarki rai baƙon duniya, jummalo kwanan keso tayi, Indo da Innah kuwa kwana sukayi basuyi bacci ba, washe gari da misalin karfe goma aka kai jummalo makwancin ta, Indo tasha kuka Ranar har idanun ta suka kasa buɗuwa, Innah ce ta kira Baba tace yaje ya nemi waya ya sanar da Haruna rasuwar jummalo.

Haka kuwa akayi Baba ya kira Abokinsa Haruna ya sanar masa.

*DUTSE LOCAL GOVERNMENT*

Hira suke ciki falon dukan su, suna zaune, har Habeeb, mustapha ne kawai baya cikin su, duban Momy Habeeb yayi yace.

” Momy akwai maganar fah da nake son na sanar dake, shi Daddy na sanar masa.

” Okey ina sauraron ka Habeeb.

” Momy daman ina son jibi idan Allah ya kaimu zan koma London, saboda ina son zan sanar dasu cewa nabar aiki dasu zan dawo gida na cigaba da aiki, so idan na koma zan tattaro duk wani abu da yake nawa na dawo, bazanfi sati biyu ba zan dawo insha Allah.

Murmurshi Momy tayi cikin murna tace.

“Alhamdulillah, daman Abunda nake so kenan Habeeb, nafi son aikin ka, anan gida Nigeria, naji daɗin wannan Albishir da kaxo min dashi, Allah kuma ya kaimu jibin lfy.

Murmurshi Habeeb yayi ya amsawa Momy da ameen sannan ya dubi, RAUDA yace.

” Ke Malama, wai yau bazamu ci abinci a cikin gidan nan bane, naga kamar baku da niyar yi.

Dariya RAUDA tayi tace.

” Kai dai kace yunwa kake ji kawai idan banda haka yaushe ma akayi breakfast, ta inda ya mustapha yafika kenan, shi babu ruwan sa, da yawan ci.

Dariya shima Habeeb yayi yace.

Wai damma shi mustapha baya gari, da yau mun gwada mun gani nida shi waya fi wani ci.

Kallon mamaki RAUDA tayiwa Habeeb, cikin Zuciyarta tace, haba shiyasa tun daya fita jiya shigota gidan nan banga ya dawo ba, ashe tafiya yayi, na shiga Uku anya wannan maganin namu akwai Sa’a cikin sa, kuwa.

Sharifa ce, tace.

” Momy da gaske ya mustapha tafiya yayi Babu Sallama yau.

Murmurshi Momy tayi tace Sharifa.

” Ehh shima baisan da tafiyar ba, sai da ya fita office ake sanar dashi, yaje inugu zasu gana da wani Criminal amma ina ga ya dawo gobe insha Allah.

” Allah ya kaimu Momy ya dawo dashi lfy.

Da ameen Dukansu suka amsa sannan Habeeb yace shi zai shiga ya kwanta.

Tashi RAUDA tayi cikin ɓacin rai tayi kitchen ita da sharifa suka bar Momy zaune a wajen.

Da dare bayan daddy ya dawo sunci abincin dare yake sanar da Momy mutuwar jummalo, sosai Momy ta taji mutuwar a jikinta, shi kanshi Habeeb yaji mutuwar domin yasan jummalo zuwan sa da yayi, yarinya ce mai nutsu da tarbiyya, gata da tausayin iyayen ta, daddy ne yacewa Momy.

” A’ishah inaga Ranar Laraba, zaku shirya gaba ɗaya zamu tafi dasina ta’aziya, da jibi nayi niyan mu tafi, to sai kuma gashi Habeeb zai koma jibin shiyasa nace, gara mu bari idan ya tafi mu kuma washe gari sai mu tafi shi mustapha munyi waya dash daga inugu zai wuce Dasina zamu haɗu acan.

” Shikenan Alhaji Allah ya kaimu jibin idan yaso saimu wuce dukan mu, har RAUDA.

Nisawa RAUDA tayi tace.

” MOMY ai ina da school babu Halin naje, zan dai koma gida idan kun dawo saina dawo nima.

” Okey Allah ya kaimu cewar Momy.

Haka kuwa akayi Ranar talata Habeeb ya wuce London tare da bawa Sharifa sakon idan taje, dasina Innah ta nuna mata Indo tace yana gaishe ta, Kuma yana mata ta’aziya, idan kuma ta samu network ta kirasa a waya ta haɗasa da Indo.

Ranar Laraba da safe su Momy suka ɗauki hanyar DASINA, daddy ne yayi waya da mustapha yake tambayar sa yaushe zai iso Dasina, sanar dashi yayi cewa sai gobe idan Allah ya kaimu, sannan daddy ya kashe wayar sa, RAUDA suka fara sauƙewa a ƙofar gidan su, kafin suka ɗauki hanya, tare da direban Daddy………………..

Dan Allah kuyi hkr da wannan wlh yau ina da makaranta, shiyasa ban samu nayi muku typing mai yawa ba.

*Vote*

*Share*

*And*

*Comments*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah ce)*

[1/31, 6:20 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*

*Nasmah ko Nasirah*

*Sara da Sassaka*

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.

Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*

____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

*P*•••••••2️⃣9️⃣ ➡️ 3️⃣0️⃣

Sha biyu dai-dai su Momy suka iso cikin ƙauyen DASINA, cincirindon mutane, suka hango sun taru, daga nesa Momy ta hango yara biyu tsakiya sai famar dakuwa suke yi, Daddy ne yace direba yayi parking, parking yayi, ko kafin Daddy ya fito Momy ta rigasa, cikin sauri ta karasa wajen, Indo ce da Garba suke famar dakuwa, yayin da Indo tayiwa garba duka, ta ɗane ruwan cikin sa, sai dukan sa, take.

” Subhanallah Momy ta furta, tare da kamo hanun Indo da niyar janyeta daga jikin Garba.

Ƙwace hanunta Indo cikin masifa tace.

” Babu ruwan ki dani, ki barni naci ubansa, wlh ko gaba aka ambaci sunana saika gudu.

Kallon mamaki Momy ke bin Indo dashi, yarinya ƴar ƙarama da ita, ta dage sai dukan ƙaton namiji take, cewa Momy tayi.

” Haba baiwar Allah, kina mace kina faɗa da namiji, ki tashi kansa nace, wannan ai rashin Hankali ne, wawiya kawai, kina mace kin zauna sai kokuwa kike da namiji.

Indo dai taƙi ɗaga Garba Kuma a hakan take yiwa Momy tsiwa.

” Ni dai wlh ba wawiya bace, kiji mata dai, daga zuwan ki, baki san meya haɗamu ba, ki hau zagina, shi namijin cewa akayi mace baza tayi faɗa dashi ba, ni bana son shishshigi, kuma niba marar Hankali bace, da hankali na ehhe😏.

Salati Momy ta ɗauka tare da riƙe baki, tana jinjina fitsaranci irin na wannan yarinyar, gaskiya ita tunda Uwar ta, ta haifeta bata taɓa ganin marar kunyar yarinya irin wannan ba, a take a wajen tsanar Indo ya ɗarsu a zuciyar momy.

Ƙara sowa Daddy sukayi shida Ishaq, yana Cewa.

” A’ishah yaya dai, muna jiranki mun jiki shuru, har yanzu basu rabu bane.

Kaɗa kanta Momy tayi tace, waɗannan ba masu rabuwa bane, Alhaji muje kawai.

” A’a A’ishah ya zakice haka, baki rabasu ba dai, ƙarasawa Daddy yayi, ya kama, hanun Indo yace, tashi a kansa kinji ƴata, babu kyau faɗa, maza tashi.

Kallon Daddy Indo tayi sai kuma ta tashi akan garba tana nunasa da yatsa tana cewa.

” Daga kai har Zainabu munafukar data turo ka, sai naci ubanku, ka faɗa mata itama saura ita, ba ita bane munafuka, har zata zugaka, tace maka munyi sadaka da mintin ka, to munyi sai axo a daure mu.

Jan Hanun ta Daddy yayi ya fitar da ita daga wajen yace maza tafi gidanku kiyi hkr ya isa haka, Momy dai bin Indo take da kallon mamaki da kuma tsana, harta bacewa kallonta, jin ihun yara da sukayi suna cewa, jama’a Indo ta kashe garba baya motsi wlh, da sauri su Daddy suka ƙarasa kan Garba, da gudu wani yaro ya tafi kiran baban Garba, taɓa ƙirjin Garba daddy yayi, yaji ai suma yayi, ana haka mahaifin garba ya iso wajen, masifa yage da zage-zage, dakatar dashi daddy yayi yace.

” Kayi hkr Mlm Usman, suma yaronka yayi ba mutuwa, ba, ruwa aka mikowa Daddy ya zubawa, garba, sai kuwa gashi yaja numfashi tare da tashi a firgice.

Sai a lokacin Mlm Usman ya gane Daddy, hanu ya mika masa yana cewa.

“Alhaji Haruna kaine cikin garin namu, ai ban gane kaba, tsabar bala’in wannan yarinyar, yarinya ta zamewa garin mu, masifa kullum da maganar da take jawo mana, to wlh tunda abun nata ya fara kaiwa da neman rai mai gari shine kawai zai rabamu da ita, tunda ta gagari iyayen ta.

Murmurshi Daddy yayi tare da cewa.

” Haba Mlm Usman meyayi zafi haka harda kai ƙara wajen mai gari dan Allah kayi hkr kabar maganar haka ta wuce, ƴar waye ce yarinyar?

” Ƴar waye kuwa bayan ƴar Amininka Mlm Musa, Allah saina kai su ƙara kagama tafiyata, shigewa Mlm Usman yayi, ba tare daya saurari me Daddy zaice ba.

Kallon Daddy Momy tayi, tace.

” Yanxu wannan ƴar Mlm Musa ce, Lallai toka ta haifi wuta, bayin Allah da haihuwar hatsabibiyar yarinya.

” Ya Isa haka wannan maganar A’ishah, Allah ya shirye ta ya kamata ki furta, bawai kike ambaton magana marar daɗi ba, shige mu tafi.

Komawa mota sukayi, ita dai Momy tana mamakin wai Indo ƴar Maryam ce, har suka isa gidan Innah basu sameta ba, domin kuwa tana gidan su Indo, wajen Mama, sai Daddy ne yace wata kila tana gidan rasuwar, bari naje na duba mu gani.

Zagawa ƙofar gidan su Indo daddy yayi, ya samu su Mlm Musa zaune a kofar gidan nasa su wajen huɗu, dake ana ɗan zuwa masa ta’aziya, kasancewar yau satin jummalo da Rasuwa.

Nlm Musa yaji daɗin zuwan aminin nasa, cikin murnar ganin juna sukayi musabaha, daddy ne yace.

“Musa ashe Jummalo kuma taxo ƙa’ida, Allah ya jiƙanta da rahama yasa ta huta.

” Ameen Alhaji Haruna, lokaci, yayi babu yanda muka iya, sai dai mu bita da addu’a.

Daddy ne yace.

” Naso muxo tun washe garin ranar da ka sanar dani, sai kuma Allah bai nufa ba, Innah ma naga bata cikin gidan nata.

Murmurshi Baba yayi yace.

” Ai Babu komai Haruna gaisuwa bata ruɓa, Innah tana cikin gida, mu karasa cikin gidan.

Shiga cikin gidan sukayi, suka taradda Innah da Mama, sai Goggo haule addar Mama, suna zaune, Goggo taji daɗin ganin ɗanta, bayan an gaggaisa ne, Innah take tambayar sa, Momy, sanar da ita yayi cewa ai sunxo suna gidanta, faɗa Innah tahau yi, tana cewa, meyasa basu sauƙa a nan ba, zasu shige cikin gidan ta, to maza yace su karaso nan.

Murmurshi daddy yayi kasancewar yasan halin mahaifiyar tasa, ya tashi yaje ya cika umurnin ta, tare suka dawo daddy ya zauna a wajen su Baba, tare da sawa aka sauke musu kayan Abincin daya kawo musu.

Da Sallama Momy suka shiga, amsa musu Mama tayi tare cewa.

” Barka da zuwa Hajiya A’ishah, lale maraba.

Zama Momy tayi cikin fara’a, sannan suka gaisa da Mama ta mata ta’aziya.

Maida hankalin ta, wajen Innah Momy tayi cikin darajawa ta gaisheta.

Amsawa Innah tayi tare da tambayar ta, mustapha da Habeeb.

” Innah Habeeb ya koma, London, mustapha Kuma yana inugu amma idan Allah ya kaimu gobe zaizo.

Allah ya kaimu Innah tace, sannan Momy ta gaishe da Goggo haule.

Ruwa da abinci Mama ta gabatar musu.

Ishaq kallon wani iri yake yiwa shinkafar, domin kuwa shi gaskiya ji yake bazai iya cin abincin ba, Sharifa Sharif Momy sukan duk sunci, amma ishaq yaƙi ci, Momy sarai ta gane nufin Ishaq wato dai abincin ne bai masa ba, shiyasa yaƙi yaci.

Daddy ma an fitar musu nasu abincin waje shida direban sa.

Kamar munafuka Indo ta shigo cikin gidan tana raɓe raɓe, tsawa Mama ta daka mata tace.

” Ke Indo, tsayuwar me kike anan baki ga mutane bane da bazaki gaishe suba.

Tura baki Indo tayi, sannan tace, to sannun ku ina wuni.

Tsabar haushi Momy bata amsa ba, sai Sharifa ce, ta amsa da lafiya.

Duban Indo Mama tayi tace.

” Ina sugern dana aike ki yake tun ɗazu sai yanxu kika ga damar dawowa.

Kame kame Indo ta fara cikin kuma tura baki take cewa mama.

” To ba, Garba bane, ina cikin tafiyata, ya tare Ni, yake cemin wai saina biyasa mintinsa da muka ɗaukar masa a shagon babansa, na rantse da Allah Mama ban kulasa ba, naci gaba da tafiya ta, shine fah ya jawo min rigata, nikuma shine na kamasa da faɗa bayan mun gama faɗan ne, na nemi kuɗin aiken da kika min na rasa wallahi Mama nidai banso yin faɗa ba, shine yasani.

” Innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un, nikam na shiga Uku dake Indo, yanxu kenan ban isa na aikeki ba, Indo, kullum sai kin ɓatar min da kuɗi, ki kuma jawo min magana cikin gari, da wanne kike so naji ne, da zafin mutuwar jummalo zanji koko da masifar da kike ɗauko min iy…………

Dakatar da Mama Innah tayi itama cikin faɗa tana cewa.

” Ya isheki haka mairo, sai wani innalillahi kike ambata kamar wacce kika gamu da masifa, to ya isheki haka, shi garban kinsan meya mata, nawa nema kuɗin da kika aiketan ina Murtala uku ce, kike famar tada jijiyar wuya, to ahir ɗinki na kara jin kinyi magana, itace ta kashe jummalo da kike cewa da zafin me zakiji, zonan ƴar Albarka, ta kira Indo.

Tahowa Indo tayi, ta zauna kusa da Innah, tare da kwantar da kafaɗar ta, akan na Innah.

Kallon mamaki Momy suke bin Innah dashi, yanda take ta ɗaurewa karya gindi, wata irin tsanar Indo ne, ya kara ɗarsuwa a cikin Zuciyar Momy.

Mama kam ta kasa magana tsabar haushin daya isheta, danta fiskanci Innah itace take ƙara, lalata tarbiyyar Indo, gashi kuma bata isa tayi magana ba.

A gidan Innah su Momy suka kwana, da safe ma da koko da ƙosai suka karya, dole ce tasa Ishaq yaci badan yana soba.

Da sassafe Baba da Daddy suna Zaune kofar gida suna taɗin yaushe gamo, suka ga, Dogarin sarki, bayan sun gaisa ne yake sanar da Baba cewa mai gari na neman sa a fada shida Indo da misalin ƙarfe goma na safe.

Amsawa Baba yayi da to, domin kuwa yasan Indo ce, yauma ta ɗauko masa magana.

Nisawa Daddy yayi tare da fara bawa Baba lbrn Abunda ya faru jiya shigowar su garin ya ƙarasa zancen da cewa, ina ga akan maganar mai gari yake neman ku, amma bazamu yanke hukunci, ba, sai munje munji kiran shi mai garin.

” Wlh Alhaji Haruna, na gaji da yarinyar Indo, da akwai Inda zan kaita, na samu tabar garin wlh dana kaita na huta, kullum cikin jawo min magana take wajen al’ummar gari

Murmurshi daddy yayi tare da duban Baba yace.

” Haba Mlm Musa, yarinta ce ke damun Indo, zata gyara idan ta girma, addu’a ya kamata mu dinga mata,a matsayin mu, na iyaye gareta, Kuma da kake maganar inda zaka kai Indo, ina ka barni, nima ai ubane ga Indo, insha Allah da Indo zamu koma Birni, karka damu.

Murmurshi Baba yayi tare da cewa.

” Alhamdulillah dako naji daɗi wlh, na samu na huta da kawo togaciya.

Dariya Daddy yayi sannan suka cigaba da zancen duniya.

Karfe tara dai-dai na safe mustapha ya shigo cikin garin Dasina…….

Kuyi hkr wlh school ya sani gaba, wannan ma dakyar na samu nayi typing ɗinsa, idan kunci karo da typing error kuyi hkr banyi editing ba.

Karku manta da cewa bana typing asabar da Lahadi.

*Vote*

*Share*

*And*

*Comments*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah)*

[2/2, 9:16 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*INDO* *ABIRNI*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

Na

Rasheedat Usman

Ummu Nasmah

Marubuciyar

Sauyin Rayuwa

Nasmah ko Nasirah

Sada da Sassaka

Tallah Tallah Tallah Tallah

Rabarine dake dauke da tsantsar soyyayah, tare da munafurci.

Akwai darasin rayuwa sosai a ciki.

Zai kuma fad’akar daku ya kuma nishad’antar daku.

Kudai ku biyo ni karku sake a baku labari.

*Ga kad’an daga ciki.*

” Wacce irin mahaukaciya ce ke, ki duba kiga yanda kika bule ni da k’asa, wawiya marar hankali, zaki kauce min da gani ko sai na makeki, useless kawai.

Tura bakin ta INDO tayi, tace wlh baxan bar nan ba sai kace kana Sona, shikenan, sai dai ni kad’ai nata sonka kai baxaka soni ba, wlh yau sai kamin irin Abunda nake gani a tibin Hajiya Inna,

Bari na tuno abun ma 🤔

Yawwa kiss, kiss suke cewa wlh sai kamin kafin nabar nan.

Zaro ido waje Mustapha yayi, yace.

” Allah ya sauwak’a naso k’azama irin ki, k’azamar k’auye, waima tukunna uban waye zai Miki kiss, da wad’annan yellow hak’waren, b’ace min da gani kafin na targad’a ki.

Murgud’a masa Baki tayi, tace

” Wlh sai ka mini, rarumo rigarsa sa tayi ta dugungune a ciki, sai tsalle take, cikin rigar sa, tana ihu, tana cewa, wayyo Allah na shiga Uku Ya mustapha yak’i mini kiss, wayyo Allah Juma’a kuxo, ni kad’ai nake sonshi shi baya Sona.

Da gudu ta shigo cikin gidan,.

Hajiya Inna dake zaune gindin murhu, ta tashi a birkice tabi bayan INDO da gudu itama.

Gudu suke sanda suka shiga d’akin innah, sannan dukan su suka tsaya, cikin Hakki Hajiya Innah tace,

” Ke Indo gudun me kike haka, meya faru macijin nan ne, ya K’ara biyo ki yauma koh.

Dariya Indo ta shek’e dashi tana nuna Innah da yatsa, tace

” Amma dai Inna ke ba k’aramar matsoraciya bace wlh, daga gani na ina gudu sai ki biyo baya na.

K’ara shekewa da dariya tayi, tana nuna Innah yanda taga Innah tayi tsamo a gefe.

Na rantse da Allah Alhaji baza’ayi wannan Auren ba sai dai kuma Idan mutuwa nayi ayi, Amma banda dai ina Raye, yarinyar da ake labarin ta addabi kowa a garin su, hatta iyayen ta sun gaji da ita bata ragawa kowa, shine ni za’a d’auko masifa a kawo min gida, to Wlh baxai yiwu ba, ku sanja lale.

” K’arya kike Habiba wannan Auren dole sai anyi shi karki manta da cewa Umarnin Hajiya ce kuma dole nabi umarnin mahaifiya ta.

” Oh haka kace koh.

” Eh haka nace.

” Shikenan to ayi mugani.

Na shiga uku ni Maryam, yarinyar nan, zaki kashe ni kwana na bai k’are ba, Yanxu INDO mai garin Kika zaga, hankalin ki ya kwanta, gashi can sun Kama mahaifin ki ta dalilin masifar ki.

” Mama kiji ki da wata magana dai, wai na jawa baba masifa, masifar mai na jawo Masa, mai garin bashi ne ya fara zagin ubana ba, shine nima na zagi Uban sa, kinga ai Anyi One One Babu bashi, kuma wlh Mama, muddun mai gari ya zagi baba koya sa aka rufe sa, to Wlh ya jawa kansa masifa dan wlh baxan barshi yasha iska a cikin garin nan ba.

Mun gaji mlm Musa, ka d’auki y’arka kubar garin nan, tunda y’arka tafi k’arfin ka, har yaushe zamu zauna yarinya tana samu cikin masifa.

Kayi hkr mai gari d’an yaune ka haifesa baka haifi Halin sa ba, wlh ina iya bakin k’ok’arina akan yarinyar nan.

” Malam zan iya kashe ko nawa ne, muddun zaka wargaza wannan Auren koda dukiya tace gaba daya zan iya mallaka maka ita, indai za’a fasa Auren nan.

Batayi tunanin ko yana d’akin ba, kawai tasa kanta cikin d’akin, dressing mirror ta nufa, tasa hanun ta da niyar d’auko turare, cikin rashin sa’a Gaba d’aya kayan saman mirrorn suka yo kasa, ji kake tas !! tas !! tas kwalabe sun fashe, a matuk’ar Razane mustapha ya farka daga baccin, dafe kansa yayi sanadin ganin INDO tsaye, ta zubawa kwalaben ido sai dariya take tana cewa.

” Maganin d’an gwalli, idan ba iskanci ba, meya had’a namijin da kayan kwalliyan Mata.

Tsawa ya daka mata, yace

“Ke mahaukaciya uban waye ya baki damar shigo min d’aki

Harara ta daka masa tare da murgud’a masa Baki tace.

” *Uban Kane*

Habiba kiji tsoron Allah ki kyale yaran nan suyi Auren su, karki bari Rabo ya kashe ki.

“Wlh Yaya baxan bari ba, sai dai Rabon ya kashe ni, idan yaso ayi bayan Raina.

Ku biyo Alkalamin Rasheedat Usman

Karku bari a baku labari

[2/2, 10:06 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*

*Nasmah ko Nasirah*

*Sara da Sassaka*

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.

Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*GODIYA*

Gareku *Hassan Tanko Hussaini 80k Mu’az* baxan gajiya da godiya gare kuba, Ubangiji Allah ya saka muku da alkairinsa, ya baku abinda kuke nema duniya da lahira, ya rabaku da baƙin cikin duniya🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*

____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

*P*•••••••3️⃣1️⃣ ➡️ 3️⃣2️⃣

Bayan yayi parking ɗin motar sane, ya nufi wajen su, Baba, dake zaune suna zancen duniya, har ƙasa ya sunkuya ya gaishe da iyayen nasa.

” Baba ya haƙurin rashi, jummalo kuma anxo ƙa’ida.

” Hkr alhamdulillah Mustapha, ya hanya.

” Hanya alhamdulillah Allah ya jiƙanta Baba yasa ta huta.

Da ameen Baba ya Amsa, Daddy ne, yace.

” Muhammad Mustapha ya hanyar dai.

” Daddy hanya alhamdulillah, tun jiya naso shigowa, to ban samu na ƙarasa Abunda nake bane shiyasa, bari na shiga cikin gidan nayiwa Mama ta’aziya.

A fito lfy daddy ya masa sannan mustapha ya shiga cikin gidan su, Indo.

Sallama yayi Mama dake sunkuye tana alwala, ne ta ɗago kanta, ta amsa Sallamar tana yiwa Mustapha sannu da zuwa, tare da ajiye masa kujera ƴar tsugunne, zama mustapha yayi yace.

” Ina wuni Mama,

” Lfy lau Muhammad ka samu isowa kenan.

” Ehh Mama na samu shigowa, ya haƙurin rashi, jummalo taxo ƙa’ida.

” Hrk alhamdulillah, jummalo kwana ya ƙare.

” Allah ya jiƙanta da rahama yasa mutuwa hutuce a gareta.

” Ameen Muhammad ameen na gode sosai, da ya aikin naka.

” Aiki alhamdulillah mama.

INDO da fitowar ta kenan daga banɗaki, tayi tozali da mustapha, wani irin tsalle ta daka tare da tahowa gaban mustapha da gudu ta tsugunna tana kallon sa, ba tare da tayi magana.

Gabaki ɗayan su, kallon Rashin hankalin Indo suke, ta tsugunna, ta zubawa mustapha ido ba tare da tace komai ba, shikam mustapha daman can kallon mahaukaciya yake yiwa indo, domin kuwa bai taɓa ɗaukar ta, cikakkiyar mutum ba, tsaki yaja tare doka mata harara.

Mamace ta dakawa INDO tsawa tace.

” Meye haka, kinxo kinsa shi a gaba sai kallonsa kike, kamar wanda kika samu tibi.

Sai yanxu Indo tayi magana, dariya tayi tace.

” Kai Mama ya mustapha nane fah, kallon sa, nakeyi ina jin daɗi cikin raina, kuma fah Mama na daɗe bangan saba, kullum fah sai nayi mafarkin sa, sai kuma ta maida kallon ta, wajen mustapha tace.

” Ya mustapha ka ƙara kyau Alkur’an, kaga yanda kayi kyau kuwa, yawwa ya mustapha, ashe daman ku biyu ne, masu kama ɗaya, kamarku ɗaya da ya Habibu, sai dai shiya fika kyawun hali, wallahi yana da kirki, ga son mutane da fara’a, amma kai kuma kullum cikin ɓata rai kake da faɗa, Allah ya Mustapha kai baƙin Hali gareka, ni da badan badan ba, koh Aradu da ya Habibu zan koma so.

Girgiza kanta Mama tayi, cikin haushin Indo tace.

” To shashasha tashi ki tafi tunda kin gama jero maganar taki, kedai Indo zanga Ranar da zakiyi hankali.

Carap Indo tayi tacewa Mama.

” Sai randa na Auri ya Mustapha zanyi Hankali Mama.

Maganar Indo dariya ta bawa mustapha sosai yake dariya yana kallon Indo, Wai sai randa na Auri mustapha zanyi Hankali, cikin Zuciyar sa, yake cewa, ashe kuwa bazaki taɓa Hankali ba, a duniya.

Ita kuwa Indo tsayawa tayi tana kallon dariyar mustapha, domin kuwa bata taɓa ganin sa, yayi dariya Kamar haka ba, sai dai idan ta mugunta ce.

” Lah Mama kiga irin abun kumatu na, a kumatun ya mustapha, tana nunawa Mama dumple ɗin mustapha, wallahi munyi anko, sai kuma ta tsume tace, Toshi ya Habibu baida shi, nidama shine yake dashi mukayi anko.

Sallama mustapha yayiwa Mama tare da bata 30k yace, gashi Mama babu yawa.

” Mai yawan kenan mustapha Allah yayi muku albarka na gode.

Fita mustapha yayi, Indo zata rufa masa Baya, Mama ta riƙo hanun ta, tana cewa.

” Komo sakarai, uwar rashin Hankali, jeki ƙarasa min, sharata maza.

Komawa Indo tayi tana tura baki tare da ɗaukar tsintsiya tana yiwa Mama ƙananun magana.

Ita dai Mama bata kulata ba, saima sallah data tayar.

A kofar gida mustapha ya samu su Daddy wannan karon harda Tanimu, hanu mustapha ya miƙawa Tanimu sukayi musabaha, har mustapha zai shige yayi gidan Innah daddy ya dakatar dashi da cewa.

” Kaga Muhammad Mustapha, kaima kazo muje, wajen mai garin tare, kafin ka shiga cikin gidan.

Dawowa mustapha yayi ba tare daya san me zasuyi wajen mai gari ba.

Baba ne yace Tanimu ya kira Indo, kiranta Tanimu yayi suka sata a gaba, har gidan mai gari.

Fadar mai garin cike take, da mutane, Mlm Usman mahaifin Garba shima yana zaune, har da garban, zama sukayi tare da gaishe da mai gari, cikin fara’a mai gari ya amsa yana cewa.

” Haruna ashe ka shigo cikin garin nan, wato dabadan abokin ka, Mlm Musa ba, bazan ganka ba harka tafi.

Dariya Daddy yayi Yace.

” Daman zanzo yallaɓoi, ai ban isa naxo garin nan na tafi ba, banxo mun gaisa ba.

Shidai Mustapha gefe ya zauna yana sauraron su, kafin mai gari ya dubi, Mlm Musa yace.

” Mlm Musa sai kuma kaji kirana koh, yanxu Mlm Usman yaxo ya kawo min togaciyar ƴarka Indo, kallon Mlm Usman mai gari yayi yace, ya faɗi Abunda yake ƙarar Indo dashi.

Dallah dallah Mlm Usman ya maida magana, ya ƙarasa da cewa, dan haka bazan yadda ba, tunda har Abun ya zamo da neman rai.

Ga nan Alhaji Haruna a gabansa akayi.

Mai gari ne yace.

” kaji Abunda yace, ke Indo anyi haka ja’ira marar mutunci, sheɗaniya, faɗa min anyi haka, dan ƙaniyar ki.

Babu tsoro fuskar Indo tace.

” Anyi mai gari, Kuma wlh ko yanxu ya sake zagina, sai nayi masa shegen duka, a wajen nan, tunda shi ɗan marar mutunci ne ni so nayi ma ace mutuwar yayi ai ba suma ba, kuma wlh niba sheɗaniya bace😏.

Baba ne ya daki bakin Indo, Yace.

‘ rufe min baki dan uwar ki, wayace kiyi magana wato dai Indo bazaki daina nemo min magana ba koh.

Narai narai Indo tayi da ido tana Cewa.

” Waye yace nayi magana kuwa idan ba, mai gari ba, sai kuma ta kalli Mlm Usman, tace wato Baba Usman kaima haka kake koh, har zaka kawo ƙarata wajen mai gari ina ƴar mitsitsiya dani, ka kawo ƙarata wajen mai gari, to mai garin ubana ne, shi da kakawo ni wajen sa, to ai saiya kashe ni idan shi mala’ikan mutuwa ne, aikin banxa kawai mai garin banxa mai garin wofi😏.

Zaro ido mustapha yayi, yana kallon Indo cikin tsoro da mamaki, to wlh yanxu kam yarinyar nan ta fara bashi tsoro, wannan wacce Irin yarinya ce.

Sam bata tsoron kowa cikin rayuwar ta.

Daddy ne, ya nisa tare da cewa mai gari

” yallaɓoi dan Allah ina neman alfarma, a sallami yarinyar nan Indo ta tafi, muyi wannan maganar mu kaɗai.

Kaɗa kansa mai gari yayi shima cikin tsoron lamarin Indo yace taje ta.

Domin kuwa wannan yarinyar tacacciyar shaiɗan ce.

Baba kuwa ya kasa magana tsabar bakin ciki har Indo ta tafi.

Mai gari ne ya fara magana, cikin kaushin Murya, da kuma fushi, domin kuwa yafi ganin laifin Baba fiye dana Indo, gani yayi kamar sune suka barta take Abunda taga dama.

” Mlm Musa, mun gaji da halin yarinyar ka, cikin garin nan dan haka kasan yanda zakayi da ita, kawai tabar garin

nan, tunda tafi ƙarfin ku, ku iyayen ta, wannan wacce irin Fitina ce, duk yaran garin nan babu wanda ake kawo ƙarar sa sai ita.

Murmurshin takaici Baba yayi sannan ya cewa mai gari.

” Kuyi hkr mai gari ɗan yaune ka haifesa baka haifi halin saba, wlh ina iya bakin ƙoƙarina akan yarinyar nan, amma kuyi hkr insha Allah indo zata bar garin nan.

Gabaki ɗaya wajen alhamdulillah suka furta, mai gari ne, yace shikenan magana ta ƙare, zaku iya tafiya.

Ran Daddy Idan yayi dubu toya ɓaci, domin kuwa yaga rashin hankali wajen mai gari, taya zaice ya kori yarinya daga gari, idan bata da wajen zuwa kuma shikenan sai dai ta shiga duniya, lallai ana mulkin jahilci cikin garin nan, tashi Baba yayi a fusace ya cewa mai gari.

” Naji na gode tunda har ka kori ƴata cikin garin nan nima ka koreni, karka manta da cewa Indo Macece ba Namiji ba, da za’ace tabar garin, wannan kujerar bata kamace kaba, domin kuwa mulkin Zalunci kake cikin wannan garin.

Kowa shuru yayi yana sauraron Baba, shiko mustapha baiga laifin Baba ba, ko kaɗan, domin kuwa duk rashin mutuncin Indo bai kamata ace an koreta, cikin garin ta, na haihuwa ba, tabbas da za’a kira Human Right suji wannan hukuncin da mai gari ya yanke Wlh sai sun ɗaure sa.

Shiko Tanimu baice komai ba, domin kuwa duk abunda akayiwa Baba indo ce ta jamasa, tashi Tanimu yayi ya fice daga fadar cikin ɓacin rai.

Cikin ɓacin rai mai gari tace, a kama Baba aje a rufesa, tashi dogarawa sukayi, Baba musu Baba ya tashi zai bisu.

A matuƙar Harzuƙe mustapha ya tashi, zaiyi kan dogarawa, Daddy yayi saurin riƙe hanun sa, tare da girgiza masa kai.

Ficewa mustapha yayi daga wajan a matukar Harzuƙe, gidan su Indo yake da niyar zuwa, domin kuwa yau sai yayiwa Indo dukan mutuwa, tunda har ta jawa mahaifinta cin mutunci.

Shi kuwa Daddy duban mai gari yayi, sannan yace.

” Yallaɓoi dan Allah kayi hkr, ka saki Mlm Musa, indai magana akan Indo ce, ta ƙare daga yau, domin kuwa nine zan tafi da Indo birni, dan Allah kayi hkr mai gari.

Abunka da mai kuɗi, dole idan ya faɗa aji, ko dan kuɗin sa, da ake son maula, umarni mai gari ya bayar aka saki Mlm Musa, tashi daddy Yayi tare da ajiyewa mai gari kuɗi, suka wuce tare da Mlm Musa.

Basuyi gida ba, sai sukayi shagon Baba, domin kuwa baba baya son komawa gida yayi tozali da Indo.

Cikin ɓacin rai ya shiga cikin gidan nasu, Mama ya samu Zaune, ina Indo kawai ya tambayi Mama ba tare da yayi sallama ba.

Tashi mama tayi da sauri tana cewa.

” Wani abun tayi maka koh?

” Wai Mama yaushe wannan yarinyar zatayi hankali ne, kodai tana da ciwon Hauka ne,?

” Me ta maka Mustapha ka faɗa min mana, oh ni Maryam na shiga Uku da halin Indo, ni rabona da ita, tun ɗazu da suka fice da Tanimu.

Ƙwafa mustapha yayi, sannan ya mayarwa Mama da Abunda ke faruwa.

Salati mama ta ɗauka, tana cewa.

” Yanxu an kama malam ɗin, shikenan ai hankalin ta, ya kwanta ta ɗaure ubanta, na rasa yaya zanyi da Indo, nayi dukan nayi faɗan nayi Addu’an amma Sam Indo Bata gyaru ba, saima Abunda ya ƙaru.

” Kici gaba da mata Addu’a zata gyaru insha Allah, domin bakin uwa baida hijabi da Ubangiji akan yaransu, ni bari na shiga cikin gida.

Har mustapha ya fice Mama na salallami.

Ita kuwa, hankali kwance ta shigo cikin gidan tana rera waƙar ta, Mama dake zaune ne, ta tashi tayi kan Indo.

” Indo kin kusa kasheni kwana na bai ƙare ba, yanxu Indo mai garin kika zaga, to hankalin ki ya kwanta, gashi can sun kama mahaifin ki, ta dalilin masifar ki.

” Mama kiji ki da wata magana dai, wai na jawa Baba masifa, masifar mai na jawo masa, mai garin ba shine ya fara zagi naba, shine na rama, ko banza anyi one one, kuma wlh mama muddun mai gari ya rufe Baba, to wlh ya jawa kansa masifa da bala’i dan wlh bazan barsa ba, saina ramawa Baba.

Aikuwa kamar wanda aka jefo mustapha cikin gidan, domin zai shiga gidan Innah ya hango shigowar ta, shine ya fasa shiga ya dawo, domin fara koyawa Indo hankali.

*Vote*

*Share*

*And*

*Comments*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah ce)*

[2/4, 6:10 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*

*Nasmah ko Nasirah*

*Sara da Sassaka*

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.

Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya 🙏🏻

Masoyana bazan manta daku ba, domin kun nunawa wannan book ɗin ƙauna, nima Rasheedat ina ƙaunar ku, sosai, ina kuma jin daɗin comment ɗinku, ALLAH YABAR ƘAUNA.

*بسم الله الرحمن الرحيم*

____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

*P*•••••••3️⃣3️⃣ ➡️ 3️⃣4️⃣

Alhamdulillah Mama ta furta tare da cewa.

” Gara da Allah ya shigo dakai, gata nan dan Allah karka barta da lafiyar ta, ka sanja mata kamannu dan ubanta, tunda ita rashin kunya tasa a gaban ta.

Danƙo Indo mustapha yayi, wannan karon bai tuna da ƙyamar taba, domin kuwa ranshi a matukar ɓace yake, gashin kanta ya riƙe da ƙarfi, wanda yasa Indo danna ƙara da ƙarfi tana cewa.

” Wayyo Allah na shiga uku Innah, mungu azzalumi zai kashe ni, ka sakeni nace mungu.

Ƙara jan gashin nata yayi da ƙarfi, saka ɗayan hanun sa, yayi ya riƙo hanunta, tare da murɗe hanun, yana murza sa, cikin salon mungunta, ba kuma tare da yace mata uffan ba, azaba iya azaba Indo ta fara kwasar sa, domin kuwa ji take kamar ana tsinka mata jijiyar hanun ta, kanta kuwa ba’a magana, bata kuma fasa ihu da zagin mustapha ba, murmurshin munguta mustapha yayi cikin izza da salon mungunta yace.

” Badai ke marar kunya fitsararriya ba, to yau zanga ƙarshen rashin kunyar ki, na rantse da Allah yau sai kinji azabar da baki taɓa jiba cikin rayuwar ki, daga yau mu ƙulla nida ke, muga shegen da zai haƙura.

Yau fah ran Indo ya ɓaci da mustapha ta manta da Soyayyar da take masa, idanunta sun juye da tsantsar jin haushin mustapha, ƙoƙarin kwacewa take amma ta kasa, duk kuma da haka bakin Indo bai mutu ba.

” Sakkani nace, baƙin mungu, azaba Kuma da kake kira aiko yanxu ka sake ni naji shi, ɗan isk………….

Bata ƙarasa ba, mustapha ya sake mata gashi tare da ɗauke ta, da wasu mahaukatan maruka, tankaɗata gefe yayi, sannan ya zaro Bell ɗinsa, yahau jibgar Indo dashi, wasu taurari masu hasken gaske Indo ta gani sakamakon marin daya sauƙa fuskar ta, tun Indo na zagin mustapha har bakinta ya mutu ta kasa magana, sai ruwan hawaye dake gudu bisa fuskar ta, wani nabin wani, idanunta kam sun koma kamar gauta tsabar ja, amma tsabar rashin imani irin na mustapha bai ƙyale Indo ba, sauƙe mata Bell ɗin da mustapha yayi na ƙarshe saiga fitsari Indo ta sake a jikinta, kallon ta yayi tare da cewa.

” Banxa ƙaramar ƴar iska, ko zaki rama ne, da kike kallo nah, da wasu shegun idanunki kamar na mujiya, gobe ma ki ƙara jawa iyayenki magana, kiga yanda zanyi dake.

Kallon Mustapha kawai Indo take ba tare data, tanka masa ba, domin kuwa wannan karon kallon tsana take binsa, dashi, tunda Uwarta ta haifeta ba’a taɓa mata irin wannan dukan ba, kuma wlh bazan taɓa ƙyale kaba dole saina rama Abunda ka min, bashi kaci, koba juma koba daɗe saina rama, duk cikin Zuciyar ta, take wannan maganar.

Mama kuwa ko kollon indo bata yiba, harkokin gabanta kawai takeyi, ta kuma ji daɗin hukunci da mustapha yayi wa Indo.

Ficewa mustapha yayi, ya tafi abunsa ba tare daya saurari Indo ba.

Tashi itama Indo tayi ta shiga ɗakin mama ta ɗauki, zanin ta, ta fito ta ɗebi ruwa da niyar shiga tayi wanka, sai me, hanun Indo ya kasa ɗaga bokitin ruwan, tsabar murɗan da yasha wajen mustapha, ihu Indo tasa da ƙarfi, a razane mama ta taho wajen, a tunanin ta wani abunne ya sami Indo.

” Meya sameki, kike wannan ihun.

” Ya karya ni, mama wlh ya karya ni, gashi hanuna ya kasa ɗaukar ruwa, ya karya ni, baƙin mungu azzalumi ɗan iska.

Kaɗa kanta Mama tayi, sannan ta ɗauki bokitin tana cewa.

” Maganin ki kenan ai badai ke marar kunya ba, wlh ni dai-dai yamin.

Zuwa mama tayi taje ta sa mata ruwan zafi, sannan ta kai mata banɗaki, domin kuwa tasan bakin Indo bazai taɓa mutuwa ba, shigewa tayi banɗakin tana zage zage.

Da sallama ya shiga gidan, da gudu su Ishaq suka taho suna, Oyoyo ya mustapha, murmurshi Mustapha yayi tare da kama Hanun su, suka ƙarasa kusa da Momy ya zauna yana cewa.

” Sannu da hutawa Momy kina shan ƙauye fah.

Dariya Momy tayi tace.

” Kaga ni kuma yanayin ƙauyen ya min, naso ace muyi sati, sai kuma Daddyn ku, yace jibi zamu koma.

” Ai dole daddy ya koma jibi, ko dan saboda shago, Ina Innah ta shiga ne, najita shuru gidan yayi daɗi babu hayaniyar ta.

” Tana tollet, za kuma ta fito ta sameka, yanxu ka shigo garin ne.

” Na juma da shigowa fah Momy, daddy ne kawai suka shiga dani gari, bai kuma sanar da Momy Abunda Indo tayi ba, kasancewar shi ba mai yawan zancen wani bane.

Sharifa ce, tace.

” Ya Mustapha sannu da zuwa, ya hanya.

” Alhamdulillah Sharifa, yauwa jiya munyi waya da Habeeb yake cemin nace miki kin manta da sakonsa ne, waiya kira layinki baya tafiya.

Kama kanta Sharifa tayi, domin kuwa sai yanxu ta tuno da aiken ya Habeeb, nata haɗasa da Indo a waya, tashi tayi tana cewa.

” Ai kuwa na manta, Momy bari na shiga gidan da akayi rasuwar nan, naje nakai sakon ya Habeeb, na ta’aziyar da yace na isar masa.

A dawo lafiya Momy tace mata, sannan Sharifa ta fice, riƙe da wayar ta ɗauke a hanunta.

Innah kuwa sai yanxu ta fito daga banɗaki, mustapha ta tarar zaune kusa da Momy, kan Mustapha tayi ta sauƙe masa ranƙwashi a kansa, tana cewa.

” Iyayen baƙin rai kuma an iso ne, guntsu iyayen baƙin hali.

Dariya Mustapha yayi, domin kuwa idan da sabo ya saba da halin Innah.

” Na iso, sai akayi yaya, wannan wacce irin mugunta ce, daga shigowata, ki tarbeni da ranƙwashi, waini Innah menene damuwar ki dani ne, kika sawa rayuwata Ido, to dai ko mayya ce, ke zaki ƙyaleni domin kuwa nafi ƙarfinki.

Harara Innah ta daka masa tana cewa.

” Koni mayya ce babu Abunda zanyi da namanka, naman baƙin hali, naci na kwashi tsiya baƙin rai, Allah ya sauwaƙa.

Dariyar draman Innah da mustapha, Momy keyi, domin kuwa tun mustapha yana ƙarami basa jituwa da Innah, gashi kuma har yanzu girman sa, tashi mustapha yayi yana cewa

” Sai kiyi kuma ai, ni bari ma naje nayi Abunda ya dameni, Momy bari naje nayi wanka

Carap Innah tayi tace

” Allah ya tura ƙeya.

Da sallama ɗauke a bakinta sharifa ta shiga gidan su Indo, Mama ta samu tana zaune tana tankaɗe, sai Goggo Asabe data shigo yanxu, gaishe su tayi, suka amsa, cewa Mama tayi Indo tana nan.

” Tana nan mama tace amma ta shiga wanka, ki zauna ga taburma yanxu zata fito.

Zama Sharifa tayi, tana jiran Indo, Baba ne, ya shigo cikin gidan da faɗa yana cewa.

” Yarinyar nan tana jamin cin mutuncin cikin garin nan, wlh da badan Alhaji Haruna yace zai tafi da ita ba, wlh da aurar da ita zanyi sadaka na huta da baƙin cikin ta.

Zaro ido Sharifa tayi jin ance mahaifinta zai tafi da Indo.

Mamace tace.

” Kayi hkr Mlm yanxu nan mustapha ya mata shegen duka, hatta hanunta ma kasa ɗagasa tayi, dan Allah kayi hkr.

” Naji nayi hkr, ki tashi ki haɗa mata kayan ta, domin kuwa Alhaji Haruna yace min gobe zasu wuce Birni.

” Birni Mama tace birni dai Mlm, yanxu Mlm kana ganin idan, ka bawa Alhaji Haruna riƙon Indo baka cutar dasu ba, kafa san Halin Indo ba mutunci gareta ba, bata tsoron kowa, muma iyayen ta, yaya muka ƙare da ita bare kuma wasu, ka duba wannan lamarin fah Mlm.

INDO data fito daga banɗaki take jin maganar Baba kamar sauƙar Aradu, ” waini Indo zanje birni, wayyo Allah wayagan ni a birni, Allah yakai damo ga harawa ko baici ba, yayi ɓarna.

” Kinga Maryam bana so karki sake min wata magana, maza ki tashi ki haɗa mata kayan ta, Abunda na saki kenan, ba cewa nayi kimin wata magana ba.

Tashi mama tayi tare da cewa, ” Allah ya baka hkr Mlm, bari naje na haɗa mata.

Ɗakin sa ya shige, cikin ɓacin rai, fitowa Indo tayi murna cike fal ranta, ita a dole zata birni, har zata shige taji Muryar Sharifa tace, ” Indo wajenki nazo ni.

Juyowa Indo tayi, tazo kusa da sharifa tace.

” Ni kike nema kuma, to gani me zan miki.

” Ya Habeeb ne, yace na kirasa a waya na baki kuyi magana.

Wangale baki Indo tayi tana dariya tace.

” Allah sarki ya Habibu ɗan albarka ashe bai manta da niba ba, haɗamu kinji, baiwar Allah.

Dariya sharifa tayi tace.

” Sunana Sharifa, kike kira na da haka.

” Sharifa, kirasa, aima bakiji Baba yana cewa zan koma garin kuba, nima naje na zama ƴar gaye kamar ke, ina zaki koya min gaye koh.

Dariya sharifa tayi sosai tace.

” Sosai ma kuwa, Indo zan koya miki, bari daina kira ya Habeeb ɗin, kiran wayar tasa Indo tayi, cikin Sa’a kuwa ta samesa, ringine biyu ya ɗauka, kasancewar video Call ta kirasa.

” Ya Habeeb kasan na kusa mantawa da aiken ka, saida ya Mustapha yaxo yanxu yake sanar dani, shine nayi maza nazo na haɗa ku.

Murmurshi Habeeb yayi tare da cewa.

” Ai daman nasan shirmen ki, zaki iya mantawa, ina Momy?.

” Tana gidan Innah ni nazo gidan su Indo ce, bari na bata.

Miƙawa Indo wayar tayi.

Karɓa Indo tayi tana dariya tace.

” Ya Habibu, shine kai kaƙi zuwa koh, sai wannan mungun ne, yaxo, sai kuma tasa kuka, ya Habibu kaga dukan daya min a jikina, duk zanen bulala, yasin Allah ya isa ban yafe masa ba.

” Zaro ido Habeeb yayi yace Indo bulala kuma me kika masa ya miki wannan ɗanyen aikin haka, kin masa laifi koh?

” Wlh ya Habibu ban masa laifin komai ba, kawai baƙar mugunta ce, irin tasa, da kuma *shishshigi shiga dangi da gana masgo, kawai fah Baba ya da mai gari ya tararwa faɗa, yauwa ya Habibu, ina ƙosan Innah data aiken na sayo mata Ranar da zaka tafi, har mukayi faɗa da wani Garba ya zubar min ka tuna.

Shuru Habeeb yayi yana tunani sai can yace.

” Ehh na tuna, ranar meya faru?

” To shine fah jiya na kama garba naci ubansa la’ada waje, shine suka kai ƙarata wajen mai gari, wai dan mai gari ya zagi Baba, shine wannan ya Mustapha yanxu ya dakeni, waini najawa Baba.

Dariya Habeeb yayi yace.

” Kai amma baki ƙyauta ba Indo, yanxu Abunda ya wuce ɗin shine kike ƙulle dashi ni ai harna manta da wannan case ɗin, yanxu kinsan me zai faru………

Ƙit kiran ya katse sakamakon ɗaukewar network, kasancewar network ɗin garin yawo yake.

Kallon sharifa tayi tace kinga ya mutu kuma bana ganin ya Habeeb ɗin

Karɓar wayar Sharifa tayi tace.

” Kinga network ne, ya ɗauke, ki bari sai zuwa Anjuma idan ya dawo saina kawo miki ni yanzu bari na koma gida.

” Shikenan idan ma baki zoba, ni zanxo da kaina ki cewa Innah ina son zuwa kuma Mama ta hanani fita, yau.

Murmurshi sharifa tayi tace.

” To zan faɗa mata sannan ta tafi ita kuma indo tayi ɗakin Mama, ta samu mama sai famar haɗa mata kayan ta, take.

Daddy zaune shida Momy da mustapha yana sanarda ita cewa zai ɗauki indo, su koma birni kuma gobe da azahar zasu tafi.

Zabura Momy tayi, cikin ɗaga murya take cewa.

” Me kake shirin faɗa minne alhaji, wacce yarinyar zamu tafi da ita, yarinyar data addabi garin su, ta gagari iyayenta, shine ni zaka kawo min masifa cikin gidana, gaskiya bazai yiwuba Alhaji.

” Kinga A’ishah baki isa hanani Abunda nayi niyya ba, nace zan ɗauki indo kuma saina ɗauketa, ina dai gidana ne, inda zata zauna ba gidan kiba, amma gaskiya kin bani mamaki A’ishah bantaba zaton haka kike ba, yanxu idan ƴarki ce haka ta faru da ita, wata tayi Abunda kikayi zakiji daɗi, karki manta da cewa ɗa na Kowa ne, ba’a masa mugunta, dan haka ɗaukar Indo Dole, kuma kema ki riketa.

Sannan kuma ki daina kiran ɗan musulmi da masifa, saboda baki san me zai zama ba gaba.

” Babu dole Wlh na faɗa bazamu tafi da itaba, kuma babu inda zamu da ita.

” To shikenan bari muga ta yanda zaki iya dakatar dani, cewar daddy.

Mustapha cikin ɓacin ran Abunda mahaifiyar tasu keyi yace.

” Haba Momy haba dan Allah, tunda yace zai tafi da ita ke ina ruwanki, kibarsa mana, meye Indo zata ƙara zata rage cikin gidan mu, dan Allah ki bari Momy ki riketa kawai saboda Allah karkiyi tunanin Halin ta.

” Rufe min baki shashasha, to bazan tafi da ita ba, wlh babu mai kaimin masifa cikin gida, yarinyar da bata da mutunci bata ragawa kowa, ina nan tamin rashin kunya har tana neman zagina to wlh banda gidana kam.

Murmurshi daddy yayi yace.

” Gyara kalamanki, kice gidan Haruna ba naki ba, idan kuma a gidan ki nake zaune saiki faɗa min naji.

Cikin fushi Mustapha ya tashi yana cewa.

” Daddy Momy dan Allah kuyi hkr da wannan maganar, ku bari dan Allah………

__________________________

Tirƙashi ana wata ga wata koya zata kasance, kudai ku cigaba da biyo ni domin jin yanda zata kasance.

*Vote*

*Share*

*And*

*Comments*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah ce)*

[2/5, 4:45 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*

*Nasmah ko Nasirah*

*Sara da Sassaka*

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.

Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*TALLAH TALLAH TALLAH*

*INA KUKE MAKARANTA LITTATTAFAN HAUSA TO KU MATSO KUSA GA DAMA TA SAMU, SHAHARARRIYAR MARUBUCIYAR NAN TAKU WATO ZAHRAN ABDUL MOMYN AHLAN TAZO MUKU DA SABON SALON LABARINTA, MAI TAKEN SUNA, (COLONEL UBAIDULLAHI) WANDA ZATA SAKE MUKU SHI FREE BA TARE DA KO SISIN KUBA SABODA TSANTSAR ƘAUNAR DA TAKE MUKU*.

*GA KUMA (WAYA KASHE ZAHARA’U) CANKAƊI WAYYO DAƊI ƳAN UWANA MAKARANTA, KARKU BARI A BAKU LABARI DOMIN WANNAN BOOK ƊIN ZAI NISHAƊANTAR DAKU, YA KUMA SAKU CIKIN RUƊANI, LITTAFINE WANDA AKA TSARA SHI, A NUTSE CIKIN HIKIMA DA FASAHA, NAIRA 200 KACAL ZAKU BAYAR KUSHA KARATU, CIKIN NUTSUWA DA KWANCIYAR HANKALI, 200 NE KAWAI*.

*SAI KUNXO GAMAI BUKATA SAIYA TUNTUƁEMU TA NUMBER MU.*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

*P*••••••3️⃣5️⃣ ➡️ 3️⃣6️⃣

” Sai kace ta bari, karma ta bari, idan bai mata ba daga nan saita koma gidan su ƙofa a buɗe take, amma dai Indo saita koma cikin gidana da Rayuwa.

Innah da tun ɗazu take jiyo hayaniyar sune ta shigo ɗakin tana cewa.

Hayaniyar me nake ji haka, tun ɗazu kamar waɗanda kuke faɗa da girman ku, a gaban ɗanku, wannan abin kunya haka.

Sanin Halin faɗan Innah Daddy shida mustapha har suna haɗa baki, wajen Cewa.

” Babu komai fah Innah muna tattaunawa ne, akan wani lamari.

Murmurshi Momy tayi cikin gadara da Kuma power tacewa Innah.

” Babu wani Abunda ake tattaunawa, sai masifa da ake neman ɗaura mana, mubar ƙauyen nan dashi.

Mustapha ɗaura hanun sa yayi a kansa, cikin tausayawa kansu, na masifar Innah da zasu kwasa idan taji Abunda ke faruwa.

” Masifa kuma, wacce irin masifa, kuma zaku kwasa, cikin garin nan, kinga A’ishah faɗa min meke faruwa?

Murmurshi daddy yayi domin kuwa, shi Momy sauƙaƙa masa magana tayi, gata ga Innah ta isheta riga da zani harda wando.

MOMY cewa tayi.

” Innah wai wannan yarinyar, hatsabibiyar wacce ta zamewa kowa masifa cikin garin nan, wai ita zai ɗauka ya koma da ita birni ni akaimin masifa gidana.

” Kinga A’ishah waye ce, Harunan zai ɗauka ya tafi da ita.?

” Waye kuma masifar da zai ɗauka, idan ba Indo ba, ƴar gidan Mlm Musa.

Zaro ido Innah tayi ta kalli Momy tace

” wa kika ce, masifar maimata min sunan naji, kamar banji da kyau ba?

Murmurshin jin daɗi Momy tayi ganin kamar Innah zata goyi Bayan ta.

” *INDO yar Mlm Musa nace Innah wannan fitinanniyar yarinyar data gagari iyayen ta*

Gyara tsayuwar ta Innah tayi tace.

” *Alhamdulillah na tabbatar da Abunda kika faɗa yanzu, A’ISHAH !! A’ISHAH !! A’ISHAH sau nawa na kira sunan ki*.

” Sau Uku ne kika kira INNAH.

” *To buɗe kunnen ki dakyau kiji, Wlh Wlh zan iya sawa Haruna ya Sakeki take yanxu anan, kuma dole ya sakeki, Indo da kike kira masifa, to nafi ƙaunar ta, fiye da Shi Haruna dana haifesa, ke uwata da ubana kawai zan iya ragawa akan Indo, Babu kuma Babbar masifa sama dake, da baƙya son ɗan wani Indo ba masifa bace, masifar da kike kira ya ƙare a kanki ke kaɗai, shi gidan harunan da kike cewa, indo bazata zauna ba, gidan uwarki ne kona ubanki, to bari kiji Indo tafi min waɗannan ƴaƴan naki 👉🏻, ta mata nuni da mustapha, ashe A’ishah kema baki da mutunci, ban sani ba, munafuka, mai siffar mutanen kirki*••••••••••

Cikin ƙunar rai da jin zafin abinda Innah ke faɗawa Momy mustapha yace.

” Ya isa haka ya isa, dan girman Allah kubar maganar nan, ina dai akan Indo ce, to ta koma Birnin mana, meyene danta koma, Momy ki janye ƙudirinki dan Allah, idan taje ma ba’a kanki zata Zauna ba, haba Momy meyasa kike haka ne, dan Allah kibar zancen nan haka ya isa.

” Karma ta janye cewar Innah, kallon Daddy tayi tace, kai Haruna, naji daɗin zumuncin da zakayi na ɗaukar Indo, ada kace na koma Birni nace maka bazan koma ba koh, to yanxu na janye, *ZAN KOMA BIRNI NIMA DA ZAMA DOMIN KUWA ƘAFATA ƘAFAR INDO, NAGA ALAMA IDAN NABAR INDO TA SHIGA BIRNI ITA KAƊAI WANNAN MATAR TAKA SAITA KORATA DUNIYA, KUMA DUK BAƘIN CIKIN KI, SAI INDO TA KOMA GIDAN HARUNA, KUMA TARE ZAMU TAFI*

Shuru Momy tayi domin kuwa bata da bakin magana tunda sun haɗe mata baki, amma ta ƙullaci, tsanar Indo cikin Ranta, kuma ta ɗau aniyar yaƙar Indo har saita nemi komawa ƙauye da kanta.

Muryar Daddy Momy taji yana cewa.

” Ya kikayi shuru A’ishah itama INNAH kiyi mata musun mana, hmm wato ni kika raina koh, nine ma rainin wayonki, ƙwafa Daddy yayi tare da ficewa daga cikin gidan ma gabaki ɗaya.

Itama INNAH fita tayi tana cigaba da zagin Momy, kallon Momy mustapha yayi, yace.

” Kiyi hkr Momy dan Allah karki sake cewa komai akan wannan lamarin, kibar maganar haka, idan zaki riƙe Indo saboda Allah ki riƙeta, Momy Indo ba gagararriya bace, *domin kuwa babu gagararre sai bararrare na tabbata zaki iya sanjawa Indo ɗabi’ar ta, meyasa baza kiyi shahada ba, wajen gyara rayuwar ta, Momy nasan halin nafiki sanin waye Indo, a cikin shaidancinta ke bakiga komai ba, Please Momy ki daina sa’insa da Daddy, Momy koni zan tayaki gyarawa Indo zama, dan ……..

” Kai rufe min baki dallah ka tashi ka tafi kaban waje.

” But Momy ki fiskance ni mana.

” Ka tashi ka bani waje nace, ko bazaka tashi bane sai na ɓata maka rai.

” Allah ya huci Zuciyar ki.

Dole mustapha ya tashi ya fita yabar Momy, zaune cikin fushi da ɓacin rai.

Innah ma dai kayan ta, ta hau haɗawa, cikin gana masgo, tana shirin tafiya birni.

Tafiya take riƙe da kara a hanun ta, tana waƙenta, har ta iso ƙofar gidan Innah, a ƙofar gida ta samu mustapha zaune yana danna wayarsa, sanda tazo daf dashi ya ɗaga idonsa, karaf suka haɗa dana Indo, harara Indo ta dakawa mustapha tare da jan doguwar tsuka, zaro idon sa Mustapha yayi, ya nuna kansa da yatsa yace.

” Ni kikewa tsuka, da harara?

Taɓe bakinta tayi, cikin halin ko inkula ta shige abunta ba tare da ta kulasa ba.

Ƙwafa mustapha yayi yace,

” Baki san waye mustapha amma Babu komai, zamu haɗu ai zaki san kin min tsuka.

Ringine ɗin wayarsa ne yasa shi maida hankali wajen wayan baƙuwar NUMBER ya gani, da kamar bazai ɗaga ba, sai kuma ya ɗauka.

Assalamu alaikum, ina wuni ya Mustapha.

Shuru mustapha, yayi indai ba ƙarya kunnen sa ya masa ba, kamar Muryar RAUDA yake ji.

” Wa’alaikumussalam, ya furta tare da cewa waye ne bangane mai magana ba.

” ya Mustapha RAUDA ce.

Murmurshin takaicin rashin Zuciya Irin na RAUDA mustapha yayi, tambayar Rainin wayo ya mata yace.

” Waye kuma RAUDA, bangane ba, wacce RAUDA kenan?

Zaro ido RAUDA tayi, cikin mamakin wai mustapha bai ganeta ba, nunawa ma yake baisan wata RAUDA ba cikin rayuwar sa.

” Ya mustapha RAUDA ce, ta gidan Alhaji Ahmed.

tsuka Mustapha yaji, tare Cewa.

” Naji menene me kike so, kiran me kika min, me zan baki?

Dibirbircewa RAUDA tayi, ta fara kame kame.

” Amm amm daman na kira na gaishe kane.

Tsuka Mustapha yaja tare da kashe kiran yana cewa.

” Allah wadaran rashin Zuciya Wlh, mutum sai kace maye ance ba’a sonka amma ka nace.

Ita kuwa Indo sarkin hankali, Babu sallama Indo ta faɗa cikin gidan tana ƙwaƙwalwa Innah kira.

Momy dasu sharifa dake zaune suka ɗago ido suka kalli Indo, Momy ji tayi kamar ta kama Indo da duka tsabar haushin ta, Indo bata ji Innah ba, saima hango su Momy da tayi zaune da murnar ta, ta ƙarasa wajen su, Momy ta fara cewa.

” Ina kwana.

MOMY bata ɗago kai ta kalli Indo ba, bare kuma ta kulata, Sharifa ce tace.

” MOMY ana gaishe ki baki jiba

Harara Momy ta saukewa Sharifa tace.

” Da ban kwana ba zata ganni.

Dariya Indo tayi cikin shiririta da rashin sanin ciwon kai, danko ita har cikin ranta bata gane Momy bata sonta ba tace.

” *Aradu kuma haka ne, da baki kwana ba bazan ganki ba, gaskiyar kine, Sharifa baki kira min shiba har yanzu.*

Murmurshin sharifa tayi tace,

” Zan kira miki shi sai ko zuwa Anjuma, yanxu banda caji.

To Indo tace, tayi ɗakin Innah tana kiran sunan ta.

Kallon sharifa Momy tayi tace.

” Wa zaki kira mata.?

” MOMY Ya Habeeb ne zan kira Mata.

Shuru Momy tayi bata sake cewa Sharifa komai ba.

Innah ce ke cewa Indo.

” Ke Uwar ƴan kira, gani nan ina haɗa kayana tare zamu koma Birni, dan bazan barki ki tafi ke kaɗai ba, aje ana miki mungun Hali, gara mu tafi Sawu da sawu, watakil idan anga idona a rage miki.

Tsalle Indo ta doka tana cewa.

” Yawwa Innah tawa nita Allah, ko a lahira ni ina aljanna ke kuma kina kano da daron masa ɗaure a kanki.

” Oh baƙar fata zaki mini, ni bazan shiga aljannar ba saina tsaya ɗauke da daron masa naga dama saina fasa zuwa birnin.

” Kiyi haƙuri Innah ta, bazan sake ba wasa nake miki.

Washe gari da safe Mama ta fitowa Indo da kayanta, suka sata gaba ita da Baba, suka mata faɗa sosai, akan ta rage rashin Hankali, tayiwa su Alhaji Haruna da Momy biyayyah domin yanxu sune iyayenta a hanunsu zaki Zauna.

Ya Tanimu ne yace

” Allah dai yasa zuwa wannan birnin ya zama sanadin shuryuwar ki.

Ameeen Baba suka amsa dashi.

Sosai Indo ta nunawa su Baba taji maganar su, sannan suka sata a gaba har gidan Innah, sun samu suma su Innah harsun fito, bayan gaishe gaishe ne, Mama tacewa Momy.

” To Hajiya A’ishah, ganan Indo, tabar hanuna yanxu ta koma hannun ki da zama, Indo bata da kirki, dan Allah kiyi hkr da ita, kisata a hanya idan kinga tayi ba dai-dai ba, dan………

Dakatar da Mama Innah tayi tace.

” Mairo ya isa haka, Indo hanuna zata zauna ba hanun wannan ba, ta nuna Momy, dan haka daina bata hkr.

Ku ɗauki kayan mu shige mu tafi, Allah ya sake haɗamu gaba tunda nayiwa makwata ban kwana, ladi ce kawai ban samu ba, kya faɗa mata.

Dole tasa Mama shuru badan taso ba, ita kuwa Momy ko a jikinta domin kuwa koda ance an bata amanar Indo ba karb’a zatayi ba.

Girgiza kansa Mustapha yayi, yana kallon Innah.

A ƙofar gida suka taradda lami da Hansai tsaye, da gudu Indo ta ƙarasa wajen su, tana cewa.

” Lami Hansai kunji zan tafi birni koh?

Hararta lami tayi tace.

” Shine ko kixo ki faɗa mana, sai ɗazu muke ji cikin gari wai zaki koma birni mai gari ya koreki daga garin nan.

” Ke nifa jiya da magaruba nake jin zamu koma birni tare da Innah, kuma dare ne yayi shiyasa ban faɗa muku ba, ƙarya ne kuma ni mai gari bai kore niba.

” To dai haka Garba yake faɗi wai an koreki daga wannan garin, yanxu shikenan Indo mun rabu.

” Ke zan dinga kawo muku ziyara, baga su Mama ba, ai zanke zuwa.

Shikenan to Hansai ta furta tace Allah ya kiyaye hanya.

Ameeen Indo tace, sannan suka je wajen motocin tare.

MOMY da Daddy dasu Ishaq mota ɗaya suka hau motar direban Daddy, shi kuma mustapha da sharifa da Innah sai Indo motar mustapha suka hau, Sharifa ce a gaban Mota Innah da Indo kuma suna baya, ƙauyanci Indo ta fara tun shigar ta motar, hanunta tasa zata kamo wani danja daga cikin motar tana cewa.

” Oh bature ma dai shege ne, Innah kiga yanda yanda motar nan ke sanyi sai kace firji, harfa ƙamshi motar take kiji kujerar ma laushi aradu.

” Hararar Indo mustapha yayi ta madubin motar ba tare daya kalleta yaja motar sa.

INDO tana ɗagawa su lami hanu har suka ɓacewa kallon ta.

*DUTSE LOCAL GOVERNMENT*

____________________________

🤪🤪🤪🤪🤪🤪 Kuyi hkr gaskiya bazan shiga cikin dutse yauba ku biyoni next page, domin ganin *INDO A BIRNI* dan yanxu ne littafin zai amsa sunan sa.

*COMMENTS ɗinku yayi sanyi, to ku sani idan baku gyara ba, nima typing ɗina zaiyi sanyi, na fara slow daman school ya sakoni gaba, daurewa kawai nake ina yin typing wlh domin ku masoyana*.

*Vote*

*Share*

*And*

*Comment*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah ce)*

[2/7, 3:57 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*

*Nasmah ko Nasirah*

*Sara da Sassaka*

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.

Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*

____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

*P*••••••3️⃣7️⃣ ➡️ 3️⃣8️⃣

“Mamy na rasa ya zanyi, mustapha baya saurarata, ko kiran sa nayi, sai ya faɗa min baƙar magana, kafin ya kashe kiran.”

Cikin faɗa Mamy take cewa RAUDA.

” Nifa RAUDA na gaji !! na gaji !! Da lamarin ki da mustapha, akan me kullum abu ɗaya yaƙi ci yaƙi cinyewa, keba mace bace, da bazaki jawo hankalin Saba, maganin ma, dana baki kin kasa Zuba masa, to yaya kike so na miki, zuwa zanyi na jawo sa, nace dole ya soki, RAUDA ki saurareni da kyau, idan zaki tashi ki nemo soyayyar mustapha to ki tashi, domin kuwa, nunawa mustapha da kike a Soyayyar ki, a fili, bazai kaiki ba, dole sai kin rage shigar masa, ki daina nuna masa maitarki a fili, ki kama Class ɗinki, cikin kirsa zaki samu ki sawa mustapha wannan maganin abincin sa, domin kuwa idan yaga kin fita harkar sa, to fah dole zai ɗauke Idonsa a kanki, sai ke kuma kibi wannan hanyar ki, samo kansa, ina fatan kin fahimce ni.”

” Eh Mamy na gane, kuma insha Allah zanyi amfani da Wannan shawarar taki.”

” Yauwa koke fah, yanxu yaushe zasu dawo daga ƙauyen?”

” Bansani ba, amma Momy tace, idan sun dawo zata kira ni.”

” Shi kenan hakan ma yayi, yanxu ki tashi kije, ki ɗaura mana abinci, ni bara naje na gyara ɗakin Abban ku.”

” To Mamy.” RAUDA ta amsa tare da tashi tayi kitchen.”

Misalin ƙarfe biyu na azahar, su Indo suka shigo cikin gidan, bayan sunyi parking ne, kowa ya fito, kalle kalle Indo take, cikin ƙauyanci, baki buɗe take kallon fulawin dake, zagaye ƙofar gidan, da gudu tayi gun fulawin tare da taɓa su, tace.

” Lah !! Innah kinga wasu Abu masu ado, Innah sun miki kyau kema, nidai aradu sun min kyau.”

Duban ta, itama INNAH takai wajen, tace.

“Sunyi kyau sosai ma, ikon Allah!! Wani abu sai birni, ki duba yanda aka shuka waɗannan Adon kamar zama aka zo duniyar ba za’a mutu ba, yayi kyau.”

Mustapha ne yaja suka da ƙarfi tare da hararar ta, ita kuwa Indo ko a jikin ta, bata sanma yana yiba, domin kuwa, ta bada hankalin ta, gabaki ɗaya, wajen wannan fulawin, murmurshi daddy yayi sannan yace.

” Sharifa, maza jeki ki jira Indo, idan ta gama kallon fulawin, sai ku shigo tare, Innah mu shiga cikin gida, zasu taho da sharifa.”

Kallon sharifa Innah tayi tace.

” Ke Sharifa, kibi Indo a hankali, banda faɗa banda tsangwama, Wlh ko kallon banxa kika mata naji labari, hmm !sai naci ubanki.”

Murmurshi sharifa tayi tace.

” To Innah naji, babu abunda zai shiga tsakanina da ƴar zinaren ki.”

Shigewa Innah sukayi da Daddy suka bar Indo tsugunne gaban fulawi, tana famar tsinka.

Murmurshi, sharifa tayi ta ƙaraso gaban Indo ta sunkuya, tace.

” Wai kyau suka miki ne? naga sai tsinka kike, me zakiyi dashi?”

Washe baki Indo tayi tace.

” Zan tarasu ne, naje nata kallon su, shigen irin waɗanda nake ganine a tibin Innah, indiyawa suna bawa masoyan su, nima masoyina zan bawa.”

Cikin mamaki Sharifa tace.

” Masoyinki kuma! Waye masoyinki a cikin garin nan?, naga dai baki san kowa ba, cikin garin nan, yanxu kika shigo, kodai ƙauye zaki aikawa saurayin naki?”

” Kiji ki Sharifa da wani zance wani ƙauye kuma, bayan ga nan ya Mustapha na, a cikin gida, nidai shine masoyina kuma shi zan kaiwa fulawar soyayyah.”

Razana sharifa tayi, cikin zaro ido tace.

” What! Wani ya Mustapha, ya Mustapha wanda na sani, na cikin gidan nan, shine saurayin naki?”

Indo tana dariya tace.

” Eh mana shine, sai dai fah, yana da baƙin Hali, gashi da masifa, kuma aradu mungu ne, azzalumi, sai dai duk da haka ina sonsa.”

Shuru sharifa tayi tare da kama baki tana mamakin rashin hankali Irin na indo, “to idan ba rashin Hankali ba, ina Indo ina ya Mustapha, lallai kam kin jawa kanki wahala wajen ya Mustapha.” duk cikin ranta sharifa take wannan maganar.

Sanin rashin hankalin Indo, zata iya zuwa gaban Momy da Daddy tacewa mustapha ga fulawar soyayyah, yasa Sharifa lallaɓa indo ta hanyar cewa.

” Kinga Indo, nikam Ranar da kukayi waya da ya Habeeb, sai naji kamar kina faɗa masa cewa ya mustapha ya miki duka?”

” Eh mana yamin duka, ranar da mukayi faɗa da Garba, kai! Amma gaskiya ya Mustapha baƙin mungu ne Wlh, ya dinga dukana fa kamar ya samu jakar sa, Kuma Allah saina rama, komai daɗewa.”

Dariya ce, taso ƙwacewa sharifa, sai ta ƙunshe ta, tace.

” To yanxu ke dan Allah mutumin daya miki wannan dukan ne, zaki basa fulawar soyayyah, duk yanda kike da ajin nan, aisai ya raina ki, haba ƙawata, ki kama ajin ki, dan Allah karya raina ki, kinsan me zai faru yanxu?”

” A’a ban sani ba saikin faɗa.” Indo ta ƙarasa maganar tana tura baki.

” Kinga karki yadda ki basa wannan fulawar, domin idan yaga yana dukan ki, kina binsa, to wlh kullum ya dinga dukan ki, kenan yana raina ki, kinga ni kuma bana son haka ta kasance, tunda kinga yanxu kin zama ƙawata, bazan so Abunda za’a raina kiba.”

Shuru Indo tayi, tana tunani, sai can ta ɗago kanta tace.

” Kuma fah haka ne, amma ai zan rama nima ba barinsa nayi ba.”

” Eh ko zaki raman dai, yau Kam karki basa fulawar nan, har sai kin rama tukunna.”

” Na yadda to, amma dai zan ɗauki, guda ɗaya na dinga kallo, suna min kyau ne.”

” To shi kenan ɗauki mu tafi.”

Ɗauka Indo tayi, sannan suka wuce cikin gidan, a falo suka taradda su Momy kowa yana zaune cikin gajiya, sai Mustapha kawai da ya haura sama, shine baya falon, ɗakin dake ƙasa a falon Daddy yace.

” Wannan ɗakin shine, wanda Innah zata zauna a cikin sa, A’ishah ku gyara ɗakin keda sharifa, ita kuma indo zata haura sama, su Zauna tare da sharifa, tunda daman bed biyu ne cikin ɗakin.”

Da to Momy ta amsa, sannan ta tashi tayi, ɗakin tana cewa Sharifa ta shiga kitchen ta ɗaura musu girki.

Daddy ne, yace.

” Kubar girkin nan, kawai bari mustapha ya fito yaje ya mana ordern abinci. ”

Innah ce, takai duban ta, gefen ta, sai taga wayam Babu Indo, duba tsakiyar falon tayi, nan ma wayam Babu Indo.

” Kai wai ina Indo ce, bandan ta, ba fah.”

Daga bayan kujerar da Innah take suka ji Muryar Indo na cewa.

” Gani nan a bayan ki, Innah, *Wallahi sanyi nake sha Allah wannan abun ƙasan sanyi garesa, shiyasa ma na kwanta, naji sanyin da kyau, Wlh Indo ƴan birnin nan wayo suke mana, suna shan daɗi Abunsu, to Innah shi wannan wani irin suminti ne, mai kwalliya*.”

Leƙa inda take maganar sukayi, tana kwance abunta ƙasan tayels sai birgima take tana taɓa shi, ita a dole tana jin sanyi.

Murmurshi daddy yayi, domin kuwa, yarinta ce tsantsa ke ɗawainiya da Indo.

” Kinga Indo taso maza karki ɗebi mura, zoki zauna nan.”

Tashi tayi tana dariya ta dawo kusa da Innah tana taɓa kujera, dannawa tayi da hanunta taji hanunta ya nutse cikin, dariya tasa, tace.

” Lah ! Wallahi Innah shima laushi garesa, da ƙarfi ta faɗa kan gurar, tana famar dariya.”

Ƙauyanci kala-kala Indo ta nuna sa, a falon, Momy ce ta fito daga ɗakin da Daddy yace na Innah ne, Bayan ta gama gyarasa, zuwa tayi tace.

” Innah an gama gyara ɗakin ki shiga muje, na nuna miki Bayan gida da yanda zakiyi amfani dashi.”

“To Innah.” tace sannan ta tashi tabi bayan Momy, itama Indo tashi tayi zata bi bayan Innah, Sharifa ta riƙo hanunta tace.

” Ki tashi muma muje namu ɗakin, tare zamuke kwana ai, muje muma muyi wanka.”

Sama suka haura ita da sharifa, suna shiga ɗakin Indo ta fara kalle-kalle cikin ƙauyanci, tace.

” *Jar Uba! Chap! Lallai fah Yanxu Sharifa nan ɗakin kine duka ke ɗaya, kuma duka kayan ɗakin naki ne, harda gado biyu, duka naki ne*?”

Murmurshi sharifa tayi tace.

” Eh nawa ne duka amma akwai ƴar abokin Daddy da take zuwa ta juma a nan, tare muke kwana, so yanxu ɗakin ya zama namu mu biyu harda ke.”

” *Wayyo daɗi nima zan fara kwana a gado mai laushi, to amma sharifa na tambaye ki mana*?”

” Ina jinki menene tambayar.?

” *Naji kince ƴar abokin daddy tana zuwa ta kwana, to ita ɗin bata da gidan uba ne, sai taxo nan ta kwana*.”

Dariya sosai Sharifa tayi, sannan tace.

” Kinga yanxu kinga ba wannan bane a gaban mu, muje banɗaki, na wanke miki wannan gashin naki, sai kiyi brush, sannan kiyi wanka.”

Taɓe bakin ta, Indo tayi sannan tabi bayan Sharifa, sosai Sharifa ta wankewa Indo gashin kanta, sunayi Indo na taɓe-taɓen kayan tollet ɗin, sannan ta bata maclean da brush tace, ta wanke haƙwaran ta, da farko Indo ƙin karɓa tayi saida suka kai ruwa rana takunna da lallashi, Sharifa ta samu ta Indo ta karɓa, tana nuna mata yanda zatayi.

” Allah Sharifa zaƙi ne, da wannan abun kamar na shanye kunfan.”

” Karfa kisha Indo, datti ne, idan kuma kinsha to cikin ki zai kunbura, Babu ruwa na.”

” To mema yayi zafi, bazan shaba, hanyar lafiya a bita da shekaru.”

Sharifa tasa Indo ta wanke bakin ta, wajen sau biyar, sannan ya ɗan fita, soso da sabulu ta bata tace tayi wanka, sannan ta fito ta barta cikin tollet ɗin tare da bata towel tace, idan ta gama ta ɗaura.

Wanka Indo tayi tas ta fito kuma ɗaure da towel ɗin, gam a ƙirjinta, hand Drayer Sharifa ta ɗauka ta jawa Indo gashin ta, cikin minti biyar gashin ya bushe tare da laushi, mai ta bata ta shafa, sannan Sharifa ta ɗauko wata, doguwar rigar ta, wanda daman ta mata kaɗan ta, bawa Indo ta saka, tare da feshe ta, da turare, fes Indo ta fito Abunda gwanin sha’awa Babu wannan ƙazantar, hakwaren ta ma sun ɗanyi haske Babu laifi, bari Indo Sharifa tayi, wajen mirro sai kallon kanta take cikin madubi, ta shige tollet Itama.

” *Aradu kayan birni akwai kyau, cankaɗi kuga yanda wannan riga tamin kyau, shin-shina jikin ta, tayi, tace, kuma fan ƙamshi nake, kuga yanda gashi nama yayi kyau*.”

Surutun ta Indo take yi har sharifa ta fito daga tollet, ta shirya suka fice zuwa fallo, da gudu Indo ta ƙarasa wajen Innah tana cewa.

” *Ya kika ganni Innah, wallahi nayi kyau, koh ban yiba Innah*.”

Dariya Innah tayi tace.

” Ai kyau kamma ba’a magana, waye ya baki kaya?”

” Innah sharifa ce, ta bani, harda turare ta samin, kinga Innah harda baki na, ta goge min.”

” Allah dai ya miki albarka sharifatu, kedai bakiyi baƙin halin uwarki ba.”

Suna cikin zancen, mustapha ya shigo Hanun sa, ɗauke da ledar take away da Daddy ya aike sa, a tsakiyar falon ya ajiye yana cewa Innah.

” Ki dai dinga zama a hankali karki karya mana kujera, ba’a saba zama ba, anfi gane ƴar tsugunno.”

” Dan ƙaniyar ka, ba’a Zauna a hankalin ba, kaji ja’iri kawai.”

” Dariya Mustapha yayi tare da Zama ya ɗauki take away ɗaya, yace.”

” Haura ki cewa Momy ganan take away ɗin na kawo, dan gaskiya ni yunwa nake ji, bazan iya Hkr har sai sun fito ba.”

Muryar Indo sukaji tana cewa.

” *Su aci-ci kenan arnan ci, ciccika rumbu, ashe dai cikin zanine da mutum bamu sani ba*.”

Zaro ido mustapha yayi yace.

” *Ke Jakar Ƙauye da wa kike*?”

Mur guɗa baki Indo tayi tace.

” *Da wanda ya tsargu nake, wanda bazai iya jira kowa ya fito aci abinci ba, dashi nake*.”

Tashi mustapha yayi yawo kan Indo, a fusace,

Bayan Innah Indo tayi da gudu, tana dariya.

Har bayan Innah mustapha yawo, zai fisgo Indo yana cewa.

” Na taɓa wasa da kene, wawiya ƙaramar ƙauye.”

Buge hanun mustapha Innah tayi, tace.

” Karka kuskura ka taɓa ta, ta, dan naga san baƙar muguntar ka, daman can ba ƙaunar ta, kake ba, kuma ƙarya tayi kai ɗin ba aci-cin bane.”

Mustapha bai saurari Innah ba, ya finciko Indo, ɗaga hanu yayi zai sauƙe mata mari yaji Muryar Daddy yana cewa.

” Kul karka fara, me ta maka daga zuwan yarinya zaka fara dukan ta.”

” Alhamdulillah! Gara da Allah ya kawo ka, to ka shiga tsakanina da wannan ɗan iskan ɗanna ka, ya fita idona dana Indo, karya kuskura ya samin yarinya a gaba.”

Murmurshi daddy yayi yace.

” Muhammad ka daina saurin hanu, fah, idan ta maka laifi ka fara mata faɗa kamin duka, kaji koh.”

” Naji Daddy” mustapha ya furta, cikin takaici ya haura sama, da kuma haushin Innah.

MOMY tana sauƙowa tana waya.

” Eh Hajiya Turai, mun dawo ɗazu, na nemi number RAUDA switch Off, so ki sanar mata cewa, mun dawo, zansa driver yazo ya ɗauke ta, da daddare idan Allah ya kaimu.”

Sallama naji Momy tayi, sannan ta katse kiran, zama Momy tayi ta buɗe ledar take away d’in, plet tasa Sharifa ta ɗauko, ta sawa kowa ta basa, jalop ɗin shinkafa ce, taji vegetables, da kuma rabin kaza a kanta, loma ɗaya Innah ta kai bakin ta, ta tofar tana cewa.

” Wlh bazan ci Abincin nan, bai min ba, aje a nemo min tuwo duk inda yake, shi zanci.”

Da sauri Momy ta ɗago ta kalli Innah, sai kuma tace.

” To Innah, bari na tashi na tuƙa miki tuwon yanxu.”

Indo kuwa cin abincin ta, take Hankali kwance tana ƙutsurar kaza, tace.

” *Amma dai Innah baki san daɗi ba, yanxu ga wannan me zakiyi da tuwo, Wlh Momy karki mata tuwo wahalar dake zatayi, idan baza taci wannan din ba, ku barta ta kwana da yunwa*.”

Zaro ido Daddy yayi yace………….

Wayyo Allah typing wahala.

*Vote*

*Share*

*And*

*Comments*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah ce)*

[2/9, 12:39 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*

*Nasmah ko Nasirah*

*Sara da Sassaka*

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.

Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

*Ina ku ke masoyan wannan shaharariyar ƙungiyar mai tarin Albarka, wace taga jiya taga yau, mai shirin ganin gobe da yardar Ubangiji, watau 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION dake group ɗin WOMEN24 TV WHATSAPP GROUP, kamar yanda a komai namu ku ke bamu goyan baya, yanzun ma muna neman wanan goyan bayan na ku wajan ganin kun zaɓi wanan kungiyar taku mai tarin Albarka a wannan gasar da za’ayi ta gaba ɗaya ƙungiyoyin social media,wanan gasar a group ɗin WOMEN24 TV WHATSAPP GROUP kaɗai za’ayi kamar yanda kuke sonmu da ƙaunar mu, yanzu ma ta hanyar zaɓen mu ne za mu gane wannan amanar da ke tsakaninmu tana nan har yanzun, wanda mun San ku masoyyanmu ne na haƙiƙa ba za ku bamu kunya ba, za mu ci gaba da suburbuɗo muku book ɗinmu kyauta kamar yanda aka saba mu dai fatanmu ku zaɓe mu, Allah ya bar so da ƙaunar da ke tsakaninmu.*

*Nasan akwai wnda za su ce basa group din WOMAN24 TV WHATSAPP GROUP ai da mun zaɓeku, tau ƴar uwa ga dama ta samu in kina son ki shiga wanan group don zaɓen wanan kungiya ta 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION ko bayan an gama zaɓe ki ci gaba da moriyar wanan group din a kan 200 kacal👌🏿ga yanda abin yake*👇🏻

*INA KUKE MASOYA LITATAFAN 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION YAU ALLAH YA KAWOMU YANDA ZA KU NUNA MANA SOYAYYAR DA KUKE MANA NAKA SAI NAKA DADIN ZAMA SAI BARE MUNA MAI FARIN CINKIN SANAR DAKU CEWA MUN SHIGA GASAR WOMEN24 TV WHATSAPP MUNA NEMAN GOYAN BAYANKU DAN GANIN ALLAH YA TAIMAKA MUN LASHE WANAN GASAR AMAN SAI DA GOYAN BAYAN,KU WAJAN ZABAR WANAN KUNGIYAR TAKU MAI ALBARKA SAI MUN JIKU ONE LOVE MY LOVELY SISTER’S*😍

Kusan cewa kungiyarmu *🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* sun cikin gangarimin gasar da award Wanda *women24 TV WhatsApp group* zasu gudanar

Awannan gasar ne za’asamu ƙungiyar da tafi kowacce ƙungiya yawan fans da Kuma bin ka’idan rubutu

Dan kisamu damar zabar kungiyarmu *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* za ki tuntuɓi wannan numban 09030159301 Dan su sakaki a *WOMEN24 TV WHATSAPP GROUP* ananne za’ayi zaɓen ƙungiyar da tafi kowacce ƙungiya yawan mabiya ita zata lashe wanan gasar.

*Women24 Tv*

Ba zaɓe kaɗai za kiyi ba,

za ki ƙaru da abubuwa da yawa Kamar haka

*Yanda ake girke-girke,*

*yanda za ki gyara jikinki,*

*yanda za kiyi makeup,*

*yanda za ki ɗaura ɗan kwali.*

Kuma suna shirye-shiryen nan na *arewa24 tv* kamar su

*TARKON ƘAUNA,*

*DAƊIN KOWA,*

*KWANA CHASA’IN,*

*JAMAI RAJA,*

*SAPNE SUHANE,*

*GIDAN BADAMASI,*

*RUƊIN ZUCIYA,*

*BAGHYA LAKSHMI,*

*AKUSHI DA RUFI,*

*AUDIO NOVEL,*

*HAUSA NOVELS.*

Kada kimanta da ranan zaɓe in kin shiga group ɗin ki zaɓi *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* tananne za ku iya nuna mana irin son da kukema ƙungiyarmu da littattafanmu.

Karku manta fa masoyanmu idan kun zaɓi labarinmu za kuyi comments ne, wannan shi ne zai nuna mana cikakkiyar ƙaunar da kuke mana, *Mun gode, Mun gode.*

Allah yabar Ƙauna da zumunci.

*P*••••••3️⃣9️⃣ ➡️ 4️⃣0️⃣

” Ƙa niyar ki A’ishatu Innan ne za’a ƙyale Saboda ke kin samu kin cika cikin ki ko.”

Tura bakin ta Indo tayi tace.

” To Daddy ita Inna ga abinci mai daɗi sai tace sai tuwo, kullum shi take ci a cikin garin mu, Allah ke Inna ƴar ƙauye ne.”

Dariya Daddy yayi sosai yace.

” To A’ishatu da ɗin innan ƴar ina ne? idan ba ƙauye ba, dukan mu, ai ƴan ƙauye ne, har ke ma.”

” Chap! Nidai Daddy, yanxu ba ƴar ƙauye bace aradu, dane nake ƴar ƙauye, amma yanzu ni ƴar Birni ne.”

Dariya Daddy yayi yana kallon inna yace.

” To inna kinji Abunda ƴar jikarki ke furtawa, wai ita ba ƴar ƙauye bane.”

Murmurshi Inna tayi tace.

” Rabu da ita ja’ira tunda ita ta koshi ai kowa ma ya kwana da yunwa bai dameta ba, indai Indo ce, ƙauye kuma shine gatan ki, Birnin dai a sama kika tsince sa.”

Ita dai Momy bata ce komai ba, a cikin zancen su, sai ma hararar Indo, da take yi ƙasa-ƙasa, tashi tayi, ta shiga cikin kitchen, ta kama aikin tuwo, domin kuwa ta ƙudurta cikin ranta cewa (idan tayi tuwon nan shine za’a ci har dare bazata sake wani girkin ba).

Sharifa ce ta dubi Daddy tace.

” Daddy ka bamu kuɗi muje kasuwa, mu sayawa Indo kaya? tunda kaga bata da wasu kaya masu kyau.”

Murmurshi Daddy ya sake yana kallon sharifa, yace.

” Babu damuwa wannan ai magana mai ƙyau kikayi, (ATM CARD ɗin sa Daddy ya ciro ya miƙawa Sharifa) gashi kije ku sayi Abunda ya kamata, sai ki dawo min da ATM card ɗin, Inna kuma idan na fita kasuwa gobe zan dawo mata da Atampopi zuwa less sai a nemi mai ɗinka musu har ita ma Indo zan kawo mata, koda yake, kinga bani ATM card ɗin nan, ku bari sai gobe da safe kuje yanxu bazai yiwu ba, dare yayi.”

Godiya Sharifa ta yiwa Daddy tare da miƙa masa ATM card din sannan ta taɓa Indo, murya ƙasa-ƙasa tace.

” Ki cewa Daddy kin gode mana.”

” Daddy na gode, Daddy za’a saya min harda, Irin wannan rigar da sharifa ta bani? wlh Daddy gare ta Daddy.”

” Murmurshi daddy yayi yace.

” Komai kike so za’a saya miki Indo, duk abunda kike so ki sanar dani ko MOMYN Ku zamu baki in sha Allah.”

Tsalle Indo tayi tana murna tana cewa.

” Yauwa! Daddyn mu, godiya nake dubu dubu, yanzu Daddy komai nake so zaka bani da gaske?”

Kaɗa kansa Daddy yayi yace.

” Eh mana zan baki komai kike so, indai baifi ƙarfi na ba.”

Tashi Sharifa tayi ta kama hanun Indo tace.

” Tashi muje ɗaki na kira miki ya Habeeb.”

Tashi Indo tayi tana dariya tabi bayan Sharifa, a ɗakin zama sukayi saman bed Sharifa ta dannawa Habeeb kira, a lokacin da sharifa ta kira Habeeb yana zaune bedroom ɗin sa, ya gama haɗa kayan sa, zai dawo gida Nigeria gobe, katse kiran Sharifa yayi sannan ya kira, ɗauka Sharifa tayi tare da cewa.

“Barka ya Habeeb, ya London?”

“Alhamdulillah! London gamu cikin ta, gobe ma nake son dawowa, da naso na shige Egypt wajen Aunty Hindu, to kuma ina tunanin hakan bazai samu ba, daman *HASINA* zan bi mu taho tare, amma munyi waya kawai zata taho jibi.”

” Wow! Yaya kace muna da babbar baƙuwa, wlh ya Habeeb naji daɗin wannan Albishir ɗin, Aunty HASINA zata zota.”

” To iya gama uwar ƴan son baƙi, ki jirata tana hanya jibi.”

Dariya sharifa tayi tace.

” Ya Habeeb ai baƙo abun sone Wlh, yauwa Ya ganan Indo tace na bata za kuyi magana.”

Cikin mamaki Habeeb yace.

” Indo Kuma! naji kamar Mustafa yace min kun dawo daga ƙauye, ko ke an barki a ƙauye ne?”

Dariya sharifa tayi tace.

” Ni dai ya Habeeb ina cikin dutse, a shango Estate, dan haka ga Indo ka tambaye ta, meya kawo ta, cikin dutse?”

Miƙawa Indo wayar Sharifa tayi tana dariya.

” Hello ya Habibu, shine ina ranar ka kashe wayar ka, bamu gama magana ba ko?”

Murmurshi mai sauti Habeeb yayi yace.

” Haba Mama na, ni na isa na kashewa uwata waya, kawai dai network ne ya katse ranar, ya akayi na jiki cikin gidan mu?”

Dariya Indo tayi tana cewa.

“Ai ya Habibu na dawo birni nima da zama, Daddy ya ɗauko mu, nida Inna yace muma mun dawo nan da zama, yace nima na zama ƴarsa, kuma yace komai zai dinga bani.”

” Masha Allah! Congratulation! To fa, yau kuma ga *INDO A BIRNI* kice ƙawata ta dawo gidan mu da zama, gaskiya naji daɗin wannan lamarin, sosai, to nima Albishir.”

Dariya Indo ta tuntsire dashi har tana kwanciya saman gado tace.

” Goro fari tas ya Habibu na.”

READ:   HADUWATA DA KE - Complete Hausa Novel

” In sha Allah gobe ina hanya nima zan dawo musha hirar yaushe gamo, nasha labari.”

Dariya tayi tace.

” Ai ya Habibu ba labari bama labarai zaka sha, Allah akwai labarai kala-kala.”

Murmurshi Habeeb yayi yace.

” Kice na kwanke kunne na, domin naji daɗin jin labarai.”

Murmurshi sharifa tayi tana mamaki yaushe ya Habeeb sukayi sabo da Indo haka.

Indo sun daɗe suna hira da Habeeb, sanda aka fara kiran sallah magrib sannan Sharifa karɓe wayar, saka Indo a gaba Sharifa tayi saida sukayi sallah tare, da daddare, bayan sun gama cin abinci, Momy ta dubi Mustafa tace.

” Mustafa ka tashi kaje ka ɗauko min RAUDA a can gidan su, yanxu ta kira ni, tana jiran azo a ɗauke ta.”

” Momy ina driver gidan su? da dole saini zanje na ɗauko ta, gaskiya Momy ta biyo driver gidan su, ya kawota.”

” Kai Mustafa! ina cewa kaje ka ɗauko ta, kana cemin drivern gidan su ya ɗauko ta, nasan da drivern gidan nasu ai nace kai kaje ka ɗauko ta, ka tashi kaje ka ɗauko min ita kafin ranka ya ɓaci.”

Inna ce, ta dube sa, tace.

” Muhammadu kaji tsoron Allah ka daina yiwa uwar ka, jayayya idan iyaye sun bada umarni bi ake, sai a samu albarka ko baka so ka tashi kaje maza.”

Harara Mustafa ya dakawa Inna yace.

” Ke kuma yaushe kika fara wa’azi? daman kin iya wa’azin ne, kika bar wannan yarinyar ta lalace.”

Baki Indo ta murguɗawa Mustafa, tana juya masa Indo tace.

” Ni dai ba lalacacciya bace ehe, sai dai idan mutum shine lalacacce.”

Kallon Indo Mustafa yayi yana huci yace.

” Da wa kike wannan maganar?”

Murguɗa masa baki ta ƙara yi, tsawa ya daka mata yace.

” Nace da Uban wa kike wannan maganar.”

Ƙara murguɗa masa baki tayi tace.

” Da *Uban wanda ya tsargu nake*.”

Zaro ido Momy tayi tana kallon Indo cikin tsana.

Wo ho ho yau dai ran maza ya ɓaci, cikin ɓacin rai Mustafa yake takawa gaban Indo kamar wani zaki yaga nama, ita kuwa Indo tana maƙale jikin Inna ko a jikin ta, da ƙarfi! Ya fisgo ta, a jikin Inna ya kifa mata mari, ƙafarta ya jida da ƙarfi Allah ya rufa asiri ta faɗa kan kujera, (domin kuwa da ta faɗa saman tayels ɗin nan kanta kam sai Abunda Allah yayi)

Tashi Inna, tayi itama zata ɗauke Mustafa da mari, yayi saurin sunkuyawa, ta mari iska, cikin zafin rai Inna, take magana.

” Uban! me ta maka? da zaka mareta, idan banda munguwar zalunci, to wlh ka mari Allah ya isa, bata yafe ba, yi hkr kinji indona tashi ki barsa da Allah.”

“Wlh Allah ya” kasa ƙarasawa tayi sakamakon mummunan kallon da Mustafa ya aiko mata, haɗiye maganar tayi, ta shige ɗakin Inna tana magana ƙasa-ƙasa, Momy ce ta kalli Mustafa tace.

” Ka min dai-dai Mustafa, gobe ma ka mata, dukan da yafi wannan, shegiya gayyar na aiye gayyar tsiya, an ɗebo min tsiya an kawo min cikin gida.”

Shidai Mustafa bai tankawa Momy ba, yayi ficewar sa, abunsa.

********************************

” Wlh Mamy kin bani dariya, yanxu to meye laifin, Abba, a nan dan kawai ya bawa ƙanin sa, 2millions ni dai gaskiya a waje na, ba komai bane sai zumunci da yayi.”

” A wajen ki, da baki da hankali ba, amma ni so nayi ya basa 50k ya ishesa, amma yaki saurara ta.”

Sallamar Mustafa ne ya katse musu zancen nasu, amsa Sallamar sukayi, sannan Mustafa ya cewa, Mamy.

” Barka da dare Mamy.”

” Barka ya hanya, da fatan kun bar Kowa lafiya?”

” Lfy lau alhamdulillah! Kowa yana lafiya.”

Yau dai RAUDA bata kula Mustafa ba, ko gaisuwa bai haɗa su ba, shima dai Mustafa ko oho, domin kuwa, baima kalli inda RAUDA take ba, bare kuma yasan da ita a wajen.”

” Mamy ni zan koma cikin mota, daman Momy ne tace nazo na ɗauki RAUDA, idan ta shirya ina jiran ta, cikin mota idan kuma bata shirya ba, driver ya kawo ta da safe.”

” A shirye take, ke RAUDA tashi kije ki ɗauko kayan ki, ku tafi.”

Tashi RAUDA tayi ba tare da tayi magana ba, shi kuma Mustafa ya fice, jim kaɗan sai ga RAUDA ta fito, kararaki sosai Mamy tayiwa RAUDA, akan ta kula sosai, da wannan maganin wannan karon.”

Gaba ta buɗe ta shiga ba tare da ta kalli Mustafa ba, tana jawo murfin motar shi kuma yaja, har suka isa cikin gidan babu wanda ya cewa ɗan uwansa komai.”

Da Sallama RAUDA ta shiga cikin falon dukan su sunq zaune har Inna da Daddy, cikin murmurshi Momy tace.

” Oyoyo my daughter, sannu da dawowa.”

Murmurshi itama RAUDA tayi tare da zama gefen Momy, ta dubi Inna cikin girmamawa tace.

” Sannu ina wuni.”

” Lafiya” Inna ta amsa, itama cikin fara’a.

Sannan ne, ta gaishe da Daddy, amsawa Daddy yayi tare da cewa Inna.

” Wannan itace jikar Alhaji muktar, Uban gida na, ƴar ɗansa ne, Ahmad takan zuwa gidan nan ta kwana biyu.”

” Ayya Allah sarki sannu RAUDATU ya iyayen naki?”

“Lafiyar su lau” RAUDA ta amsa.

Momy ce tacewa RAUDA.

” Inna ne mahaifiya a cikin gidan nan.”

Shigowar Indo da sharifa ke nan falon, Sharifa tana cewa.

” Oyoyo Aunty RAUDA, tun ɗazu nasa ran zuwan ki, naji shuru ashe kina hanya.”

Magana RAUDA zatayi, sai kuma ta fasa sakamakon haɗa Ido da sukayi da Indo, Dam! Dam! Dam! Ƙirjin RAUDA ya buga, haka kawai taji Zuciyar ta, na dukan uku-uku sakamakon ganin Indo da tayi.

” Waye wannan Momy?” RAUDA ta tambayi Sharifa.

Murmurshi sharifa tayi tace.

” Oh Sunan ta, Indo ƴar uwar mune, ta dawo gidan nan yanxu da zama, Indo ga Aunty RAUDA, wacce nake gaya miki jiya.

Murmurshi Indo tayi cikin halin ko inkula tace.

” To Sannun ta, nikam zanje na kwanta Allah bacci nake ji.”

Sharifa ne tace.

” Bismillah kije ki kwanta amma dai ki tabbatar kinyi wanka kafin ki kwanta.”

“To” Indo tace sannan ta haura, Mustafa dake tsaye ƙofar ɗakin su yaga shigewar Indo, da sauri ya bita cikin ɗakin tare da dannawa ƙofar key………

*Vote*

*Share*

*And*

*Comments*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah ce)*

[2/11, 3:11 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*

*Nasmah ko Nasirah*

*Sara da Sassaka*

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.

Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*Congratulation ƙawalliyata momyn Ahlan ina taya ki murnan fara sabon book ɗinki, COLONEL UBAIDULLAHI Allah ya baki ikon rubuta Abunda zai amfani al’umma*.🙏🏻

*PLEASE ƴan Uwa ku tayani da addu’a, ina da muhimmiyar buƙata, kusani cikin Addu’ar ku a sallar ku, biyar, Allah ya biya min buƙata ta*🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

*P*••••••4️⃣1️⃣ ➡️ 4️⃣2️⃣

Danƙo gashin Indo Mustafa yayi, cikin zaro mata Ido ya ce.

” Uban waye kika zaga ɗazu, ɗan ubanki! Nace! Uban waye kika zaga?”

Cikin azaba Indo ta ce.

” Cewa nayi uban wanda ya tsargu, ai bance uban………..”

Ba ta ƙarasa ba, Mustafa ya haɗata da bango, tare da shaƙo wuyan ta, ya fara magana cikin zafin rai.

” Na rantse da Allah, idan baki fita harka ta ba, wlh wata rana sai na illata rayuwar ki, ki bar ganin kina tsiya cikin ƙauye ana ƙyale ki, to wlh nan ba ƙauye ba ne, ko ni nan sai na ɓatar dake a duniya a neme ki a rasa, banza daƙiƙiya jakar ƙauye, a kan me zaki dinga shiga harkata? da kinsan yanda na tsaneki na tsani ganinki ma a duniya, wlh da baki shiga harkata ba.”

Wata ƙaramar wuƙa Mustafa ya ciro a cikin aljihun sa, wacce take ajiye a cikin ɗakin su, suke yanka fruit da ita, ya nunawa Indo ya ce “Muddun ba ki fita cikin harkata ba, sai na illata ki da wannan wuƙar na kashe ki kowa ma ya huta.”

Idon Indo yayi jajajur, duk rashin hankalin Indo da haukarta, yau ta ji zafin abin da Mustafa ya mata, domin kuwa Indo tana da zuwa, mussaman ma idan taga za’a ci mata mutunci, da ƙarfi ta ture Mustafa, cikin faɗa ita ma take ce masa.

” In sha Allah kuwa zan bar cikin harkar ka, kamar yanda kace ka tsaneni haka nima yau na tsaneka, bana sonka, idan ka kashe ni sai meye, Inna ce take tsoron mutuwa, ba niba, ka rubuta ka ajiye, daga yau idan ka ƙara ganin na shiga cikin rayuwar ka, ka kashe ni, amma muddun ka shiga cikin rayuwata saina shiga taka.”

Tana gama faɗar haka ta faɗa saman bed sai kuma ta sake wani marayan kuka, tana kiran sunan Mama. Tabbas yau ne rana ta farko da ta ji tsanar mutum cikin ranta, domin kuwa duk mutumin da zai ce ya tsaneka ba ƙaramin maƙiyinka ba ne.

Sake baki Mustafa yayi yana mamakin maganganun da Indo ta faɗa masa, shi kallon yarinyar da ba ta san komai ba yake mata, sai ƙauyanci da hauka, amma ji yanda take zaro magana, cikin mamakin nata ya fice daga ɗakin. Yana buɗewa Sharifa da RAUDA na sako kansu za su shiga cikin ɗakin, hararar su yayi tare da musu mungun kallo ya shige, cikin sauri Sharifa ta faɗa ɗakin domin kuwa ta san Indo tana cikin ɗakin kuma ga Mustafa ya fita, aikuwa zarginta ne ya zama gaskiya yanda ta samu Indo kife tana sharɓar kuka.

” Lafiya Indo? me ya same ki, Please me aka miki, ki faɗa min mana Indo?”

Shuru Indo tayi ba ta kulasu ba, sai ma shafa gashin mta, da tayi tana tuno yan da Mustafa ya jamata da ƙarfi.

” Dan Allah Indo kiyi hkr ki faɗa min me ya same ki?”

Tashi Indo tayi cikin tsawa da kuma ƙarfi ta ce.

” Na rantse da Allah duk randa aka wayi gari Mustafa ya karye, to ni ce, wlh! Sai ya san ya min mugunta, na kuma tsanesa kamar yanda ya tsaneni, nida shi shege ka fasa a cikin gidan nan”

” Haba Indo, Mustafa kawai kika kira babu yaya, bai kamata ba, koma meya miki ai yayanki ne koh?”

Cikin tsiwa ta ce.

” Ba yayana ba, ubana ne shi, nace ubana ne shi, na faɗa Mustafa, idan sunan ubana na kira, sai na ji?”

Cikin tsawa RAUDA ta ce.

” Wai ke ya haka ne sai rashin kunya kike yiwa mutane, ana baki hkr kina rainawa mutane wayo, to kar Allah yasa ki hakuran mana.”

Hanu Indo ta ɗagawa RAUDA tana cewa.

” To fa! wai daman cin danƙo harda su kaza, ke kuma a suwa, to wlh kar ki kuskura ki fara shiga cikin sha’anin Indo, domin kuwa Indo ba kanwar lasa bace, idan kuma kika ƙi, to kema *mu zuba mu gani*, mtsss.”

Ta ja doguwar tsaki tana, hararar RAUDA, hannu RAUDA ta ɗaga za ta zabgawa Indo mari, Indo tayi saurin riƙe hanun RAUDA kafin ta ƙarasa fuskar ta, tana cewa.

” Karki fara wannan gangancin! Domin kuwa duk randa hanun ki, yayi kuskuren taɓa fuska ta, sai kin gwammace ba ki sanni ba cikin rayuwar ki, idan kuma kin ce ƙarya ne, ki gwada ki, gani ki bar ganin kin girme ni, to wlh girman ki ba zai bani tsoro ba, *dan funkun-funkun bata kilishi* tsap zan iya dukan ki Wlh, ni maza ma basu share wajena ba, bare kuma ke, *girman kazar Agric, girman falo ni kuwa girman ƙauye ce, naci tuwo na ƙoshi dan haka ƙarfin mu, ba zai taɓa zuwa ɗaya ba* Dan haka ki kiyaye, *in kunne ya ji jiki ya tsira*.”

Tana gama faɗin haka tayi saman gado ta kwanta ba tare da ta kalli Sharifa ba.

Shuru sharifa ta yi, kawai ba tare da ta tankawa Indo ba, sai ma nema mata shirya da tayi wajen Ubangijin halitta ( lallai Indo wannan halin naki kin dinga shan wahala kenan wajen ya Mustafa) cikin Zuciyarta, Sharifa ke wannan maganar.

Cikin tsawa RAUDA ta cewa Indo.

” Ke! Jakar ƙauye tashi ki bani gadona, na kwanta domin wannan gadon mallaki nane, saboda ni aka sashi a ɗakin nan, dan haka sai ki sauƙa kiyi shimfida a ƙasa tunda daman an saba da kwanciya a gadon bono.”

Murmurshi Indo tayi tana daga kwance ta ce.

” To Jakar Birni, dole ai na tashi na baki gado, tunda ubanki ne ya ajiye gadon, idan kin isa ki zo ki ɗaga ni da ƙarfi.”

Cikin jin haushin su, Sharifa ta ce.

” Ya isa ya isa! Haka haba wannan wani irin masifa ce, yanxu ke RAUDA fisabilillah da girman ki, zaki biye Indo kuke sa’insa, kinyi ƙanwa ta biyu fah da Indo, just 12 years he is younger akan me to zaki biye ta, ni kaina nafi Indo bare ke, just ki kama mutuncin ki dan Allah, idan akan gado ne, mu kwanta a nawa gadon mana gani nayi zai ishe mu.”

Carap Indo tayi ta ce.

” Kar ma ta kama idan har *ba ta ji kunyar yasar da girman ta ba nima bazan ji kunyar takawa ba*.”

Kallon sharifa RAUDA keyi tana cewa.

” Bayan wannan yarinyar kike bi Sharifa, duk wannan rashin Kunyar da tayi wa ya Mustafa, ba ki ga laifin ta ba, har kike bani rashin gaskiya iye Sharifa?”

” Mustafa ubanki ne shi, da zakiji haushi danna masa rashin kunya, to sai kixo ki rama masa *ƴar shishshigi mai kalen dangi*.”

Cewar Indo.

” Kinga RAUDA ni fa ba bayan Indo nabi ba, gaskiya ce kawai na gaya miki, idan kuma ranki ya ɓaci kiyi hkr.”

RAUDA ba ta ce musu komai ba ta fice a fusace daga cikin ɗakin.

Kallon Indo Sharifa tayi ta ce.

” Ke kuma kin ƙyautawa kanki, yanxu fisabilillah meye amfanin masifa, dan Allah ki ragewa zuciyarki wannan faɗan ki zauna da kowa lafiya,” zama tayi ta ce, dan Allah Indo kiyi hkr ki daina cewa Mustafa, ki kira sa da yaya dan Allah, ki daina masa rashin kunya.”

Indo za tayi magana kenan, Momy ta faɗo ɗakin cikin faɗa tare da ɗauke Indo da mari.

” Gidan ubanki ne! nan da har zaki zage ta, koko ke gadon na ubanki ne! da kinsan yanda na tsaneki da ba zaki dawo gidan nan da zama ba, kin addabi al’ummar garin ku, kin fi ƙarfin iyayen ki, shine ni za’a ɗauko min ke akawo min cikin gida, to bari kiji na gaya miki, RAUDA ta fi ki power cikin gidan nan, domin kuwa nafi ƙaunar ta, fiye dake, sauƙa ki bata gadon ta, idan ya so ki kwana a ƙasa daman kin saba da wahalar ƙauye, fitinanniya.”

Tunda Momy ta fara magana Indo take binta da ido Yayin da hawaye ke tsere saman kumatunta, tashi tayi ta fice da gudu tana ihu da ƙarfi.

” Wayyo! Allah Inna na shiga uku na lalace, wayyo! Za su kashe ni, Inna ki taimake ni.”

Da gudu Inna ta fito jin ihun Indo, shima Daddy fitowa yayi daga nasa ɗakin a firgice, Mustafa da yasan hali bai wani damuba a nutse ya fito ya tsaya bakin ƙofar ɗakin sa, tare da harɗe hanun sa, a ƙirji yana kallon ikon Allah.

Inna ce tace.

” Meya sameki? Kike ihu da tsohon daren nan, Amanar Allah.”

” Inna zagina tun ɗazu RAUDA take da suna ko waye? Takeyi wai bazan kwana a saman gado mai laushin nan ba, wai sai dai na kwana a ƙasa, shine ta turo Momy ta ce na kwana a ƙasa, tunda ni fitinanniya ce.”

Salati Inna ta ɗauka tare da tafa hanu tana cewa.

” A cikin gidan nan aka miki wannan tozartar, saboda ita RAUDATU gidan ubanta ne, nan, bani hanya na wuce?”

Girgiza kansa Daddy yayi shi wlh yayi tunanin wani mungun abu ne ya sameta, har zuciyarsa tana tsinkewa, Daddy a zuciyarsa yake cewa (lallai Mlm Musa kana shan haƙurin zama da Indo, yarinta yayiwa yarinyar yawa) haurawa sama Daddy yayi ya shige ɗakin sa, ba tare da yayi magana ba.

Inna na shiga ɗakin ta samu RAUDA tsaye tana gyara gadon, ita kuma Momy tana tsaye tana zagin Sharifa kan shiga harkar Indo da takeyi, mari Inna ta ɗauke RAUDA dashi ta ce.

” Kema nan ɗin gidan ubanki ne, da har zaki mallaki gado, iye! Samun waje kiran sallah da usur, ki ji min yarinya da ina miki kallon mai hankali ashe kema tantiriyar shegiya ce, to bari na sanarda ku, har ita uwar taku dake tsaye, ko wannan 👉🏻 tayi nuni da sharifa, ba ta isa tayiwa Indo gadara cikin gidan nan ba, duk abun da take so cikin gidan nan sai tayi shi, haura gado ki kwanta, Indo daga yau wannan gadon ya zama mallakar ki, na ga shegen da zai hanaki kwana a kansa.”

Dariya ce ta ƙwacewa Mustafa dake tsaye bakin ƙofar shi abun da ya basa dariya yanda Inna ta ɗauke RAUDA da mari, ta riƙe kumatunta sai zubar da ƙwalla take, a zuciyarsa cewa yayi ( Allah yasa tayi zuciya gobe ta koma gidan su, maganin mutumin da ba zai zauna inda Allah ya ajiye sa ba, sai ya ƙetaro iyakar wasu, wannan daidai kikayi Inna) juyawa yayi, yayi shegewar sa, cikin ɗakin sa.

Indo kuwa hayewa tayi ta kwanta abunta tana dariya ƙasa-ƙasa, ƙwafa Momy tayi ta cewa RAUDA.

” Ki hau gadon Sharifa ku kwanta, gobe zansa a kawo wani gadon, kiyi hkr.”

Taɓe bakin Inna tayi ta ce.

” Oho dai, wannan gadon kam na Indo ce, Amanar Allah, kuma ki shige kiyi ɗakin ki, karma na kauce ki samin yarinya a gaba.

Shigewa Momy tayi, ta fice, itama Inna ficewa tayi, RAUDA kuwa gadon Sharifa ta kwanta cikin ƙunar rai da tsanar Indo, Sharifa kuwa tsabar haushin su, duka mussaman RAUDA, domin kuwa ita ce ta jawo wannan masifar da tun farko ta bi shawarar ta, sun kwanta tare ba ta je ta kira Momy ba, ai da duk bata kai ga haka ba, tollet ta shige tayi wanka sannan tazo ta kwanta cikin kayan Bacci ba tare da ta kalli ko ɗaya daga cikin su ba.

Washe gari da wuri RAUDA da sharifa suka tashi, tare da tashin Indo suka fara aikin gida tare, kasancewar ita Indo ba ta da ƙiwiyar aiki, ita ce ta musu wanke wanke, su kuma suka ɗaura breakfast, Indo da RAUDA kuwa suna haɗa ido sai hararar juna, san da suka gama aiki sannan suka koma ɗaki, jan hanun Indo Sharifa tayi har toilet ta miƙa mata brush ta ce goge kamar yadda kikayi jiya, tsayawa tayi kanta har ta gama, sannan ta fito ta bata waje domin tayi wanka.

Bayan Indo tayi wankan ne ta fito kamar jiya ta shirya, Sharifa rasa wani kaya zata bawa Indo tayi kasancewar ta fi Indo ƙiba, ba lallai bane kayan ta, yayiwa Indo, wata doguwar riga ta ƙara bata ta saka, sun ɗan mata yawa kaɗan haka tasa su.

Haka dukkan su suka shirya suka fito daining, kowa ya haɗu a daining ɗin har Inna, gaishe su sukayi, sanda Indo take gaishe da Momy daƙyar ta amsa tana kumbure-kumbure.

Bayan sun gama breakfast ɗinne Daddy ya dubi Mustafa ya ce.

” Habeeb ya kiran a waya yace zai taso, 6:00am but ka ga kenan zai iso before 12 dan idan ka fita office zaka je ka ɗauko sa, sannan kuma munyi magana da principal na matrix acadamy, akan karatun Indo, mun gama magana dashi cewa, Indo zata Zauna a ss1 tunda acan garin nasu tana js2 ne, yace zai bamu amma ya ce dole sai an mata enterview idan taci sannan hakan za ta kasance, so za ku tafi tare da ita.”

Da to Mustafa ya amsawa Daddy ba tare daya masa musu ba, duk da ransa bai so ba.

Sharifa kuwa karɓar kuɗi tayi a hanun Daddy ta ce zata kasuwa ta sayowa Indo kaya.

Himar Sharifa ta bawa Indo, ta fito tana tura baki ta bi bayan Mustafa.

Gaba Indo ta shiga Mustafa ya ja da ƙarfi ba tare daya kalleta ba, suka ɗauki titi, sunyi nisa sosai ba tare da kowa ya kula ɗan uwansa ba, parking Mustafa yayi a gefen hanya tare da ficewa yana waya ya shiga, wani shago, Indo kuwa kalle-kallenta kawai take, karaf idonta ya hango mai baro cike da *KARKASHI* buɗewa tayi ta fice da gudu tayi wajen mai karkashin, tsayawa tayi ta ce.

” Sannu mai KARKASHI”

” Yauwa sannu yarinya”

” Baba dan Allah taimaka ka bani karkashin nan guda biyu dan Allah badan halina ba.”

Murmurshi mai karkashin yayi tare da bata, ya samata cikin leda, godiya ta masa ta ruga da gudu ta koma cikin motar tana dariya, Mustafa ya ɗan juma cikin shagon kafin ya fito suka tafi, ba tare daya lura da wani leda hanun Indo ba.

Alhamdulillah cikin ikon Allah suka yiwa Enterview kuma alhamdulillah ta samu ta haye, saboda Indo ko a ƙauye bata ƙin karatu Kuma tana da lura da fahimta, muddun kuma ba ta gane abu ba sai ta tambaya, gida ya dawo da ita ya sauƙe ta sannan ya wuce ɗauko Habeeb yana mitar yau an kashe masa times ɗin aikinsa.

A nutse yake sauƙowa daga jirgin cikin nutsuwa fuskarsa kuma ɗauke da murmurshi, har ya karasa sauƙowa, da sauri Mustafa ya karasa ya rungume ɗan uwan nasa, suna dariya, cikin.

” Your Welcome my Bros”

Cewar Mustafa.

Habeeb yana murmurshi yace.

” Welcome bros ya aiki.”

” Aiki alhamdulillah bros.”

Jerawa sukayi suna hira har cikin mota, suna taɗin su cikin farin ciki, a harabar gidan Mustafa ya sauƙe Habeeb yana cewa.

” Sorry bros, bazan samu ƙarasawa cikin gida ba, akwai wani case ɗin da zan karɓa ne, so munyi agriment da mutumin zamu haɗa yanxu, jibi zamu shiga kotu, so ina so naje ƙara bincike sosai.”

Murmurshi Habeeb yayi tare da cewa.

” Karka damu bros Allah ya dawo da kai lafiya ya kuma bada Sa’a.”

Murmurshi Mustafa yayi tare da cewa “ameen” sannan yaja motar sa ya fice shi kuma Habeeb yaja postal dinsa zuwa cikin gidan, babu kowa cikin falon sai Indo ita kaɗai ta zubawa tibi ido sai dariya take ita ɗaya kamar suncacciya, kasancewar RAUDA ta tafi makaranta, ita kuma Sharifa ta tafi kasuwa, sayowa Indo kaya, sallama Habeeb yayi yana murmurshi, da gudu Indo ta tashi tana “Oyoyo ya Habibu”

Dariya Habeeb keyi, yace.

“Oyoyo Mamana, ke ɗaya ce cikin gidan?”

” A’a Inna da Momy suna ɗakinsu, Daddy ya fita ita Kuma Sharifa taje kasuwa siyomin kayan ƴan gayu”

Dariya Habeeb yayi sosai yace.

” Eyye kice zamu sha kallon gayu cikin gidan nan, gaki kuma ƴar cas-cas dake gwanin ban sha’awa, amma fa zakiyi kyau har ki gaji.”

Dariya Indo tayi tana fari da ido tace.

” ai ya Habibu sai nafi kowa kyau cikin gidan nan, wankan safe daban na rana daban, ya Habibu nayi kyau har saina gaji”

Dariya sosai Habeeb yayi yace.

” Kinga Mamana bari naje nayi wanka tukunna na fito, dan zancen mu bazai ƙare ba”

Sama ya haura yana murmurshi ɗakin Momy ya shiga tare da Sallama, amsawa Momy tayi tana zaune bakin gado ta haɗe rai fuskar ta a haɗe, cikin sauri Habeeb ya ƙarasa yana cewa.

” Momy lafiya meya same ki?”

Kallon Habeeb Momy tayi tace.

” Ka iso kenan?”

” Eh Momy na iso Please Momy meya sameki?”

Ajiyar zuciya Momy ta sauƙe tace.

” Hmm! Habeeb yarinyar nan ce, bana son ganin ta, cikin gidan nan, na tsane ta, na tsane ta, gashi kuma Alhaji yace dole saita zauna cikin gidan nan”

Cikin rashin gane inda zancen Momy ya dosa Habeeb yace.

” Momy wacce yarinya ne, kike faɗa, wacce har zata takura ki haka?”

” Wannan yarinyar mana Indo wacce mahaifinku ya taho da ita nan, daga zuwa ta’aziya aka haɗomu da masifa”

Cikin zaro ido da tsantsar mamakin Momy Habeeb yace.

” What! Momy Indon ce masifar, ƴar mutum ce, Momy kamata yayi ki nema mata shiriya wajen Ubangiji, ki kuma taya iyayen ta, gyarata, bawai ki dinga, faɗar magana marassa kyau a kanta ba, Momy yanxu Indo ce, zata zame miki matsala cikin gidan nan, duk yaran dake cikin gidan nan basu zamo matsala gare ki ba, sai ita, Momy shifa ɗa na kowa ne, baka san wanda zai taimake ka ba gaba, Please Momy dan Allah karkiyi…………”

Cikin tsawa Momy ta katse Habeeb ta hanyar cewa……..

Wlh typing wahala.

Please dan Allah karku manta ku sani cikin Addu’ar ku🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻

*Vote*

*Share*

*And*

*Comments*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah ce)*

[2/12, 2:34 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*

*Nasmah ko Nasirah*

*Sara da Sassaka*

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.

Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*TALLAH TALLAH TALLAH*

Ina kuke makaranta littattafan Hausa to ku matso kusa ga dama ta samu, domin kuwa na sake kintsawa da shirin tsaf domin sake gabatar muku da sabbin Novel’s ɗina masu taken👇🏻

*RUƊANIN ZUCIYA BIYU*

*SO BAI SAN JINI BA*

Zan sake muku wannan book ɗin na *So bai san jini ba* free, 12/3/2020 idan Allah ya kaimu, ku dai ku kasance dani, domin book ɗin yazo da sabon salon labari, wanda na rubuta shi cikin nutsuwa hikima da basira.

*RUƊANIN ZUCIYA BIYU* Shi kuma zan sake muku shine Bayan na kamalla book ɗina na *Indo a birni* amma shi Ruɗanin zuciya biyu na kuɗi ne, zan sake muku shi a farashi ƙalilan, 200 kawai zaku biya kusha karatu cikin nutsuwa, ku dai ku shirya karku bari a baku labari, domin wannan book ɗin ya haɗa abubuwan al’ajabi da yawa, Soyayya tausayi, ƙiyayya, son Zuciya, da dai sauransu ku dai ku kasance da alƙalamina har zuwa ranar da zan fara sakin wannan book ɗin.

*بسم الله الرحمن الرحيم*

____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

*P*••••••4️⃣3️⃣ ➡️ 4️⃣4️⃣

“Wai me! wannan yarinyar take muku ne, da gaba ɗaya kuke ƙaunar ta, duk tabi ta lashe muku zuciya, to wlh idan ma iyayenta na can ƙauyen sun asirce kune, to wlh ni nafi ƙarfin su, kuma alƙawari na ɗaukar wa kaina saina kori yarinyar nan daga cikin gidan nan.”

Girgiza kansa Habeeb yayi ba tare daya ƙara cewa Momy komai ba, ya fice daga cikin ɗakin cikin ɓacin rai, yana mamakin halin mahaifiyar tashi, yanda ta sauya lokaci ɗaya akan yanda yasan ta a baya.

Ƙwafa Momy tayi tare da cewa.

” Aikin banxa aikin wofi! Yarinyar da tafi ƙarfin iyayen ta, ta addabi garin su, shine ni za’a ɗauko min ita a kawo min cikin gidan, ita Inna har zata biyo ta, a zauna ana cimin mutunci akanta to wlh Abunda baxai yiwu bane idan har Inna ta cigaba da bin bayan yarinyar nan ni kuma na ƙalla da cin ubanta! cikin gidan nan kenan.”

Haka Momy ta dinga mita ita ɗaya cikin ɗakin.

Shiko Habeeb shigewa yayi ɗakin su tollet ya shige, ɗaure da towel yayi wanka ya fito, ringine ɗin wayar sa, yaji ɗaga wayar yayi yana murmurshi tare da furta *HASINA* a hankali, ya ɗan juma yana wayar kafin ya katse, shiryawa yayi cikin jallabiya, sannan ya ƙara ƙarfin Ac ya kwanta tare da rufe idonsa yana son hutawa.

A gajiye Sharifa ta shigo cikin gidan, kusa da Indo ta Zauna tana cewa.

” Wash! Allah na wlh na gaji sosai.”

Dariya Indo tayi tace.

” Sannu Sharifa, har kin dawo?”

” Na dawo Allah yau na gaji cikin kasuwar nan, kinga kayan ki” (ta turowa Indo kayan gaban ta)

Buɗe kayan Indo tayi tana kallon su tana dariya, cikin murna, dogayen Riguna ne, masu tsadar gaske, tare da riga da siket masu shegen kyau, dariya tayi tace.

” Aradu sunyi kyau Sharifa, sai dai kuma banga atampa ba fa cikin kayan.”

Murmurshi sharifa tayi tace.

” To uwar rashin haƙuri, idan Daddy ya dawo zai taho da Atampopi sai mukai ɗinki gobe.”

Dariya tayi tare da cewa.

” Yauwa sai yanxu naji magana, Sharifa ya Habibu ya dawo, ɗazu.”

” Dan Allah da gaske kike ya Habeeb ya dawo?”

” Allah da gaske nake ya dawo yana sama yace zai huta.”

Murmurshi sharifa tayi tace.

” Kaya na sunxo, bari nima naje nayi wanka kafin ya fito.”

Haurawa sama Sharifa tayi tare da ledar kayan Indo, su Ishaq ne, suka dawo daga school da gudu Sharif ya faɗa jikin Indo yana cewa.

” Aunty Indo yau kamar kece na gani a makarantar mu, kunyi fannin ƴan Secondary school ss keda ya Mustafa, har zan fito sai uncle din mu ya hanani.”

Dariya Indo tayi tace.

” Nice wlh, daman makarantar kuce, nima ai nan Daddy ya saka Ni, ashe zamu dinga tafiya tare, ai da nasan ajin ku aradu da saina shiga.”

Ishaq ne yace.

” Lah! Aunty Indo kema yanxu ƴar makarantar muce, to aike Secondary ne, mu kuma primary fa, to yaushe zaki fara zuwa?”

” Oho nima ina na sani, sai sanda Daddy yace na fara tukunna.”

Momy da take sauƙowa daga step ta hango su Ishaq maƙale jikin Indo ya sata daka musu tsawa tare da karasowa wajen da sauri, ta kama kunnen su tace.

” Kai! Sharif, me kuka tsaya yi anan to daga yau karna ƙara ganin ku, kusa da wannan abar tsiyar”

Zaro musu Ido tayi tace kunji ko baku jiba.

Da sauri suka haɗa baki wajen cewa.

” Munji Momy bazamu sake ba.”

Sake musu kunnen tayi tace.

” Maza ku haura ku cire uniform” maida kallon ta, tayi wajen Indo tace mata.

” Ke kuma ki fita harkar yarana, dan bazaki lalata min tarbiyyar yara ba, ke kin lalace nima kixo ki cuceni ta hanyar koyawa yarana munguwar ɗabi’ar ki.”

Shuru Indo tayi tana kallon Momy tare da tunanin meye ne munguwar ɗabi’ar tata, sai kuma ta kawar da kanta daga kallon momy ta tashi tayi ɗakin Inna, tsuka Momy taja sannan ta zauna.

Inna tana shan Baccin ta, Indo ta kwanta Kusa da ita, sai kuma ta shiga tunanin maganganun Momy, tashi Indo tayi kamar wanda aka tsikareta, ta fito ta wuce Momy a falo ta haura sama, ɗakin su Mustafa ta faɗa tana Sallama taji shuru, shiga tayi tana karewa ɗakin kallo yanda yasha ado kamar ɗakin mace, komai a shirye tsaf, a kwance taga Habeeb yana bacci, zama tayi gefen sa, tare da kiran sunan sa, sanda ta kira kusan sau uku sannan Habeeb ya buɗe idonsa.

” Mamana lafiya?”

Tura bakin ta, tayi tace.

” Lafiya lau daman zan tambaye kane?”

Tashi Habeeb yayi yace.

” Naji tashi mu fita waje sai muyi maganar acan ko.”

Tashi tayi suka fito, ganin Momy cikin falon yasa Habeeb yin compaunt ɗin gidan, Itama Indo bayansa tabi, Momy kuwa taɓe bakinta tayi, bayan sun shige taci gaba da kallon ta.

Waje Habeeb ya samu ya zauna kan wasu kujerun roba dake zagaye a gefe, itama Indo zama tayi, Habeeb ya dubeta yace.

” Ina sauraron ki Mamana, menene tambayar?”

” Ya Habibu wai da gaske ina da munguwar ɗabi’a ?”

Zaro ido Habeeb yayi yace.

” Wa yace kina da munguwar ɗabi’a ?”

” Momy ce wai karsu ishaq su sake kulani ina da munguwar ɗabi’a ”

Girgiza kansa kawai Habeeb yayi cikin ɓacin rai akan abunda Momy takeyi, shidai da baisan Momy da wannan halin ba, to meya sauya Momy haka lokaci ɗaya, kodai akwai Abunda Indo ta mata ne, wanda bata ji daɗin saba? Duban Indo yayi yace.

” Ke baki san meye munguwar ɗabi’a bane?”

” Ya Habibu da na sani ai bazan tambaye kaba, Allah ban sani ba.”

Murmurshi Habeeb yayi yace.

” To bari na faɗa miki, na farko shine kin cika yawan faɗa, sannan baƙya hakuri, kina da rigima, ba kuma kya nutsuwa sannan baƙya jin magana, shine fa kawai munguwar ɗabi’a, kuma da zaki gyara ko, ba ƙaramin burge kowa zakiyi ba, ke kanki zakiji ki, kinfi da jin daɗi, kuma ma ba kince min zaki rage yawan rashin jiba, ko kin manta alƙawarin da kika min?”

Tura baki Indo tayi tace.

” Ban manta ba fa ya Habibu kuma Allah na rage, kaga yanxu ma baki na har brush nake, kaga ta buɗe masa haƙori, tace kuma Allah ya Habibu zan daina rashin ji, kuma zan nutsu, to ya Habibu ya ake nutsuwa?”

Dariya sosai Habeeb yayi yace.

” Good question Mamana, kinga ki daina yawan magana, ki kuma daina faɗa ki dinga tsafta, idan manya sunce kiyi, to kiyi idan sunce ki bari to ki bari.”

” Allah ya Habibu nama daina su daga yau, zanke jin maganar kowa.”

Dariya Habeeb yayi sannan suka cigaba da taɗinsu, suna dariya harda tafawa, a wunin Ranar Habeeb biyewa Indo yayi, suka ta shashanci kamar yara ƙanana.

Da la’asar lis Momy da sharifa na kitchen, ita kuma RAUDA tana cikin ɗaki tana kwance, kasancewar ta dawo daga makaranta a gajiye, Inna Kuma da Indo sai Habeeb suna zaune falo, Mustafa ya shigo, zama yayi kusa da Inna yana cewa.

” Hajiya tsohuwa mai ran ƙarfe, me zan samu ne?”

Hararar Mustafa Inna tayi tace.

” Aiko ina da abun bayarwa bazan baka ba, gara na bawa Habibu tunda ya miki sanin ya kamata.”

Gabaki ɗayan su, dariya sukayi Mustafa da Habeeb, Habeeb ne yace.

” Haba Inna Angon naki, zaki ce babu baisan ya kamata ba.”

” A’a yanxu bana Auren dashi, gwara na dawo da Auren kanka Habibu sai nafi samun kwanciyar hankali akan wannan ɗan baƙin ran tsiyar.”

Fakar idonsu Indo tayi ta ruga ɗaki da gudu, karkashin nan ta ɗauka wanda ta jiƙasa ya jiƙu yasha yauƙi har ya gaji, ta fito da sauri ta laɓe bakin ƙofar ɗakin su, tana jirar Mustafa.

Dariya Mustafa yayi yana cewa.

” Nima bana Auren kije na miki saki uku, saiki tare wajen Habeeb ɗin” ya ƙarasa maganar yana dariya tare da haurawa sama.

Ganin tahowar Mustafa da Indo tayi ya sata kwasa da gudu taje ta kwara wannan ruwan karkashin, ta koma ɗakin nasu da gudu, tare da hararar RAUDA dake kwance tana Bacci ba tare da tasan tana yiba, Allah sarki Mustafa shiko tafiyar sa yake ba tare daya kawo komai cikin ransa ba, taku ɗaya yayi ƙofar ɗakin nasu, ya kawo ƙafarsa ata biyu, yaji wani irin santsi ya ɗebesa, ji kake *Tim* Mustafa ya sauƙa kasan tayels, wani irin ƙarar Azaba Mustafa yasa tana riƙe kunkumin sa, ya runtse idonsa, a firgice suka haura saman cikin gudu, harta RAUDA dake bacci saida wannan ƙarar ya tashe ta, kusan tare suka fito da RAUDA, Habeeb kan Mustafa zaiyi a gigice, Indo tayi karaf tace.

” Ya Habibu rufawa kanka asiri karka taka wajen nan idan ba so kake, kuma kuyi jinya ku biyu ba.”

Turus Habeeb ya tsaya yana duban Indo cikin tuhuma yace.

” Me kike nufi da kar muyi jinya mu biyu?” Tare da tsareta da idanun sa cikin tuhuma yake mata tambayar?”

” Ni fa ba wani abu bane gani nayi mutum ya faɗi bamu san meya kada shiba haka kawai kaima ka hau ba tare da ka kula ba.”

Inna ce tayi carap tace.

” Kuma gaskiya ce maganar Indo, ke dai Allah ya miki Albarka da kika kular damu.”

Momy kuwa ta gigice za tayi kan Mustafa dake zaune daɓas cikin azaba ya kasa tashi saima runtse ido da yake, ko kafin Momy ta ƙarasa Habeeb ya lura da ruwan dake kwance ƙasa, yayi saurin cewa Momy.

” Dakata Momy! Kamar ruwa nake gani kwance a ƙasa.”

Tsayawa Momy tayi tare da kai duban ta, ƙasa, kusan tare suka sunkuya da Habeeb, hanun su, suka saka sai sukaji yauƙi sosai, saurin duban juna su kayi Momy tace.

” Yauƙi meya kawo yauƙi cikin gidan nan, rabon da muyi amfani da yauƙi ko muyi miyar yauƙi cikin gidan nan, an daɗe, to wa ya zuba yauƙi?”

Saurin duban Indo Habeeb yayi, rashin gaskiya ƙarara ya hango cikin idanunta, ya Kuma san tabas itace kawai zata iya wannan ɗanyen aikin cikin gidan nan, duban Momy yayi yace………………

Kuyi hkr da wannan wlh yau ina busy ne, naso nayi yafi haka yawa.

Please karku manta dani cikin Addu’ar ku🙏🏻

*Vote*

*share*

*and*

*Comments*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah ce)*

[2/13, 1:04 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*

*Nasmah ko Nasirah*

*Sara da Sassaka*

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.

Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*Jinjina*

Bazan gaji da jinjina gare kuba, waɗannan jarumai, Yaya Mu’az Hassan Tanko Hussaini 80k Yaya Hayat, Ubangiji Allah ya biya muku bukatun ku na Alkairi, ya haskaka muku rayuwar ku, muna matuƙar godiya gare ku, bisa Taya mu posting da kuke, Allah ya saka da Alkairi🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*

____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

*P*••••••4️⃣5️⃣ ➡️ 4️⃣6️⃣

” Momy kiyi tunani dai da kyau, ko kinyi amfani da kuɓewa ko karkashi, su Ishaq su gani su ɗauka suyi wasa dashi, kinga dai nan kam kowa da hankalin sa, ba wanda zai ɗauki karkashi harya zubar” Habeeb ya faɗawa Momy haka ne saboda yasan yanda take son Ishaq da Sharif bazai bari ta tsananta bincike ba.

” Babu wani tunanin da zanyi domin kuwa ni banyi amfani da duk abunda ka kira ba, rabona dasu na kusa shekara, sai dai kuma idan aljanu ne, suka zubar.”

Takaici da haushi ne, ya ishi Mustafa, cikin ɗaga murya yace.

” Ni! Wannan maganar ta isheni haka, koma waye ya zuba dai yanxu kam ya wuce, tunda dai ya riga da yayi Aikin sa, kuma koma waye ne, zan binciko shi da kaina, kaga Habeeb ni tsallako ka kamani na tashi, ba bincike bane a gaba na.”

Harara Habeeb ya aikawa Indo yanda babu wanda zai lura da hakan, sannan ya tsallaka tare da miƙawa Mustafa hanu hanun nasa Mustafa ya kama tare da tashi da ƙyar, a bakin gado ya zauna yana wash, duka biyosa sukayi ɗakin suna masa sannu, RAUDA ce, cikin rau-rau da idanu kamar zatayi kuka tace.

” Sannu ya Mustafa”

Bai ɗaga kai ya kalle ta, ba bare kuma ya amsa, ganin haka da sharifa tayi ya sata juyawa ta fice daga ɗakin ba tare data masa sannu ba, Habeeb ne, ya buɗe jakarsa ya ɗauko magani ya bawa Mustafa tare da ruwa, karɓa Mustafa yayi ya haɗiya, tare da kwantawa yana lunshe idonsa, cikin Azaba, towel Momy ta ɗauko ta sunkuya ta goge masa yauƙin ƙafar tasa, tare da ɗauko karamin baho da ruwa ta wanke ƙafar tas, sannan ta juya, a bakin ƙofa ta taradda RAUDA tana mopping ɗin wajen da aka zubar da karkashin, murmurshi Momy tayi tace.

” Sannu RAUDA Allah ya miki Albarka.”

Da ameen RAUDA ta amsa sannan Momy ta shige, Inna kuwa a cikin sai sannu take yiwa Mustafa ta kasa dainawa, tana cewa.

” Sannu Muhammadu, ko wani mungun ne, yayi wannan aikin sai Allah, Allah dai ya toni asirin sa, koma waye, bari kaga naje na dafa ruwan zafi nazo na gasa maka ƙugunnaka.”

Shi Mustafa koma kallon Inna baiyi ba, bare ya bata amsa, saima Habeeb ne ya zaro ido yace.

” Inna wani ruwan zafi kuma? muna zaune lfy ga magani tasha, to mudai bama bukatar ruwan zafi, muna da magani ya ishe mu.”

” To likita bokan Turai to tun kafin a haifi ubanku ake amfani da ruwan zafi, wajen maganin ɗumuwa wai kaima ɗan zamani, zaka wani kira min magani, sai kuje kuta amfani da maganin naku ai” tana gama faɗin haka Inna ta fice.

Dariya Habeeb yayi tare da duban Mustafa yace.

” Sannu Bros, Allah kasha wahala, sosai faɗuwa saman tayels ai akwai Azaba.

” Kai dai bari Bros Habeeb wlh ji nayi kamar wanda ake zare min rai, kaji kunkumi na kuwa, rufin asirin ma, ban faɗi akan ƙafata ba, Allah inaga da karyewa zanyi.”

” Sannu bari naje na haɗa maka ruwan zafi kayi wanka, tunda Inna daga wasa tayi fushi tace ta fasa tausaka, ni bari naje na haɗa maka.”

Dariya Mustafa yayi yace.

” Rabu da Inna, ni jeka haɗa min ko zanji sassauci.”

Shigewa tollet ɗin Habeeb yayi yana dariya.

Dariya sosai Indo takeyi tana riƙe cikin ta, domin kuwa ko banxa yau ta rama dukan ta, na ƙauye daya mata, tana cikin dariyar ne, Sharifa ta shigo cikin ɗakin duban Indo tayi tace.

” Ke kuma dariyar me kike haka, kamar wacce aka miki Albishir da gidan Aljanna?”

” Babu komai fa, kawai wani abu na tuno shiyasa nake dariya.”

Kaɗa kanta Sharifa tayi ta zauna tana ɗaukar wayar ta, tare da cewa.

” Ki tashi kije ki ɗauki kayan ki, ki sasu cikin drower.”

Da to Indo ta amsa tana dariya ta tashi ta nufi drower, shigowar Habeeb cikin ɗakin yasa Sharifa ɗaga ido tana kallon sa, bai kalli Sharifa ba, ya nufi Indo tare da hama Hanun ta, sukayi waje, kallo Sharifa ta bisu dashi har suka fice, RAUDA dake tsaye tsakiyar falo taga Habeeb sun wuce riƙe da hanun Indo, ta bi bayan su da sauri, Habeeb bai sake Indo ba, saida sukaje garden ɗin gidan sannan ya sake ta, RAUDA samun waje tayi ta ɓuya inda bazasu ganta ba, duban Indo Habeeb yayi yace.

” Meyasa kika watsa masa yauƙi a ƙofar ɗaki?”

” Ya Habibu ni kuma na watsa masa yauƙi?”

” Eh ke ina kallon ki, ai sanda kika watsa masa” Habeeb ya gayawa Indo haka dan ta faɗa masa gaskiya.

Shuru Indo tayi tana tura baki taƙi magana.

Kallon ta Habeeb yayi yace.

” Okey bazaki sanar dani ba ko? Shikenan bari naje na sanar da Momy cewa kece kika watsa yauƙin.”

Magana tayi tana haɗa rai tace.

” To ba shi bane yake min mugunta, ranar a ƙauye yamin duka harda kunbura min jiki, ranar kuma a falo ya dakeni, shine shekaran jiya kuma ya zageni, ni kuma shine na rasa da Abunda zan rama shine na zuba masa karkashi ya faɗi, shima yaji in akwai daɗi.”

” Good! Zargina ya kasance gaskiya, to waima tukanna a ina kika samu karkashin?”

” Randa ya kaini makaranta ne, ya tsaya ya shiga wani kanti, shine ni kuma naga mai karkashin na fita na roƙesa, shine sai ya bani biyu.”

Rufe baki RAUDA dake maƙale jikin bango tayi tana zaro ido, a hankali yanda bazasu ganta ba ta juya tayi cikin gida domin kai rahoto.

Girgiza kansa Habeeb yayi, cikin mamakin halin Indo, zama yayi sannan yace mata itama ta zauna, zama Indo tayi, Habeeb ya dubeta tare da cewa.

” Zan roƙeki a karo na uku na kuma saka miki doka cikin gidan nan, idan baki daina ba, Allah babu ruwana da ke cikin gidan nan, bazan kuma sake kulaki ba.”

Shuru tayi tana haɗa rai, kafin Habeeb ya cigaba da cewa.

” Daga yau babu ruwan ki da Mustafa, karki ƙara shiga harkokin sa, in kin gansa ki gaishe shi kawai idan kuma ya saki aiki ki masa ki daina raina sa doka ta ɗaya kenan, doka ta biyu, karki yadda ki dinga yiwa Momy Rashin kunya, duk abunda ta miki wanda bakiji daɗin saba, ki bata hkr kiyi shuru, karkice zaki mayar mata magana, doka ta uku, kinga ki daina cewa kina son Mustafa domin yanxu ke karatu kika saka a gaba ba soyayya, ba kinga yanxu ke karatu ne ya kamace ki ba soyayya ba, idan kin nutsu kinyi karatu zaki taimaki rayuwar ki, domin kuwa gaba zaki zama cikakkiyar mutum, zaki taimaki kanki da iyayen ki, ki nutsu dan Allah ki gyara rayuwar ki, ki zamo kamar kowace ƴa wacce ko wacce uku take alfahari da ita” karo na farko da Habeeb ya kira sunan Indo na gaskiya yace ” A’isha ki dubeni da kai ki kuma kalli ƙwayar idona ina son ki ajiye wannan Abunda zan faɗa miki cikin zuciyarki da ƙwaƙwalwar ki, na tabbata gaba sai kin tuno dashi duk sanda Hankali ya mamaye jikinki, *KI SANI CEWA MAI SONKI DA GASKIYA SHINE WANDA ZAI GAYA MIKI GASKIYA CIKIN RAYUWAR KI, YA KUMA NUNA MIKI HANYA MAI KYAU A’ISHA MAI SONKI DA GASKIYA BAZAI TAƁA KYAMAR KIBA KO YAYA KIKE, KI SAKA ARANKI CEWA NI HABEEB MASOYINKI NE NA GASKIYA, BANA JIN DAƊI IDAN HAR MUTANE SUNA AIBATAKI, PLEASE DAN ALLAH BADAN NIBA KI GYARA HALINKI*.”

Shuru Indo tayi Yayin da jikin ta yayi mungun sanyi, tabbas maganganun Habeeb sun shiga jikin ta, babu mutumin daya taɓa maganganu masu ratsa jiki sai yau duban Habeeb tayi cikin sanyin murya wanda bansan Indo tana dashi ba tace.

” *YA HABIBU IN SHA ALLAH BAZAN SAKE ABUNDA NAKE BA ZAN SANJA DAGA YAU, ZAN KUMA YI KARATU KAMAR YANDA KA UMURCE NI, DAGA YAU BAZAN SAKE FAƊA DA KOWA BA NA DAINA KAYI HKR*.”

Murmurshi Habeeb cikin jin daɗi yace.

” Good ƙanwata, na gode yanxu tashi ki koma ciki Allah ya miki Albarka.”

Da ameen Indo ta amsa sannan ta shige cikin sanyin jiki, a falo ta taradda Momy tsaye rike da ƙogu tana jiran shigowar Indo RAUDA na tsaye gefen ta, Inna kuwa tana zaune gefe Indo na shigowa Momy ta finciko ta, tare da ɗauketa da tagwayen maruka, a har zuƙe Inna ta tashi tayi kan Momy, sarin shan gaban Inna Indo tayi, tana girgiza mata kai tare da cewa.

” Karkice komai Inna ki barta ta hukunta ni idan na mata laifi ne, Inna duk abunda za’a min cikin gidan nan, na rokeki da Allah karki ƙara magana, Inna na sauya a Indon da kika sani da, Inna ko kin manta Maganar Mamana sanda zamu taho garin nan, cewa tayi bani da wata uwar da ta wuce Momy yanxu, dan haka ki barta tayi hukunci gare ni.”

Sake baki Inna tayi tana kallon Indo a fiska dai indon da ta sani ne, amma a kalamai kuma ba Indo da ta sani bane, ” ikon Allah Inna ta furta, tare da ɗaga hanu tana cewa, alhamdulillah! Abunda nake faɗawa iyayen ki kenan suyi hkr wata rana Allah zai shirye ki, gashi kuma yau lokacin yaxo” shigewa Inna tayi ɗaki tana cewa Momy ” ke kuma kinji kunya Wlh ki rasa wa zakisa a gaba sai wannan ƙaramar yarinyar.”

Taɓe baki Momy tayi tana cewa Indo.

” Wani sabon salon iskancin kika ɗauko kenan, shegiya mayya, wato bari ki kashe min ɗa ko harda zuba masa karkashi, Allah bai kashe sa ba, ke baki isa ki kashe shiba, ɓace min a nan kafin na illata ki, munafuka kawai.”

Shigewa Indo tayi ba tare da tacewa Momy komai ba, RAUDA ce ta dubi Momy tace.

” Munafurci ne fa Momy, Allah Momy bana ƙaunar yarinyar nan.”

” Yo to nima RAUDA ƙaunar ta nake ne, dole tasa take zaune cikin gidan nan badan ina soba wlh, kinga wuce gije ki ƙarasa girkin nan, na gaji.”

To RAUDA tace tare da shigewa kitchen ɗin, Indo kuwa tayi cikin ɗakin su, ta buɗe drower ta kintsa kayan ta, sannan ta zauna gefen kujera guda ɗaya dake cikin ɗakin tayi tagumi tana tunanin maganganun Habeeb, a fili tace.

” Mutum Shida kawai ke sona cikin gidan nan Inna Sharifa ya Habibu Daddy sai su Sharif, ya Habibu in sha Allah bazan baka kunya ba, na sanja daga yau.”

haka Indo ta wuni cikin sanyin jiki ranar, da daddare Bayan dawowar Daddy suna zaune Momy tace RAUDA taje ta dauki abincin Mustafa ta kaimasa ɗaki bazai iya saukowa ba, tashi RAUDA tayi cikin sauri ta haura cikin ɗakin su, ta ɗauko maganin da Mamy ta ta dawo cikin kitchen ɗin, buɗe kololin abincin tayi cikin tsarguwa tana leƙe-leƙe ta zuba maganin cikin abincin, haurawa tayi cikin sallama,ta shiga ɗakin, amsawa Mustafa yayi, Habeeb dake kwance ya zurawa system ido, murmurshi Habeeb yayi tare da cewa.

” Ƴar ƙanwata kece tafe?”

” Nice ya Habeeb ai nayi fushi da kai tunda ka dawo ko Magana Babu.”

Dariya Habeeb yayi yace.

” Sorry sis ai kinga tunda na dawo bakya nan kina school ɗazu Kuma ina busy, just sorry.”

” Shi kenan ina tsaraba ta?”

” Tana cikin jaka, sai da safe zan bawa kowa tashi.”

Murmurshi RAUDA tayi tare da cewa”Allah ya kaimu” duban Mustafa tayi tace.

” Ya Mustafa wai ga Abinci inji Momy?”

Sai yanxu Mustafa ya ɗago kai ya kalli RAUDA yace.

” Ki mayar da abincin nan, kice na koshi yanxu nasha yoghout bana jin yunwa sai dai kuma indan Habeeb zaici sai ki ajiye.”

Murmurshi Habeeb yayi tare da cewa.

” Tunda nine ciccika rumbu ko, to nima na koshi tunda tare muka sha yoghout ɗin, ƙanwata miyar da abincin kinji.”

Wani irin baƙin ciki ne ya shaƙewa RAUDA ƙirji yanxu kam ta fara cinkewa da lamarin Mustafa dole tayi hkr dashi koda kuwa hakan zai zamo sanadin mutuwar tane, juyawa tayi cikin haushi ta koma falo, ranta ɓace ta cewa Momy.

“sunceƙoshi wai sunsha yoghout.”

” Okey mayar kitchen sai kixo muci abincin.”

Mayar RAUDA tayi taxo ta zauna, haka suka ci Abincin ranta ɓace.

Bayan sun gama cin abincin ne Indo ta tashi tayi ɗakin su, tare da kwanciya har yanzu Zuciyarta tunanin maganganun Habeeb yake, a haka RAUDA da sharifa suka shigo suka sameta, babu wanda ta kula cikin su, sai Sharifa ce taxo kusa da ita tace.

” Wai Indo meye yake damunki ne, naga tun ɗazu jikin ki da sanyi?”

Murmurshi Indo tayi tace babu komai Sharifa kawai bana jin daɗin jiki nane, bari ma naje nayi wanka Naxo na kwanta kawai.”

” Shi kenan Amma ni sai nake gani Kamar akwai Abunda yake damunki?”

Murmurshi tayi tare da shigewa tollet tana cewa babu komai.

RAUDA tabe baki tayi, tana yiwa indo kallon banxa, ita kam Indo bata sanma tana yiba.

A falo kuwa Habeeb ne ya sauƙo, suke taɗi da Daddy inda Daddy yake cewa.

” Wato Habeeb na muku magana akan aure duk kunyi shuru ko, to wlh na kusa maganin ku, tunda baza ku fito da mata ba, ni zan fitar muku, sadakar ku zan bayar.”

Daga Momy har Habeeb dariya sukayi sosai, Habeeb ya dubi Daddy yace.

” Haba Daddy abun kuma har ya kai ga sadaka?”

” Ya kai mana tunda kinƙi nemowa ai saini na nemo muku, tunda na gaji da ganin ku haka, kun riƙa min cikin gida har kun riƙe.”

Dariya Habeeb yayi tare da cewa.

” Kwantar da hankalin ka, Daddy nikam na samu matar aure, verry soon zan kawo muku ita ku ganta, sai dai kuma kayi sadakar Mustafa nikam na samo.”

Dariya Momy tayi tace.

” Shina Babu mai sadakar sa, domin kuwa ya sanar dani cewa, ya fidda matar Aure shima, Kuma ba kowa bace face RAUDA.”

Da sauri Habeeb ya ɗago ido ya kalli Momy cikin mamaki, domin kuwa zai iya rantsuwa da Ubangiji cewa Mustafa bazai furta wannan maganar ba, sai dai kawai Momy ta faɗi son ranta.

Daddy kuwa cikin farin ciki ya furta.

” Masha Allah! Lallai abu yayi kyau Allah ya sanya Alkairi, insha Allah gobe zan zauna dashi Mustafa naji daga bakin sa.”

Murmurshi Momy tayi tare da cewa.

” Allah ya kaimu.”

Tashi Habeeb yayi haura sama yana mamakin maganar Momy, sai kuma ya kasa sanar da Mustafa Abunda yake faruwa.

Washegari bayan sunyi breakfast misalin sha ɗaya, Habeeb ya fita cikin sauri yana sanar da su cewa zaije ya taro *HASINA* a airport, murmurshi daddy yayi yace adawo lfy.

Murmurshi Mustafa yayi yana cewa.

” A dai rage rawar kai Bros ka taka a hankali kar zumuɗi ya saka gagara riƙe sitiyarin motar.”

Dariya Habeeb yayi tare da cewa.

” Kai dai zauna kawai cikin gida tunda ka gamo da lalurar ƙafa, da nace kazo kamin rakiya.”

Murmurshi Mustafa yayi yace.

” Haba Yaro waya fada maka, ai tunda na hauro wannan step ɗin babu inda bazanje ba, kai dai baka son rakiyar ne.”

Dariya Habeeb yayi tare da ficewa yana cewa ” ba wani.”

Indo kuwa tashi tayi da gudu rike da hijab ɗinta a hanu ta bi bayan Habeeb tana kiran sa, tsayawa Habeeb yayi sanda ta iso kusa dashi tace.

” Ya Habeeb zan raka ka?”

Murmurshi Habeeb yayi tare da cewa.

” Muje Mamana” tare da buɗe mata murfin motar, dariya Indo tayi sannan ta shige, shima ya shiga yaja motar yana tsokanar Indo.

Sun ɗan juma cikin airport ɗin kafin jirgin Egypt ɗin ya sauƙa, tunda ta fara saukowa Habeeb ke kallon ta yana murmurshi, itama murmurshin ne ɗauke fuskar ta, tana kare masa kallo, fara ce kyakkyawa doguwa, tasha doguwar riga, fuskar ta yane da farin gyale, sanda taxo daf dasu Habeeb cikin farin ciki yace.

” Welcome to the Nigeria my sweet heart.”

Cikin murmurshi ta mayar masa amsa da cewa.

” Welcome sweetie na.”

Please karku mantani cikin Addu’ar ku dan Allah🙏🏻🙏🏻

*Vote*

*Share*

*And*

*Comments*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah ce)*

[2/17, 6:17 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*

*Nasmah ko Nasirah*

*Sara da Sassaka*

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.

Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*

____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

*P*••••••4️⃣7️⃣ ➡️ 4️⃣8️⃣

Kallo *HASINA* take bin Indo dashi cikin rashin sani, lura da hakan da Habeeb yayi ya sashi murmurshi tare da cewa.

” Ƴar Inna kenan sunan ta Indo wacce nake baki labarin ta kullum.”

Murmurshi HASINA tayi tare da rungumo Indo jikin ta, tana cewa.

” Sannu sis, ashe da rabon zamu gana, ina jin labarin ki kullum wajen sweetie na, na ƙagu na ganki, sai kuma gashi yau mun haɗu, ina sonki” HASINA ta furta tare da mannawa indo kiss a kumatunta.

Murmurshi Habeeb yayi sosai cikin jin daɗin yanda HASINA ta ɗauki indo ƴar uwa.

Indo kuwa murmurshi tayi tana cewa.

” Nima ina sonki Aunty HASINA, sannu da zuwa.”

” Yauwa sannu ƴar ƙanwata” duban Habeeb tayi tace ” sweetie zamu iya ƙarasawa gida yanzu.”

Murmurshi Habeeb yayi tare da buɗewa HASINA gaban motar ta shiga, ita kuma indo ya buɗe mata baya sannan shima ya shiga suka tafi.

Duban Mustafa Momy tayi tace.

” Mustafa kazo ka sameni cikin ɗaki ina son magana da kai.”

Da to Mustafa ya amsawa Momy sannan Momy ta haura sama, bayan ta Mustafa ya tashi yabi yana ɗan ɗingishi, a bakin gado Mustafa ya zauna yana duban Momy kafin Momy ta fara magana.

” Mustafa tambayar ka nake son nayi,?”

” Ina sauraron ki Momy Allah yasa na sani.”

Duban Mustafa Momy tayi cikin haɗa rai tace.

” Mecece ni a wajen ka?”

Cikin mamaki Mustafa ya dubi Momy yace.

” Momy! Wacce irin tambaya ce wannan? ke uwace a gare ni, wacce banda wanda ya fiki duk faɗin duniyar nan.”

” Alhamdulillah! To idan har ka ɗauke ni matsayin uwa, umarni nake son na baka, Kuma dole sai kabi domin kuwa na yanke hukunci tun jiya, dan haka baka isa tsallake umurni na ba.”

Duban Momy yake cikin son jin wani Abu ne wannan wanda Momy ta ɗauke sa seriours haka.

” Momy Please faɗa min menene wannan wani irin umarni ne, wanda bazaki faɗa min kai tsaye ba, har sai kin min tambaya?”

” Umarni nake baka, da ka Auri RAUDA a matsayin Suruka ta, ka sanar da mahaifin ka cewa itace ka zaɓa a matsayin matar Aure, karkuma ka sake ka sanar dashi cewa nice na saka ka Aure ta.”

Tunda Momy ta fara maganar Mustafa yake kallon ta, domin kuwa jin maganar yake kamar almara, wai shine zai Auri RAUDA, kai! Ina inpossible! Bazai taɓa yiwuwa ba, banda dai RAUDA kam.

” Magana nake kayi shuru” cewar Momy.

” Momy Please da gaske kike wannan maganar ko wasa kike min, in wasa ne dan Allah Momy ki daina?”

Duban sa Momy tayi tace.

” Kaga wasa cikin Ido na, nace! Kaga wasa cikin ido na, na faɗa maka RAUDA itace zaka Aura, ko bazaka iya bin umarnin nawa bane?”

Tashi Mustafa yayi yana kallon Momy tare cewa.

” Dan Allah! Momy ki sauƙe wannan umarnin a kaina, wlh bana son RAUDA ban taɓa sonta ba, kuma bazan taɓa sonta ba, Momy bana sonta dan Allah ki janye maganar ki akaina Please Momy.”

Cikin tsawa Momy tace.

” Umarni nake baka a matsayi na na uwarka, Kuma dole kabi idan kana neman albarka cikin Rayuwar ka, idan kuma kace ka tsallake magana ta, to kuwa babu ni babu kai, RAUDA ita nake so ka aura ta kasance surka cikin gidan nan kuma ina da tabbacin zamuyi alfahari da ita matsayin Suruka cikin gidan nan haka kaima sai kayi alfahari da ita kasancewar ta mata gareka.”

Ƙaɗa kansa Mustafa yayi yana duban Momy kafin yace.

” Momy ki faɗa min ko wani irin umarni zan bisa Amma dan Allah ki janye wannan maganar Auren, wlh Momy bana son RAUDA, bana kuma tunanin akwai wani alfahari da zanyi da Auren ta, karki sa na kasance cikin nadama bazan taɓa ganin hasken RAUDA cikin idanuna ba, Momy kibar kowa ya auri zaɓinsa, idan ita tana sona, tofa Momy ni bana sonta, Please Momy?” Ya ƙarasa maganar yana haɗa hanun sa biyu alamun roƙo.

” Kaga babu sauyi cikin magana ta, na riga da na yanke hukunci dan haka ka daina faɗa ina faɗa!” Momy ta ƙarasa maganar cikin tsawa.

Shima Mustafa tashi yayi cikin fushi yace.

” Bazaki faɗa na faɗa ba Momy tabbas ina neman albarka cikin Rayuwata, ba kuma zan tsallake umarnin ki ba, zanbi umarnin ki, kamar yadda kika umarce ni, sai dai Momy ina son kisan cewa, zan Auri RAUDA ne badan soyayya ba kuma duk Auren da babu soyayya cikin sa, ba’a samun farin ciki shi kuma aure yana buƙatar farin ciki, sai dai zanbi umarnin ki zan aure ta kamar yadda kika ce, sai dai bazan taɓa sonta ba cikin rayuwata, ke kike son RAUDA ba niba, zamuyi wata irin rayuwar Aure ne, wanda babu daɗi cikin sa bare kuma a samu kula da farin ciki na tsaneta bana sonta, na sanar dake haka ne, saboda duk abunda zai faru daga baya karku zarge Ni, ku fara zargan kanku kiyi idan na ɓata miki rai cikin maganganu na, ina faɗa miki ne iya gaskiyar Abunda yake cikin raina ne” yana gama faɗin haka ya fice daga ɗakin cikin ɓacin rai, gabaki ɗaya gidan ya bari.

Taɓe bakin ta Momy tayi tana cewa.

” Auren RAUDA babu fashi, ko baka sonta dole zaka sota gaba ko dan ladabin ta, da biyayyar ta, yaushe zan barka ka fita waje neman aure bayan ga yarinya mai hankali da nutsuwa cikin gida, ka gama fushin ka, Aure dole sai anyi shi.”

da wani irin matsiyacin gudu ya figi motar sa, gudu kawai yake kan hanya, ba tare daya damu da gangancin da yake yi bisa titi ba, Allah ne kawai ya isar da Mustafa Inda ya nufa, lfy wani madaidaicin gida ya shiga, ko sallama baiyi ba, ya faɗa ɗakin bisa kujera mai ɗaya ya zauna tare da riƙe kansa dake ƙoƙarin barin jikin sa, Umar dake kwance bisa kujerun falon ne, ya tashi yana cewa.

” Mustafa lfy, ka shigo haka a birkice?”

Mustafa bai kulasa ba, saima kwantar da kansa da yayi jikin kujerar har yanzu yana riƙe da kansa.

” Haba Mustafa Please mana tell me, what is your problem?”

Sai yanxu Mustafa ya ɗago idanunsa da sukayi jajur kamar gauta, yayi magana cikin ƙunar rai yace.

” Umar wai ni! Wai ni! Za’a yiwa Auren dole, momy ta rasa waye zata haɗani da ita sai wannan macen marar kamun kai, wacce sam bana ƙaunar ta cikin Rayuwata ban taɓa tsanar mutum ba irin yanda na tsaneta.”

” Bangane mai kake nufi ba Barrister, wani irin Auren dole kuma wa zai maka Auren dole kana ɗa namiji, ba mace ba, naga dai mata akewa auren dole to kai kana namiji wa zai maka Auren dole?”

Ɗago kansa Mustafa yayi ya fara bawa Umar labarin Abunda Momy ta sashi ya kare maganar tare da cewa, “meyasa Momy bazata haɗa ta da Habeeb ba, tunda sunfi shiri.”

Umar abokin Mustafa ne, har Habeeb tare sukayi makaranta shima kuma Barrister ne, court ɗaya suke aiki da Mustafa wannan shine dalilin da yasa umar sukafi shiri da Mustafa fiye da Habeeb, duban Mustafa Umar yayi tare da zama yace.

” Hmm! Babbar magana Lallai Momy ta kira ruwa, amma ni sai nake gani tun farko wannan abun kamar laifin kane mustapha.”

Ɗago idanunsa da suka ci ja kamar borkono Mustafa yayi yana duban Umar kafin yace.

” Laifi na kamar ya ban fahimce kaba?”

” Eh laifin kane kamar yadda kaji na furta, tunda Daddy ya daɗe yana muku maganar ku fidda matan aure, kaga shi Dr Habeeb yana da tasa budurwar Hasina, amma kai kullum aka maka maganar Mace sai kace har yanzu baka ga matar Aure ba, wlh Mustafa da badan nasan halinka ba, zan iya cewa kana neman matan banxa ne tunda kake ƙin maganar Aure, Hujja ta Kuma itace, kana da jaraba ma’ana kai namiji ne mai buƙatar mace, amma sai kace ko wacce mace bata maka ba, idan kuma bance kana neman mata ba, to zance kana da ALJANAR da ta Aure ka take hana ka Aure.”

Tsuka Mustafa yaja yana duban Umar yace.

” Uwar Aljana ce ta Aure Ni, ba Aljana ba, ya ina faɗa maka matsala ta, domin samo solution kana kawo min wata nonse magana.”

Dariya sosai Umar yayi kafin yace.

” Ai baka da wani solution Barrister, domin kuwa duk wani masoyin ka na gaskiya shawara ɗaya zai baka shine yace maka kabi umurnin mahaifiyar ka, kuma ni gaskiya banga wani aibi a wajen RAUDA ba, duk inda cikakkiyar mace zata tsaya mai ji da kanta, RAUDA ma zata tsaya a nan, tana da ilimi da wayewa, kawai Mlm kabi umurnin mahaifiyar ka, ni shawarar da zan baka kenan, duk kuma wanda zai baka shawara saɓanin wannan ba masoyinka bane.”

Murmurshin ƙarfin hali Mustafa yayi tare da cewa.

” Kun kasa fahimta ta, Umar ana Aure ne domin a samu kulawa da kwanciyar hankali, kuma waɗannan abubuwan basa kasancewa sai tare da Soyayya, ka sani cewa ni mutum ne, mai son soyayya da kulawa, taya zan iya bawa RAUDA kulawa tunda bana sonta, taya zan saurari kulawar ta, tunda bata burgeni, wlh Umar bana hango Alkairi cikin wannan Auren da ake shirin kulla min, wlh bana son RAUDA ina tsoron Abunda zai faru bayan Auren nan, domin kuwa zamuyi zaman cutar kaine, kuma bana fatar haka cikin rayuwar Aure na, ina cikin tashin hankali Barrister Umar.”

” Kayi hkr Mustafa ka daurewa zuciyar ka kabi umurnin mahaifiyar ka, na tabbata Allah zai dubi wannan biyayyar da kayiwa mahaifiyar ka, ya baka farin ciki, cikin Rayuwar ka, koda daga baya zaka iya ƙara Aure idan ka samu wacce kake so ko nace zaɓinka, ka sawa zuciyarka salama.”

” Hmm! Shi kenan Umar zanyi amfani da shawarar ka, amma dai RAUDA kam bana sonta, bazan kuma taɓa gajiya da furta cewa bana sonta ba.”

Rarrashin Mustafa Umar ya cigaba da yi har ya ɗan sake kaɗan, suka ci gaba da zancen duniya.

” Momy! Momy! Momy!

Hasina ce mai ƙwalawa Momy kira tun daga falo, tana dariya, Inna ta hango zaune tayi wajen ta da gudu tana cewa.

” Oyoyo tsohuwa mai ran ƙarfe.”

Ture hanun Hasina Inna tayi tace.

” Ni cika ni, ƴaƴan yahudu, kunje kun tare can wata uwa duniya kun manta da iyayen ku, barin ma ke, ko ta wayar ma bakya neman mutum, to ita uwar taki, ai tana nema na, dana zama mata dole ta neme ni, tunda nice uwarta dana haife ta.”

Dariya Hasina tayi tace.

” Haba tsohuwa ban manta da kece kika haifi ummin ba, ai bare ki min tuni, yanxu ba gashi nazo ba, ai sai kuma kiyi hkr Inna na, kakata ta kaina.”

Dariya Indo tasa tana duban Inna tace.

” To kiyi dariya mana Inna kin haɗa fuskar, ya Habibu zo mu mata cakulkuli tayi ta Dole.”

Dariya Habeeb yayi tare da cewa.

” Ai kuwa ƙanwata ina ga hakan zamuyi tunda taƙi sakin fuskar.”

Hararar su Inna tayi tana dariya tace.

” ja’irai sai kuxo kuyi cakulkul ɗin mu gani, ke kuma na yafe miki badan halin ki ba.”

Gabaki ɗayan su dariya sukayi Hasina ta faɗa jikin Inna tana cewa bari naji ɗumin kakata.

Sosai sukayi hira da Inna kafin HASINA ta haura sama bedroom ɗin Momy da taji shuru tun shigowar ta babu labarin Momy, itama Indo nasu ɗakin ta nufa Momy tana Bacci HASINA ta sameta murmurshi tayi sannan ta fice zuwa ɗakin su Indo, ta samu Indo zaune tayi tagumi tana tunani, zama HASINA tayi ta dafa kafaɗar Indo tace.

” Sweet sis tunanin me kike haka?”

Ɗago kanta Indo tayi ta dubi HASINA, sai kuma idanunta suka ciko da hawaye tace.

” Aunty Hasina ina son ganin Mamana, jiya sanda nayi mafarkin jummalo tazo tana kuka tace min wai nabar Mama ita kaɗai babu mai taimaka mata da aike, ni dai gida zan koma, kuma kinga kullum Momy sai ta dinga hantara ta, tana zagina.”

Shuru Hasina tayi kafin tace.

” Kinga sweet sis, ya Habeeb ya faɗa min dalilin da yasa aka kawo ki, gidan nan domin kiyi karatu, dan haka ki daina zancen zaki koma ƙauye ki dinga yiwa Mama addu’a wata rana ai zakije ki ganta, kuma zata ji daɗin ganin ki, idan kina karatu, karki damu da zagin da Momy take miki, zai shige wata rana Babu Abunda yaxo zama duniya, komai nisan jifa ƙasa zai faɗo ki dinga sawa zuciyar ki salama, kiyi hkr kinji sweet sis, ki kuma cire damuwa a cikin ranki.”

” Shi kenan Aunty na daina.”

” Yauwa sweet sisi na, yanxu bari na watsa ruwa na fito.”

Mustafa daga gidan su Barrister Umar darect school ɗin su RAUDA ya wuce dake yasan department ɗin su, cikin Sa’a kuwa ya hango ta, tana zaune gefe ita da wasu ƴan mata biyu, tsayawa yayi gefen su tare da harɗe hanun sa a ƙirji cikin taƙama da gadara ya ce.

” Ƴan mata kuyi hkr ku bamu waje zanyi magana da wannan yarinyar” yana nuna RAUDA da baki.

Tashi ƴan matan sukayi ɗayar tana kallon Mustafa har tana tuntuɓe, harara RAUDA ta zabgawa Salima kafin ta maida kallon ta, kan Mustafa tace.

” Ya Mustafa sannu da zuwa, yau kaine da kanka?”

Cikin gadara Mustafa yace.

” Ba wannan bane ya kawo ni, na zone na baki shawarar da zata amfani Rayuwar ki, dashi.”

Cikin mamaki RAUDA tace.

” shawara Kuma ya Mustafa?”

” Yes Shawara, gaskiya na jinjinawa ƙoƙarin ki da kuma jajurcewar ki, akan Abunda kike so, kinyi Nasara gaskiya, Amma akan mahaifiyata! Ba niba, tunda har kikayi nasarar sace Zuciyar mahaifiyata, har take bani umurnin cewa na Auri Mace marar aji da kamun kai Irin ki, to kisani ina mai baki shawarar Cewa kije ki warware wannan Auren da ake shirin ƙullawa, domin kuwa wannan Auren muddun kika kuskura kika bari akayi wannan Auren, to ki sani cewa, Lahira sai yafi miki wannan Duniyar daɗi, domin kuwa gidana *KABARI NE ZAI ZAMA MIKI KI SHIRYAWA LIKKAFIN KI, DOMIN KUWA DOLE SAI KIN LULLUƁA SA, A ƘARSHE INA SON NA ƘARA SANAR DAKE CEWA BANA SONKI NA TSANEKI*.” Ya ƙarasa maganar yana takewa RAUDA ƙafa tare da murza yatsun ƙafar tata da takalmin sa.

Ɗago kanta RAUDA tayi tana murmurshi ta cewa Mustafa.

” Gaskiya naji daɗin wannan Albishir naka, domin kuwa ban taɓa jin farin ciki a rayuwata Irin na yau ba, bazan je na dakatar da Momy ga hana wannan auren ba, domin kuwa koda ace yau aka ɗaura min Aure da kai gobe na fito, alhamdulillah buri na ya cika, na shiryawa Rayuwar *ƘABARI* a cikin gidan ka, muddun kuwa dakai zanyi Rayuwa cikin wannan Kabarin, a ƙarshe ina son na sanar da kai cewa *INA SONKA INA KUMA ƘAUNAR KA*.”

Murmurshi mai sauti Mustafa yayi Kafin yace.

” Kin taɓa ganin inda akayi rayuwar kabari mutum biyu, kabari gida ne na mutum ɗaya tal dan haka ki daina kusanto inuwar rayuwar ki, dani domin kuwa ban kamace kiba, bare har nayi rayuwa dake, da zaki shekara kina furta kalmomi soyayya gare ni ni kuma sai na shekara goma ina furta kalmomi na ƙiyayya gare ki, yafi miki Alkairi ki nemawa kanki abokin rayuwa wanda ya dace da rayuwar ki, ki daina ƙoƙarin shiga gonata domin kuwa duk mutumin da yayi ƙoƙarin kutse cikin wannan gonar tawa, a ƙarshe mummunan irin ne yake fitowa daga wannan gonar.”

A razane RAUDA ta ɗago kanta ta kalli Mustafa, shi kuwa murmurshi ya mata tare da ɗaga mata gira, cikin ƙarfin hali tace.

” Me kake nufi cikin waɗannan kalaman naka?”

” Ba kya buƙatar amsa daga gare ni, zaifi miki Alkairi kije ki yiwa kanki hisabi” yana gama faɗin haka ya juya ya tafi, sai kuma ya tsaya tare da ƙara duban RAUDA yace “Hukunci ya rage gareki ki zaɓi wuta ko ki zaɓi ni’ima, dan dabara ya rage ga mai shiga rijiya, idan kunne yaji.” Kafin ya shige cikin motar sa yana murmurshi, tare da kannewa RAUDA ido.

_______________________________

Wlh naso nayi typing yafi haka yawa, amma kwana biyun nan ina busy kuyi hkr dani, dan Allah ku sani cikin Addu’ar ku, ina da matsala🙏🏻🙏🏻🙏🏻

*Vote*

*Share*

*And*

*Comments*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah ce)*

[2/19, 8:53 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*

*Nasmah ko Nasirah*

*Sara da Sassaka*

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.

Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya 🙏🏻

Masoyana na gode sosai da Addu’ar ku gare ni, kuma ina sa tsammanin Ubangiji zai amshi Addu’ar ku gare ni.

Masu min magana akan book ɗin Ruɗanin zuciya biyu, kuyi hkr dan gaskiya ba yanzu zan fara posting ɗin sa ba, Saboda bani da full times ɗin da zanke posting book biyu, kuma kunga bazan karɓi kuɗin kuba nazo bana muku typing akan lokaci, dan haka ina ga sai na gama wannan book ɗin na Indo a birni, ga waɗanda suka min magana cewa zasu turo kuɗin su, kuyi hkr har sai randa zan fara sakin book ɗin, dan gaskiya bazan karɓi kuɗin ku yanxu ba, ban fara posting ɗin book ɗin ba.

*بسم الله الرحمن الرحيم*

____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

*P*••••••••4️⃣9️⃣➡️5️⃣0️⃣

Shan gaban motar RAUDA tayi tana cewa.

” Koda kuwa kullum zaka dinga yankan naman jikina ne bazan taɓa bijirewa Auren ka ba, sai ma farin ciki da zanyi masoyina shike yankan naman jikina, ba kuma zanji zafin wannan yanka ta da kake ba, Saboda tsantsar soyayyar da nake maka, ina sonka me yasa ba zaka soni ba? a tunani na, nice macen da nafi dacewa ka Aura ka Kuma soni iya iyawar ka.”

Dariya sosai Mustafa keyi yana nuna RAUDA da hanu.

Cikin ƙula da jin haushi RAUDA tace.

” Meyasa kake min dariya bayan ni ba mahaukaciya bace?”

Cikin dariyar Mustafa yace mata.

_”To kuwa tabbas kin haɗa jini da mahaukatan, domin kuwa muddun ke ba mahaukaciya bace, ba zaki dinga furta waɗannan munanan kalaman naki ba, ke mahaukaciya ce, ta gaske ma kuwa mai shirin zuwa turu ma’ana (gidan mari) idan ba mahaukaci ba babu wanda zaiyi ƙoƙarin shiga inda aka tsane sa, ki kauce ki bani hanya! Tun kafin nabi kanki da wannan motar, kuma nabi kan banza, kinga sai na huta da wannan tsinannan nacin naki dangin Mayu_.”

Kaucewa RAUDA tayi daga gaban motar tasa, idanunta na tsiyayar da ruwan hawaye.

Murmurshi yayi tare da cewa.

” Ba yanxu ya kamata ki fara zubar da wadannan hawayen naki ba, ya kamata ki adana su domin kuwa gaba zasu miki amfani mussaman ma idan kika shigo cikin gidana hawayen da zakiyi kukan ma sai kin rasa su, domin suma hawayen daɗi ne yake sawa suzo duk sanda Azaba tayi Azaba to ba’a ganin hawaye a fuskar mutum ” yana gama faɗin haka yaja motar sa, tare da bule ta da ƙura, RAUDA Zama tayi daɓas tana hawaye tare da cewa.

_”So baka min adalci ba, zuciyata meyasa zaki kamu da son wanda bai san kina yiba, tabbas kin cuceni da kika kamu da Soyayyar Wanda bai damu da ke ba” tana maganar tana dukan ƙirjin ta da karfi_.

Sanda taci kukan ta, ta ƙoshi sanna ta tashi ta kama hanyar gida.

Mustafa sanda yayi sallar magaruba kafin ya dawo cikin gidan, Momy da Hasina sai Inna suke zaune a falon yayin da Momy da Hasina suke ta famar magana suna dariya sai gefen su kuma RAUDA ce zaune tayi shiru tana tunani, da murmurshi fuskar Mustafa ya nufo Hasina yana cewa.

” Wai wai wai! Yau kuma cikin gidan nan mun banu da magana uwar surutu an shigo” tare da zama gefen su ya cigaba da cewa ” Momy karfa ki biyeta ta saki tsamin baki dan wannan ba ƙaramar parrot bane.”

Dariya Momy tayi tace.

” Babu wani tsamin baki da ƴata zata sani, ku baku dameni ba sai ita.”

Murmurshi yayi yace.

” Nayi shuru tunda haka kika ce Momy” ya ƙarasa maganar yana murmurshi tare da cewa Momy.

” Ina su Ishaq ne?”

” Suna sama yanxu suka haura.”

Duban Mustafa Hasina tayi tana dariya tace.

” Alhajin miskilanci, ana yine har yanzu ko an daina?”

Murmurshi ya mata tare da cewa.

” Tunda kinzo saiki saka ido kiyi kallo saiki auna fahimtar ki.”

Gabaki ɗaya dariya sukayi har Momy tace.

” Iyayen bawa mutum magana a dunƙule ba, to shi kenan zanyi kallon tunda Allah ya kawo ni gidan.”

Dariya kawai Mustafa yayi kafin shima Habeeb suka sauƙo da Indo suna taɗi, kusa da Mustafa Habeeb ya zauna Indo kuma kusa da Inna ta zauna, dariya Habeeb yayi yace.

” Alhajin Allah yaushe ka shigo cikin gidan?”

“Yanzu bari ma ka gani na tashi naje na wanke jikina.”

A fito lfy Habeeb ya masa Inna kuwa harara ta sauƙewa Mustafa tace.

” Allah ya tura ƙeya Uban ƴan bakin hali.”

Murmurshi kawai Mustafa yayi ba tare daya kula Inna ba, dan yasan neman faɗa take.

Duban Indo Habeeb yayi yace.

” Hajiya Indo Jiya Daddy yace muje na yanka miki uniform zaki fara tafiya school so gobe idan Allah ya kaimu da safe ki shirya keda Aunty ki, zamuje kasuwa ko.”

” To ya Habibu Allah ya kaimu” sai kuma tayi shiru tare da jingina jikinta da kujera.

Duban Indo Habeeb yayi yace.

” Mamana lafiyar ki kuwa tun jiya nake ganin sauyi a tattare dake, kamar wacce kike cikin damuwa, me yake damunki?”

” Babu Abunda yake damuna nikam” ta mayar masa amsa.

Murmurshi Habeeb yayi yace.

” Banda dai babu kam, tunda dai gashi yanayin ki ya sauya.”

Sharifa dake sauƙowa daga step ne tace.

” Tambaye ta dai ya Habeeb, dan nima tun jiya naga alamar damuwa daga gare ta, na kuma tambaye ta taƙi cemin komai.”

Ko kafin Habeeb yayi magana Hasina ta riga sa, dake ita tasan damuwar Indo.

” Kunga tunda tace muku babu komai ai sai kuyi hkr ku ƙyaleta, kinga sweet sis ɗina tashi mu wuce ɗaki kafin su saka miki ciwon kai.”

Tashi Indo tayi suka wuce ɗaki, murmurshi kawai Habeeb yayi ba tare da yace komai ba, Momy da RAUDA kuwa kusan tare sukayi tsaki suna bin Indo da mungun kallo, Inna ma dai nata ɗakin ta wuce.

Da daddare Daddy ya kira Mustafa da Habeeb akan zancen Auren su, inda Habeeb ya gabatar da Hasina a matsayin matar da zai aura Mustafa cikin takaici da baƙin ciki ya sanar da Daddy cewa RAUDA ya futar, Daddy yaji daɗin zabin yarannasa sosai, inda yace zaije ya musu tambayar Auren, da suka koma ɗaki sosai Habeeb yayi mamakin Mustafa da yace ya zaɓi RAUDA a matsayin matar Aure, cikin murmurshin takaici mustapha ya ceqa Habeeb.

” Ka daina kiran RAUDA a matsayin zaɓi na, ka kira ta a matsayin zaɓin mahaifiyata, domin kuwa itace kawai take sonta ba niba, ni dai kawai nayi biyayya ne ga umurnin ta, amma hakan ba yana nufin cewa zanyi Rayuwar Aure da RAUDA bane.”

Ajiyar Zuciya Habeeb ya sauƙe Sannan yace.

” Nasan da wannan umarnin tun kafin ka sani nayi shuru ne kawai ban sanar da kai ba, sai dan ina tunanin ko Momy zata janye maganar daga baya, ashe bata janye ba, a gaskiya Momy tayi kuskuren haɗa Auren da babu Soyayyar namiji cikin ta, ina ma laifin ace macen ce bata so shi namijin ke so, da ƙiyayyar zata zo da sauƙi, Ubangiji Allah ya kyauta ya daidaita tsakanin ku.”

Taɓe bakin sa Mustafa yayi tare da shigewa tollet abunsa.

Washe gari misalin ƙarfe 1 Habeeb da Hasina da Indo suka wuce kasuwa suka yan kowa Indo uniform, daga nan ɗinki suka bayar da zumar a dinka kafin suje su dawo, Hospital suka shige Habeeb ya biya kuɗi akan a yiwa Indo wankin haƙori, tas kuwa aka wanke, haƙorin Indo har wani sheƙi suke, kamar basu taɓa yin yellow ba, Habeeb kuwa sai tsokanar Indo yake har suka dawo wajen mai ɗinkin suka karba daga nan ma SUPER MARKET suka shige suka sayo kayan ciye-ciye kalala Sannan suka dawo gida.

______________________________

Allah sarki rayuwa wai Hausawa suka ce sannu sannu bata hana zuwa sai dai a daɗe ba’a jeba, Indo ta fara tafiya makaranta cikin Sa’a da kuma Nasara domin kuwa tafi kowa ganewa cikin ajin nan inda tayi sabuwar ƙawa mai suna Zahra yar gidan deputy governor, sosai jinin su yazo ɗaya da Indo, gashi kuma dukansu gifted ne, haka kuma an sata islamiyya a nan cikin unguwar tasu, hakan sai yasa Indo yanxu bata da lokacin kanta daga ta dawo daga boko sai kuma ta wuce islamiyya, asabar da Lahadi kawai take da time nan ma da daddare bayan isha malamin da Habeeb ya ɗauka mata na lesson yake zuwa, haka kuma aikin gida, takan taya Momy koda ran Momy baiso ba, domin kuwa har yanzu akwai ƙiyayyar Indo cikin Zuciyar Momy.

Yau Indo a gajiye ta shigo gidan, zama tayi kusa da Inna tana dariya tace.

” Hajiya Inna ya naga yau sai famar haɗa rai kike wani abu ne ya faru?”

” Me kuwa zai faru Indo kawai dai yau haka na tashi.”

Murmurshi Indo tayi tace.

” Inna kenan, yauwa Inna ya Habeeb ya dawo daga Hospital ɗin nasu kuwa?”

Harara Inna ta watsawa Indo tace.

” Meye kuma wani cospital, ni ki daina min wannan turancin naku.”

Dariya sosai Indo keyi tace.

” Kai Inna bafa cospital ba, Hospital ake cewa, ma’ana asibiti nake nufi.”

“To bai dawo ba, sai ki tashi kije ki cire kayan makarantar ki samu kici abinci.”

Tashi Indo tayi tana dariya ta haura step tana ƙoƙarin cire bag ɗinta, wani irin wawan karo taji tayi da mutum taga-taga Indo tayi zata faɗi a kan step ɗin, cikin jin tausayin ta idan ta faɗi a step ɗin ya sashi saurin tallafo ta jikin sa, runtse idanta Indo tayi tana jiran sarautar Allah, sai taji ta, kwance ƙirjin mutum, shiko wani irin shokin yaji kamar wanda wutar lantarki ta jasa, a hankali Indo ta buɗe idonta, ras ta sauke su fuskar Mustafa ya Wani haɗa rai, kafin ya saketa yana mata mungun kallo tare da cewa.

” Ke dai kullum cikin Hauka kike, sam baki da hankali cikin jikinki” ya ƙarasa maganar tare sauƙe mata ranƙwashi bisa kanta.

Riƙe Inda ya ranƙwashen tan Indo tayi tana hararar Mustafa itama, ido cikin Ido tare da murguɗa masa baki, zaro idanunsa yayi yana nuna kansa da yatsa yace.

” Ni kike harara da murguɗawa baki lallai kuwa yau jikinki zaiyi tsami cikin gidan nan” bakin nata Mustafa ya kama ya murɗe da ƙarfi, sanda hawaye suka zubo fuskar Indo, da ƙyar ya sake mata baki, rugawa da gudu Indo tayi sanda tazo daf kofar ɗakin su tace.

” Allah ya isa mungu azzalumi, Allah ya saka min.”

Biyota yayi da gudu, ko kafin ya shigo ta faɗa cikin ɗakin tare da danna key, ƙwafa Mustafa yayi tare da kaɗa kansa ya shige.

Cikin sauri Mustafa ya nufi hanyar waje, Muryar Momy yaji tana cewa.

” Kaga kazo idan fita zakayi ka wucewa RAUDA da waɗannan kayan nata gidan su, tace min daga makaranta gida zata wuce, sai ka miƙa mata su.”

Haɗa Ransa Mustafa yayi yace.

” MOMY ba can zanje ba yanzu ni office zan shige kawai ki bayar a kaimata.”

” Ban bayar an kai matan ba, ka ɗauka ka kai mata ko kuma ranka ya ɓaci wai Mustafa meyasa kake min musu ne, duk sanda na maka Magana akan RAUDA?”

” Nifa Momy ba musu nake miki ba, kawai ba hanyar zanbi bane.”

” To ko ba hanyar zakabi ba, ka ɗauka ka kaimata idan yaso sai ka dawo kayi hanyar taka.”

Ɗaukar kayan Mustafa yayi cikin ɓacin rai ya fice, ita kuwa Indo bayan ta cire kayan ta, ta fito cikin sauri tayi kitchen, Momy ta samu tsaye tana aikin yankan koɓewa.

” Sannu da aiki Momy”

Harara Momy ta sauƙewa Indo tace.

” Wai ke bazaki fita cikin sha’anina bane kafin nace ki daina kulani dole ne saikin kulani, koni uwar kice, wani wai sannu kin sani aiki ne da zaki cemin sannu, dallah! Ɗauki Abunda ya kawo ki ki fice daga cikin kitchen ɗin.”

Wannan karon Indo bata damu da zagin da Momy ta mata ba, domin kuwa idan da sabo yanxu ta saba da zagin Momy ɗaukar abincin ta, Indo tayi ta fice daga kitchen ɗin, Hasina da sharifa ta tarar cikin falon kusa dasu ta zauna taci abincin, suna taɗi.

Shiko Mustafa a ƙofar gidan su, RAUDA ya tsaya ya miƙawa mai gadi kayan RAUDA yace gashi ya shigar musu gida sannan ya wuce abunsa, mai gadi kuwa har cikin falo ya kaiwa mami kayan, tambayar sa tayi waye ya basa, ya amsa mata da Mustafa, wani ashar mamy ta sauƙe tare da cewa.

” Amma wannan yaron akwai shege mai taurin kan tsiya, Wato shi yafi ƙarfin ya kawo min kayan har cikin ɗaki gara ya bawa mai gadi ya kawo, badai an kusa Auren ba, zanyi maganin wannan taurin kayin naka daga kai har Uwar taka………….

Kuyi manage da wannan bani da times ne sosai kwanan nan, ayyuka sun min yawa ga school.

*Vote*

*Share*

*And*

*Comments*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah ce)*

[2/21, 4:52 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*

*Nasmah ko Nasirah*

*Sara da Sassaka*

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.

Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*

____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

*P*••••••5️⃣1️⃣ ➡️ 5️⃣2️⃣

Haka Mamy ta gama mitar ta ita kaɗai ta gaji tayi shiru.

Yau Indo ana gida Babu islamiyya kasancewar yau Alhamis, tana cikin su Sharifa da Hasina, sai zance suke, har la’asar lokacin shiga kitchen yayi, tare suka shiga dukan su, komai tare suke basa ware Indo kasancewar ta ƙarama a tsakanin su, Sharifa ce ta dubi Indo tace.

” Indo yau fa kece zakiyi girkin nan, ehe kiyi mu gani ko kina gane yanda mukeyi kullum dan kinsan ya Mustafa yana son matar da ta iya girki sosai” Sharifa ta ƙarasa maganar cikin zolaya.

Haɗa fuska Indo tayi tace.

” Allah ya sauwaƙa ni bana son ya Mustafa yanxu, Allah na tsanesa dama rashin Hankali yasa nake cewa ina sonshi, mungu ne kuma azzalumi.”

Zaro ido Sharifa tayi tana kallon Indo kafin tace.

” Oh yanxu kina da hankali kenan, ya Mustafa da kullum kike kira kina so yanxu kice bakya sonsa.”

Murmurshi Indo tayi tana duban Sharifa kafin tace.

” Aunty Sharifa kenan, nayi Hankali yanxu Aunty Sharifa, na fara sanin menene ciwon kaina, menene kuma rayuwa, kuma duk ta sanadiyyar ku na fara sanin hakan, da ke da ya Habeeb da Aunty Hasina, sai aminiyata Zahra, kune kuka fara nuna min rayuwa da kuma nutsuwa, har nazo na fara fuskanta, zan iya miki rantsuwa da Allah cewa bana son ya Mustafa, dama kwalliyar sane kawai yake burgeni ko a da ma rashin Hankali yasa nake cewa ina sonsa, kwalliyar sa kai yake burgeni ni kuma saina ɗauki hakan a matsayin soyayya, ya Habeeb shine wanda ya banbance min haka ya nuna min yanda zan gane Soyayyar gaskiya tun daga nan na fuskanci cewa bana son ya Mustafa, na kuma fuskanci hakan, dan haka ni babu Soyayyar ya Mustafa cikin raina.”

Ga baki ɗayan su shuru sukayi suna mamakin sanjawar Indo lokaci ɗaya mussaman Sharifa da tafi Hasina sanin waye Indo, cikin Zuciyar Sharifa take cewa, (Allah buwayi gagara misali, lallai ilimi haske ne cikin rayuwar ɗan adam da kuma zama cikin wayayyun mutane, ya kan sa mutum ya sauya ɗabi’un sa, wai yau Indo ce tasan ciwon kanta, tabbas yarinyar tana da good brench ikon Allah)

Hasina ce ta dawo da sharifa daga duniyar tunanin da ta lula ta hanyar cewa.

” Kinga ɗaura girkin nan maza kar dare yayi mana.”

Ɗaurawa Indo tayi suna kallon ta, harta kamalla cikin mamaki yanda Indo tayi girkin ta tsaf Kamar yanda su Hasina keyi, lallai Indo tana da ƙwaƙwalwa, dariya Sharifa tayi tana zolayar Indo tace.

” Masha Allah! Sweetie na ta iya girki, Allah komai yayi dai-dai kinyi ƙoƙari.”

Dariya Itama Indo tayi tace.

” Aunty Sharifa ke da kinyi zaton bazan iya bane cap ai Babu kalan abincin da bazan iya ba cikin gidan nan.”

Dariya dukansu sukayi cikin haɗin baki su kace.

” Ai kuwa munga alama, gashi kin bamu mamaki.”

Ɗaukar abincin sukayi suka jera su saman daining, sannan suka wuce ɗaki wanka.

Zaune yake cikin office tun ɗazu yake jin alamun mararsa na ƙullewa, Sanin abun zai iya tashi masa haiƙan ya sashi tashi cikin sauri ya fice daga office ɗin, motar sa ya shiga yaja da ƙarfi yana cije lips ɗinsa Allah ne kawai ya iso da Mustafa gida lfy, domin kuwa shi kaɗai yasan abinda yake ji, babu kowa cikin falon da ƙyar ya haura step ɗin, yana shiga ɗakin ya zuɓe saman bed sai kuma ya fara mutsu-mutsu yana cizon lips ɗinsa, tare da riƙe marar tasa dake sara masa.

Indo da ta fito daga bedroom ɗin su zatayi na Inna sai taga ƙofar ɗakin su Habeeb buɗe, hakanne ya sata kutsa kanta cikin ɗakin domin ita a zaton ta ya Habeeb ne ya dawo daga Hospital, sallama tayi kusan baki uku jin babu wanda ya amsa mata ka wai sai ta shige cikin bedroom ɗin, zaro ido tayi ganin Mustafa kwance dai mutsu-mutsu yake, ga hawaye kwance fuskar sa, Indo Sarkin tausayi, da sauri ta ƙarasa bakin bed ɗin tana cewa.

” Ya Mustafa meya sameka, baka da lafiya ne?”

Shuru Mustafa ya mata ba tare daya amsa mata ba, yana cigaba da mutsu-mutsun sa, cikin azaba domin baida bakin magana a yanxu, da ƙyar ya ɗago hanunsa yana mata nuni da drower alamun ta ɗauko masa drog ɗin sa, ita kuwa Indo bata gane me yake nufi ba, haurawa saman bed ɗin tayi ta kamo hanun Mustafa tana cewa.

” Ya Mustafa sannu kona kira Momy ta kaika asibiti, kaga baka da lfy har kuka kake yi.”

Mustafa baiyi magana ba saima jawo Indo da yayi jikin sa tare da ƙanƙameta gam yana ƙoƙarin zura hannun sa cikin rigar ta, ƙoƙarin ƙwace kanta Indo take tana cewa.

” Ya Mustafa meye haka, ka sakeni dan Allah naje na kira maka Momy ta kaika asibiti, malamin islamiyyar mu yace haramun ne namiji yake taɓa jikin mace” tana maganar ne tana ƙoƙarin ƙwace jikin ta daga garesa, shiko Mustafa baima san tana yiba shidai burin sa, kawai ya kamo breast ɗinta da suka fara ɗan tasowa, domin kuwa Mustafa baya cikin hankalin sa.

A nutse bakinsa ɗauke da Sallama ya shigo ɗakin, turus ya tsaya yana kollon Mustafa na kokuwa da Indo, wani irin maƙoƙon baƙin ciki ne ya tsayawa Habeeb a rai, da sauri ya ƙarasa wajen nasu, cikin zafin nama ya fisgo Indo da ƙarfi, ya wullo ta ƙasa yana mata mungun kallo, shiko Mustafa ɗago kansa yayi da ƙyar ya kalli Habeeb kafin ya ƙara danƙe marar sa, yana juyi, hanun Indo Habeeb yaja sannan ya wurga ta waje yana nunata da yatsa, simi-simi Indo ta shige bedroom ɗin su ta faɗa bisa bed sai kuma ta saki kuka mai sauti.

Komawa ɗakin Habeeb yayi, tare da buɗe drower ya ɗaukowa Mustafa drog ɗin sa da ruwa ya tallafo sa, sannan ya basa yasha, cikin minti biyar ya fara haɗa gumi sai kuma bacci mai nauyi ya ɗebesa, ficewa daga ɗakin Habeeb yayi ya faɗa nasu Indo cikin faɗa, Allah yaso babu Kowa cikin ɗakin su Hasina sunyi bedroom ɗin Inna, harara Habeeb ya zabgawa Indo kafin yace.

” Kukan munafurcin me kike, ki faɗa min meya kaiki bedroom ɗin mu, ki faɗa min! Nace?” Ya ƙarasa maganar cikin tsawa.

Ja da baya Indo tayi tana riƙe bakin ta, sa kuka ke ƙoƙarin ƙwace mata, cikin tsorata da lamarin ya Habeeb ga Idonsa sun koma red colour mutum da bai taɓa mata tsawa ba, shine yau yake mata, mutumin dako laifi tayi sai dai ya mata faɗa cikin nasiha, shine yau yake mata wannan ihun a kai, cikin tsoro tace.

” Na Na Naje neman kane shine na gansa yana kwance baida lfy shine nace kona kira masa Momy ta kaisa asibiti, shine ya jawo ni jikinsa.”

” Ya jawo ki jikinsa koko ki haura bed ɗin har ya samu damar jawo ki, ba nace ki daina shiga bedroom ɗin mu ba, har sai kinyi sallama an miki izini ba?”

” Ka faɗa min kayi hkr bazan sake ba.”

Ƙwafa Habeeb yayi sannan ya fice daga cikin ɗakin, koda daddare da suka zo cin abinci babu Mustafa domin kuwa bai tashi ba, da Daddy yace a kirasa sai Habeeb yace kar a tashe shi baya jin daɗin jikin sa, Indo kuwa tana gefe jikin Inna sai satar kallon ya Habeeb take, ganin yayi banza da ita kamar babu ita a wajen ko inda take bai kalla ba, idanunta ne ya ciko da ƙwalla tayi saurin gogewa, bata san kuma duk abunda take Habeeb yana kallon ta, ta kasan idanunsa, sosai ta basa tausayi ganin yanda take goge hawaye a ɓoye, duk da haka yayi fuska bai kulata ba, Daddy ne yace.

” Habeeb yaya maganar ginin da zaku tayar ne, a nan cikin Estate ɗin, naji har yanxu kunyi shuru bakwa magana?”

” Daddy ai jibi za’a fara ginin in sha Allah mun gama magana dasu, zasu mana part biyu.”

” Okey yayi Allah ya taimaka, jiya Daddyn Hasina ya kira ni kan cewa yaushe za’a tsaida ranar Auren amma nace masa suyi hkr har ku kammala ginin gidan ku, ya kuma fuskance ni, ita kuma Hasina ashe tunda tazo bata je wajen ƴan uwan mahaifinta ba? sai jiya Alhaji Ibrahim ɗin ke sanar dani.”

Dariya Habeeb yayi yace

” Daddy gobe take da niyar zuwa daman taje tayi sati daya a can.”

” Okey Allah ya kaimu” Daddy ya furta tare da wucewa bedroom ɗin sa, Momy ma bata juma ba, ta wuce nata bedroom ɗin, Indo ma bin Inna tayi tace nan duniya ɗakin Inna zata kwana, tambayar ta Hasina tayi ko sun mata laifi, tace babu komai ita dai kawai zata kwana ɗakin Inna ne , ina itace tace su rabu da ita yau taga alamar Yan iskan tane suke kusa da ita, dariya sukayi kafin suma suka shige nasu bedroom ɗin, a ɗaki Inna ritsa Indo tayi tace ta faɗa mata ko akwai Abunda aka mata ne, taga kamar taci kuka amma Indo tace nan duniya babu komai haka dole Inna ta ƙyaleta.

Mustafa bai farka ba sai wajen goma na dare, wanka yayi tare da zuwa ya zauna ko mai bai shafa ba, kansa ya riƙe yana tuno Abunda ya faru ɗazu tiryan-tiryan pic ɗin abun ke faɗo masa, da ƙarfi yace “NO!”

Ɗago kansa Habeeb yayi ya kalle sa, kafin ya kawar da kansa yana cewa.

” Ya kamata ace na baka shawara wacce kullum nake son furta maka ita nake tsoron girman kanka zai hana ka ɗauka” Habeeb bai saurari me Mustafa zaice ba ya cigaba da cewa ” ya kamata ka riƙe RAUDA matsayin matar so, tunda tana sonka kuma bata da wani aibu duk abunda mace mai ji da kanta take dashi itama RAUDA tana dashi, ka manta da……..

Da katar da Habeeb Mustafa yayi ta hanyar ɗaga masa hanu alamun yabar maganar baya so, murmurshi Habeeb yayi tare da kauda kansa ya kuma yi shurun ba tare daya ƙara cewa komai ba.

Wasa wasa yau kimanin kwanaki biyar Habeeb baya kula Indo ko kallon ta baya yi, Indo ta damu sosai da sauya mata da Habeeb yayi, gashi kuma tunda wannan abun ya shiga tsakanin ta, da Mustafa bata ƙara sashi cikin idanunta ba.

Zaune take a makaranta sun fito break ita ɗaya kusa da bishiyar maina ta tafka tagumi, Zarah da tazo kusa da itane ta zauna tare da dafa kafaɗar Indo tace.

” Lafiya ƙawata tun ɗazu nake neman ki cikin makarantar nan ashe nan kika taho?”

“Eh” kawai Indo tace mata a takaice.

Zahra ƙara cewa Indo tayi.

” A’isha Meya same ki naga kamar ranki a ɓace yake?”

” Nace miki babu! Ko kin isheni da tambaya.”

Murmurshi Zahra tayi kafin tace.

” Allah ya baki haƙuri ni a nawa tunanin mun riga da mun zama ɗaya haka kuma damuwar mu ma zata kasance ɗaya, ashe abun ba haka yake ba a wajen ki, Nice kawai na ɗauke ki aminya wacce nake iya sanar dake damuwata ba tare da shamaki ba.”

Sanyi jikin Indo yayi, ta kamo hanun Zahra tana tace.

” Sam ba haka bane ƙawata baki da shamaki da damuwa ta, kawai raina ne yake ɓace sakamakon daina kulani da Ya Habeeb yayi, sam banjin daɗin haka mussaman yanda ya Habeeb ya dauke ni tamkar ƙanwar sa wacce suka fito ciki ɗaya, amma yau fushi yake dani kwana biyar kenan baya kulani, abun yana damuna sosai cikin zuciyata.”

Cikin mamaki Zahra tace.

” What! Ya Habeeb shine yake fushi dake har ya kai 5dys bai miki magana ba, wani irin laifi kika masa haka mai girma A’isha da har zaiyi fushi dake haka?”

Cikin zubar da hawaye Indo take mayar Zahra abunda ya faru.

” Gaskiya A’isha laifin kine taya har zai jawo ki jikinsa ba tare da kece kika haura bed ɗin ba, gaskiya laifin kine.”

Duban Zahra Indo tayi tace.

” Kina nufin kema kina zargi na kenan?”

” Ko kaɗan bana zargin ki, A’isha, kawai na baki laifin kine na kuskuren kusantar sa da kikayi, sanda kika gansa haka kamata yayi kije ki sanar da mahaifiyar sa, ba wai ki tsaya kusa dashi ba, shi kanshi ya Habeeb ba wai yana zargin ki bane kawai ransa ne ya ɓaci kan cewa yace miki karki dinga shiga ɗakin saida izini kuma yana da gaskiya, ke kuma kika taka masa dokarsa, Allah A’isha bansan wannan Mustafan naku ba, amma na tsane sa, mussaman yanda kike bani labarin tsanar da ya miki.”

” Yanzu Zahra meye mafita?”

” Mafita ɗaya ce A’isha kije ki bawa ya Habeeb haƙuri ina da tabbacin kuma zai yafe miki.”

” Shi kenan zanje in sha Allah.”

” To ki tashi mu koma Class kinga an kaɗa tun ɗazu, kafin malami ya shigo Class.”

Tashi Indo tayi suka shige Class ita da Zahra.

” Ina ƙara sanar dake a karo na biyu dan ubanki! Idan har na kara kashe kuɗi na, naje na karɓo miki taimako wajen malami kikayi sakaci dashi, ƙyale ki zanyi kije kisha wahalar, don wannan karon har uwar tasa ba zamu bari ba, naga ƙiyayyar tasa tayi yawa.”

RAUDA ce tace.

” Wallahi Mamy wancan lokacin ma ba wasa nayi da shiba nayi iya ƙoƙarina, abunne kawai yaci tura, amma yanxu kam in sha Allah zanyi ƙoƙari.”

” Dako kin taimaki kanki, munyi magana da Gambo tace na bari sai anyi Auren muje wajen malamin.”

” To Allah ya kaimu Mamy.”

________________________________

Fan’s kuyi hkr da rashin bin comments ɗinku da banayi kwana biyun nan hakan ta faru ne sakamakon rashin times da banda shi amma ina ganin sharhin kowa kuma ina matukar jin daɗin yanda kuke comments domin kuwa kuna bani ƙwarin gwiwwa.

*Vote*

*Share*

*And*

*Comments*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah ce)*

[2/24, 12:47 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*

*Nasmah ko Nasirah*

*Sara da Sassaka*

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.

Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya 🙏🏻

Fan’s Kuyi hkr da rashin jina da ba kwayi akai-akai wlh banda time ne sosai.

Masu min sharhi ina mungun jin daɗin sharhin ku domin kuwa yana faranta min rai, kuyi hkr da rashin reply da bana muku, ina mungun sonku irin sosai ɗin nan❣👌🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*

____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

*P*•••••••5️⃣3️⃣ ➡️ 5️⃣4️⃣

” Mamy jiya naso tambayan Daddy kuɗin less ɗin nan sai kuma ya fita kafin na tashi.”

” Oh kinga nima na manta aida na tambaya miki shi, yanzu kam sai dare kuma idan Allah ya dawo dashi lfy, ni ya Maganar Salma ne da khabeer, har yanzu shuru ko babu wani labari?”

” Hmm! Bari kawai Mamy abun babu daɗi domin kuwa khabeer ya yaudari Salma, ya koma neman ƙawarta Safiya, harma ya tura gidan su an basa.”

” Subhanallah! Shi khabeer ɗin ne ya aikata haka, amma gaskiya yayi asara wlh ya cuci yarinyar nan duk irin soyayyar da take masa, to Allah ya saka mata.”

” Ameeen dai Mamy amma dai khabeer ya cuci Salma.”

” Tashi RAUDA kije ki shirya kixo ki tafi min aiken nan.”

Tashi RAUDA tayi tare da cewa “to Mamy” kafin ta wuce ɗakin ta.

Tsaye suke bakin get ɗin makarantar tun ɗazu aka tashi amma driver baizo ya ɗauke su ba su Ishaq sun damu su tafi gida yunwa suke ji, itama Zahra taƙi tafiya a cewar ta, sai anzo an ɗauki Indo kafin itama su tafi, shuru shuru har wajen 3:00pm babu labarin drivern gidan su Indo, hakan ce tasa Zahra duban Indo tace.

” A’ishatu Musa, ya kamata fa ku shigo motar gidan mu, sai mu sauƙeku unguwar ku, mu wuce.”

Hararar Zahra Indo tayi tace.

” Yau kuma wani salo kika ɗauko na kiran sunana harda na tsoho na, to muje ku sauƙe mu, bansan uzirin daya hana Idi zuwa ɗaukar mu ba gashi harna bari school bus ta tafi aida mun bisu.”

Dariya Zahra tayi tace.

” Ganan motar gidan mu ne zaki hau school bus, aiko har mu gama school ba zamu taɓa hawa school bus ba, dalla! Malama shiga mota mu wuce.”

Cikin dariya Indo suka hau motar sannan driver yaja suka wuce, suna tafiya Habeeb na shigowa cikin school ɗin cikin sauri domin kuwa Daddy ya kirasa yace yau Idi driver bazai samu fitowa aiki ba, baida lafiya dan haka koshi ko Mustafa wani yaje ya ɗauko yara a school, fitowa Habeeb yayi yana dube-dube cikin makarantar babu kowa ciki, dawowa yayi wajen mai gadi yake tambayar sa yaushe ɗalibai suka watse, sanar dashi mai gadi yayi cewa

” ai yanxu wasu suka wuce da yara tun ɗazu suke jiran mai ɗaukar su baizo ba, shine naga sun hau motar gidan gomnati, sun tafi maybe ko zasu sauƙe sune a unguwar su.”

Ajiyar Zuciya Habeeb ya sauƙe tare da hura iska daga cikin bakinsa yace.

” Okey na gode Baba Bari na koma gidan nagani.”

A ƙofar Estate ɗin suka sauƙe su Indo sannan suka wuce suna ɗaga musu hanu, da gudu su Ishaq suka wuce ita kuwa Indo cikin nutsuwa ta shigo, babu kowa cikin falon sai Mustafa shi kaɗai yana kallon ƙwallo, Indo Bata kallesa ba, ta ɗaga kanta ta shige har ta fara haura step ɗin taji Muryar Mustafa yana cewa.

” Keeeeeeee! Ƴar ƙauye.”

Murmurshi Indo tayi ba tare data tsaya ba, ta cigaba da taka step ɗin abunta cikin nutsuwa tare da aji, domin kuwa yanxu Indo tasan ciwon kanta, amma har yanzu tana nan da halinta na rashin son raini da wulaƙanci, a karo na biyu taji ya ƙara cewa.

” Keee! Fitinanniyar ƙauyen DASINA, ko bada ke nake Magana bane?”

Juyowa Indo tayi still har yanxu fuskar ta ɗauke da murmurshi tace.

” Na’am mungun cikin birni Sarkin girman kai na cikin gidan su.”

Zaro ido Mustafa yayi yana kallon Indo cike da mamakin yaushe ya fara wasa da Indo harta raina sa haka, shi idanunsa ma idan ba ƙarya suka masa ba, gani yake kamar yarinyar tayi fresh ta girma, har wani hips ta ajiye haka ma ƙirjin ta ya ɗan taso, lallai girman ɗan mutum babu wuya, zaro ido yayi cikin tsawa yace.

” Wa! Kike gayawa wannan maganar?”

Cikin rashin tsoro Indo tace.

” Ga wanda ya kira fitinanniyar ƙauyen DASINA dashi nake.”

Murmurshi Mustafa yayi yace.

” Eh lallai Bahaushe yayi gaskiya da yace ɗan ƙauye yafi ɗan dako sanin hanyar tashi, tabbas ɗan ƙauye bai iya samun waje ba, sai yafi ɗan gari zaƙewa, ko da yake ai babu damuwa tunda daman haline tunna ƙauye kuma ai daman shi ɗan ƙauye kullum yana cikin jahilci bazai taɓa wayewa ba.”

Cikin jin Zafin maganganun Mustafa Indo ta cije laɓɓen ta, ta mayar masa da amsa da cewa.

” Ashe kuwa jahillai suna da yawa cikin gidan nan ina ga zasu iya kai su uku, kaga kenan ai ƴan ƙauyen muna da yawa saimu haɗu muje muta jahilcin” tana gama fad’in haka ta haura da sauri ba tare da ta tsaya ta saurari Abunda Mustafa zaice ba.

Ai kuwa Indo tabar Mustafa cikin tunanin waye ƴan ƙauye jahilai ukun, wannan shine idan baki yasan Abunda zai faɗa baisan me za’a mayar masa ba, ya daɗe yana nazari sai can amsar ta faɗo masa, wato Indo tana nufin *INNA DA DADDY DA KUMA ITA KANTA* lallai yarinyar nan ta faɗa masa baƙar magana wato wai itama ta iya azanci lallai kuwa bashi taci kuma saita biyasa.

Habeeb da sauri ya shigo falon jin hayaniyar su Ishaq a sama shine ya tabbatar masa cewa sun dawo, duban Mustafa yayi yace.

” Wai daman kana cikin gidan nan baka fita ba?”

Mustafa bai dubi Habeeb ba idanunsa na bisa tibi yace.

” Eh yau banda aiki, sai tomorrow, harka dawo kenan?”

” Ba dawowa nayi ba, yanxu zan koma Daddy ne ya kirani yace, naje na ɗauko yara a makaranta shi yasa na dawo.”

Indo dake cikin ɗaki sama-sama take jiyo Muryar Habeeb cikin sauri ta fito daga cikin ɗakin Habeeb kamma harya fice, da gudu ta fita itama, kallo ɗaya Mustafa ya mata sannan ya kawar da kansa.

” Ya Habeeb! Ya Habeeb! Ya Habeeb!”

Jiyowa Habeeb yayi tare da tsayuwa har Indo ta ƙaraso ta tsaya a gaban sa tare da haɗa hanunta biyu tayi narai-narai da idanunta tace.

” Dan Allah ya Habeeb kayi hkr na tuba bazan sake ba, wlh zanke jin maganar ka.”

Murmurshi Habeeb yayi tare da cewa.

” To sarkin kuka maida hawayen naki ya isa haka, daman so nake ki gane laifin ki da kanki ki gyara kuma kin gane, komai ya wuce.”

Dariya sosai Indo tayi tace ya Habeeb na gode sosai in sha Allah kuma bazan sake ba, ya Habeeb ina Aunty Hasina ban ganta ba, nasan dai Aunty Sharifa ta tafi school?”

” Hasina taje gidan su sai next week zata dawo.”

Ɓata ranta Indo tayi tace.

” Shine ta tafi kota jiran na dawo muyi sallama, gidan bazai min daɗi ba tunda babu Aunty Hasina.”

Murmurshi Habeeb yayi tare da cewa.

” Haba Mamana ai next week kamar yanxu ne, karki damu kinji idan na dawo zamuje gidan nasu.”

Dariya Indo tayi sannan ta koma ciki shima Habeeb ya wuce nasa wajen aikin.

Hausawa sunce sannu sannu bata hana zuwa saidai a daɗe ba’aje ba, cikin wata huɗu su Mustafa suka gama ginin gidan su na a gani a faɗa, domin kuwa gidan ya amsa sunan sa gida, Momy itace da kanta ta haɗa kayan Auren su, komai Momy itace da ƙawarta Hajiya Ruƙayya suka haɗa sun kuma haɗa musu kayan aure masu inganci Atampopi da less a shagon Daddy aka ɗauko su, sauran kaya kuma a kasuwa suka saya set ɗin akwati ma kowacce 12 aka mata, shidai Mustafa duk wannan Abunda ake baya gabansa domin kuwa shi mantawa ma yake da wata RAUDA bare kuma yayi tunanin zaiyi Aure, haka Itama Indo duk abunda ake akan harkar bikin babu ruwan ta ciki, bai kuma dameta ba, saima murna da take ya Habeeb ɗinta zaiyi Aure, RAUDA kuwa tunda taji labarin za’a kawo kayan Auren ta ranar talata take rawar kai ita da mahaifiyarta.

Ranar talatar kuwa Momy ta gayyaci ƴan uwa da abokan arziki aka kai kaya gidan su RAUDA, Mamy da ƙawayen ta, da ƴan uwa sai buɗe kayan suke suna son barka, tsakanin ta da Allah Mamy take guɗa tana cewa RAUDA tayi goshi, bayan kowa ya watse daga gidan Mamy da RAUDA suka nutsu suna kallon kayan duba Mamy RAUDA tayi tace.

” Ikon Allah Mamy ko a mafarki ban taɓa zaton cewa ya Mustafa zai aure ni ba, sai gashi cikin ikon Allah wai wannan kayan aure nane nake gani gaba na wanda ya Mustafa, sai dai kullum tunani nake wani irin zaman Aure zanyi da ya Mustafa, Mamy baya soni ko kaɗan cikin rayuwar sa, nasan wannan auren nawa da zaiyi umurnin Momy kawai yabi ya kuma sanar dani cewa rayuwar kabari sai yafi min daɗi fiye da rayuwar gidan sa, ina tausayin kaina Mamy.”

Tsuka mai ƙarfi Mamy taja tana duban RAUDA tace.

” Kuma sai aka ce miki tsayawa zanyi ina kallon ana walaƙanta ki kullum ina gaya miki cewa bazan taɓa bari Mustafa ya wulaƙanta ki ba, domin kuwa saina mayar miki dashi kamar tandar waina zaki juya sa cikin son ranki, dan haka ki daina saka damuwa cikin ranki lokaci kawai nake jira nayi maganin sa.”

Duban Momy RAUDA tayi tare da cewa.

” Mamy bana son ace da asiri nake neman Soyayyar Mustafa, Mamy jiya na karanta wani Novel mai suna *Sara da sassaqa* Mamy na tsorata da soyayyar da ake neman ta da asiri, domin kuwa baya tasiri, komi jumawa asirin zai karye Mamy wannan littafin dana karanta ya ƙara min haske mu daina asirin nan Mamy mu nemi Soyayyar Mustafa da addu’a, nikam Mamy har ga Allah ko kinje wajen malami bazan yi amfani da maganin ba.”

Duka Mamy ta kawowa RAUDA tana cewa.

” Dan ubanki ance miki Abunda ake faɗa cikin Novel gaskiya ne da har zai sanyaya miki jiki duk ƙarya ne kuma dan ubanki sai naje wajen malami kuma dole kiyi amfani da shi.”

” Mamy Wlh gaskiya suke faɗa kuma wlh haka ne abun yake kasancewa ni dai Mamy wlh ba zanyi amfani dashi ba, domin kuwa ina son ya Mustafa bana son ace gaba zai rabu dani……”

________________________________

Mu haɗu next Page wlh da ƙyar na samu nayi wannan typing ɗin, ina school kuma gashi banjin daɗin jiki na.

*Vote*

*Share*

*And*

*Comment*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah ce)*

[2/25, 10:23 AM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*

*Nasmah ko Nasirah*

*Sara da Sassaka*

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.

Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*

____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

*P*•••••••5️⃣5️⃣ ➡️ 5️⃣6️⃣

Cikin masifa da bala’i Mamy ta taso tayo kan RAUDA da zagi.

” Dan ubanki! Ni kike gayawa Allah to tun kafin a haifeki na sansa, kuma shi wannan asiri da kike cewa baya tasiri, to shima ubanki dashi na gama samun kansa, meyasa nawan har yanzu bai karye ba, tashi ki bani waje dan ubanki shegiya marar zuciya wai ke ga mai soyayya, to ki biye soyayya kisha wahala har kina kira min wai wani kin karanta novel kin tsorata da harkar malamai.”

Ita dai RAUDA tashi tayi ta shige bedroom ɗinta ba tare da ta kula Mamy ba, mita mami ta dinga yi ita kaɗai tana cewa “ita kanta RAUDA ma, zata ci ubanta tunda ita ƴar Soyayya ce, shegiya mai son maso wani, kina sonshi yana tsangwamar ki, amma tsabar rashin Zuciya kice kina tausayin sa.”

_______________________________

Kallon Hasina Momy tayi tace.

” Hasina kinga kayan naki sunyi ko?”

Murmurshi HASINA tayi tace.

” MOMY ai ba sai na gani ba duk abunda kuka saka ai sunyi kyau, jiya ma Ammi ta kiran tace zasu zo next week tunda bikin saura one month.”

” Eh ta sanar dani munyi waya ai jiya, har take………

Shigowar Indo da gudu ne ya sasu maida hankalinsu gareta tana haƙi ta sun kuya gaban Momy tana kuka tana cewa.

” Momy! Inna Momy! Inna” tana maganar tana nuna ɗakin Inna cikin tashin hankali.

Tashi Momy tayi tana cewa.

“Meya samu Inna, ki faɗa min mana?”

Hasina ce tace.

” Momy muje muga menene yake faruwa” ai kuwa cikin sauri suka shiga cikin ɗakin tana kwance sau ɓari jikinta yake yi hancinta kuma sai fitar da jini yake, idanunta kuma sun ƙafe sai rawar sanyi take, cikin tashin hankali Momy ta kira Daddy tana sanar dashi, Hasina ce da tayi nisan Hankali ta kira Habeeb a waya kasancewar sa babban likita, cikin minti talatin suka shigo cikin gidan Habeeb Daddy Mustafa, a gigice sukayi Hospital da ita, take akayi emagency da ita Habeeb da doctor Ibrahim sune akan Inna, su Daddy duk suna tsaye suna jirin fitowar su, sun kusa 2 hours kafin aka fito da Inna zuwa ɗakin hutu, Habeeb duk ya haɗa gumi cikin tashin hankali, yake duban Indo domin ita yake tausayawa yanda take ta famar sharɓar kuka harda majina, Daddy ne da Momy sukayi kan Habeeb suna tambayar ya jikin Inna, jikin sa a sanyaye ya dubesu yace.

” Da sauƙi Daddy tana ɗakin hutu amma karku shiga tukunna saboda tana buƙatar hutu mun mata allurar bacci” Daddy da Mustafa ya duba yace” Daddy muje office .” Bin bayansa sukayi suma cikin sanyin jiki, Bayan sun zauna ne Habeeb ya fara magana.

” Daddy ko kasan Inna tana ɗauke da ciwon jeji kuwa, ma’ana (conser)?”

Cikin tashin hankali Mustafa yace.

” What conser fa kake faɗa anya kuwa binciken ku ya baku dai-dai kuwa?”

Shi kuwa Daddy ajiyar Zuciya ya sauƙe tare da cewa.

” Yes tana dashi amma gaskiya ya daɗe da barin jikinta tun kafin na baro ƙauyen mu?”

” Daddy bai bar jikin ta ba, saima ƙara ƙarfi da yayi a jikinta, Daddy meyasa baka kai Inna hospital ba, domin a dinga mata check up, tunda kasan tana da wannan mummunan ciwon, kuma yana da hatsarin gaske.”

Mustafa ne ya dakatar da Habeeb da cewa.

” Please Malam ka daina mana Maganar baya, kayi mana bayanin Abunda ke faruwa yanzu meye kuma solution?”

Iska Habeeb ya hura daga bakin sa yace.

” Inna tana cikin step ɗin da mawuyacin abune ta ƙara sati ɗaya a duniya domin kuwa, ya tsinka mata hanjin ta, gashi kuma ya taɓa mata huhu so Daddy babu wani solution, sai dai muta addu’a akwai kuma maganin da zamu ɗaura ta, akai amma ba wai lallai bane yayi amfani a jikin ta.”

Wasu hawaye ne masu zafi suka zubo a fuskar Mustafa tare da jingina kansa jikin kujerar yana furta.

” Innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un Allahumma ajirni fil musibati! Wacce irin ƙaddara ce ta faɗo kan Inna, yanxu Inna ce take cikin wannan tashin hankalin Habeeb yanzu babu yanda za’ayi koda ƙasar waje a fitar da ita, wlh zan iya sadaukar da dukiyata gaba ɗaya muddun za’a ceto rayuwar Inna, please Habeeb ka taimaka karmu rasa Inna.”

Duban Mustafa Habeeb yayi shima idanunsa sun ciko da hawaye yace.

” Bros banda wani solution wlh ko ƙasar waje aka fitar da Inna bazata wuce wannan lokacin ba, tabbas Ubangiji shine wanda yasan iya rayuwar mutum a duniya babu kuma wanda yasan ranar mutuwar wani, amma ciwon Inna yana nuna cewa bazata haura wannan kwanakin ba, domin kuwa hanjin ta yayi damege ga kuma huhunta ya samu matsala shima, amma zan kira doctor John naji tunda shi babban likita ne cikin ƙasar Indiya.”

” Yauwa ka kira sa, Allah yasa a dace.”

Daddy kuwa yayi shuru yama rasa me yake masa daɗi, baya kallon laifin kowa sai na mai bawa Inna maganin gargajiya a ƙauye domin kuwa yasan mahaifiyar sa tana da wannan mungun ciwon, yayi la’akari da cewa ta warke tuntuni sakamakon maganin gargajiya da take amfani dashi, hakan yasa mahaifinsa yace Inna ta warke inji mai basu maganin kuma tun daga lokacin ciwon bai ƙara tashi ba, hakance tasa suka ɗauka da gaske ta warke, ashe Inna bata warke ba, ɗaga Hanun sa Daddy yayi sama yana cewa.

” Ya Allah kaine wanda ka ɗaurawa mahaifiyata wannan ciwon ya Allah idan wannan ciwon na sauƙi ne, Allah ka yaye mata, idan kuma na tafiya ne Allah ka bata sa’ar tafiya cikin sauƙi ka kuma gafarce ta” cikin hawaye Daddy ya ƙarasa Addu’ar kafin ya dubi ƴaƴan nasa yace ” kuyi hkr kusa Inna cikin Addu’ar ku Allah ya zaɓa mata abinda yafi zama Alkairi cikin wannan ciwon rayuwa ko mutuwa, Habeeb ka tambayi likitan duk yanda kukayi ka sanar dani, sannan bana son ku sanar da mahaifiyar ku da ƙannan ku wannan maganar kunsan su mata ne, Zuciyar su bata da ƙarfi.”

Da to suka amsa kowa jikinsa yayi sanyi, haka suka fito, Habeeb hanun Indo ya kama suka zaune gefe yace.

” Wai kukan me kike haka ne, bayan jikin Inna da sauƙi har ta samu bacci.”

Cikin kukan ta dubi Habeeb tace.

” Ya Habeeb jinin meye yake fitowa daga hancin Inna, kuma sai rawar sanyi take, ya Habeeb haka Jummalo tayi rawar sanyi da zata rasu, bana son Inna ta mutu ta barni ina sonta ya Habeeb.”

” Wa yace miki Inna zata mutu, Inna bazata mutu ba, muna tare da ita zata samu sauƙi mu koma gida muyi rayuwar mu tare, ki share hawayen.”

Goge hawayen Indo tayi tana ɗan dariya Habeeb yace Inna zata warke, ɗakin da aka kwantar da Inna Habeeb ya shiga ya dubata har yanzu tana Bacci bata farka ba, fitowa yayi yace zasu iya shiga amma banda hayaniya, da gudu Indo ta shiga kafin su Momy suka shigo, gefen Inna Indo ta zauna tare da kifa kanta dai-dai fuskar Inna tana kallon ta, ta kuma riƙe hanunta, shima Mustafa gefen Inna ya zauna tare da rike ɗaya hanun nata yana tofa mata addu’a, haka suka kasance har ƙarfe biyar na yamma Kafin Inna ta farka kuma a nutse ta farka, bin kowa take da kallo tare da ƙarewa ɗakin kallo, Indo ta duba ta dubi Mustafa da Habeeb, sai hawaye ya zubo mata hanun Indo ta ƙara danƙewa tana murmurshi mai haɗe da kuka cikin ƙarfin hali tace.

” Indo kinyi kuka ko? gashi idanunki sunyi jajur, ki daina kuka zan samu Lafiya kinji.”

Girgiza kansa Habeeb yayi cikin tausayin halin da Indo zata shiga idan ta rasa Inna domin kuwa Rayuwa bazata mata daɗi ba, babu Inna.

” Inna da gaske zaki tashi bazaki mutu ki barni ba? Dan Allah Inna karki mutu kinji.”

Murmurshin ƙarfin hali Inna tayi tace.

” Mutuwa ai dole ce babu wanda zai hana kansa mutuwa idan lokacin sa yayi” Mustafa ta kalla daya sunkuyar da kansa yayi shuru cikin damuwa, dukan kafaɗar sa Inna tayi cikin wasa duk dan ta basu ƙarfin gwiwwa su daina shiga cikin damuwa tace ” kai kuma Sarkin baƙin rai me yake damunka? Kaima baka so na mutun ne, to ai mutuwa dolece akan duk wani ɗan adam, amma dai bazan mutu ba, saina ga auren ka, nasan shine damuwar ka ko?”

Wannan karon Mustafa bai ɗago kai ya kalli Inna ba, domin kuwa yasan suna haɗa ido da ita dole sai hawaye ya zubo masa cikin idanunsa, tashi yayi cikin sauri ya fice daga ɗakin, duban Habeeb Inna tayi tace “zo Habeeb kusa dani muyi magana” matsowa Habeeb yayi kusa da Inna ta dubi su Indo da Momy tace su fita zatayi Magana da Daddy da Habeeb, fita sukayi ya saura ɗakin daga Inna sai Habeeb da Daddy, duban su tayi ta fara magana.

” Amana nake son na baku, dan Allah ko bayan rayuwata karku bari Indo ta walaƙanta ku kula da ita ku riketa amana kamar yanda zaku riƙe ƴaƴan ku, idan har kuka bari Indo ta wulak’anta bayan rayuwata to nice kuka wulaƙanta idan har kuka bari hawaye na baƙin ciki ya zuba fuskar Indo to hawaye nane ya zuba, ku kula da rayuwar ta, ku bata farin ciki idan ta kauce daga hanya ku dawo da ita kan hanyar dai-dai ina ji a jiki na bazan rayu ba, naso ace na rayu har naga ƴaƴan Indo, amma Ubangiji na bai nufi hakan ba, Haruna ku dinga kai Indo ƙauye tana gaishe da iyayen ta sannan cikin Habeeb ko Mustafa ka Aurawa ɗaya a cikin su Indo karka umarni ne wannan, bana son wani ya auri Indo ba ɗaya daga cikin su ba, wannan itace amanar da zan baku idan Hindu ta zo bayan raina ku bata Indo ta tafi da ita kafin zafin mutuwata ta fita daga zuciyar ta, sai ku dawo da ita cikin gidan ka, nasan matar ka A’isha bazata kula da Indo ba shiyasa ku na baku amanar ta.”

Ga baki ɗayan su hawaye ne yake gudu saman fuskar su, murmurshi Inna tayi sai kuma ta fara tari tare da jini cikin bakin ta, gabaki ɗayan su kalmar shahada suka ɗauka, bakin su Inna tabi tana kalmar shahada har Allah yayi ikon sa, Allah sarki rai baƙon duniya yau dai ga Inna da bata son mutuwa ta tafi tabar duniyar ta koma zuwa ga mahaliccin ta, kuka Habeeb yasa mai tsuma Zuciya kafin ya durƙusa kasa yana kukan Daddy kuwa zani yaja ya rufe Inna yana Allah ka jiƙan mahaifiyata Allah ka karɓi baƙon cin ta Allah ka yafe mata, hawaye kuwa yana tsere saman fuskar sa.

( Ana son idan mutum yazo mutuwa wanda ke kusa dashi ya dinga kalmar shahada, idan har Allah ya bawa wannan mamacin Sa’a sai kuga shima ya ɗauki wannan kalmar shahada bawai kuta zunduma kuka ba kuna cewa wayyo Allah katanga ta faɗi wayyo mun shiga Uku, wannan duk basu da kyau domin kuwa kuna ƙarawa mamaci azaba ne, gara kayi hawaye ka kuma bishi da addu’a wannan shine gatan da zaka masa)

Kama hanun Habeeb Daddy yayi suka fito waje cikin firgici su kayo kansu ganin yanda Habeeb yake kuka, Mustafa yana kallon halin da Habeeb yake ciki ya tabbatar da cewa Inna ta rasu, zama kawai yayi tare da dafe kansa dake ƙoƙarin barin jikin sa.

” Momy Inna ta tafi ta barmu Inna ta mutu ta barmu da kewarta Momy babu Inna cikin wannan Duniyar………

Karar da Indo tayi shine ya hana Habeeb karasa maganar tashi, yankan jiki tayi ta faɗi, sukayi kanta da gudu, suna girgiza ta………..

*Vote*

*Share*

*And*

*Comments*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah ce)*

[2/28, 9:48 AM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*

*Nasmah ko Nasirah*

*Sara da Sassaka*

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.

Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*

____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

*P*••••••5️⃣7️⃣ ➡️ 5️⃣8️⃣

Girgiza Indo Habeeb da Hasina suke cikin tashin Habeeb yake cewa.

” Indo! Indo ki tashi dan Allah karki mutu kema wlh muna son rayuwar ki, idan kin mutu sai nafi kowa baƙin ciki cikin wannan duniyar ƙarshe ma, rayuwata ta ƙare cikin baƙin cikin rashin ki, pls Indo ki tashi dan Allah” yana maganar ne cikin zubar hawaye da ɗimauta yama manta da cewa shi doctor ne, Mustafa da tun ɗazu yake zaune ya rasa me yake yiwa rayuwar sa daɗi domin shi gani yake daɗi shine yake kawo kuka shi so yake ya samu yayi kukan ko zaiji sassauci cikin zuciyarsa amma kukan yaƙi zuwa yasan duk yanda Habeeb suka shaƙu da Inna bai kai yanda shi suka shaƙu ba, shida ko wani weekend cikin Dasina wajen Inna kafin ta dawo birni da zama ko daddy bazai kaisa jin wannan mutuwar ba, cikin ƙarfin hali ya taso yazo har gaban Indo ya sunkuya tare da kai kansa ƙirjin Indo, cikin zaro ido ya ƙara maida kunnen sa sosai, still dai Indo bata motsi, doctor ya fara kwalawa kira cikin sauri yana cewa.

” Doctor! Doctor! Doctor”

Da sauri doctor Ibrahim da doctor Jamil suka nufo su cikin sauri, kan Indo suka sunkuya tare da ƙwalawa nurse kira, emagency aka shigar da Indo, su Habeeb tsayawa sukayi cirko-cirko, cikin tsoron abunda zaije ya dawo, Momy kuwa ita ko a jikin ta, domin ji take dama Indo ce ta mutu tabar Inna, Zama tayi tare da haɗa tagumi tana jinjina mutuwar Inna, doctors duk yanda sukayi ganin Indo ta farfaɗo amma ina abu yaci tura allurai suka mata tare da sa mata drip sannan suka fito da ita zuwa cikin ɗakin hutu, doctor Ibrahim fitowa yayi yana sharce gumi tare da kallon su Daddy yace su biyosa office, bayan sun shiga ne dukansu har Mustafa, doctor Ibrahim ya dubesu tare da cewa.

” A gaskiya yarinyar nan bata farfaɗo ba duk Abunda muka san zamu iya munyi amma bata dawo cikin hayyacinta ba, da alamu dogon suma tayi sakamokon firgici da ta samu, so munyi mata allura tare da sa mata drip, zamu jira muga nan da 24 hours ko zata farfaɗo, sannan kuma bawai farfaɗowar tata bane abun damuwa yanda zata farfaɗo ɗin, idan har ta sake farfaɗowa a firgice, za ta iya samun heart atack, Abunda kuma bama son ya kasance, so gaskiya tana buƙatar Addu’ar mu gabaki ɗaya.”

Innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un! Kawai Habeeb yake furtawa tare da wasu hawaye masu zafin gaske, yana cewa.

” shike nan na shiga uku zamu rasa ta itama, doctor Ibrahim ka taimake ni kar Indo ta samu heart atack pls ina cikin ɗimuwa bazan iya taimakon Indo ba domin bazan iya aikata komai ba.”

Tsaki Mustafa yaja tare da tashi ya nufi frig ɗin dake cikin office ɗin robar swan water ya ɗauko tare da cup ya tsiyayi ruwan, duka binsa da kallo sukayi, Daddy ne yayi ƙarfin halin cewa.

” Muhammadu me zakayi da ruwa ana magana kayi shuru?”

Dam! Gaban Mustafa ya faɗi jin Daddy ya kirasa da sunan da Inna ke kiran sa, duk da haka bai kula Daddy ba, saima addu’a daya fara jerawa cikin ruwan (fatiha yayi ƙafa 11 nasi 3 falaq 3 ayatul kursiyo 3 amanarrasulu 3) ya fice daga office ɗin riƙe da cup ɗin a hanun sa, ga baki ɗayan su tashi sukayi suka bi bayan sa, su Momy ma dake waje ganin shigewar Mustafa ɗakin da aka kwantar da Indo ga kuma su Daddy sun bisa ya sasu binsu suma Mustafa durƙusawa yayi a gaban Indo tare da zuba ruwan a hanun sa, ya shafa mata a fuskar ta da hanun ta zuwa ƙafafuwan ta, sannan a hankali ya buɗe bakinta yanda ruwan zai shige mata ya dinga zuba mata a hankali kafin ya ajiye cup ɗin ya fice daga cikin ɗakin yayi na Inna nan ma binsa sukayi, gaban Inna ya durƙusa ya yaye mayafin da aka rufeta dashi ya fara cewa.

” Nasan kina jina Inna mayar min da amsa ne kawai bazaki iya ba, tabbas idan nace banji baƙin cikin rabuwa dake ba, nayi ƙarya, Inna ke kakace wacce ko wani jika zaiyi alfahari dake, nasan ɗazu kinso kiji murya ta, sai dai kash na kasa mayar miki da martani sakamokon kuka dake niyar ƙwace min, zanta miki addu’a Inna daga nan har nawa ƙarshen numfashin Allah ya karɓi bakwancin ki Inna, Allah yasa mutuwa ta kasance hutu a gareki Allah ya baki ikon amsa tambayoyin ki cikin sauƙi ya yaye miki duhun kabarin ki, ya haskaka miki shi ya kuma faɗaɗa miki shi” sai yanzu kukan ya ƙwacewa Mustafa, ya zauna daɓas tare da dafe kansa yana kuka mai tsuma Zuciya, zama kusa dashi Habeeb yayi suka haɗa kai sai kuka suke kamar ba maza ba, Daddy ne ya dubesu tare da cewa.

” Me kuke yi haka Muhammadu yanzu ka gama nema mata rahama wajen Ubangijin ta shine kuma yanzu zaka zauna ka mata kuka, ko kun manta ba cewa kuka azaba ne ga mamaci karku manta yanzu Inna Addu’ar mu take buƙata ba kuka ba, shine kawai gatan da zamu mata ku tashi muje gida da Inna domin muyi gaggawan kaita makwancin ta, Hasina keda sharifa ku tsaya wajen Indo.”

Daina kukan sukayi har Momy da su Hasina, sannan su Sharifa suka koma ɗakin da Indo take suna goge hawayen fuskar su.

Haka suka koma da gawar Inna gida Daddy da kansa ya kira malam musa mahaifin Indo ya sanar dasu rasuwar Inna, Mlm Musa yaji wannan mutuwar sosai, ko mama da taji kuka tayi sosai Kamar itama ranta zai fita, domin kuwa uwa ta ɗauki Inna wacce tayi naƙuda ta haifeta, gabaki ɗaya garin Dasina ya ɗauka da rasuwar Inna, Mlm Musa hkr ya bawa Daddy akan cewa kar akai Inna a jirasu suna zuwa yanzu, dattawan garin Dasina gabaki ɗaya sun taho har maigari Mama da Goggo Hali sai Inna Saude da Lami ƙawar Indo tace itama sai taje ta yiwa indo ta’aziya, cikin 1hours suka iso cikin birni, Mama da Goggo Hali da kuma Inna Saude sune sukayi Inna wanka tare da mata sutura, Allah sarki rai baƙon duniya, haka aka kai Inna makwancin ta ba tare da Indo taga gawar Inna ba, Habeeb da Mustafa sosai suka yiwa Inna Addu’a bisa kabarin ta, ƙofar gidan alhaji Haruna cike yake da mutane ƴan karɓar gaisuwa, cikin gida kuwa Mama ce ta dubi Momy tace.

” Hajiya a’isha banga Indo ba tunda nazo ni?”

Cikin halin ko inkula da halin da Indo take ciki Momy tace.

” Tana asibiti tunda Inna ta rasu ta yanki jiki ta faɗi tana can har yanzu bata farfaɗo ba.”

” Innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un! Allah sarki Indo sabo turken wawa, dole ki faɗi Indo koni uwarki dana haifeki ban miki gata da ƙaunar da Inna take miki ba, Allah ya baki lfy ya baki ikon hkr da rashin Inna.”

Taɓe baki Momy tayi tace

” Ameeen.” Daga nan bata ƙara cewa Mama komai ba, itama Mama bata ƙara cewa komai ba.

Shigowar Mamy da RAUDA sai Hindatu ƙawar Mamy shine yasa Momy maida hankalin ta, kansu tana dariya kamar ba mutuwa akayi ba, tana cewa.

” Sannun ku da zuwa Hajiya Turai kune tafe yanzu, maraba ku iso ku zauna.”

Zama sukayi Mamy tana yiwa su mama wani irin kallon ƙyama, kusa da Momy ta zauna suka gaisa tare da yiwa juna ta’aziya, basu gaishe da Mama ba, sai RAUDA kawai ta gaishe ta, cikin mutunci kuwa Mama ta amsa sannan ta tashi tabar musu wajen tayi wajen su Goggo hali, ta samu Lami tasa Inna Saude a gaba cewa lallai sai an kaita wajen Indo, Mama ce tace tayi hkr sai Daddy ya shigo zata masa magana ya kaisu wajen Indon.

Hajiya Turai duban Momy tayi tace.

” Hajiya A’isha ashe kuma kin rabu da damuwa, tsohuwa ta ƙara gaba.”

Dariya Momy tayi tace.

” Ke dai bari kawai daman itace ta takura ni cikin gidan nan, kuma yanzu ta bani iska, duk da naji zafin mutuwar ta, amma dai gaskiya nafi jin daɗin bani iska da tayi, yanzu ne zansan yanda zanyi na kora wannan shegiyar yarinyar ƙauye, kinsan tana can asibiti ta yanki jiki ta faɗi har yanzu bata farfaɗo ba, ni dama shigewa tayi tacan kowa ya huta.”

Dariya sosai Mamy take harda shewa tace.

” Ba dole ta faɗi ba taga asirin ta zai tonu, za’a koma ƙauye wacce ta shigo da ita birnin ta wula, Allah dai ya kyauta amma dai karki barta ta ƙara wani zamani cikin gidan nan.”

Takaici da haushin iyayen nata shine yasa RAUDA tashi ta fice tabar musu wajen Ishaq ta kamo tace yaje ya mata magana da ya Mustafa ta masa ta’aziya, da gudu kuwa Ishaq ya fita, gun Habeeb yaje yana cewa ya Habeeb ina ya Mustafa, sai yanzu Habeeb ya lura cewa Mustafa baya wajen, dudduba Wajen yayi yaga babu Mustafa har wajen su Daddy yaje baya nan, cewa ba Ishaq yayi yaje yace Mustafa yana zuwa, zama yayi yana mamakin ina Mustafa ya shige.

Mustafa kuwa asibiti ya koma, domin kuwa haka kawai ya tsinci kansa da son sanin halin da Indo take ciki, su Hasina suna zaune sunyi tagumi babu mai cewa ɗan uwansa komai, Mustafa ya shigo, zama yayi gefen gadon yana ƙarewa Indo kallo, kafin ya fara tofa mata addu’a, yana cikin tofa mata Addu’ar ne Sharifa taga hanun Indo ya fara motsi, da sauri ta karasa tana cewa

” ya Mustafa hanunta yana motsi.”

Duban hanun nata yayi ya cigaba da addu’a yana roƙa mata sauƙi wajen Ubangijin ta, (ƴan uwana mu kasance masu yawan addu’a ga mu kanmu da ƴan uwan mu, domin kuwa shi alƙur’ani waraka ce ga dukkan ciwo da damuwa) a hankali Indo take buɗe idanunta harta buɗe su duka amma idanunta na zubar da ruwan hawaye tana kiran sunan Inna, riƙo hanunta Mustafa yayi yace.

” Ki daina kukan haka ki yiwa Inna Addu’a kinji.”

Fisge hanunta Indo tayi tana cewa.

” Na daina kuka fa kace! Ta yaya zan daina kuka bayan na rabu da gatana uwata wacce take sona a kowanne Hali, wacce ta ɗauki damuwata nata haka ma farin ciki na, ta maidashi nasa, take min duk abunda nake so koda kuwa ranta baya sonsa, tana take laifi na, ta mayar dashi ba laifi ba, take bani duk wani Abunda nake so muddun kuwa tana dashi, ka faɗa min! Taya zan daina kuka! Ta ƙarasa maganar tana sakin wani irin kuka mai taɓa ZUCIYA tana dafe ƙirjin ta, ta cigaba da cewa “zuciyata zafi take min ji nake kamar zata bar jikina, ina ma ni mutuwa ta ɗauka tabar Inna, Ina kin tafi kin barni cikin ƙunci da damuwa banda wani farin ciki a yanzu, ku tashi ku kaini naje muyi bankwana da Inna nayiwa gawarta kallon karshe, duk da har abada hoton fuskar ki bazai taɓa goguwa cikin idanuna ba.”

Allah sarki Indo ta bawa kowa tausayi a wajen babu wanda yace mata an binne Inna gudun faruwar wani abun, da kanshi Mustafa yaje ya karbo sallama wajen doctor, suka tafi gida, tunda suka shigo cikin gidan Indo bin kowa take da kallo ba tare da tayi Magana ba ɗakin Inna ta wuce su Mama ta samu zaune, da gudu Lami ta faɗa jikin Indo ta saki kuka tana Cewa.

” INDO Innan mu ta mutu ta barmu, Inna tana sonmu tana karɓa mana faɗa ta bamu kuɗi, idan mukayi fushi ta rarrashe mu, yanzu kuma ta tafi ta barmu.”

Hawayen ta Indo ta share tana ɗaga jikinta daga na Lami tace.

” Zo muje ki rakani na yiwa Inna bankwana ina son na ganta kafin su binne ta, na mata Addu’a.”

Tashi Mama tayi ta kamo hanun Indo ta Ajiye ta, ta fara mata magana cikin rarrashi.

” Indo kiyi hkr ki daina wannan kukan haka, Inna ta rasu bazamu iya dawo da ita ba, gatan da za ki yiwa shine addu’a, kuka ba naki bane da kiyi kuka da kar kiyi Inna dai ba dawowa zatayi ba, yanzu ki Zauna kiyi mata addu’a, an kai gawarta makwancin ta tun ɗazu……”

INDO bata jira Mama ta gama magana ba ta fita da gudu ko takalmi babu ƙafarta, fitowa Mama tayi da Inna Saude suka bi bayan ta, su Momy ma tashi sukayi suna binsu da kallo, Indo kuwa babu Inda ta tsaya sai wajen Daddy, faɗawa tayi jikin Daddy ta saki kuka mai tsuma Zuciya tana cewa.

” Daddy meyasa kuka binne Inna ta, ba tare da kun jira na ganta ba, meyasa Daddy” ta ƙarasa maganar tana sharce majina idanunta kuwa sun kunbura suntum daƙyar take iya buɗesu, cikin tausayin halin da take ciki Daddy ya mata magana cikin muryar rarrashi.

READ:   Mahaukaci - Complete Hausa Novel

” Kiyi hkr dole yasa muka kai Indo ba tare da mun tsaya kinga gawarta ba, nasan wannan mutuwar kece a kayiwa amma kiyi hkr ki sawa Zuciyar ki dangana, ki ta yiwa Inna addu’a shine gatanta gareki.”

” Daddy bazan iya hkrn rashin Inna ba, meyasa kowa yake bani hkr babu wanda ya bawa ita mutuwar hkr sanda tazo ɗauke min Inna, Daddy nima bazan yi hkr ba, kawai ku dawo min da Inna na.”

Cikin hasala Baba dake zaune gefe yace.

” Kar Allah yasa ki hkr dan gidan ku, iskancin banza kawai, ana rarrashin ki kina yiwa mutane iya shege, tashi kibar wajen nan tunda bazaki iya hkr ba shashashar banza, kedai har abada bazaki taɓa Hankali ba” Baba ya ƙarasa maganar cikin faɗa.

Habeeb wani irin zafi yaji cikin Zuciyar sa, yanda Baba ke yiwa Indo faɗa baiga damuwar da take ciki ba, tashi Mustafa yayi yaje ya kamo hanun Indo ba tare daya kula kowa ba, yayi cikin gida da ita, juyawa suma su mama sukayi, Daddy ne ya dubi Baba yace.

” Mlm Musa bai kamata kana yiwa yarinyar nan faɗa ba, kasan yanda suka saba da Inna dole ne ta shiga cikin ɗimuwa, rarrashin ta, ya kamata ayi bawai a mata faɗa, har mu samu ta dawo dai-dai.”

” Haka ne Alhaji Haruna kasan wani lokacin Indo tana da ban haushi, amm nikan ya banga Hindu ta iso ba har yanzu?”

” Ɗazo na sanar da mijin nata kamal amma nace karya sanar da ita sai sunzo saboda gudun damuwa kasan tana da Hawan jini, zuwan su zai kai gobe kasan sai sunyi visa.”

” Allah ya kaimu” Baba ya furta yana tagumi, Alhaji Ahmed mahaifin RAUDA dake gefe ya dubi Daddy yace.

” Gashi kuwa mummunan Hawan jini ne da ita, Allah dai ya bata dangana.”

” Ameeen” Daddy ya furta.

Ɗakin su Mustafa ya wurga Indo cikin hasala shima ya hau mata sababi.

” Wani irin Zuciya ce dake da bata hkr, ƴaƴan da ta haifa ma sunyi hkr da rashin ta bare kuma ke, ana rarrashin ki kina ƙi, to idan ba zakiyi hkrn ba, ya zakiyi zaki dawo mata da rai ne ko kiyi hkr ko kar kiyi Inna dai ta mutu kuma babu mai dawo da ita sai dai tarihi, idan kinga dama kita kuka daga nan har taki mutuwar tazo ta sameki” yana gama faɗin haka ya fice a fusace, kuka Indo tasa tana cewa.

” Shike nan na shiga Uku Inna kin mutu kin barni gashi har an fara zagina, dan Allah Inna ki dawo” birgima take tana kukan, Sharifa ce ta sunkuya kanta tana cigaba da rarrashin ta, daƙyar suka samu Indo tayi shiru sai kuma ajiyar Zuciya da take.

Sai da magaruba su Mamy suka yiwa Momy sallama suka tafi, Daddy kuwa sun jima a waje har 10:30pm suka shigo, tare suka kwana da Baba ɗaki ɗaya, daman saura kam tunda aka dawo daga maƙabarta suka juya Dasina.

Su Mama ɗakin Inna suka kwana, Indo kuwa tana bayan Sharifa a maƙale dan ko cikin dare ance bacci ɓarawo ne, amma dai ranar ita Indo bai sace ta ba, haka ta kwana tana tunanin Inna wani tayi kuka wani kuma tayi ajiyar Zuciya mussaman idan ta tuno rayuwar su ta ƙauye haka ta kwana cikin tunani.

Washegari misalin ƙarfe 1 na rana jirgin su Aunty Hindu ya sauƙa, Idi drever shine yaje da Mustafa suka ɗauko ta, tun a hanya Aunty Hindu taga face ɗin Mustafa babu walwala ba kamar yanda ta sansa ba, tun ƙofar gidan da Aunty Hindu ta hango a cike da mutane ta fara tambayar Mustafa me yake faruwa, Mustafa baice mata Inna ce ta rasu ba, saima cemata da yayi babu komai, get aka wangale musu suka shiga cikin gidan, cikin sauri Aunty Hindu tayi cikin gidan, domin ita dai bata yadda ba, duk da taga yayan nata a waje amma hankalin ta bai kwanta ba, dam gaban Aunty Hindu ya buga ganin Mama meron Dasina zaune cikin falon ga kuma su Inna Saude, dube-dube ta fara bata hango Inna cikin falon ba, a fili ta furta.

” Allah yasa ba Inna bace ta Rasu.”

Daga bayan ta Daddy yace “Zauna Hindu”

Zama Aunty Hindu tayi tana dube-dube, Kafin Daddy ya dubeta yace.

” Hindatu kinsan dai Allah shine yake bayarwa ko?” ɗagawa Daddy kai tayi alamar ehh.

” To alhamdulillah! Sai nake ga ai wanda ya maka kyauta ya karɓi abunsa ya fika sonsa ne, bai kamata miji haushi ba ko ranmu ya ɓaci, Hindatu ki ɗauki ƙaddara na rashin Inna da mukayi mu cigaba da aika mata addu’a zuwa makwancin ta, ina ga wannan shine dai-dai.”

Dafe kanta Aunty Hindu tayi idanunta na zubar da hawaye take furta innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un!

Tafi minti goma a haka kafin tace……………..

________________________________

Masu min tambaya da bincike akan cewa meyasa na kashe Inna, zan baku amsar ku yanzu, akwai waɗanda suka biyoni ta private da yawa wasu suce min bai kamata na kashe Inna ba, wasu kuma suce min meyasa na kasheta, to ina son kusan wani Abu👇🏻

Ita mutuwa babu ruwan ta da baka da kowa koda kuwa wannan mutumin shine kaɗai gatan ka indai tazo Sai ta ɗauke sa, koda kuwa mutumin shine kaɗai gatan ka a duniya, zata ɗauke sa, kuma haka Allah bazai bar bawansa ya wulaƙanta ba, dan ya rasa wannan gatan nasa ita mutuwa dole ce,dan haka maganar bai kamata Inna ta mutu ba bai taso ba, karku manta da mutuwa tana ɗauke uwa da Uba lokaci ɗaya ta rabasu da ƴaƴansu babu ruwan ta da wannan ƙaunar da take tsakanin su kuma su rayu.

kudai ku cigaba da biyoni cikin labarin domin jin yanda rayuwar Indo zata kasance bayan Inna.

Ina Alfahari daku masoyana a koda yaushe😘

*Vote*

*Share*

*And*

*Comments*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah ce)*[3/2, 3:29 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*

*Nasmah ko Nasirah*

*Sara da Sassaka*

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.

Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*WLH DA NIYATA NA DAINA RUBUTA WANNAN BOOK ƊIN, DOMIN KUWA AN ƁATA MIN RAINA FIYE DA TUNANIN KU, IDAN HAR KA TAMBAYI MUTUM BOOK TA PRIVET SAI KIYI HKR, KI JIRA WATAƘIL BATA ONLINE WATA ƘIL KUMA MESSAGE NE SUKA MATA YAWA SHIYASA BATA MAYAR MIKI AMSA BA, AMMA TSABAR RAININ HANKALI ZAKI WANI CEMIN WAI INA DA GIRMAN KAI, IDAN MA NA KUƊI NE NA FAƊA MATA ITA ZATA IYA BIYA KO NAWA NE, TUNDA TAGA YANZU WRITER’S KUƊI MUKA SAKA A RANMU MUN MAIDA SOCIAL MEDIA KASUWANCI, SAI KI FAƊA MIN WAYE BAYA SON KUƊI KO KUMA A INANE BA’A NEMAN KUƊI, DA KIKE WANNAN MAGANAR WACE WRITER’S KIKA TAƁA SAWA DATA, KOKO TUN FARKON BOOK ƊINA KINJI NACE NA KUƊI NE, BABU KOMAI KANKI KIKA YIWA KIJE GABA ZAKI HAƊU DA DAI-DAI KE NA BARKI DA ALLAH*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

*P*•••••••5️⃣9️⃣ ➡️ 6️⃣0️⃣

“Naji zafin mutuwar Inna sai dai kuma nafi jin Zafin rashin ganawar da ba muyi ba da ita har ta koma ga mahaliccin ta, shekara 6 rabona da nasa mahaifiyata cikin idanuna, hakan ne idan na tuno nake jin zafi cikin zuciyata, nasan mutuwa rigar kowa ce, jiranta yake sai dai naso ace nasa Inna cikin idanuna koda sau ɗaya ne, Allah ya jiƙanki da rahama Inna yasa can yafi miki nan” ta ƙarasa maganar tana goge hawayen cikin idanunta, Aunty Hindu ta bawa kowa mamaki domin kuwa tafi kowa ɗaukar ƙaddara, da dauriya.

Wunin Ranar Aunty Hindu tare suka yisa dasu Mama Momy kam dama bata cika shiga cikin su ba, Indo kuwa ɗaki ta wuni cikin tunani, lokaci ɗaya tayi wani irin faɗawa idanunta su faɗa suma, hawaye kuwa har yanzu yaƙi barin idanunta ba.

Yau Litinin akayi sadakar bakwai ɗin Inna, kowa yayi haƙuri ya dangana ya barwa Ubangijin sa lamarin sa, haka Indo itama ta haƙura amma har yanzu taƙi sakewa jikin a sanyaye yake, su Mama sai haɗa kayan su suke zasu koma ƙauye gobe, Indo ce ta shigo cikin ɗakin tana ƙarewa kayan Inna kallo, wani zanin Inna ta hango, sai ta tuno, randa Ilu ya biyota da gudu ta faɗa gidan Inna, itama Inna ta bi bayan ta da gudu tana sababi har Indo take cewa ( lafiya Indo kike gudu kodai yauma macijin ya sake biyoki.

yanzu ke Inna idan macijin ne sai na tsaya har ki iso ban rufe ƙofa ba, ai wlh kafin ki ƙaraso na juma da rufe ƙofar nan sai dai kuma kisan tayi.

Amsa Inna ta mayar mata da cewa.

“Amma dai ke Indo akwai ja’irar yarinyar yanzu dan baki da mutunci sai ki rufe ƙofar ki barni a waje wato idan ma kasheni macijin zaiyi ke baki damu ba, *to bari muga idan na mutu ina zaki dinga samun taliyar turawa kina ci, naga kuma wanda zai dinga karɓa miki faɗa tunda gani nane baƙya ƙaunar yi ina numfashi a duniya*)

Wasu hawaye ne masu zafi suka zubowa Indo ta goge a fili tace.

” Allah sarki Inna, kin tafi kin barni a lokacin da nafi kowa buƙatar ki, baki mutu ba, sai dai kika kawo ni inda zan samu taliyar turawa, sai dai bana buƙatar sa, ke nafi buƙata a yanzu Inna.”

Girgiza kanta Mama tayi ta ajiye kayan da take ninkewa ta dawo kusa da Indo ta zauna tana duban tace.

” Yanzu ke Indo ba zakiyi Hkr ba, ki cire damuwa cikin ranki Indo so kike ki sawa kanki cuta, meyasa bazaki ɗauki ƙaddara ba? duk sanda Inna ta faɗo miki cikin ranki ki mata addu’a.”

Goge hawayen Indo tayi tace.

” Mama na ɗauki ƙaddara, so nake ki koma dani ƙauye Mama bazan iya zama cikin gidan nan babu Inna ba, hankali na tashi zai dinga yi, Mama nafi son zaman a yanzu fiye da zaman cikin gidan nan domin kuwa wahala zan dinga sha tunda babu Inna kusa dani, dan Allah Mama ki koma dani ƙauye.”

Cikin tausayin Indo Mama tace.

” Nima haka naso cikin raina nafi so na koma tare dake domin kuwa na fiskanci cewa Hajiya bata sonki cikin gidan ta, ko daga yanayin yanda take kallon hakan ya nuna min cikin idanunta bata miki kallon soyayya, sai dai bani da ikon da zan saki a gaba mu tafi domin kuwa mahaifin ki shine mai wannan ikon nasan kuma shima bazai yi haka ba, ko dama can da zaki dawo birni ba da Inna zaki dawo akan ke kaɗaice zaki dawo, Inna tace ita lallai ƙafarki ƙafarta, to kinga ai idan muka ce zamu koma dake Alhaji Haruna bazai ji daɗi ba, tunda shine wanda ya ɗauko ki, ke dai ki cigaba da Hkr duk abunda zaki gani ko kiji wanda bai miki daɗi ba cikin gidan nan kiyi hkr dashi komai mai wucewa ne, ki cigaba da yiwa Hajiya A’isha biyayya har Allah ya rabaku, domin ke macece ba mai dauwama a cikin gidan bane.”

Sosai Mama take yiwa Indo nasiha har ta samu ta saki jikin ta, sukayi hira, da yamma lis Indo suna Zaune ita da Hasina da Aunty Hindu, tana yiwa Indo tsifar kanta a cewar ta, kitson Indo ya tsufa, sosai Aunty Hindu take son Indo, hira suke gwanin ban sha’awa, suka jiyo sautin motar gidan gwamnati, koda Indo taji tasan motar gidan su zahra ne, cewa Aunty Hindu Indo tayi.

” Ummi bari naje compaunt naji kamar Muryar su Zarah ne bari naje na duba.”

Sake mata kai Aunty Hindu tayi tana dariya tace adawo lafiya, Hasina ce tace.

” Ai kuwa ɗazun nan nake zancen ta cikin raina nace Zarah dai shuru ko ta’aziya bata zo mana ashe suna hanya.”

Murmurshi Indo tayi tace.

” Basa nan ai sunje sunyi tafiya Kano jiya suka dawo Aunty Sharifa ai ta kira min ita munyi waya.”

Tana gama faɗin haka Indo ta fice zuwa compaunt ɗin, aikuwa zarahn ce, da gudu Indo taje ta rungume Zarah tana cewa.

” Ƙawata kece tafe sannu da zuwa, yaushe kuka dawo?”

Dariya Zarah tayi tace mune tafe dai baki ga momma bane”

Sam Indo bata kula da momma ba sai yanzu tana dariya ta ƙarasa wajen momma tana cewa.

” Momma ai ban ganki ba, sai yanzu sannu da zuwa.”

Dariya ita ma momma tayi tace.

” Ina kuwa zaki ganni hankalin ki ya tafi wajen ƙawarki, ina su Ishaq?”

Tana murmurshi Indo tace.

” Suna ciki momma mu ƙarasa, gashi kuwa Mamana tazo Allah yayi zaku gana”

Tare suka ƙarasa cikin falon, sosai momma tayiwa Momy ta’aziyar Inna, sai dai bata samu Daddy ba, ya fita Indo Mama taje ta kira suka gaisa da momma, sun ɗan juma Zarah taso su sami ishashshen lokaci da Indo sai dai babu halin hakan gashi sunyi hutun makaranta bare tace zasu haɗu a can, sallama momma ta musu tare da sawa aka sauƙe musu kayan abinci mota guda, kuɗi momma ta bawa Mama dubu ɗari tace babu yawa tayi Hkr sosai mama tayi godiya har compaunt Indo ta raka su, Mustafa da yayi parking ne yake karewa motocin dake cikin gidan kallo cikin mamakin wasu baƙi ne suka zo gidan, daga nesa Mustafa ya hango kamar Hajiya Zubaida, ƙara buɗe idanunsa Mustafa yayi sosai tabbas dai Hajiya Zubaida ce, to me kuma ya kawo ta cikin gidan mu, haɗa fuska Mustafa yayi dan karma ta kulasa, itama dai momma gani take kamar Barrister Mustafa, sanda suka zo daf da juna kafin momma ta gane cewa Mustafa ne, ganin da gaske Mustafa zai shige bai mata magana ba, yasa momma tare sa tana cewa.

” BARRISTER yau kuma ni zaka gani ka wuce ba tare daka kulani ba?”

Cikin haɗa fuska Mustafa yace.

” Barrister Zubaida, daman akwai dokar da tace idan na ganki dole sai na miki magana, ko kin manta da cewa na tsani mata irinki mai take mutuncin mace ƴar uwata, wacce sam bata kishin jinsin ta, oh ashe daman kina da ƴarinya mace kike wannan rashin imanin”

Duban Mustafa momma tayi cikin jin Zafin maganganun sa, tayi murmurshin dole tace.

” Ya kamata kake manta Abunda ya faru a baya tunda dai gashi har kayi nasara a kanmu so meye na fushi mune waɗanda ya kamata ace munyi fushi dakai da kayi Nasara a kanmu, duk da wancan lokacin kaƙi karɓar aikina yanzu ma ina da aiki a karo na biyu, wanda zan baka maƙudan kuɗaɗe, muddun zaka karɓi Case ɗin.”

Murmurshi Mustafa yayi kafin yace.

” Baki da wata dukiya wacce zata ruɗeni a wajen ki, wacce har ki iya siyata dan haka kibi wani sarkin ba niba.”

Yana gama faɗin haka ya juya yayi cikin gida.

Habeeb daya naɗe hanu yana tsaye yana jin duk abunda suke tattaunawa, Habeeb sam baiji daɗin Abunda Mustafa yayiwa Barrister Zubaida ba, domin kuwa shi yasan komai da ya faru tsakanin su da Mustafa, ƙarasawa Habeeb yayi wajen nasu yanda yaga ita Zarah ta hasala ranta ya ɓaci ganin yanda Mustafa yake gayawa mahaifiyar ta Magana duk sanda suka haɗu, wannan ba shine karo na farko ba, hakan ne yasa zarah tsanar Mustafa duk da momma ta sanar da ita Abunda ya faru, itama Indo kallo take binsu dashi cikin sarƙaƙiya tare da jin haushin Mustafa.

” Sorry Barrister Zubaida, kin san halin mutumin naki so karki wani damu da Halin sa, kallon Zarah yayi yace kiyi hkr kema karkiji haushin sa, haka shi yake bai cika yafiya ba.”

Murmurshi momma tayi tace.

” Karka damu Habeeb” tana faɗin haka ta shige cikin mota cikin zafin rai, itama Zarah shiga tayi tana cewa Indo.

” Ni da gidan ku har abada Indo bazan ƙara tako inda aka ciwa mahaifiyata mutunci ba”

Cikin rau-rau da ido Indo tace.

” Please Zahra ni me na Miki ba laifi na ba kice bazaki ƙara zuwa gidan nan ba, nima ai ba gidan mu bane”

Zarah dai bata cewa Indo komai ba suka ja motar su suka tafi, Indo wani irin murɗan baƙin ciki taji har wani ɗaci take ji cikin ranta Abunda Mustafa ya Aikata mata, ya wulaƙanta mata baƙi waɗanda suke darajata da mutunta ta, waɗanda suka ɗauke ta ɗaya da ƴarsu ta cikin su, juyawa tayi cikin gidan a hasale har bata ganin gabanta zabar ɓacin rai, a falo kuwa ta same su, tsayawa tayi kan Mustafa cikin faɗa da ɗaga murya tace.

” Wani irin mutum ne kai wanda sam baka da kawaici cikin rayuwar ka, meye wannan baiwar Allah ta maka kake wulaƙanta ta a gaban ƴarta, yanda kaci mutumcin wannan matar kaima Allah ya kawo wanda zai tozarta ka cikin al’um………..”

Bata ƙarasa ba taji wani kyakkyawan mari saman fuskar ta, danƙo gashin ta Mustafa yayi yana cewa.

” Ni sa’an kine dan ubanki koko ni sa’an wasan kine banza daƙiƙiya ƴar ƙauye, jaka har zaki tsaya a kaina kina son gaya min Magana, ita Barrister Zubaida ƙanwar uwarki ce ko ta ubanki, da har zaki tsaya a kaina kina neman zagi na, naga alamar har yanzu baki san ni waye bane” ya ƙarasa maganar yana gwara Indo da gini, tare da murɗe mata hanu, hanun sa yasa still ya daki bakin Indo da ƙarfi sai kuwa ga jini, wani irin ƙara Indo tasa tare da fara zagin Mustafa.

” Allah ya isa tsakani na dakai baƙin mungu wlh yau ko kasheni zakayi cikin gidan nan saina faɗa maka cewa Allah ya haɗaka kaima da wanda zai wulaƙanta ka cikin al’umma, ka kasheni na faɗa!” Ta karasa maganar cikin ƙara wanda yasa Mama da Aunty Hindu dake ɗaki fitowa da gudu, ran Mustafa Idan yayi dubu to ya ɓaci kan Indo ya nufo gadan-gadan da niyar ya ɓallata kowa ya huta, cikin Zafin nama Habeeb yasha gaban sa, yana cewa.

” Haba Bros Haba dan Allah yanzu kai saika biyewa Indo Idan ita bata da hankali ai kai kana dashi, bana son kana biyewa Indo karka manta da cewa yarinya ce ƙarama wacce kayi ƙanwa da ita wajen ta uku ko biyu.”

Harara Mustafa ya sauƙewa Habeeb yana cewa, kauce daga gabana ka bani hanya naje naci uban wannan yarinyar ko zan huce, daga bayan su sukaji Muryar Aunty Hindu tana cewa kauce ka basa hanya ya kashe ta ma ƙarshe kenan tunda shi baida mutunci, duban Momy tayi tace yanzu ke A’isha kina Zaune kina gani ɗanki zai kashe ƴar mutane kin kasa yin magana”.

Mama kuwa batayi magana ba domin tasan halin Indo ba daɗi take dashi ba, bare kuma dama can inuwar su bata zuwa ɗaya da Mustafa.

*Vote*

*Share*

*And*

*Comment*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah ce)*

[3/3, 1:21 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*

*Nasmah ko Nasirah*

*Sara da Sassaka*

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.

Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*Babu komai fa masoyana karku damu komai ya wuce, yanzu ma na fara muku typing ɗin Indo karkiji komai ana mungun tare*😄❤

*بسم الله الرحمن الرحيم*

____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

*P*••••••6️⃣1️⃣ ➡️ 6️⃣2️⃣

Cikin ƙaraji Indo ta ce ni yama kasheni na huta, tun da nake a rayuwata ban taɓa cin karo da mutumin daya tsaneni ba Irin ka, ka kasheni sai ka huta, *NA TSANEKA! NA TSANEKA*” Ta ƙarasa maganar tana kuka mai tsuma Zuciya, tare da haurawa sama da gudu.

Duban Mustafa Aunty Hindu tayi tace.

” Ka kyauta, daɗin me kaji daka daki baiwar Allah, ba laifin ka bane laifin mahaifiyar kace da ta zuba maka Ido kake jibgar yarinya, kuma indai mugunta kasa a gaba, kaje kayi idan da akwai riba” itama tana gama faɗin haka ta juya, Momy kuwa ko a jikinta bata tankawa Aunty Hindu ba, ta cigaba da kallon ta, Shima Habeeb haurawa yayi sama, ƙwafa Mustafa yayi tare da zama yana cije lips ɗinsa, Habeeb kuwa ɗakin su Indo ya tura, tana kwance ruf da ciki tana cin uban kuka bakinta kuwa ya kumbura suntun, sai kuka take, sunan ta Habeeb ya kira, shuru tayi da kukan ba tare da ta amsa ba, Habeeb bai damu da rashin ansawar ta ba yace.

” Meyasa bakya jin magana ta, sau nawa nake ce miki ki daina yiwa Mustafa rashin kunya, ban faɗa miki ba nace ki daina shiga cikin sha’anin sa tunda yace baya sonki cikin rayuwar sa, amma kin ƙi gashi kuma jikin ki yana faɗa miki daman Hausawa sunce *duk wanda baiji bari ba zaiji hoho* karki fasa shiga rayuwar sa, kece cikin wahala” ya ƙarasa maganar yana nuna Indo da yatsa.

Tashi Indo tayi tana sharce hawayen ta, cikin Muryar kuka tace.

” Yanzu ya Habeeb duk abunda ya Mustafa yayi baka gani ba, a gaban ka fa ya zagi momma kana kallo matar da tazo har gidan nan domin ta’aziya shine ya cimata mutunci, amma wai laifi na kake gani shi baida laifi kenan?”

Cikin tsawa Habeeb yace.

” Ina ruwan! Ki da Abunda ya yiwa Barrister Zubaida kin san meyake tsakanin su, kin san meta masa, ke kanki da kinsan Abunda yake tsakanin su, bazaki damu ba bare har kiyi tunanin shiga tsakanin su, ba yau suka fara gayawa juna magana ba, ita kanta Barrister Zubaida ta ɗagawa Mustafa ƙafa ne yau kawai saboda cikin gidan su tazo, ina ruwanki da shiga Abunda bai shafeki ba.”

” Ya Habeeb ban gane abunda kake nufi ba, wani irin hali momma take dashi? wanda har zaka ce ya Mustafa baida laifi duk irin wannan cin mutuncin da ya mata a gaban ƴarta.”

” Bance tana da mungun Hali ba, sai dai abinda take wani lokacin bata kyautawa, Barrister Zubaida, ƙanin ta, ya taɓa yiwa wata yarinya fyaɗe ko nace sunyi mata fyaɗe, ƴar talaka lis ce yarinyar wanda basu da cin yau bare na gobe, iyayen yarinyar hankalinsu ya tashi sosai, har takai ga sun kai ƙara human Right, su kuma human Right suka shigar da ƙara kotu, a lokacin Hajiya Zubaida lowyer ce Babba, amma taƙi shigawa ɗan uwanta Case, gashi suna da kuɗi sosai mahaifinsu babba ne a cikin siyasar ƙasar nan, hakan ce tasa suka nemi Mustafa suka yaudare sa da cewa sharri aka yiwa ƙanin nata ba shine yayi fyaɗen ba, suka sashi ya karɓi Case ɗin, dake shi lowyer ne mai zaman kansa, yayi duk wani bincike bai gane cewa Sadiq shine yayi fyaɗen ba, suka shiga kotu, Mustafa yayi duk yanda zai yi yasa aka kori ƙarar, kinsan meya faru?”

Girgiza kanta Indo tayi alamun bata sani ba.

” Wannan ƙanin Barrister Zubaida shine yayi fyaɗen, gashi kuma an riga an kori ƙara a kotu, sosai Mustafa yaji zafin yaudarar sa da sukayi, gashi kuma ba’a juma da ƙorar ƙarar ba Allah yayiwa yarinya da aka yiwa fyaɗen rasuwa, daga baya Mustafa ya kasa Hkr gani yake kamar Allah bazai barshi akan haƙƙin wannan yarinyar Mustafa shida kansa ya shigar dasu Hajiya Zubaida ƙara akan abiwa yarinyar haƙƙin ta tare da hujja mai ƙarfi mustafa ya shiga kuto ko a karo na biyun Hajiya Zubaida da kanta ta tsayawa ɗan uwanta a kotu, kan cewa sam ba shi ya aikata wannan laifin ba, sai dai Mustafa ya fita hujja, wanda hakan yasa alƙali ɗaure ƙanin Barrister Zubaida har na tsawon shekaru goma a gidan kaso, ki faɗa min wake da laifi tsakanin su?, ki daina shiga Abunda bai shafeki ba, wanda baki da masaniya akai sam Mustafa baida laifi cikin wannan lamarin, laifin sa ɗaya kasa manta abunda ya faru shiyasa ko da yake jibgar ki banyi magana domin kuwa baki da gaskiya ko kaɗan”.

Jikin Indo sosai yayi sanyi, amma sai dai har yanzu tana jin haushi da tsanar Mustafa cikin ranta, bata kuma ɗaga kanta ba har Habeeb ya fita daga ɗakin.

Koda daddare Mama sosai ta yiwa ƴarta nasiha, tare da mata faɗa akan ta daina yiwa Mustafa rashin kunya ta daina shiga sha’anin sa muddun bai sata a ciki ba, sosai dai Mama ta yiwa Indo faɗa.

Washegari kuwa mama da su Baba suka ɗaga zuwa Dasina, Indo ji tayi kamar tabi su amma sai dai babu halin hakan.

Sati Uku da rasuwar Inna Aunty Hindu suka koma gidan su dake gida dubu nan cikin Jigawa, amma sai dai bata koma da Indo ba, Hasina ce kawai suka tafi tare, aka bar Indo da sharifa.

A hankali rayuwa take tafiya, jituwa kuwa sam babu tsakanin Mustafa da Indo, yau Watan Inna shida da rasuwa a yaune Kuma aka saka Ranar Auren su Mustafa da Habeeb sati biyu rak, Aunty Hindu da kanta tazo ta ɗauki Indo tace sai bayan biki zata dawo.

Da sauri ta fito hanun ta riƙe da school bag ɗin ta, tana cewa.

” Aunty Hasina kiyi sauri kizo ki sauƙe ni zanyi let fa.”

Fitowa Hasina tayi tana dariya tace.

” Muje na sauƙe ki kafin ki cinye ni”

Dariya Indo tayi tana yiwa Aunty Hindu sai ta dawo ta fice.

A makarantar Hasina ta sauƙe ta sannan ta juya, cikin Class ɗin su ta shiga Ss3 dake ma sun kusa fara jarabawar barin Secondary School, Zarah Indo ta samu tana zaune a sit ɗin su dake yanzu ta ɗan sanjawa Indo tun abunda ya faru tsakanin su da Mustafa, hanu Indo ta miƙawa Zarah sukayi musabaha, daga nan bata ƙara cewa Zarah komai ba, ganin da zarah tayi Indo bata da niyar kulata yasa ta cewa Indo.

” A’ishatu Musa meya sameki naga yau kamar kin sanja min?”

Ɗago kanta Indo tayi tace.

” Bangane na sanja miki ba, na sanja miki ko kin sanja min? Me kike so na miki Zarah kin daina min magana sosai kin rage shiga harkata so kike ni nata bin ki kina min wulaƙanci, an miki laifi a gidan mu, bani na miki ba, amma na baki Hkr kika ƙi haƙura kuma nima kinsan dai gidan nan ba gidan mu bane amma na baki hkr kika ƙi to ya kike so na miki Banda nima na fita harkar ki.”

Murmurshi Zarah tayi tace.

” Ƙawata ba dai fushi ba, wlh raina ne ya ɓaci sosai amma komai ya wuce, kiyi hkr ka kinji bestie na”

Dariya itama Indo Tayi tace.

” Babu komai ƙawata ya wuce nima a waje na”

Sosai suka ta taɗin su kamar babu abunda ya taɓa shiga tsakanin su.

“Mustafa wai ya haka ne kam, tun jiya nake maka Maganar wani hole ya kamata ace mun kama na diner amma kayi burus dani ka ƙi Magana.”

Tsuka Mustafa yaja ba tare daya ɗago ya dubi Habeeb ba yace.

” Naga alamar tun jiya bakin ka yake ciwon magana to Allah ya yaye maka.”

Haushi ne ya kama Habeeb yace.

” Baƙar magana zaka faɗa min saboda ina ta binka akan harkar bikin ka, to Allah ya baka hkr.”

Murmurshi Mustafa yayi yace.

” Meye kuma abun fushi Bros, nima fa ban ɗauki wannan auren da zanyi ba Aure, kaine zakayi Aure ba niba kaida zaka Auri zaɓin ka, dan kaje ka kama hole ɗinka ni babu wani kuɗina da zan kashe kan wannan banzar yarinyar wacce bata da wani daraja cikin idanuna, Wlh Habeeb ni tausayin ta nake ji muddun ta shigo cikin gida na, badai Momy tace sai anyi Auren ba, to ayi.”

“Mtss haba Mustafa wai meyasa bazaka ɗauki ƙaddarar ka ba, ka Rungumi zaɓin mahaifiyar ka, sai Allah ya sa maka Soyayyar ta cikin ranka ya kuma Albarkaci auren muddun ka yiwa mahaifiyar ka biyayya da kake maganar kai bazaka kashe kuɗin kaba ai bance ka kawo sisin kwabon ka ba ni zanyi komai a aljihu na.”

Dariya sosai Mustafa yayi yana yiwa Habeeb kallon sakarai yace.

” Ubangiji Allah karya taɓa samin soyayyar ta cikin zuciyata, kai kasan yanda na tsani YARINYAR nan kuwa kaga tunda kaga zaka iya ɗaukar ɗawainiya bismillah kaga ba sai naje ba, sai su saka a tsakiyar su tunda Abunda yayi Mustafa ai shine yayi Habeeb ko? ni sai yanzu ma ka tuno min da cewa Momy tace lallai sai dai naje na bata kuɗin da zatayi hidimar bikin, ni da zaka taimake ni ma na baka ka kai mata ba saina jeba, dan wlh banson zuwa gidan su, nasan kuma munafuka zata sanar da Momy cewa banje ba.”

” Mtsss kazo ka jani ka sani dole na kai maka ubana tunda nine mijin nata, kuma wlh kasa a ranka sai kaje dener” yana gama faɗin haka Habeeb ya fice yana hararar Mustafa.

Murmurshi Mustafa yayi shima ya tashi ya shiga wanka da niyar yaje ya miƙa mata kuɗin ya wuce office.

A falo Habeeb ya ci karo da Momy da sharifa suna ta rigima akan cewa zata gidan su Hasina ta kwana ita kuma Momy ta hana, duban Sharifa Habeeb yayi yace

” Sarkin ƙorafi ta cikin gidan nan meya faru haka kike haɗa baki?”

Ƙara haɗa bakin Sharifa tayi tana cewa.

” Ya Habeeb kaga jiya Hasina ta kira ni……..” Bata ƙarasa maganar ba Habeeb ya bige bakinta yace.

” Aunty zaki ce ba Hasina gatsal ba dan gidan ku” ya ƙarasa maganar yana zaro mata Ido.

Dariya sharifa tayi tace.

” To Aunty Hasina ina shike nan, tace zan rakata kasuwa shine nacewa Momy zan kwana idan naje, taƙi yadda.”

Dariya Habeeb yayi yana duban Momy yace.

” To Momy gareki kiyi kibarta zuwa gobe da safe ta dawo pls MOMYN mu.”

MOMY cewa tayi.

” Ba fa zata kwana ba, ita kaɗai take tayani aiki cikin gidan nan idan taje ta kwana da wa zanyi aikin.”

” To Momy ai nace miki da wuri zan dawo da sassafe ma.”

Daƙyar dai Momy ta yarda Sharifa tayi kwana ɗaya.

Dariya Habeeb yayi tare da cewa.

” Muje na sauƙe ki to tunda kin shirya saina wuce daman zanje na ɗauko Indo a school Idan mun ɗauko ta, sai na sauke ku nayi tafiya ta.”

Harara Momy ta watsawa Habeeb tana cewa.

” INDO dai Indo dai cikin bakin ka kullum, kamar wanda kuka fito ciki ɗaya shashasha marar lissafi ka zaune sai bautawa yarinya ƙarama kake.”

Tana gama faɗin haka ta haura sama tana cigaba da mita, shidai Habeeb baice komai ba saima cewa Sharifa da yayi muje, tsalle Sharifa tayi tace.

” Yauwa yayana muje daɗi na dakai akwai tausayawa na ƙasa dakai ba Irin ɗayan ba, kullum rai a haɗe kamar an aiko masa da saƙon mutuwa.”

Zaro ido Habeeb yayi tare da cewa.

” Me kika ce, to bari mu juya wajen ɗayan saiki maimaita a gaban sa kafin mu wuce, tunda ke baki da kunya.”

Dariya sharifa tayi tace.

” Rufa min asiri ya Habeeb ai yana ji yau saiya kusa kasheni cikin gidan nan.”

Dariya shima Habeeb yayi yace” matsoraciya kawai” suka wuce suna wasa da dariya da Habeeb kamar ba kanwar sa ba.

“Mamy ya maganar Family And friends ɗin nan ne da kika ce za’ayi kuma kinga yau saura 10 days Auren fa.”

Duban ta Momy tayi tace.

” Ina sane za’ayi shima, sannan gobe yani zata zota ta fara miki gyaran jiki da wasu abubuwan, sannan Asabe ta aiko min da wasu magungunan mata, zaki fara amfani dasu yau, dubu ashirin na karɓosu wajen ta”

” Shike nan ba damuwa kice gobe su Aunty yana mutan Barno ana hanya”

Ehh Mamy tace, kafin suka cigaba da zancen yanda bikin zai kasance.

Mustafa daya juma cikin gidan nasu tsaye compaunt ɗin, baiga kamal ba mai masa iso cikin gidan, gashi kuma shi baida numbern RAUDA, wajen mai gadi ya nufa tare da cewa ya taimaka ya masa magana da RAUDA, tashi Baba mai gadi yayi ya shiga kira masa ita shi kuma ya koma mota.

Da sallama Baba mai gadi ya shiga bayan sun gaisa ne ya sanar dasu cewa Mustafa yana jiran Indo a compaunt, duban Baba mai gadi Mamy tayi tace” kaje kace mishi ya iso” da to Baba ya amsa sannan ya fice.

A Mota ya samu Mustafa yake sanar dashi sakon nasu murmurshi Mustafa yayi yana ganin RAUDA tama raina masa Hankali, ai yasan da falon nasu yace tazo ta samesa a nan, kuɗi ya ciro ya miƙawa Baba mai gadi yace.

” Gashi Baba dan Allah kayi hkr ka miƙa mata wannan kace gashi inji Momy kuɗin data aiko tana bukata na hidimar biki, sannan kace mata banyi niyar shigowa ba ba kuma zan shigo ba.”

Shidai Baba ɗan aike ne karɓa yayi ya tafi kaiwa, shi kuma Mustafa jan motarsa yayi ya fice daga cikin gidan, bayan Baba mai gadi ya isar da saƙon Mustafa ne Momy ta tashi cikin hasala tana cewa.

” Tirƙashi lallai wannan yaron ya raina mu, ta dubi RAUDA tace gashi dai dan ubanki da kike tausayin sa ya fara shuka miki tsiya tun kafin ki shiga cikin gidan sa, kuma dan ubanki dole ne kibi umurni na, domin ganin na kwato miki ƴancin ki.”

To fa fan’s sai ku shirya zuwa biki, dan nasan akwai ƴan hana biki maraici musamman iklas ƙamshi da sis munaya da maryam, Hafsat ma dai ba’a barta a baya ba😄

*Vote*

*Share*

*And*

*Comments*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah ce)*

[3/5, 9:33 AM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*

*Nasmah ko Nasirah*

*Sara da Sassaka*

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.

Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*WANNAN PAGE ƊIN SADAUKARWA NE A GARE KA AUNTY MU’AZ KYAUTA NA BAKA IDAN KANA SO SAI KA TAIMAKA WA KULSUM ƊINKA TA KARANTA KODA KAƊAN IDAN KASO KA HANATA NIDAI INA BAYA INA SHAN KALLO, UMMA MUHAMMAD NAJAMANGA HAJIYAR AUNTY MU’AZ*😆😆

*بسم الله الرحمن الرحيم*

____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

*P*••••••6️⃣3️⃣ ➡️ 6️⃣4️⃣

Ajiyar Zuciya RAUDA ta sauƙe tana kallon Mamy cikin damuwa kafin tace.

” Shike nan Mamy duk abunda kika ce dai-dai ne ni wannan magani da kika damu dashi banga amfanin sa ba amma……..”

Dakatar da ita Mamy tayi tana cewa.

” Amma meye marar zuciya, wa’azi zaki minne uwata, shige kibar wajen nan na daina ganin ki a gabana dan ubanki.”

Shigewa ɗaki RAUDA tayi ta zauna bakin bed ɗin ta, tare da haɗa tagumi tana tausayin kanta na son mutumin da baya sonta, bata kuma ganin laifin kowa sai na Zuciyarta da ta tilasta mata son Mustafa, goge hawayen idanunta tayi a fili tace.

” Kiyi hkr Mamy koda kin bani maganin nan bazan iya amfani dashi ba, baida wani fa’ida sai ma biyu babu da mutam zaiyi, dan haka bazan yi wannan kuskuren ba Mamy kema Allah ya ganar dake, da na yiwa Mustafa Asiri na gwammaci naje nata zaman Hkr da wahala a gidan Mustafa, Allah ya sa ya soni wata rana ni shine fata na” ta ƙarasa maganar tana goge hawayen nata kafin ta kwanta tana tunanin duniya.

A falo kuwa mamy ne ta dannawa Yana kira tana ɗagawa Mamy ta fara cewa.

” Aunty Yana karfa ki manta da saƙona na maganin nan wajen Malam Alamguburo, kinsan dole sai munyi maganin yaron nan naga alama baida mutunci, dan namiji zuma ne saida wuta, kice masa karya manta harda na mahaifiyar yaron dan gara mu ƙara riƙeta sosai karta kawo mana matsala gaba.” Shuru Mamy tayi sai can naji tace “to shikenan Aunty Yana sai kin zoki Allah ya kawo ki lafiya” kafin ta kashe wayar tana ƙwafa tana zagin Mustafa.

Washe baki Indo da take tsaye ita da Zarah tayi sakamakon hango motar ya Habeeb da tayi, da sauri ta ƙarasa tana cewa Zarah “sai mun haɗu gobe ki gaishe min da momma”

“Zataji” Zarah tace tana dariya kafin ta gaishe da Sharifa da Habeeb cikin fara’a kuwa Habeeb ya amsa kafin Indo ta faɗa cikin motar tana dariya, Habeeb yaja suka tafi.

” Aunty Sharifa gidan Ummi zaki kema kenan?”

Murmurshi Sharifa tayi tace.

” Eh mana kun gudu kun barni ba dole na biyo ku ba, gidan ya min shuru babu daɗi.”

Habeeb ne yace.

” Ai kurame ne mu Dole gidan ya miki shuru, aiko da nasan Abunda yasa kika baro gida kenan da bansa Momy ta barki kin fito ba.” Ya ƙarasa maganar yana murɗe mata kunne.

Dariya Sharifa tayi tana ƙwace kunnen ta daga hannun Habeeb tace

” Ya Habeeb ai fast is fast present continue, yanzu kam, tunda harna fito magana ta ƙare.”

Dariya Indo tayi tace.

” Ya Habeeb, an fara biyan kuɗin neco kasan mun kusa gamawa, Daddy kuɗin waec kawai ya biya min kuma duka ƙawaye na biyu suka biya neco And waec.”

Murmurshi Habeeb yayi tare da cewa.

” Oh sweet ƙanwata kice mun kusa girma zamu gama Secondary School, eyye babyn na ta girma to karki damu gobe in Allah ya kaimu zan shigo makarantar naku na biya miki ina ga dai idan ban manta ba 25k suke biya ko?”

” Eh ya Habeeb haka ne 25k ne.”

” Okey to zan shigo gobe in Allah ya kaimu dole sweetie na tayi duka biyu Itama, har jam ma zan biya miki insha Allah.”

Dariya Indo tayi cikin farin ciki, sai kuma Malam sani ya faɗo mata cikin ranta yanda yake rarrashin ta kullum tayi karatu da tsafta, duban Sharifa tayi tace.

” Aunty Sharifa akwai uncle ɗinmu na ƙauye Mlm Sani ina alfahari dashi sosai, ko yaushe shine yake sani a hanya cikin rarrashi har minti da doya yake saya min dan nayi karatu da tsafta, kamar dai yanda ya Habeeb yake min, bazan manta da alkairinsa gare ni ba, Aunty kullum naga ya Habeeb sai na tuno dashi ko yana koyarwa har yanzu sai Allah.”

Murmurshi Sharifa tayi tace.

” Allah sarki daman haka wasu Mlm suke suna da kirki wasu kuma mugaye, Allah ya saka masa da Alkairi, ni kuwa duk sanda zaki ƙauye sai na baki ƙyauta kin kai masa.”

Dariya Habeeb yayi tare da cewa.

” Ai kuwa nima zan kawo tawa gudumowar insha Allah.”

Dariya sosai Indo tayi cikin murna da farin ciki, haka suka ƙarasa suna raha, a ƙofar gidan Habeeb ya sauƙe su yace shi bazai shiga ba, yana sauri sai dare zai shigo, shigewa sukayi cikin gidan Indo na ɗagawa Habeeb hanu.

Murmurshi Habeeb yayi tare da jan motar sa har ga Allah duk sanda ya saka Indo cikin idanunsa yakan ji wani sanyi cikin ransa, yana samun nutsuwa sosai a duk sanda yake tare da ita koda kuwa yana cikin damuwa ne sai yaji duk wannan damuwar ta kau sakamakon gani Indo kusa dashi, Muryar ta kuwa jinta yake kamar sarewa amma duk da haka Zuciyarsa bata yadda son Indo yake ba, cikin shauƙi da Happy Habeeb ya nufi inda zaije.

Shiko Sarkin baƙin hali, H/court ɗinsu ya ƙarasa darect, office ɗin sa ya nufa, Barrister Umar ya tarar Zaune yana duba wasu files dariya Mustafa yayi ya zauna yana cewa.

” Mutanen sama kuma yaushe aka fito, yau harka rigani shigowa kenan?”

Dariya Barrister Umar yayi yana cewa.

” Ai yanzu dole na rigaka shigowa ango, tunda kasa Auren nan a gaba naga alamar ka fara let.”

Murmurshi Mustafa yayi ba tare daya ɗago ba yace.

” Kuna bani mamaki wlh kaida Habeeb, ni wannan auren da kuke kiran sa da suna Aure, ni fah bai dameni ba dashi da babu duka ɗaya ne a wajena, so ni har mantawa nake da Auren, kasan kuwa sunan dana sawa wannan auren?”

Girgiza kansa Barrister Umar yayi yana duban Mustafa yace “a’a”

Murmurshin gefen baki Mustafa yayi tare da cewa.

” *Auren tushe Auren ko oho* domin kuwa bana buƙatar matar da ake ƙoƙarin liƙa min, kallon ta nake tamkar maciji kububuwa wlh babu Soyayyar RAUDA ko kaɗan cikin Raina ” ya ƙarasa maganar yana ɗago kansa ya dubi Barrister Umar.

Barrister Umar kuwa cikin mamakin irin ƙiyayyar da Mustafa yake gwadawa RAUDA yake kallon sa kafin yace.

” Ni ko Mustafa menene Aibun RAUDA da baka sonta haka, naga duk abunda miji yake nema ga matar sa RAUDA ta haɗa su, so meyasa kake ƙinta? Tana da ƙyau diri zati, tana da ilimin addini tare da na zamani, tana da tarbiyya Uwa Uba ta iya girki, to ka faɗa min menene Aibun ta?”

Murmurshi Mustafa yayi shima yana duban Barrister Umar yace.

” Barrister Umar ai ita soyayya babu ruwan ta da ilimi ko kyau ko wani nasaba, idan kana son Mutum ko yaya yake bazaka gani ba komai kuwa munin halinsa, haka kuma ƙiyayya idan baka son mutum duk qualities ɗin sa shima bazaka gani ba, so kaga kenan amsar tambayar da kamin ta fito anan, mu buɗe wani shafin wannan kam mu ajiye sa a gefe domin naga alamar baka son Gaskiya.”

Taɓe bakin sa Barrister Umar yayi ba tare daya cewa Mustafa komai ba akan maganar yace.

” Okey ga files ɗinnan na Case ɗin Sadiya Ibrahim ne, na gama haɗa duk wasu information yana ciki amma SADIQ yace na sanar dakai cewa an ɗaga shara’ar sai ranar 5 ga watan 5.”

Karɓar files ɗin Mustafa yayi yana cewa

“sun ƙara wata ɗaya kenan nan gaba? Hakan ma yayi zamu ƙara samun enough time na bincike, bari na duba su idan ina neman wasu information ɗin zan maka magana.”

” To” Barrister Umar yace yana ƙoƙarin tashi tare da cewa.

” Bari na koma nawa office ɗin akwai ayyukan daya kamata nayi.”

“A fito lfy” Mustafa yace Kafin Barrister Umar ya tafi.

HASINA sosai taji daɗin zuwan Sharifa, haka Aunty Hindu, ranar tare suka fita kasuwa har Indo, Dake Hasina bata da wata ƙawa cikin Nigeria, Sharifa ta ɗauka matsayin ƙawa duk da cewa ta girme ta.

Habeeb kuwa bai karya alƙawarin Indo ba washe gari yaje ya biya mata kuɗin neco da jam.

Biki yanzu sai kankama yake yayin da ko wani ɓangare biyun suke gyara ƴaƴan su, Aunty Hindu kuwa da kayan fruit da kuma na gargajiya take yiwa Hasina nata maganin matan dan kuwa sosai take bawa Hasina fruit wani ta haɗa tayi blanding ɗinsa wani kuma ta bata shi haka taci zuma kuwa sosai take bawa Hasina take amfani dashi, sosai Aunty Hindu ta gyara Hasina ciki da waje, wani shegen kyau Hasina tayi domin kuwa tunda aka fara mata gyaran jiki Aunty Hindu ta hana koda Habeeb yaga Hasina, Aunty Hindu cewa mai gyaran jikin tayi, itama Indo a mata gyaran jiki, haka kuwa akayi matar tare ta dirje musu jiki, su kuwa Mamy maganin mata ta dinga ɗirkawa RAUDA, amma gyaran jiki kam babu laifi ta gyaru sosai domin kuwa kunsan gyaran barebarin Barno, ba daga baya ba.

Duk hidimar bikin Mustafa babu ruwan sa ciki Habeeb ne yake shi ɗaya, dan shi Mustafa rabonsa da yaga RAUDA ma harya manta, bare kuma ya wani damu da hidimar Auren ta, a cewar sa fa kenan.

Yau dai biki saura kwana Uku, sosai gidan Momy ya cika da ƴan Uwa da abokan arziki hatta ƴan uwan su Daddy dake garin Dasina sunzo mama kuwa bata samu damar zuwa ba wannan karon, Indo da taji labarin zuwan ƴan Dasina taso zuwa gidan Momy tagansu Aunty Hindu ta hana tace ta bari sai gobe suma zasu zo su wajenta, Aunty Salima ƙanwar Momy da Hajiya Addiyo yar Momy, suna zaune a ɗakin Momy, Aunty Salima take tambayan Momy cewa.

” Nikam Hajiya a’isha wani holl aka kama ne na dener, kinsan fa dole zani.”

Murmurshi Momy tayi tace,

” Ni dai gaskiya bani da masaniyar inda zasuyi, amma bari su shigo kya tambaye su.”

Ai kuwa haka akayi Mustafa yana shigowa Aunty Salima ta tambaye sa, taɓe bakin sa Mustafa yayi cikin halin ko inkula yace.

” Ban sani ba amma ki tambayi Habeeb ya sani shi tunda shine uban ƴan rawar kai na bikin, ya faɗa min inda za’ayi amma gaskiya na manta” Kuma sarai Mustafa yasan inda za’ayi kawai ya tsani yaji ana masa maganar auren nan domin yaga Aunty Salima kamar neman magana take.

Sake baki Aunty Salima tayi tana kallon Mustafa cikin mamakin Angon da baisan inda za’ayi denern sa ba, taɓe baki itama Aunty Salima tayi tace.

” Allah ya yaye maka wannan shegen halin naka da wannan miskilancin naka idan ma ka sani kaƙi faɗa minne kaika sani zan kira Habeeb ɗin ai zai gaya min” ta ƙarasa magana tana ranƙwashin kan Mustafa ta wuce tana kiran Habeeb a waya.

Murmurshi Mustafa yayi yana cije bakin sa ya shige ɗakin su sakamakon jin mararsa ta fara ƙullewa, drower ya buɗe ya ɗauki tablet ɗinsa yasha, saurin faɗawa saman bed yayi domin kuwa yasan ciwon nasa ne yake neman tashi masa lumshe idanunsa yayi yana jin wani irin felling.

Zama Indo tayi tana duban Hasina tace.

” Dan Allah Aunty Hasina ki ƙira min Zarah na sanar da ita maganar Auren nan nima dai ya Habeeb yace ina gama Secondary zai saya min wayar nan na huta da aron taku.”

Dariya Hasina tana cewa.

” To ƴar gidan Habeeb ta hanun daman sa, jeki ɗauko wayar tawa saman wadrop ki kira ta”

Tashi Indo tayi tana dariya tace.

” Faɗi kanki tsaye Aunty Hasina nice nan ta hanun daman ya Habeeb ɗina” ɗaukar wayar taki ta dannawa Zarah kira kasancewar ita zarah tana da waya.

Can gidan su RAUDA kuwa sosai Mamy take ɓarin kuɗi na auren ƴarta ta, ta shirya family friend da za’ayi gobe misalin ƙarfe goma na safe, za’ayi kamu Kuma da yamma ƙarfe huɗu, ita dai Hasina tace ba zatayi wani bidi’a ba, ko dener ma da zatayi Habeeb ne yasa dole sai tayi da dan ita ne wlh bazata yi ba, walima kawai ita tasa a ranta za tayi.

Da sauri Mamy ta shiga kitchen ta buɗe wani coler da yake ɗauƙe da naman kaza sai ɗayan kuma tuwon semo ne lafiyayye Mamy ta barbaɗa wani magani mai kamar gishiri a saman miyar, Gambo ta ƙwalawa kira ƙawar sheɗancin nata, da sauri Gambo ta shigo tana cewa

” ya akayi kin gama komai?”

Ajiyar Zuciya Mamy tayi tace.

” Na gama gashi kije cikin gidan ki tabbatar da cewa Hajiya a’isha taci Abincin nan, Bayan ita karki bari wani yaci ki tabbatar ita kaɗai taci ƙawata, kinsan dole ne mu riƙe Hajiya A’isha a Hanun mu sai yanda mukayi da ita, kafin mu dawo kan shegen ɗannata mai taurin kan tsiya.”

Dariya Gambo tayi kafin tace.

” Ai karki damu Hajiya Turai kinsan ni kin san halina, dole nayi aiki bisa ƙa’ida.”

Kuyi hkr da typing error idan kun samu wlh ban samu nayi editing ba yau🙏🏻

Ku sani cikin Addu’ar ku ina da abu mai mahimmanci da zan aiwatar Allah ya bani Sa’a yasa nayi cikin nasara🙏🏻

*Vote*

*Share*

*And*

*Comments*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah ce)*

[3/7, 4:41 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*

*Nasmah ko Nasirah*

*Sara da Sassaka*

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.

Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*

____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

*P* 6️⃣5️⃣ ➡️ 6️⃣6️⃣

Gambo har ɗakin Momy ta shiga, suna cike cikin ɗakin Momy da ƴan uwanta, bayan sun gaggaisa ne, Gambo ta dubi Momy tace.

” Hajiya A’isha, aiko ni fa Hajiya Turai tayi wajen ki, ina son mu ɗan fita daga waje.”

Murmurshi Momy tayi tare da tashi tana cewa.

” Okey muje babu matsala.”

Aunty Salima ne tayi carap tacewa Gambo.

” Menene cikin kulan kike riƙe da ita gam, idan abun daɗi ne ai sai ki bamu mu sawa bakin salatin mu,” tana maganar tana ƙoƙarin jawo kular daga hannun Gambo.

Ƙara damƙe kular Gambo tayi tana cewa.

” Babu komai fa ciki na biya gidan ƴar uwata ne na karɓo ta tafi da abinci bata dawo da ita ba, shine yau nabi na karɓo”

Maida hanunta Aunty Salima tayi tana cewa.

” Okey ai nayi zaton abun daɗi ne ciki”

Fitowa falo sukayi Momy ta dubi Gambo tace.

” Lafiya kuwa Turai ta aiko ki yanzu cikin wannan hatsaniyar bikin?”

Murmurshi Gambo tayi cikin salon munafurci da yaudara tace.

” Lafiya lau wlh Hajiya, daman abinci ne ta girka muku tace tasan yanzu haka kina can baki samu kinci abinci ba, shine tace dan Allah na taimaka mata na kawo miki abincin nan na tabbatar kinci kafin na tafi.”

Murmurshi Momy tayi tana tace.

” Allah sarki ai kuma kamar tasan banci abincin ba, ai da wannan maganar ne dama baki taso ni ba, sai muyita can to na gode kawo na shiga dashi ciki, na ci acan”

Ai kuwa Gambo ƙin bawa Momy tayi ta shiga da kwanon ciki, sai ta wayan ce da cewa.

” Ai kuwa Hajiya bazan baki abincin nan ki shiga dashi ba zaki iya mantawa dashi, ko kuwa a cinye gashi abincin baida yawa, ita kuma danke kawai tayi, gashi ta bani amanar cewa na tabbatar kinci kinga kuwa ai dole na cika amana.”

Ita kuwa Momy Zuciyarta ɗaya tayi dariya tana Cewa.

” Oh ikon Allah Hajiya Turai sai kace wata yarinya ta ɗauke ni, to shikenan bani naci kya sauƙe amanar taki” Momy ta faɗa tana zama.

Ai kuwa cikin farin ciki Gambo ta miƙawa Momy kular tana zama itama, Momy na cin abincin Gambo na mata taɗi harta cinye abincin duka, ta dubi Gambo tace.

” Shikenan ina ki ce mata na gode daman kuwa yunwa nake ji”

Dariya sosai Gambo tayi tace.

” Insha Allah saƙonki zai isa da wuri yanzu ma kuwa.”

Murmurshi Momy tayi tace.

” To na gode”

Tafiya Gambo tayi cikin happy tana dariya, Gambo bata juma da fita ba Momy ta yunƙura da niyar tashi sai taji wani irin jiri taji ya fara ɗibanta, kanta kuwa ji tayi kamar yana juya mata dole yasa Momy komawa ta zauna, tana dafe kanta, tafi 15minute a haka kafin taji komai ya lafa mata, sannan ta tashi ta shiga ciki.

Bacci sosai Mustafa yayi sakamakon tablet ɗin da yasha, ya tashi kenan ya shiga wanka yana fitowa Habeeb na shigowa cikin ɗakin ransa a haɗe cikin faɗa Habeeb ya fara magana.

” Abunda fa kake Mustafa baya dacewa Wlh, wani irin rashin imani ne wannan Mustafa, tunda aka fara maganar auren nan, sam baka saka bakin ka, ciki baka san komai kan wannan auren ba, hatta sabuwar riga kaƙi ɗinkawa a dalilin wannan auren, sai nine naje na kai a ɗinka mana, na gaya maka cewa a Ammar holl za’ayi dener nan kayi burus dani kamar baka jiba, ɗazu nake magana da RAUDA take sanar dani cewa rabon da ta ganka tun ranar da tabar gidan nan, tunda aka fara maganar auren nan baka je kun tattauna ba, wlh kaji tsoron Allah, kuma wlh dole kaje dener.”

Mustafa share Habeeb yayi kamar baiji Abunda yake faɗa ba, ya cigaba da shafa mansa, ƙara tunzura Habeeb yayi wato ma Mustafa ya maida shi mahaukaci ko, da zaiƙi kulasa, gaban mirron Mustafa yaje tare da ƙwacen man dake hanun Mustafa yana cewa.

” Wai mahaukaci ka maida nine, ina faɗa maka gaskiya akan rashin kyautatawar ka kayi banza dani, Abunda kayiwa RAUDA ya dace kenan ka burus da yarinyar mutane, wlh kabar ganin yarinyar nan tana sonka shi yasa kake wulaƙanta ta, ka sani cewa ka sani cewa jarabawa ce Soyayyar ta a gareka, Kuma kaima bakafi ƙarfin Allah ya ɗaura maka wannan jarabawar ba, wlh mai Sonka yafi maƙiyinka ko yaya yake, ka gyara rayuwar ka, domin kuwa akwai kurakurai cikinta da yawa duk da nasan ɗabi’ar kane tun muna yara amma dai kayi ƙoƙarin gyarawa, shi ɗan adam ba abun wulaƙantawa bane”

Murmurshin gefen baki Mustafa yayi yana duban Habeeb kamar yau ya fara ganin sa kafin yace.

” Oh ƙarata ta kawo maka, to gani hukunta ni ubana, ita dan uwarta meye damuwar ta da rayuwata ne, idan ƙarata ta kawo sai ka hukunta ni, idan kuma saƙo ta baka kace mata injini ta tuno maganar da mukayi da ita a cikin makarantar su, ya isheta amsarta ya fito, banza nacecciyar Mace marar aji da kamun kai” Mustafa ya ƙarasa maganar yana tsuka.

Murmurshin takaici Habeeb yayi tare da cewa.

” Bazan hukunta kaba, duniya ce kayi duk abunda kaga dama, akwai ranar da zaka ɗebi adashen daka zuba cikinta shi Allah ai ba azzalumin bawa bane.” Yana gama faɗin haka ya wuce tollet ba tare daya ƙara cewa komai ba, Mustafa bakinsa ya taɓe tare da ɗaga kafaɗar sa alamun wannan damuwar kane.

Yau juma’a, da misalin karfe tara na safe, RAUDA sukayi family And friends su Aunty Salima sunzo sosai ƴan uwan Momy sai dai basu gayyaci ƴan dasina ba wai acewar su ƙauyawa ne su, cikin tsari kuwa sukayi family friends ɗin RAUDA tayi kyau sosai, cikin doguwar riga, baka su Indo basu ko leƙo wajen family And friends ɗinsu ba, da yamma akayi ma akayi kamu, washe gari kuma sukayi walima har da Hasina waje ɗaya sukayi, sosai amaren sunyi kyau, Halima wacce suka zo daga Dasina sanda ta hango Indo bata gane ta ba, domin kuwa tayi kyau sosai harta gaji, gashi tasha ƙunshi baƙi da ja hanu da ƙafa, tasa wani blue ɗin doguwar riga an mata rolling ɗin ɗankwalin rigar a kanta, tasha makeup kuwa, sosai tayi kyau, suna gefe tare da Zarah suna taɗi harda dariya, har aka watse a wajen walimar Indo Allah baisa taga Halima ba.

Washegari da safe asabar tun ƙarfe tara Habeeb yake ta ƙoƙarin shiryawa zuwa wajen taron ɗaurin Auren nasu wanda za’a ɗaura 11am Mustafa kuwa yana kwance ko a jikin sa, sai famar games yake, wacce wayar Habeeb yayi daga hanun sa ɗago kansa Mustafa yayi yana kallon Habeeb yace.

” Ya dai malam zaka wani wacce min waya kamar wanda taka na ara.”

Kafin Habeeb yayi magana Barrister Umar ya shigo yana cewa.

” Wai ya baku fito bane kam, tun ɗazu baƙi suƙe jiran ku, ga inspector khabeer ma can Angon Nasreen da Zuhura mutanen Gombe ya samu isowa, harda inspector Muhammad Angon Saude, Doctor Naseer ma Angon Nasmah shida Na’eem Angon Nasirah suma ba’a barsu a baya ba, duk suna jiran ku a falon baƙi, harda Conel Ubaidullahi Sarkin miskilanci, sai kuyi hanzari naga kamar time na neman ƙure muku.”

Saurin tashi Mustafa yayi yana cewa

“seriours su Doctor Naseer sunzo da gaske?”

Dariya Barrister Umar yayi yana cewa.

” Zuwan nasu ya baka mamaki ko? Sunzo da gaske yanzu haka suna falon baƙi na Daddy.”

Tollet Mustafa ya nufa yana cewa Habeeb

” kaci Albarkacin su da babu wanda ya isa ya fitar dani daga cikin ɗakin nan duk nacin mutum.”

Girgiza kansa Habeeb yayi tare da cewa.

” Gani nayi danni suka zo tunda nine na gayyace su ba kaiba, kuma zuwa ɗaurin aure dole mutum yaje duk iskancin miskilancin mutum.”

Murmurshi kawai Mustafa yayi ya shige tollet, cikin 50 minute Mustafa ya shirya, wow yayi mungun kyau kuwa cikin fararen shaddar, gashi kuwa ya kifa hula zanna idan ka gansa saika rantse da Allah yana son Auren nan kuwa zuwan abokanan nasa ne yasa shi wannan shirin tare suka fita Habeeb yana zungurin Mustafa cikin tsokana, murmurshi kawai Mustafa yake yiwa Habeeb domin kuwa yau yasan Habeeb yana cike dashi ne, wajen su Daddy suka fara nufa suka gaishe shi tare da abokanan harkokin sa, kafin suka wuce wajen abokanan nasu.

Isar su wajen sun tarar su zaune sai faman hira suke da Sallama suka shiga Habeeb yana cewa.

” Barkan ku da zuwa ashe dai za’a Hallaci bikin namu.”

Dariya Inspector Muhammad yayi yana cewa.

” Mun Hallaci wannan bikin ne dan kai badan wannan Sarkin miskilancin ba, daya kasa gayyatar mu.”

Murmurshi kawai Mustafa Yayi tare da zama yana cewa.

” Bafa Aure na kuka zo ba auren Habeeb kuka zo domin kuwa shine wanda zaiyi Aure ba niba.”

Sai a lokacin inspector khabeer yayi Magana yana cewa.

” Ayya yaro daina cika mana baki sanda zakuyi ƙumus a ɗaki kaida RAUDA waya sani, bare kuma gashi Allah ya ɗaura maka jarabar Mata, kunga kuwa kura taga nama ai kuma sai kai hari, ansamu Abunda ake nema har cikin gida.”

Gabaki ɗayan su dariya sukayi Naseer yace.

” Jarababbe ko kuma jarabbabu kai ɗin ma khabeer baya ne, ko dan kai yanzu ka haɗa mata biyu abun yazo maka da sauƙi, bari dai nayi shuru karka ce zan maka gori.”

Sosai Mustafa yake dariya yace.

” Wow Doctor Naseer daɗi na da kai badai faɗan gaskiya ba, kuma dai alhamdulillah duk jarabata bana neman matan banza ko?”

Murmurshi khabeer yayi tare da cewa.

” Kaima da kace, yanzu kuma an wuce wajen sannan kuma duka mata na babu matar tushe duk nice na zaɓosu da kaina.”

Murmushi Habeeb yayi yana Duban Conel Ubaidullahi Kafin yace.

” Ganan ɗan uwan ɗayan ai Uban miskilancin tsiya, ana magana kayi shuru, halin naku ai ɗaya ne, gaka har yanzu shuru ka kasa fitar da matar aure Allah yasa kaima Momy ta maka Auren dole Irin na abokin tsiyar taka.”

Hararar Habeeb Ubaidullahi yayi yace.

” So what kai Auren haɗi yake ɗagawa hankali, an gaya maka dan ammin Auren dole sai ya dameni, wlh ko a jiki na, sai naga dama na kalleta, bare har ta dameni.”

Dariya Habeeb yayi tare da cewa.

” Ƙaryar banza kawai, ku tashi mu tafi kunga 10:45 saura 15 minute so ku tashi muje.”

Tashi sukayi suna raha har wajen ɗaurin Auren, Allahu Akbar alƙawarin Allah ya cika inda Mlm Musa mahaifin Indo da yazo ɗaurin Auren Daddy ya wakilta shi daya amshi Auren ƴaƴan nasa, cikin ƙanƙanin lokaci aka ɗaura Auren Muhammad Mustafa Haroun da RAUDA Ahmad muktar akan sadaki dubu hamsin wanda Daddy shine ya biya musu sadakin, bayan an ɗaura nasu ne aka zo aka ɗaura na Muhammad Habeeb da Hasana Yusuf (Hasina) suma akan sadaki dubu hamsin, cikin murna da farin ciki jama’a ke musabaha dasu suna musu murna, a wannan lokacin bazaka taɓa gane halin da Mustafa yake ciki ba farin ciki ko baƙin ciki, Habeeb kuwa sai washe baki yake yana murna.

Malam musa har gidan Aunty Hindu yaje ya mata murna suka gaisa da Indo sun daɗe suna hira kafin Mlm Musa ya koma, da saƙon Indo na cewa ya gaishe da Ya Tanimu da Mama.

Guɗar Gambo shine ya tabbatarwa da mutanen gidan an ɗaura Auren Mamy itama guɗar ta ɗauka tana murnar cikan burin ƴarta, da kuma nasarar da tayi na cin maganin da Momy tayi, dama an riga da anyi jere tun jiya.

Camma gidan su Hasina ƴan uwa sai taya ta murna suke, Indo kuwa sai shiga take cikin kaya tana fita, zarah ma tazo zata kwana washe gari ta koma, Abba mahaifin Hasina da Aunty Hindu sosai suka yiwa ƴar tasu nasiha game da rayuwar Aure, haka ƴan uwa da abokanan Arziki ma, Hasina tasha kuka sosai, kafin da yamma akazo aka ɗauke su zuwa gidan Momy, an riga kai RAUDA kafin HASINA, a ɗakin su da suke kwana sanda suke gidan aka ajiye su, da nufin bayan an watse su koma ɗakin su, Da daddare misalin ƙarfe tara aka fara shirye-shiryen zuwa wajen dener sosai ake haɗa amaren wajen kwalliya, Bayan mai kwalliyar ta gama musu ne Hasina tace ta yiwa Indo, sosai matar ta yiwa Indo makeup, Wannan karon ma baƙar doguwar riga mai ɗauke da fararen Stone, Indo ta saka dake tana mungun son dogin rigunan, matar yanewa Indo kanta tayi da mayafin rigar, sosai tayi wani mungun kyau.

” Kaga Mlm dan Allah ka shirya mu tafi kaga fa dare yana yi, kuma wajen yana can cike da mutane mune ake jira, dan Allah kayi hkr ka tashi ka shirya mu tafi, karka nunawa duniya cewa baka son zaɓin mahaifiyarka Idan kayi haka Momy ka tozarta ba RAUDA ba, domin kuwa duniya zata ɗauka cewa babu girmamawa tsakanin mu da mahaifiyar mu, pls dan girman Allah badan niba ka shirya mu samu mu wuce.”

” Kaga Habeeb kaje kawai babu Inda ni zanje, ai biyayya kam na yita tunda harna yarda aka ɗaura Auren, to dan banje dener ba sai me, ai tun wuri na sanar dakai cewa bazanje ba, kaga ka tafi kar dare ya maka, ka ƙyale ni karka samin ciwon kai.”

Habeeb ƙin tafiya yayi ya tsaya yiwa Mustafa magiya, da ƙyar da suɗin goshi Mustafa ya yadda zaije kafin ya tashi ya shirya.

Zarah ce take cewa Indo.

” Wai A’isha wata motar zamu shiga ne kam, tun ɗazu muna tsaye anan ya kamata ace mun tafi wajen dener nan koh.”

” Gacar Mota muje mu shiga naga yanzu kamma kamar saura su Aunty Hasina, idan wannan motar ta tafi muje kawai mu shiga wannan ɗin.”

Ita ɗin kuwa suka shiga suka wuce wajen dener, Indo basu shiga cikin hole ɗin ba, suka tsaya a waje, sun juma sosai zaune kafin motar amaren ta shigo hole ɗin, kiɗa aka sake, tare da sauƙe musu wani red ɗin capet tun daga bakin hole ɗin har wajen motar tasu, Habeeb yana riƙe da hanun Hasina suka fito, shiko Mustafa yafi 20minute daga cikin motar ya ƙarewa RAUDA kallo wacce taci kwalliya cikin wani green ɗin less, kanta na sunkuye, taɓe baki Mustafa Yayi tare da damƙo hanunta cikin salon mugunta yana murza jijiyar hanun, runtse idonta RAUDA tayi cikin azaba, murmurshin gefen baki yayi tare da cewa.

” Ina tayaki murnar kawo kanki da kikayi cikin maƙabarta, gaskiya na jinjinawa ƙoƙarin ki na ganin kin dage sai da kika *AURENI DOLE* sai dai ina ƙara tuna miki cewa karki manta da maganar da na miki cikin makaranta” yana gama faɗin haka ya jawo hanun nata yana murmurshi a yanda suka fito zaka rantse da Allah suna Soyayya, tsabar bariki irin na Mustafa, sanda suka gama shiga kafin su Indo suma suka shiga, sosai wajen ya tsaru da decoretions kayan ciye-ciye da Shaye-Shaye kuwa kala-kala a wajen, babu abunda yake tashi a wajen sai sautin kiɗa, kafin aka fara gabatar da dener, Barrister Umar tunda ya hango Indo yaji wani Soyayyar ta ta tsarga masa cikin zuciyarsa, komai yake hankalin sa yana kanta, ai kuwa sai kace wacce akace Mustafa ya ɗago kansa carap ya hango Indo, da farko bai gane ta ba, saida ya ƙara tsura mata Ido Kafin ya gane Indo ce, tayi wani bala’in kyau lokaci ɗaya yaga ta dawo masa cikakkiyar budurwa, ga ƙirjinta ma masha Allah wani bugawa Zuciyar Mustafa Yayi da ƙarfi wani irin baƙon yanayi yaji a jikin sa tun daga babbar yatsar ƙafarsa har zuwa cikin ƙwaƙwalwar sa, saurin dafe ƙirjin sa yayi yana cigaba da kallon ta, haka shima Habeeb duk abunda ake hankalin sa, yana kan Indo ya kasa ɗauke idanunsa a kanta, ita kuwa Indo duk abunda suke sam bata san suna yiba, zancen su kawai suke da zarah suna dariya, jin an sanja salon kiɗa, mai sautin waƙar da Hamisu bireka yayi wai taken son dangin mutuwa, da sauri Indo ta ɗago kanta tana duban inda sautin ke fitowa domin kuwa tana mungun son waƙar, ai kuwa tashi Indo Tayi ta shiga tsakiyar taron ta ɓalle da rawa sosai Indo take rawar jin salon waƙar yana tsumata, komai na jikinta juyawa yake, ga shi Allah ya azurta Indo da hips, aikuwa mazan dake wajen kamar wanda suke jira suka rufu kanta suna sake mata kari, dam dam! Zuciyar Mustafa take harbawa wani irin ɗaci yake ji cikin Ransa ganin yanda wasu ƙatti suka rufu kanta suke mata kari, Habeeb kuwa wani irin zafi shima yaji cikin zuciyarsa tare da mungun jin haushin Indo na Wannan rawar da take wasu ƙattin banza su ruhu kanta, yunƙura Habeeb yayi da niyar zuwa ya janye Indo daga wajen, amma ina kafin ya tashi tuni Mustafa ya rigasu, ita kuwa ko a jikinta idanunta sun rufe rawa kawai take, taji an danƙi hanunta da ƙarfi, da sauri ta tsaya da rawar tana duban Mustafa idanunsa sunyi jawur gwanin ban tsoro, kowa dake wajen shuru yayi yana ƙare musu kallo, ganin yanda fuskar ango ta sauya lokaci ɗaya, itama RAUDA kallon ikon Allah take, da ƙarfi ya fisge ta, yayi waje da ita tana tirjewa amma ina sanda ya fita da ita, saurin tashi Habeeb yayi zaibi Bayan su Hasina tayi saurin riƙe hanunsa tana girgiza masa kai ƙwace hanunsa Habeeb yayi yabi bayan su cikin sauri….

Wayyo Allah fan’s ku fa yi hkr dani na rashin samun typing akai-akai ina da uzuri da yawa, kunsan bana typing asabar amma wlh yau haka na dage na muku, saboda na kwana biyu banyi typing ba, kuyi hkr da typing error ban samu nayi editing ba typing ɗin sauri nayi🙏🏻.

*Vote*

*Share*

*And*

*Comments*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah ce)*[3/10, 3:04 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*

*Nasmah ko Nasirah*

*Sara da Sassaka*

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.

Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya 🙏🏻

Gaskiya fan’s I love you Lodi-Lodi da alamun dai page ɗin jiya ya muku sweet yanda naga kuna ɓarin ruwan sharhi daga ko wani groups gaskiya kun matuƙar burgeni😘

*بسم الله الرحمن الرحيم*

____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

*P*••••••6️⃣7️⃣ ➡️ 6️⃣8️⃣

Mota Mustafa ya buɗe tare da wurga Indo ciki ya rufe ƙofar da ƙarfi kafin ya zaga ya buɗe gaba ya shiga, ya tada motar da ƙarfin gaske cikin tashin hankali Indo ke kallon Mustafa tunda taga Mustafa yana mata wannan jan cikin haɗa rai to tabbas yau baƙar muguntar sa kanta ya sauƙa, cikin ranta take cewa ( yau kuma kaina zai sauƙe hashin Auren dolen da Momy ta masa, wayyo Allah na mungu zaici zalina ) shiko jan motar kawai yake baya ko kallon gaban sa yanda ransa yakai matuƙa wajen ɓaci, Habeeb daya fito da sauri ne, yaga Mustafa ya ja motar harya fice daga cikin hole ɗin, kama kansa Habeeb yayi tare da jan dogon tsaki, tunani ya fara na yabisu ne kokuwa ya dakata har a gama dener, wata zuciya ce tace masa (karka bita ka tsaya wajen dener karkuyi abun kunya babu kai babu Mustafa, Idan kunyi haka duniya zata zage ku) komawa ciki Habeeb yayi amma duk hankalin sa ya tafi garesu.

Cikin hole ɗin kuwa RAUDA sai raba Ido take taga ta inda Mustafa zai iso shuru-shuru babu Mustafa sai ma ganin Habeeb da tayi ya shigo hole ɗin, shi kaɗai, ga baki ɗaya hole ɗin ya birkice da kananun magana kowa yana tofa albarkacin bakinsa akan Mustafa da Indo wasu suce sonta yake wasu kuma suce babu wata soyayya kawai ƙanwar sa ne, shiyasa baiji daɗin rawar da tayi ba, wasu kuma suce Masha Allah yarinyar ta burgeni wlh dubi yanda take rawar nan fa kamar na sace ta na gudu wannan zata dace da zama jarumar Film, shima Barrister Umar hankalin sa ya tashi ganin kamar alamar Mustafa kishin Indo yake, kasa zama yayi cikin hole ɗin ya zille ya gudu gida cikin matsanancin ƙaunar Indo, duban Habeeb da ransa ke ɓace RAUDA tayi tace.

” Ya Habeeb ina ya Mustafa yake? Ta tambaye sa cikin sanyin jiki Zuciyarta sam babu daɗi.

Habeeb ma da ransa ke ɓace a taƙaice yace mata.

” Ya koma gida.”

Dam ƙirjin RAUDA ya buga, Hasina kuwa zaro ido tayi waje kusan tare suka ce.

” Ya Habeeb gida kuma yanzu? Bayan ba’a gama dener ba.”

Cikin gajiya da tambayan tasu gashi kuma ransa yana ɓace a hasale yace.

” Ehh! Abunda kuka ji nace dan Allah ku ƙyale ni.”

Cikowa idanun RAUDA yayi da hawaye sai yanzu ta fara gaskata Maganar Mustafa wato da gaske yake wulaƙanta rayuwar ta zaiyi, tabbas ko yanzu ya wulaƙanta ta, tunda har ya iya tafiyar sa gida tun kafin a tashi daga dener ya wulaƙanta ta a gaban ƙawayenta da ƴan uwan ta, da ta gayyata wajen, me zata ce musu indan sun tambaye ta, ina Mustafa ya tafi, ita har ga Allah bata kawo komai tsakanin Indo da Mustafa ba, domin tasan babu shiri a tsakanin su bare tace yabi mace, dafe kanta tayi tana ambaton Allah cikin ranta dake mata ƙuna tana hangen wacce irin rayuwar aure za suyi da shi, a fili tace “Allah ka kawo min ɗauki cikin lamari na” kafin ta tashi tana layi zata fice daga hole ɗin, tashin da tayi shine ya fara jawo hankalin mutanen dake hole ɗin, lura da hakan da Habeeb yayi ne, yasa shi saurin tashi ya tare ta yana cewa koma ki Zauna.

Zama tayi tana kallon Habeeb idanunta na ƙoƙarin zubar da hawaye, taji Muryar Habeeb ƙasa-ƙasa yanda babu mai jinsa sai ita yana cewa.

” Kiyi hkr ki zauna a ƙarasa dener nan pls kar muyi abun kunya cikin hole ɗin nan kina son muji kunya ne, na rantse da Allah da nasan Mustafa zai mana wannan abun kunyar Wlh da banyi tunanin fara wannan dener ba, nima kaina daure zuciyata nake domin ji nake kamar zata faso ƙirji na, pls sorry ki zauna har a gama denern nan.”

Cikin rawar murya RAUDA tace.

” Abun kunya kam ai an riga da an yisa idan na Zauna ina zan cewa mutane miji na yaje, ko yanzu ya nunawa duniya cewa bana gabansa babu amfani zama na a wajen nan ka barni na tafi kawai babu wani abun kunya daya saura wanda baiyi shiba.”

” Ki zauna nace babu ruwanki da Abunda mutane zasu ce, ni nasan Abunda zan faɗa musu.”

” Amma ya Habeeb……..”

Ɗaga mata hanu Habeeb yayi yace.

” Please ya isa haka maganar na baki Hkr idan idan kuma bazaki iya zama ba, ga hanya jeki sai ku bawa duniyar ƙofar zagin namu da tushe.”

Komawa RAUDA tayi ta zauna tana jin wani baƙin ciki cikin zuciyarta tare da danasanin zuwa wannan dener, Habeeb kuwa zuwa yayi ya karɓi speaker ya sanar cewa, Mustafa bazai samu dawowa ba a masa afuwa sakamakon kanshi dake ciwo, haka kawai ya faɗa yayi shuru tare da komawa ya zauna, yawanci babu wanda ya yarda da maganar Habeeb tunda a idanunsu mustafa ya fice da Indo, haka denern ya kasance wani iri, sanda aka kira ango da amarya Habeeb umurtar RAUDA yayi da ta fito, tare ya watsa musu kari duk abinda zai yiwa Hasina ya yiwa RAUDA duk dan ya rage mata damuwa hakanne kuwa ya ragewa RAUDA raɗaɗin Mustafa cikin ranta, sosai Sharifa ma ta zuba musu kuɗi ranta babu daɗi akan Abunda yayan nata Mustafa Yayi, shi kuwa da yake can gida Zaune Barrister Umar Indo ta tafi da zuciyarsa, ya kuma sawa ransa cewa saiya nemo Soyayyar ta, haka aka tashi denern badan yayi daɗi ba.

Hon! Hon! Hon! Hon! Mustafa yake ta dannawa, a ƙofar Estate ɗin nasu, da sauri mai gadi ya buɗe masa, danno hancin motar yayi, ba tare daya dai-dai ta parking ba, ya tsaya ya fito tare buɗe gidan gaba, ya finciko Indo da ƙarfi, yana jan hanunta binsa kawai Indo take kamar raƙumi da akala domin tasan yau ta shiga uku hanun Mustafa, duk da babu abunda ta masa tana ganin zaluncin sa ne kawai ya juyo kanta, babu kowa cikin falon duk sunyi bacci wasu kuma suna can wajen dener kasancewar dare yayi kusan 12pm ɗakin sa Mustafa Yayi da ita tare da wurgi da ita tsakiyar ɗakin faɗuwa Indo tayi tare da bige kanta jikin mirror, riƙe kanta tayi tare da bin Mustafa da kallon tsana, komawa yayi ya sawa ɗakin key sannan ya dawo wajen dressing mirrom su ya buɗe kuɗi ne masu shegen yawa ya ɗebo tare da watsawa Indo a jiki yana cewa.

” Gasu nan domin ina da tabbacin sune suka shigar dake filin rawar, to gasu basai kin saida jikinki ba kafin ki samu, wai kema kin girma ko kinga kin fara ajiye nono da hips shine bari ki fara neman kuɗi da jikin ki, bari ki fara tallen su shine za’a san kin girma, shidai ɗan ƙauye har abada baya taɓa hankali” ya ƙarasa maganar yana take mata yatsun kafar ta tare da mitsikkesu a tayels, wani irin ƙarar Azaba Indo tasa tana ƙarewa kuɗin kallo tare da mummunan tsanar da tayiwa mai su cikin sakewar zuciya take cewa.

” Allah ya sauwaƙa na saida jiki na don kuɗi, wlh nafi ƙarfin haka domin ni kuɗi basa gaba na tunda babu abunda aka rageni da shi ana biya min dukkan buƙatu na, da kake cewa ƴan ƙauye basu da hankali, ai bani kaɗai bace Yar ƙauyen cikin gidan ashe sauran ma kenan basu da hankali Kuma wlh Allah ya isa ban………..”

Bata ƙarasa ba Mustafa ya shaƙo wuyan ta ya haɗa ta da gini ya matseta wanda har tana iya jiyo sautin numfashinsa yanda jikin su ya haɗu cikin ɗaga murya yake cewa.

” Faɗa min waye sauran ƴan ƙauyen faɗi nace kafin na illata ki cikin gidan nan, wato Daddy ya baki kinci kin ƙoshi ai dole ki fara zagin sa.” Yana murɗe bakinta da ƙarfi.

Cikin azaba Indo ta fisge hanunta daga bakin ta tana masa wani mungun kallo tama kasa tanka masa domin kuwa yanzu ya kawota wuya, tasan tana buɗe bakinta zata iya zagin Mustafa gara kawai tayi shuru ta barsa da Allah, Momy da tazo wucewa ne taji kamar magana ta cikin ɗakin su Mustafa yasa ta zuwa wajen ta tura ƙofar cikin Sa’a kuwa ta buɗu ashe sanda Mustafa yasa key ɗin ya manta bai murɗa ba, sake baki Momy tayi yanda taga Mustafa maƙale jikin Indo sun manne a bango cikin tsawa tace.

” Sannun ku munafukai nace sannun ku”

Saurin juyowa sukayi dukan su suna kallon Momy yayin da Mustafa Yayi saurin komawa gefe, yana sosa kansa cikin mamakin yanda Momy ta shigo ɗakin bayan yasa key, Indo kuwa ta kasa magana sai ma sunkuyar da kanta ƙasa da tayi, matsowa Momy tayi kusa dasu tare da ɗaga hanu ta wankawa Indo mari tana nunata da yatsa bakinta har ɓari yake take cewa.

” Daman ai biri yayi kama da mutum shegiya munafuka jarababbiya, ai wannan uban nono da kika tara a ƙirjinki lokaci ɗaya da alamar tambaya da waɗannan shegun masaka-masakan ɗuwawu da kika haɗa, ashe maza ake bi, wato duk na wajen basu isheki ba, har sai kinzo zaki lalata min ɗa ko baƙar munafuka.”

Wannan ne karo na farko da Indo taji ta fara tsanar Momy wani irin baƙin ciki tare munguwar tsanar Mustafa take ji cikin ranta domin kuwa koma me Momy zata gaya mata shine ya jawo mata, wasu hawaye ne masa zafin gaske suke tsere saman fuskar Indo, Inna ce kawai ta faɗo cikin ranta domin kuwa tasan da tana nan babu mai ci mata mutunci, shima kansa Mustafa yaji mungun haushin maganganun Momy mussaman ma da take kiran cewa Indo tana bin maza ya tabbata da kowa zaiyi shaidar cewa Indo tana bin maza, shi kuwa zai iya tsayawa a ko ina ya ƙaryata wannan zargin domin yasan wacece Indo tun tana cikin zanin goyon ta, duk halin sai dai masifa da neman magana da kuma rashin jin magana, amma Banda dai neman maza kam tabbas wannan ba halinta bane, domin kuwa bata kula wasu maza ma bare kuma harta bisu da lalata, muryar Momy itace ta katsewa Mustafa tunanin sa ta hanyar cewa.

” Kai kuma shashashan banza mace tazo ta sakaka gaba ka fara biye mata za kuyi shashashan ci, to dan ubanka daga yau na raba ka da ita, kallon Indo Tayi tace, fice kibar ɗakin nan wacce ta kasa samun tarbiyya wajen iyayen ta.”

Da gudu Indo ta fice tana kuka mai tsuma Zuciya ta faɗa ɗakin su, shi kuwa Mustafa sai yanzu ya dubi Momy yace.

” Momy meyasa kikayi haka, Abunda kike tunani ba haka bane, Indo bata da laifi bata kuma neman mazan banza Momy laifi tamin nake………..”

Cikin tsawa Momy tace.

” Rufe min baki dan ubanka munafiki kaima, Uban meya dawo da kai daga wajen dener bayan su suna can babu wanda ya dawo idan ba jawo ka tayi kuzo ku tambaɗe ba, kai kuma gaka na mamajo shine ka biyota simi-simi kuka taho, kasan Allah ka fita harkar yarinyar nan kafin raina ya ɓaci da kai ka riƙe wannan yarinyar RAUDA itace matar ƙwarai ka fita harkar wannan ƙaramar karuwar.”

Runtse idonsa Mustafa Yayi yana jin Zafin maganganun Momy ya rantse da Allah da wani ne yau yake munanan waɗannan munanan maganganun akan indo wlh Allah ne kawai zai rabasa dashi, sai dai babu yanda ya iya da Momy, gefen ta yabi ya fice ba tare da yace komai ba, domin bazai iya tsayuwa yana sauraron maganganun Momy ba.

Fita itama Momy tayi tana mita, sosai Indo take kuka bata taɓa zaton tsanar da Momy ta mata yakai haka ba, wanda har zata mata ƙazafin zina Abunda bata taɓa kusanta ba, harsu Hasina suka dawo Indo tana cin kuka, zama Zarah tayi kusa da ita cikin tashin hankali tana tambayan Indo me mustafa ya mata amma Indo ta ƙi musu magana harta su Hasina sunyi sunyi Indo taƙi magana ga mutane cike cikin ɗakin ganin Indo bata da niyar shuru yasa Hasina kiran Habeeb a waya ta sanar dashi daman kuwa shima ya kasa zaune ya kasa tsaye na rashin sanin wani hali Indo take ciki, domin kuwa yasan mawuyacin abune su wanye lafiya da Mustafa tunda daman kanwarsu ba jiƙa take ba, cikin sauri ya ƙarasa cikin ɗakin daman ita RAUDA nata damuwar ya isheta tana gefe ko kallon Indo batayi ba, Habeeb duk yanda yaso Indo Tayi magana taƙi dole yasa ya ƙyaleta ya fita cikin tashin hankali, Habeeb ranar kasa runtsawa yayi yana tunanin halin da Indo take ciki sai yanzu ya fara fuskantar cewa son Indo yake, saurin dafe ƙirjin sa yayi yana cewa.

” Na shiga uku zuciyata baki min adalci da zaki kamo da Soyayyar Wanda nakewa kallon ƙanwar da muka fito ciki ɗaya wacce matata ta ɗauke ta ƴar uwa, Allah ka taimake ni karka ɗaura min abunda bazan iya ba, karka ɗaura min abunda zai zamo damuwa a gareni” haka Habeeb ya kwanta ba tare daya kalli Mustafa dake gefen sa ba domin kuwa yana jin mungun haushin sa.

Da gudu ta faɗo jikinsa tare da raɗa masa cikin sanyayyiyar Muryar ta mai daɗin sauraro cewa.

” Sweet heart yau nayi let ɗin shigowa ɗakin nan ko, sorry na tsaya rarrashin Amra be, har tayi bacci kafin nazo ga Daddyn ta” tura sa tayi suka faɗa saman bed ɗin haɗe bakinsu tayi waje ɗaya tana masa wani irin hot kiss hanunta kuwa yana bisa marar sa sosai suke neman ruɗa junansu da salon nasu, juyawa yayi da ita ta koma ƙasa ya dawo saman ta, bakin sa ya manna a Breast ɗinta yana musu wani irin tsotsa hanunsa na murza nipple ɗinta babu abunda yake sai nishi da sambatu yana cewa.

” Karki barni A’ishat idan kika barni mutuwa zanyi Wlh ina……..”

Ɗaka masa duka da Habeeb yayi wanda ya damesa da uban nishi shine ya katsewa Mustafa mafarkin da yake, saurin tashi Mustafa Yayi ya zauna ya haɗa Uban gumi riƙe kansa Mustafa Yayi cikin tashin hankali, A fili ya furta

“meke shirin faruwa dani karde ace son yarinyar nan nake, banta wannan mafarkin da ko wata mace ba sai ita, meyasa zata ziyarci mafarki na, *YA ALLAH*”

Habeeb dake gefen sane yace.

” Wacce yarinyar kake magana, wacce har kayi mafarkin kana saduwa da ita?”

____________________________

Tirƙashi lallai da akwai Magana a gaba, ko wacce Irin amsa Mustafa zai bawa Habeeb shin ya zaman RAUDA zai kasance a gidan Mustafa, shin zaman lafiya zai ɗaure tsakanin Habeeb Hasina da Indo tunda gadai Habeeb kamar yana son Indo, wannan shi ake kira ana wata ga wata kenan, ku cigaba da biyoni domin jin yanda zata kasance.

Kuyi hkr da typing error banyi editing ba🙏🏻

*Vote*

*Share*

*And*

*Comments*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah ce)*

[3/11, 10:45 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*

*Nasmah ko Nasirah*

*Sara da Sassaka*

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.

Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya 🙏🏻

😄😄😄 Sai tambaya ake min kan cewa Aunty Hauwa (Maman Uswan) da Aunty FAUZA ƴar Amanar kainuwa uwa mabada Mama, meye ɗina ne😄.

To bari na baku amsar ku👇🏻

To gaskiya duk cikin media sune wanda zan bigi ƙirji nace ina ji dasu yayuna ne kuma aminai nane, sune waɗanda sukafi kowa kula da lamurana cikin media, domin kuwa ina Ƙaunar su tamkar yadda nake ƙaunar ƴan uwana na jini.

_*sis Munaya And sis Maryam ina mungun ƙaunar ku kamar yadda kuke ƙaunata ana mungun tare🤝🏻❤*_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

_*P*••••_ 6️⃣9️⃣ ➡️ 7️⃣0️⃣

Dafe kansa Mustafa Yayi yana jinjina wannan mafarkin da yayi, dole ma sai yayi wankan tsarki, Habeeb ganin Mustafa baida niyar basa amsa ya sashi ƙara maimaita masa tambayar, dubansa Mustafa Yayi kafin yace.

“Bani da amsar tambayar ka Mlm, tunda kaga nayi shuru ban baka amsa ba ai sai ka ƙyale maganar ko kai ka cika yawan ƙwaƙƙwafi”

Taɓe bakin sa Habeeb yayi cikin nuna halin ko inkula yake cewa.

” Baza dai ka bayar ba kawai zakace, idan ma mafarkin RAUDA kayi ai sai kayi hkr gobe warhaka kuna nan tare gado ɗaya Sarkin ƴan jarabar tsiya wlh har tausayin RAUDA nake yi😄.”

Tsuka mai ƙarfi mustafa yaja tare da tashi ya shige tollet tsabar haushin maganar Habeeb yasa bai tanka sa ba, murmurshi Habeeb yayi ya koma ya kwanta yana tunanin Indo, ko tayi bacci ta daina kukan ko har yanzu tana kukan, wayarsa ya ɗaga tare da dannawa Hasina kira, dan gaskiya bazai iya bacci ba sai yasan halin da Indo take ciki, cikin bacci Hasina taji wayanta yana ringine buɗe idanunta tayi ta ɗauki wayar My Sweet ta gani rubuce saman screen ɗin wayar ɗagawa tayi tana mamakin kiransa cikin wannan tsohon dare, ɗagawa tayi tare da Sallama, yana amsa sallamar yace

” ina Indo, Allah dai yasa ta daina kukan tayi bacci?”

Shuru Hasina tayi tana jinjinawa irin tausayin da Habeeb yake yiwa Indo duban Indo Tayi da take manne jikin Zarah taci kuka harta gaji bacci ya ɗauke ta, sannan ta mayar da hankalin ta kan wayar tace mishi.

” Tayi shuru tun ɗazu tayi bacci saika kwantar da hankalinka ka kwanta kayi bacci”

Murmushi Habeeb yayi tare da cewa.

” Da ɗin hankali na a tashe yake aka ce miki” ya faɗa mata yana dariya.

Murmurshin itama tayi tace.

” Gashi kuwa alamun ka ya nuna hakan RAUDA ne dai har yanzu ba tayi bacci ba ta sawa kanta tunani”

Girgiza kansa Habeeb yayi yana tausayin RAUDA domin kuwa dole sai tayi hkrn rayuwa da Mustafa.

” Kinga Sweet heart dan Allah ki rarrasheta tayi hkr ta kwanta ta cirewa kanta damuwa, daman tasan dole ne saita fiskanci ƙalubale akan rayuwar aurenta da Mustafa so ki bata hkr ta kwanta dare yayi.”

” Shikenan zan gwada sai da safe”

“Allah ya tashe mu lfy” Habeeb ya furta yana kashe wayan sai yanzu hankalin sa ya kwanta jin ance Indo tayi shiru har tayi bacci kwanciya shima yayi yana jan bargo cikin nishaɗi, Mustafa kuwa bayan yayi wankan tsarki ne ya dawo ya kwanta tare da rufe idanunsa saurin buɗe idon yayi domin kuwa yana rufe idon nasa hoton Indo yake gani tsaye gabansa tana murmurshi, ƙara rufe idon nasa yayi still dai Indo ce yake gani, wani irin dogon tsaki yaja tare da tashi ya zauna tsakiyar gadon yana riƙe da kansa, kusan wannan daren zance Mustafa baiyi bacci ba, haka ya ƙaresa cikin tunanin Indo domin kuwa itace ta kwana tana yawo cikin ƙwaƙwalwar sa.

Washe gari da safe Indo ta watstsake ta farka bata tashi cikin wata damuwa ba duk da dai Abunda Momy da Mustafa suka mata yana zaune dam cikin ranta bata kuma yadda ta haɗu da Momy Mustafa Habeeb ba, ta kama hanun Zarah suka gudu driver ya kaisu gidan Aunty Hindu, da yamma kuwa akazo aka ɗauki zarah zuwa gidan gwamnati, sanda Habeeb yake jajen Indo ne Hasina ta sanar dashi cewa ta koma gida tunda safe, Habeeb yaji haushin komawar Indo ba tare daya sata cikin idanunsa ba, da daddare Daddy gaba ɗaya ya haɗa iyalan nasa yana musu faɗa game da rayuwar Aure sanda Daddy ya gama musu faɗa sannan Momy tayi nata, a ƙarshe suka sa musu albarka kafin kowa ya shige da matarsa cikin gidan sa, part ɗin nasu yayi mungun kyau ita RAUDA komai Ash color suka samata cikin gidan nata, ita kuma Hasina suka sa mata pink and purple color.

Habeeb ne dake zaune da matar sa ya furta.

” Alhamdulillah yau rana ce mai matukar muhimmanci a cikin rayuwata, ranar da Allah yasa na ganki cikin gidana a matsayin matar Aure”

Murmushi ɗauke bakin Hasina tace.

” Tabbas Allah shine abun godiya daya haɗa masoya biyu a ƙarƙashin inuwar Aure ɗaya waɗanda suka juma suna ƙaunar junansu, ina roƙon ubangina daya bani ikon maka biyayya har ƙarshen rayuwata, bana fatan Allah ya nuna min ranar da zan saɓa maka”

Murmushi Habeeb yayi tare da cewa.

” Ameen ya Allah yanzu sai ki tashi muje muyi alwala muyi Sallah raka’a biyu mu godewa UBANGIJIN mu”

tashi Hasina tayi ta shige tollet ta ɗauro alwala kafin shima Habeeb ya shiga ya ɗauro tasa alwalar, sallah sukayi raka’a biyu kafin Habeeb ya kama goshin HASINA yana jero addu’a.

اللهم اني اسالك خير ها و خير ما جبلتها عليه و اعوذ بك من شرها و شرما جبلتها عليه.

Bayan ya gama Addu’ar ne ya mata wasu ƴan tambayoyi game da addinin ta, kuma Alhamdulillah HASINA ta amsa su, sosai Habeeb yayi farin cikin yanda HASINA tasan addinin ta sosai, shirin bacci sukayi suka kwanta, cikin dare Hasina taji kamar ana lalubarta a hankali ta buɗe idanunta, cikin dump light ɗin dake ɗakin taga Habeeb ne domin kuwa har yayi nasarar rabata da ƴar rigar dake jikinta, daren ranar Hasina tasha wuya Hanun Habeeb daman ance duk wayon amarya sai ango yasha romonta.

RAUDA kuwa tunda suka shigo cikin part ɗin nasu suka rabu da Mustafa domin kuwa a falo ya barta ya wuce bedroom ɗinsa, ba tare daya ko kalleta ba, zama RAUDA tayi falon tana jiran ko Mustafa zai shigo, har 12:00pm shuru babu labarin Mustafa, har bacci ne ya ɗan saceta tayi ta farka babu Mustafa, tashi tayi da niyar ta shiga bedroom ɗinna sa, har ta fara tafiya sai kuma tayi tunanin karta shiga ya mata wulaƙanci, baya ta dawo tare da neman nata bedroom ɗinta ta shige, Zama RAUDA tayi bakin gado tare da sakin wani marayan kuka, sosai take kukan domin kuwa baƙin ciki ne ya cika mata zuciya, wai ace yauce First night ɗinta, yazo mata cikin baƙin ciki, mijin da take so take ƙauna shine ya ɓata mata darenta na farko gidan miji, sosai RAUDA ke kuka tana baƙin cikin yanda wannan Ranar data daɗe tana jira yazo mata a haka, tabbas bacci ɓarawo ne, amma wannan daren baiyi nasarar sace RAUDA ba, kwana tayi tana shan kuka.

Shi kuwa Mustafa yama manta da wata halitta RAUDA cikin gidan, yana shiga bedroom ɗin nasa tollet ya shige ya watsa ruwa daman babu wani abokin da suka gayyata ya rakosu, su kaɗansu suka taho da matan su, bayan ya shirya tsaf cikin shirin Bacci, ya jawo system ɗinsa, ya juma sosai akan system ɗin kafin ya kashe tare da turata gefe ya kwanta, yana kwanciya kuwa saiya Indo ta fara yawo cikin idanunsa tun daga rayuwar ta na ƙauye har zuwa yanzu shi kaɗai yake murmurshi tare da ƙanƙame filo yana juyi a fili ya furta cewa.

” Shatuu kina mungun kyau idan kina cikin firgici” mirginawa gefe yayi yana riƙe da filonsa a ƙirjinsa, ya cigaba da cewa, ” alhamdulillah bishiyata ta girma tunda harta fara fidda reshe, Burina ya cika na ganin Indo Tayi Hankali, sai kuma yanzu na sa miki ido game da ko wanni namiji, domin ke ɗin mallaka tace, tun ba yau ba, murmurshi mai sauti yayi yana tuno sanda ya kaiwa Inna ziyara randa zai dawo gudun da Indo take tana Cewa ” *ya Mustafa dan Allah karka tafi ban gaji da kallon ka ba, ya Mustafa kifiyar sonka ta sokeni* still dai murmurshin ya ƙara yi yana cewa, ” Abunda ya hanani sauraron ko wacce mace kenan duk da lalurar da nake tare da ita domin ni naki ne ke kaɗai ba tare da wata ba.”

Mustafa kwana yayi yana shauƙin Indo har mafarki yayi suna saduwa, sosai kuwa ya samu farin ciki cikin wannan bacci domin kuwa ta jiyar dashi daɗin da bai taɓa jiba cikin wannan mafarkin yayin da RAUDA kuwa ta kwana cikin baƙin ciki.

Washe gari da safe RAUDA tana idar da sallar asuba ta fara gyaran gidan ta, domin kuwa RAUDA fannin iya girki da tsafta gwanace a wannan fagen tas ta gyara gidan ta, kitchen ta shiga da niyar ɗaura girki taga gas ɗin ba’a ɗura mata gas ciki ba, gashi kuma electri ɗinta ba’a mata setting ba, dole yasa RAUDA dawowa falo ta zauna badan taso ba, Mustafa shine bai fito ba sai 11:00am cikin shirin aiki ya fito hanunsa riƙe da ƙaramar jakar aikin sa, tare da key ɗin motar sa, nocking sukaji anayi a ƙofar falon, Mustafa ƙofar ya nufa tare da buɗewa, Ishaq ne tsaye hanunsa riƙe basket na Abinci, waje Mustafa ya basa ya shige, sannan shima ya dawo falon, gaishe shi Ishaq yayi, Mustafa ya amsa yana dariya tare da cewa.

” Autan Momy ina Sharif ɗin na ganka kai ɗaya?”

Dariya Ishaq yayi tare da cewa.

” Tare muka zo yayi part ɗin ya Habeeb zai miƙa abinci nima yanzu zan tashi na shiga can ɗin kallon RAUDA yayi yace Aunty RAUDA ga Abinci inji Momy”

Murmushi RAUDA tayi ta karɓa tare da cewa.

” Ka cewa Momy mun gode, idan kaje ka gaishe min da sharifa.”

Da to Ishaq ya amsa tare da tashi ya fice daga part ɗin nasu, duban Mustafa RAUDA tayi tace.

” Sannu da fitowa, ina kwana”

A taƙaice ya amsa mata da cewa “lafiya” yana ƙoƙarin fita.

Ganin fita zaiyi yasa RAUDA cewa.

” Ya Mustafa ba kayi breakfast ba zaka fita”

Bai kalleta ba yace.

” Bana buƙata ko kinga na miki kama da wanda yake jin yunwa? Koko na taɓa buƙatar abinci daga wajen ki?

Girgiza masa kai RAUDA tayi alamar a’a, shima bai ƙara cewa komai ba ya fice.

RAUDA ba tayi ƙoƙarin dakatar da Mustafa ba daga fitar da zaiyi duk da bata ji daɗin fitar tasa ba, amma dole tayi shuru gudun kar tayi magana ya zageta.

Dafe kanta tayi hawaye na ƙoƙarin zubo mata tasa hanu ta goge tare da dafe kanta tana Addu’ar Allah ya kawo mata sauyi cikin rayuwar Auren ta, tana son mustafa Kuma insha Allah zata yi ƙoƙarin ganin ta dawo da hankalin mijinta gare ta da wannan tunanin RAUDA ta wuni.

Su kuwa Hasina Rayuwar su suke cikin farin ciki, da mutunta juna, suna matuƙar son junansu, Habeeb ya ɗauki hutun aiki harna tsawon sati biyu domin yaci amarcin sa, sai dai duk da wannan cin amarcin da Habeeb yake Indo tana maƙale cikin zuciyarsa, da ita yake kwana yake tashi haka kuma kullum yakan yawan damun Hasina da zancen Indo, bata kawo komai cikin ranta haka take biye masa.

A kwana a tashi babu wuya wajen ubangi yau satin su Mustafa biyu da Aure yayin da kuma RAUDA sam bata samun farin ciki, kullum cikin ɓacin rai take cikin gidan ko sau ɗaya kuwa Mustafa baiyi tunanin shiga ɗakin RAUDA ba, ma’ana babu wata alaƙar aure da ya taɓa shiga tsakanin su, suna Zaune ne kowa yana harkarsa cikin gidan, koda wasa kuwa RAUDA ta shiga zabgar Mustafa ranar ta shiga uku wuni zaiyi yana ci mata mutunci, haka RAUDA take zaman hkr cikin gidan bata kuma taɓa tunanin gayawa Mamy halinda take ciki ba

INDO kuwa yau baki har kunne, sun kammala zana jarabawar barin Secondary School, wato neco, cikin dariya Indo ta dubi Zarah tace.

” Bestie na har yanzu ba’a zo ɗauka ta ba, kawai ki wuce, dan gaskiya yau bazan biki ba, dole zan jira azo a ɗauke ni.”

Dariya Zarah tayi tace.

” Ai kuwa ni na tafi sai munyi waya kawai”

” Shikenan ki gaishe da momma sai nazo”

Zarah bata juma da tafiya ba Habeeb ya shigo cikin school ɗin, tun daga nesa ya hango ta tana tsaye ta harɗe hanun ta a ƙirji, har gabanta yaje yayi parking, buɗe motar yayi yana dariya, sai yanzu Indo ta lura da Habeeb domin bata ɗago kanta ba, bare taga waye yayi parking saida taji ƙamshin turarensa ne, sannan ta fahimci ya Habeeb ne, murmurshi tayi tare da cewa.

” Ango kasha ƙamshi kaine tafe.”

Murmushi Habeeb yayi tare da cewa.

” Ba kin manta da niba, tunda kika koma wajen AUNTY Hindu, shigo mu wuce.”

Shiga Indo tayi tana dariya tace.

” Ai ya Habeeb ko zan manta da kowa, bazan manta da kai cikin rayuwata ba, ya Habeeb ina Aunty Hasina tana lfy.”

” Ban sani ba, tunda kinƙi zuwa gidan mu, itama tayi fushi dake tunda akayi Auren nan baki taɓa zuwa wajen mu ba.”

Murmushi Indo tayi tace.

” Ya Habeeb bawai naƙi zuwa bane Allah banson naje ne Aunty Hasina tace saina je wurin Sarkin muguntar nan, Allah ya Habeeb na tsani ganin ya Mustafa, bana sonsa na tsane sa.”

Zaro ido Habeeb yayi sai kuma yayi murmurshi yana ɗago wata ƙaramar leda tare da cewa.

” kinga ni ba Wannan ba, hingo riƙe alƙawarin ki, tare da ciro wani ƙaramin gift ya buɗe, zobe ne mai kyauwun gaske anyi masa kwalliyar love cikin sa kuma anyi rubutu da *A&H* ya miƙa mata tare da mata umarni da ta saka, ƙarba tayi ta saka tana murna sannan ta buɗe ledar da ya bata, waya ce mai kyawun gaske ƴar dai-dai ƙirar infinix hot 8…………..

Ku ƙara hkr dani a kan hkr na rashin typing akai-akai da kuma typing error dan gaskiya kwana biyun nan Banda time ɗin editing.

*Vote*

*Share*

*And*

*Comments*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah ce)*

[3/15, 9:54 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*

*Nasmah ko Nasirah*

*Sara da Sassaka*

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.

Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*

____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

*P*••••••7️⃣1️⃣ ➡️ 7️⃣2️⃣

Sosai Indo take dariya tana murnar wayar da Habeeb ya bata domin kuwa tana mungun son waya, kallon Habeeb Indo tayi cikin dariya tace.

” Ya Habeeb na gode sosai Allah ya saka da Alkairi, ya Habeeb kamin abubuwan Alkairi da yawa cikin rayuwata, kaine mutum na farko daka fara kawo min haske cikin rayuwata, har abada bazan taɓa mantawa da Alkairin ka gare ni ba, ina roƙon ubangina daya bani ikon kyautata maka nima, duk da nasan bazan taɓa biyanka Abunda ka min ba.”

Sosai Habeeb yaji daɗin yanda Indo tayi farin ciki da wannan kyautar daya mata, murmurshi yayi cikin jin daɗin ganin farin ciki kwance fuskar ta yace.

” Karki ƙara min godiya danna miki wani abu, haƙƙi ne a kaina na miki, nidai fatana karki taɓa cire wannan zoben daga hanunki domin kuwa yana da matukar muhimmanci a rayuwata, ke bazaki gane muhimmancin saba sai nan gaba kaɗan, kimin alƙawarin cewa duk sanda na sanar dake manufata ta baki wannan zoben zaki amshi buƙatata kimin alƙawarin cewa bazaki kula ko wani Namiji ba da sunan SOYAYYA”

Dam! Dam! Dam! Gaban Indo ya buga domin kuwa ita yanzu ba yarinya bace da zata kasa gane manufar wannan maganar da Habeeb ke mata tabbas idan ta fahimce sa dai-dai ya Habeeb yana sonta, innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un ta maimaita cikin zuciyarta domin kuwa tabbas zargin ta idan ya kasance gaskiya to da wani Ido zata kalli Aunty Hasina, wata Zuciyar ce tace mata, ina bama haka bane ya Habeeb bazai taɓa sonki ba, kawai ya Habeeb yana son yaga kin mayar da hankali ki akan karatun kine shiyasa yace karki kula ko wani Namiji, nasan ya Habeeb bazai taɓa sona ba, domin ni ɗin ba ajinsa bane ƴar ƙauye wacce ta fito cikin ƙauyen ƙayau, bazai taɓa sona ba, kawai so yake yaga rayuwata ta inganta, har yanzu idonta bai gane mata irin zoben daya bata shima akwai a nasa hanun ba, Habeeb ne ya katse mata tunanin ta da cewa.

” Kinyi shiru ƙanwata, baki bani amsa ba.”

Rasa me zata cemasa tayi, domin kuwa tana mungun jin kunyar ƙin yarda da buƙatar sa, tana kuma tsoron ta amincewa bukatar sa ya zamo mata matsala daga baya, wani dabara ne ya faɗo mata cikin ranta, kafin tace masa.

” Ya Habeeb Babu kyau ɗaukar alƙawari saboda kar wata rana a samu matsala mutum ya kuskurewa wani abu guda ɗaya daga ciki, kaga sai Allah ya kama mutum da wannan alkawarin, domin shi alkawari ba abun wasa bane abune mai girman gaske, *ya Habeeb insha Allah zan kiyaye wannan dokar taka, zan kiyaye sosai amma sai dai ban ɗauki alƙawari ba, zan dai ga nayi ƙoƙarin kiyayewa*.”

Ajiyar Zuciya Habeeb ya sauƙe sai yanzu ya ƙara tabbatar da cewa Indo tayi Hankali ba Indon da ya sani bane a baya, sai yanzu ya gane cewa Indo tasan addinin ta yanda ya kamata, tabbas yaji daɗin yanda ta masa bayani kuma ya fahimce ta, duban ta yayi cikin murmurshi yace.

‘ shikenan Allah ya baki ikon kiyayewa.”

” Ameen ya Habeeb na gode sosai.”

Sun ɗan juma suna hira kafin Indo ta shiga cikin gida shi kuma Habeeb ya wuce.

Daf da zata shiga ɗaki taji Muryar Aunty Hindu tana cewa

” Ke Nana ( dake haka take kiran ta dashi) ina kika juma haka, lokacin tashin ku harya wuce, driver taje school ɗin bai ganki ba kinsa Hankalin mu ya tashi nida Abban ku?”

” Ummi ya Habeeb ne ya ɗauko Ni, mun jima dashi a compaunt ɗin gidan nan, ina ga saɓani mukayi da driver Kuma shima drivern ai na jirasa baizo ba har ya Habeeb yazo.”

” Okey to maza haura ki samu ki cire uniform ɗin, kizo kici abinci, Abban ku tun ɗazu yake jiranki yana sama kije ki sanar dashi kin dawo .”

Tana dariya tace.

” Yanzu kuwa Momy daman Nima ina son ganin Abba zan nuna masa wani abu.”

Murmushi Aunty Hindu tayi tace.

” Zaki nuna masa wani ko zaki karɓi kuɗin shopping ƙarshen wata yayi kayan makeup Yayi Low.”

Dariya Indo tayi ta shige bedroom ɗinta da gudu tana cewa ” Ammi babu ruwan ki tsakanin mu da Abba munfi kusa”

Dariya itama Aunty Hindu kafin tace.

” Ai daman bance da ruwana ba bare naji kunya, naga alamar yanzu so kuke ku haɗe min baki cikin gidan nan.”

Dariya kawai Indo tayi kafin ta wuce ɗaki.

💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞

Rayuwa gudu yake, yayin da rana ku suke komawa awanni sati biyu ke komawa sati ɗaya, su Indo results ɗin su ya fito kuma alhamdulillah tayi nasaran samun 9 credit, results Yayi kyau sosai, kowa yayi murna da wannan result ɗin mussaman Daddy da Abba, kwatsam lokaci ɗaya komawar su Aunty Hindu Egypt ya taso cikin gaggawa, Aunty Hindu da Abba sun yanke shawarar cewa zasu tunkari Daddy da zancen ya basu Indo su koma Egypt da ita idan yaso sai tayi joining ɗin University ɗinta acan Egypt ɗin da wannan shawarar suka yanke cewa zasu je su sami Daddy da zancen Domin suna matuƙar son zaman Indo tare dasu, Aunty Hindu ta yanke shawarar cewa satin gaba kafin su koma Egypt zata ɗauki indo suje Dasina.

Kwance yake bisa cinyarta, taɗi suke cikin SO da ƙaunar juna tare da mutunta juna, domin kuwa suna matuƙar son junan su hakan ne ya basu damar samun kyakkyawar alaƙa a tsakanin su, cikin SO da ƙauna ta dubesa tace.

” Sweetie na gaskiya nayi fushi sosai da ƙanwar ka, har nayi 5 month cikin gidan nan taƙi zuwa kai kuma ka hanani zuwa gidan, gaskiya nayi missing ɗin su sosai pls ka barni mana koda daddare ne naje shap-shap na gansu na dawo.”

Murmushi Habeeb dake kwance ya ɗaura kansa bisa cinyar Hasina yayi tare da cewa.

” to ina dai ga wannan ƙanwar tawa ba zuwa gidan nan zatayi ba, dan wlh kullum na mata zancen nan saita fara min kwana kwana ita a dole bata son zuwa ta haɗu da dodonta Mustafa ki haƙura da zuwa gidan nan tukunna sai nan gaba kaɗan.”

Murmurshi SOSAI HASINA tayi tace.

” Lallai Indo ta sawa kanta aiki, nifa ina tunanin akwai Abunda ya haɗata da ya Mustafa RANAR denern mu, akwai Abunda ya mata tun Ranar na fahimci bata son ƙara haɗuwa dashi, amma dan Allah sweetie na, ka taimaka ka jawo min Indo cikin gidan nan koda ƙarfi ne tunda ka hanani zuwa.”

Dariya sosai Habeeb shima yayi tare da cewa.

” Har da ƙarfi zan jawo ta ko kin manta cewa shalelena ne ita na dai jawo ta a hankali banda ƙarfi kam dan banson shalelena tasha wahala.”

Dariya Hasina tayi tace.

” To mai shalele jawo ta a hankali, nifa gani ma nake kamar da biyu tsakaninka da Indo, ko dai zaka ƙara ƴar gida-gida ne, kaga shikenan gani ga ƙanwata kusa mu zauna abunmu.”

Dam! Ƙirjin Habeeb ya buga cikin zuciyarsa yake cewa ” kardai HASINA ta gano Abunda yake cikin zuciyata, kai ina bazata gane ba domin soyayyar da nake yiwa Indo batayi ƙarfin da za’a ganeta cikin sauƙi haka ba, kawai ta faɗa ne cikin wasa” Kafin ya maida dubansa gareta cikin waskewa yana dariya yace.

” Idan kina buƙatar haka aini a wajena babu laifi, kawai sai kije ki nema min Soyayyar ƙanwata kinga shikenan na zama ɗan gata, nasa ƙannena a tsakiya nake kallon ku ina walwala.”

Murmushi yaƙe HASINA tayi domin kuwa ita tuntuni ta gama ganewa cewa Habeeb son Indo yake, cikin rashin nuna damuwa tace.

” Ai kuwa zanje ka amsa cewa kana sonta kaga idan banje na nemo maka Soyayyar ba, nasan kuma da wuri zata amsa domin kuwa mijina ajin farko ne babu macen da zatace bata sonsa, nasan kuma mijina mai adalci ne akan komai, dole kuma naso Abunda mijina yake so, domin farin cikin sa shine nawa” ta karasa maganar tana murmurshi tare da kanne masa Ido.

Sanyi ƙalau jikin Habeeb yayi tare da jin wani irin kunyar HASINA, tabbas Hasina matar soce itace ake ƙira da matar rufin asiri mai danne damuwar ta, domin farin cikin mijinta, anya kuwa zuciyata kin min adalci da kike neman haɗani da matata mai ƙaunar ganin farin ciki na, tabbas da ana iya cire Soyayya da ƙarfi cikin Zuciya to dana cire soyayyar Indo cikin zuciyata, domin kuwa Hasina bata cancanci kishi da Indo ba, tashi Habeeb yayi daga cinyar Hasina yana cewa.

” Wato ko kishi na baƙya yi, shikenan saiki ɗebi ƙafa kije nema min Soyayya, saboda ki nunawa duniya baƙya sona, shikenan aina gane matsayina a wajen ki tunda har neman kai kike dani” yana gama faɗin haka ya wuce bedroom ɗinsa yana haɗa fuska shi a dole yaji haushi matarsa , bata kishin sa.

Murmushi HASINA tayi tana dafe ƙirjin ta, cikin zuciyarta take cewa ” nafi kowa kishin ka, mijina sai dai Soyayyar da nake maka bazai sani tauye maka haƙƙinka ba, ina maraba da duk abunda zaka kawo a matsayin kana sonsa, zan kuma tayaka sonsa koda zuciyata bata so hakan ba’ tashi tayi tare da shigewa kitchen itama domin gabatar da Abincin Rana.

Zaune take ta haɗa uban tagumi, tayi baƙi ta rame bata da abunyi kullum sai tunanin rayuwar aurenta da sam bata jin daɗin sa, ” anya kuwa Mustafa yana tsoron Allah wani irin ƙiyayya yake mata, bata masa gwaninta komai tayi a kushe yake, kullum yana cikin mata faɗa anya kuwa bazan sanar da Mamy halin da nake ciki ba ko zan samu mafita, sai kuma wata Zuciyar tace mata, a’a karki fara sanar da ita domin kuwa bata da wata mafita data wuce na wajen malamai kiyi hkr ki cigaba da zama da mijinki a haka har Allah ya kawo miki ƙarshen wahalar ki” tana cikin tunanin ne taji Muryar sa yana cewa.

” Kee! An kawoki cikin gidan nan ne domin ki share gindi ki zauna, ki tashi ki fita ki wanke min mota tayi datti ina son zan fita yanzu, maza na baki 30minute Kuma Wlh kika haura koda 5 minute ne, zaki gane kurenki a waje na, badai kince Aure na kika zaɓa ba, dole kuma ki bauta min shashasha mayya kawai.”

Runtse idonta RAUDA tayi da ƙarfi wasu zafafan hawaye na gudu bisa fuskar ta tana jin wani zafi cikin ƙirjin ta, kafin ta buɗe idanunta tana duban Mustafa tace.

” Haba Ya Mustafa ganan masu wanke motoci cikin gidan nan, ni kuma meye zai haɗani da wanke mota, yanzu fa na gama maka wanki na share compaunt ɗin gidan nan yanzu na zauna ko hutawa banyi ba, kuma yanzu kace naje na wanke idan mutane suka shigo suka ga ina wankin mota me zance musu gani nake kamar ba mutunci na bane.”

A fusace Mustafa ya yo kan RAUDA yana cewa.

” Uban waye ya tilasta miki Aure na daman an faɗa miki cewa kina da mutunci ne, to bari kiji na gaya miki duk abunda ya kasance nawane cikin gidan nan, dole ne sai kin bauta masa domin kuwa ke baki da wani banbanci da karen cikin gidan nan kinga kuwa aishi kare baida mutunci dan haka Babu ruwana da wani amsar da zaki bawa mutane, ki fice kije ki wanke min mota zan fita kafin ki hasala ni, Wlh na miki ɗan banzan duka kuma ki wanke dole *ai daman na sanar dake cewa zaman kabari sai yafi miki wannan zaman gidan nawa daɗi, kikace kinji kin gani, kinga kuwa ke kika jawa kanki*”

Sanin halin Mustafa yasa RAUDA ficewa daga falon cikin takaicin abubuwan da Mustafa yake mata na rashin mutunci ko kunya baya ji wajen motar ta nufa tana zubar da hawaye tana fita shi kuma ya jawo system ɗinsa, pictures ɗin Indo ne, wanda Habeeb ya taɓa ɗaukar ta sanda yaje dasina ya turo masa ta whatsapp, tare da video, murmurshi ya sake yana duban pic ɗin tare da danna video dariya sosai Mustafa yake yana kallon shiriritar Indo na da, A fili ya furta *MY SHATUU NA INA MATUƘAR KAUNAR KI HAƘIƘA SONKI YA DAƊE A CIKIN JININA DA TSOKA TABBAS KECE RAYUWATA, NASAN KUMA KEMA NINE RAYUWAR KI, DOMIN KUWA NASAN KO YAUSHE NINE MAƘALE CIKIN ZUCIYAR KI, KINA MIN SON DA BAKYA YIWA KANKI NI NASAN WANNAN, LOKACI KAWAI NAKE JIRA NA BAYYANA MIKI SOYAYYA TA, I LOVE SHATUUU NA*” ya ƙara sa maganar kamar wacce Indon take kusa dashi yana sakin murmurshi, cikin shauƙi da annashuwa.

Ita kuwa RAUDA Allah daya taimake ta har ta gama wankin motar babu wanda ya zo ya ganta sai mai gadi cikin sauri ta shiga cikin falon sanda ta isa daf dashi tace.

” Ya Mustafa na gama wankin motar”

Yana jinta yayi shuru bai kulata ba, sanda tayi magana kusan baki uku sannan ya ɗago kansa tare da duba agogon hanunsa, ganin da yayi ta gama da wuri Kafin ma time ɗin daya sa mata ya cika ya ɗago tare da cewa.

” Na fasa fita da ita ki koma ki wanke min farar da take gefen waccar ɗin da ita zan fita”

Wani irin baƙin ciki ne ya zowa RAUDA wuya gagara Magana tayi domin kuwa tasan tana buɗe baki kuka ne zai kwace mata, juyawa kawai tayi da gudu ta fice daga falon, shi kuwa wani murmurshin mugunta ya saki tare da furta ” kaɗan ma kika gani ba kince ke mayya bace to mu zuba mu gani waye zai gaji tsakanin ni dake.”

Wanke motar kawai take lokaci zuwa lokaci tana goge hawaye, kamar daga sama Indo ta faɗo cikin gidan, har zata wuce kamar wadda akace ɗago idanunki, sai ta hango RAUDA sai famar wanke mota take, ƙara leƙawa Indo Tayi domin tabbatar da gaskiyar Abunda idanunta yake gane mata, tabbas kuwa RAUDA ce, taɓe bakin ta Indo tayi tasa kanta da niyar shigewa part ɗin Habeeb sai kuma taji bazata iya wucewa ba sai taji Abunda yasa RAUDA wankin mota Bayan kuma ga mai wankin motar a cikin gidan, nufar wajen Indo Tayi tare da Sallama, ɗago idanunta RAUDA tayi da sukayi jawur tabbacin sunci kuka ta amsar sallamar, karo na farko da Indo ta fara kiran RAUDA da Aunty tace.

” AUNTY RAUDA, lafiya kike wanke mota da kanki bayan ga mai wankin a cikin gidan?”

Murmushin da yafi kuka ciwo RAUDA tayi tace.

” Ehh Wlh haka kawai yau nake son wankewa mijina motar da zai fita da kaina, shima sanda yace min na bari baya so na wahala , yanzu ma yana tollet baisan na fito ina wankin ba, ya su Aunty Hindu naji ance kina wajenta yanzu.”

Shuru Indo tayi badan ta yarda da maganar RAUDA ba domin tana da masaniyar cewa Mustafa baya son RAUDA a Dole ya aureta, tasan kuma halin muguntar sa, sarai zai iya sata wankin motar ma, cewa tayi.

” Ayya to kawo na tayaki ki samu ki gama da wuri Kafin ya fito daga wankan”

” A’a ki barsa kawai Indo YANZU zan gama ai nama kusa”

Murmushi kawai Indo tayi tare da sunkuyawa ta ɗauki tiyo ɗin ruwan tana cewa, ki dinga wankewa ni zan dinga zuba miki ruwan, haka kuwa sukayi RAUDA na wankewa Indo na zuba mata ruwa.

Tashi yayi daga zaunen da yake tare da zuwa bakin window domin ganin halin da RAUDA take ciki, fes idanunsa suka sauƙa kan Indo da suke wankin mota tare da RAUDA, zaro idanunsa yayi tare da cewa.

” What INDOn tasa wankin mota Lallai wannan YARINYAR ta raina ni, ta rasa wa zata saka aiki sai *SHATUU NA* lallai kuwa yau zaki gane kurenki cikin gidan nan”

fitowa yayi a matuƙar harzuƙe ya nufosu yana huci……….

Please bazan gaji da cewa kuyi hkr da yanayin typing ɗina ba, ban samu ina muku typing kullum hakan ta faru ne sakamakon makaranta daya sani gaba🙏🏻

*Vote*

*Share*

*And*

*Comments*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah ce)*💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*

👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*

*Nasmah ko Nasirah*

*Sara da Sassaka*

*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.

Allah yabar ƙauna.

*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri’ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah! Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin taliƙai daya bani lafiya cikin ikon sa da hikimar sa, Gaskiya masoyana bansan da wani irin baki zan muku godiya da nuna farin ciki na gareku a bisa addu’oin ku gare ni, naji daɗin yanda kuka nuna kulawa gareni wanda suka kiran a waya tare da text message gaskiya bazan iya lissafa yawan ku, na gode sosai Allah ya bar zumunci.*

*ZULAIHAT MUSA GARBA* Na gode ƙwarai da Alkairin ki gareni Allah ya bar ƙauna.

*بسم الله الرحمن الرحيم*

____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

*P*••••••7️⃣3️⃣ ➡️ 7️⃣4️⃣

” Keeeeeeee RAUDA!”

Ya furta da ƙarfi tun kafin ya ƙaraso wajen, a matuƙar tsorace ta juyo tana kallon sa, domin kuwa tasan wannan kiran da yake mata babu Alkairi a cikin sa, itama Indo juyowa tayi tare da haɗa fuska tamau tana kallon sa, domin kuwa yau da shirin ko ta kwana tazo gidan yana mata mugunta zata rama wlh.

” Uban waye ya saki bata wankin mota?” Ya karasa maganar yana nuna mata Indo.

RAUDA bakinta na rawa tsabar tsoron sa tace .

” Bani na bata ba itace tace zata tayani shine ta ɗauki tiyo nike wankewa ita ruwa kawai take zuba min ba wani aiki mai wahala take min ba.”

” Jakar gidan ubanki ne da zaki bata aiki ko ruwan da take zuba miki shima ba aiki bane koko cewa nayi kije ki nemi wanda zai taya ki raguwar banza raguwar wofi”

“Daman za’a rina nasan kaɗan daga cikin muguntar sa baƙin azzalumi” Indo ta furta cikin zuciyarta Da ƙarfi ta furta masa cewa.

” Kaiiiiiiii! Kaiiiiii! Zaginki fa yake kina jinsa kin sunkuyar da kanki ƙasa bazaki rama ba, uba fa baifi Uba ba, kinyi shuru kina jinsa ai Wlh duk wanda baiji kunyar zagin ubanka ba to kaima karkaji kunyar zagin nasa Uban domin kuwa kowa yana son nasa Uban ke kuma kinyi shuru kina jinsa yana zage miki Uba.”

Ita dai RAUDA bata ce MUSU komai ba ta cigaba da wankin motar amma cikin zuciyarta tana jin zafin abinda Mustafa yake mata har tana jin kamar ta rama.

Shiko Mustafa Duban Indo yayi tare da cewa.

” Allah ko rasa kunya ɓerar tanka to Ko zaki rama mata ne, idan zaki rama mata to bismillah ƙaramar marar kunya taho ki rama mata nace .”

Taɓe bakin ta tayi tare da cewa.

” Akan me zan rama mata, kunfi kusa ƙauye da haɗeja matar kace tunda ita tace bata da Zuciya ai shikenan sai taje tata haɗiyar baƙin ciki amma wlh dama ni mutum ya zaga Wlh babu abunda zai hanani ramawa, tunda shi mutum baƙin azzalumi ne mungun gaske wanda matar sa ma bazai raga mata ba, ni dai daga yau na daina tsoron ka, *NA DAWO MAKA INDON ƘAUYEN DASINA DA KA SANI A BAYA YANZU BABU BARIN BASHI KANA MIN YASIN ZAN RAMA NA DAINA TSAYAWA KANA ZALUNTA NA BABU GAIRA BABU DALILI*, Aunty RAUDA ki ja masa Allah ya isa tunda kina tsoron ki rama ya kasheki Allah ya miki sakayya mungu kawai mai cin zalin mutane.” Tana gama faɗin haka ta juya a guje tayi part ɗin Habeeb tana murguɗa masa baki.

Murmushi kawai Mustafa Yayi domin kuwa duk kalma ɗaya data fito daga bakin ta wani sanyi yake ji take masa cikin kunnen sa da zuciyarsa, sanda ya gama murmurshin sa yaga ta ɓacewa ganin sa kafin ya kalli RAUDA data zuba masa yace.

” Sai ki ƙarasa wankin ai kin zuba min ido kamar zaki cinyeni nama ɗanye.”

Kauda kanta kawai RAUDA tayi sannan ta maida hankalin ta ga wanki shi kuma ya juya ya fice zuwa part ɗin Momy yana murmurshi, ajiyar Zuciya RAUDA ta sauƙe tare da neman sauƙi cikin rayuwar Auren ta wajen ubangi.

Faɗawa ɗakin tayi kamar wacce aka jefota tana dariya tare da haki.

“AUNTY HASINA! AUNTY HASINA!”

Fitowa Hasina dake cikin kitchen Tayi tana cewa.

” Muryar wa nake ji kamar ta Indo kodai kunnena yake min ƙarya.”

Dariya Indo dake zaune bakin kujera tayi tace.

” Ni ɗin ce dai Kinsan Ammi ce ta aiko ni wajen Momy shine na fara shigowa nan kafin na ƙarasa Wajen MOMYN yau dai nazo naga Aunty na kafin na wuce.”

Hararar ta Hasina tayi tana cewa.

” Wato ma ba zuwa min kikayi na musamman ba, Albarkacin aiken Ammi naci kika ratso min, lallai Indo kirkin ki yayi over to ki tashi ki koma na yafe gaisuwar tunda bani da darajar da zaki kawo min ziyara.”

Cikin shaƙiyanci da dariya Indo take cewa.

” Please sorry my AUNTY na my sweetie na my hantata my tsokar jiki na, kinsan dai bama haka dake, zanzo ne mu kwana biyu next week kiyi hkr.”

Zama Hasina tayi tare da cewa.

” Ƙarya kike babu wani zuwan da zakiyi mu kwana biyu, hakanma da kika zo na gode miki badan halin kiba.”

Dariya kawai Indo Tayi Kafin suka cigaba da hiran duniya da Hasina sun ɗan juma kafin Indo ta tambayi ya Habeeb sanar da ita Hasina tayi cewa yana bacci har Indo ta fito daga cikin gidan Habeeb bai tashi ba, Hasina kuwa har bakin get ta rakata, wannan karon Indo bata ga RAUDA da Mustafa ba, haka kuma bata sanar da Hasina Abunda ya faru ba, saka hanunta Indo da zatayi ta buɗe get ɗin idanun Hasina suka sauƙa kan zoben da Habeeb ya bawa Indo, Ras gaban Hasina ya faɗi (idan ba ta ɓata gani ba kamar Habeeb yana da Wannan zoben exactly a hanun sa, *H$A* me waɗannan kalmomin suke nufi idan zargina ya kasance gaskiya yana nufin *HABEEB & A’ISHATU* innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un tabbas Habeeb son Indo yake na shiga Uku sai kuma tayi saurin cewa Auzubillah”)tayi saurin koran sheɗan dake shirin mata haɗuba tare da cewa Indo.

” Ki gaishe da Ammi da Abbah idan kin koma naji ya Habeeb na cewa next week zasu koma Egypt ko”

” Zasu ji ba next week sai ƙarshen watan nan, dan sai munje Dasina mun dawo ma”

” Okey Allah ya kaimu kya gaishe su”

” Zasuji”

Indo ta furta tare da ficewa daga cikin gidan, ta nufi part ɗin Momy DARECT sallama tayi carap taji Muryar sa ya amsa mata da cewa

” amin Wa’alaikimussalam ƴan Mata har kin gama gudun kinzo kin sameni.”

Zaro ido Indo tayi tasan tabbas sai ya ci ubanta cikin gidan nan, gashi kuma babu halin juyawa Momy na cikin falon, wani mungun murmurshi Indo ta saki tuno yanda Momy ke son RAUDA gashi kuwa yanzu ya gama gana mata azaba harda zagin uba, ai kuwa cikin mugunta tace.

” Allah ya baka hkr ya Mustafa gani nayi gaskiya na faɗa maka bai kamata ka dinga sa Aunty RAUDA wankin mota ba, sannan kuma ai zagin da ka mata bai dace ba ka zagi ubanta, duk wanda ya zagi uban wani kuma malamai sunce nasa Uban ya zaga” ta ƙarasa maganar tana maida dariyar ta ciki tare da kallon action ɗin Momy.

Zaro ido Mustafa Yayi cikin tsoron Indo da mamaki ta ” wato dai shi mai hali baya fasa halinsa sai dai ya ɗauki hutu tana nan dai a Indon da ya sani ta ƙauye har yanzu, ko kafin ya gama maganar zucin nasa ya jiyo hargowar Momy tana cewa.

” Ke ƴar nan waida gaske ne abunda kike faɗa, RAUDA ya yiwa wannan ɗiban albarka haka wankin mota”

” Kwarai kuwa Momy idan ƙarya nake kije ki tambayeta kiji ko ki tambayi mai gadi kiji tana wankewa yana zagin ta, shine danna faɗa masa gaskiya yake neman cin zalina nima.”

Ta ƙarasa maganar tana dariyar zuci, duban Momy Mustafa Yayi tare da cewa.

” Karki yarda da maganar ta Momy ƙarya take wannan ma ai ba Maganar da hankali zai ɗauka bane taya zansa mace wankin mota Bayan kuma ga mai wankin motar, idan ma babu mai wankewa ai nima zan wanke kayana, amma kuma tunda tace kije ki tambayeta to bari na kira miki ita tazo sai ki tambayeta”

Ya ƙarasa maganar yana duban Indo yanda Momy bata gansa ba ya kanne mata Ido domin kuwa yasan RAUDA bazata taɓa cewa shine ya sata wankin Mota ba.

Zaro ido itama Indo tayi tana kallon Mustafa daya dage yake ƙaryata ta akan gaskiyar ta, ita kuwa Momy dukkan su dubansu take kafin tace.

” Nifa daman bawai na yadda da maganar wannan *HATSABIBIYAR YARINYAR BANE* nasan kaɗan daga cikin sharrin ta taga ta haɗa tsakanin ɗa da uwarsa kuma ta Allah ba taki ba munfi ƙarfin ki.”

Wani irin ƙuna Zuciyar Mustafa take jin kalmar da Momy take kiran Indo dashi marar daɗin ji ya rasa menene Indo ta tsarewa Momy a Rayuwa da ta tsaneta haka, ita kuwa Indo bata damu da kalmar Momy ba saboda ba yau ta fara zaginta ba, juyawa kawai tayi ta fice daga cikin gidan ba tare data isar da sakon da Aunty Hindu ta aiketa ba, duban Momy Mustafa Yayi yace.

” Haba Momy haba Momy meyasa kika tsani YARINYAR nan ne haka, Momy ƙiyayyar da kike gwada mata yayi yawa pls ki sassauta wannan ƙiyayyar, saboda baki san me zata zama a gareki gaba ba, duk ɗan adam da kika gani yana da ranar da zai maka wata rana.”

Cikin masifa Momy take cewa.

” To ubana yimin wa’azi kaji, wannan YARINYAR banzar bata da wani rana da zata min cikin Rayuwata yarinyar da bata yiwa iyayen ta rana ba saima gagarar su da tayi suka kawo mana masifa cikin gida ni ranar me zata min bana buƙatar Ranar ta.”

Mustafa ya buɗe baki da niyar Magana kenan yaji gyaran Muryar Daddy a bayan su hakanne ya sashi fasa maganar da zaiyi tare da cewa.

” Barka da fitowa Daddy”

” Yauwa barka, kana nan kenan”

” Ehh Daddy ina nan ”

” Daman kuwa ina son ganinku ai, Uwarku Hindu ta sanar dani cewa tana son ranar Friday za ayi family meeting a Cikin gidan nan, so shine daman zan sanar daku saboda ku samu ku Hallaci wajen idan kun haɗu da Habeeb zuwa Anjuma ka sanar dashi.”

” To shikenan Daddy Allah ya kaimu ranar Friday ɗin zan sanar dashi insha Allah”

Mustafa sun juma suna taɗi da Daddy har aka kira azahar suka tafi masallaci tare.

Tafe Barrister Umar yake cikin motar sa, duk wani binciken sa ya gama akan Indo ya kuma tabbatar da cewa bata da wani saurayi, har yanzu, so dan haka yanzu ne yake da damar da zai dasa Soyayyar sa cikin zuciyarta dashen da babu wani mahalukin da zai iya tonewa, da wannan tunanin ya tsaya bakin get ɗin gidan Aunty Hindu hon ya danna sannan mai gadi ya buɗe parking space dake cikin gidan ya nufa ya samu yayi parking sannan ya fito yana Cewa mai gadi ya shiga ya sanar da AUNTY cewa Barrister Umar yazo, haka kuwa akayi mai gadi yaje ya sanar da AUNTY Hindu zuwan Barrister Umar sanarwa tayi cewa ya shigo, bayan mai gadi sanar da Barrister Umar sakon sane ya shiga falon da Sallama, Indo dake zaune ta haɗa fuska tamau Aunty Hindu tayi tambayan duniya Indo taƙi sanar da ita Abunda ya faru amsa sallamar Barrister Umar Aunty Hindu tayi, tana cewa.

” Ashe dai yau ina da babban baƙo cikin gidan nan, lallai wata sabon gani yaushe rabon da na ganka wajena.”

Dariya Barrister Umar yayi yana zama saman onester yace.

” AUNTY Aikin namu ne sai a hankali kinsan bamu da wani lokaci na kammu, kullum muna cikin aiki, daga mun gama wannan shara’ar muke shiga wannan.”

Duk Maganar da Barrister Umar yake hankalin sa yana kan Indo take Zaune tana tsume ta haɗa fuska kamar wacce zata danna ihu Aunty Hindu ce tace.

” Gaskiya ne kuna fama da aiki, to ya aikin naku da Hajiyar taka.”

” AUNTY aiki alhamdulillah! Hajiya kuma tana lafiya, AUNTY Wannan ƙanwar tawa kuma meya sameta naga sai famar haɗa fuska take, ko dai dukanta kikayi” ya ƙarasa maganar cikin zolaya yana dariya kasancewar sa mutum mai son wasa da dariya.

Dariya Aunty Hindu tayi tace.

” Gata nan dai babu laifin tsaye babu na zaune tunda ta dawo daga gidan su abokan ka take famar baƙin hali take ta haɗa fuska, ta kuma ƙi sanar dani Abunda ya faru” duban ta ta mayar kan Indo tace.

” A’isha kina ganin yayanki bazaki gaishe shiba”

Tana turo baki tace.

” Ina wuni yaya”

Dariya Barrister Umar yayi yace.

” Bazan amsa wannan gaisuwar ba, tunda tun farko baki son gaida ni, dubi yanda kukayi muni da kika tsume ko kinsan kinfi kyau idan kina dariya, mussaman wannan dumple ɗin naki idan suna loɓawa, sai kiyi kyau haƙwaran ki kuma tamkar tauraro idan kina murmurshi haka kuma suke haske tamkar watan dabya kwana sha huɗu, to meyasa kike son ɓata kyawun ki da haɗa fuska, ki daina fushi bai dace da kyakkyawar fuskar kiba.”

Kunsan Indo da son ganin ana yabonta aikuwa take ta fara murmurshi harda dariya, tace.

” Da gaske ina da kyau haka kullum Zarah take cewa ina da kyau amma ni bana yadda sai kuma gashi ka sanar dani yanzu”

Murmushi Aunty Hindu tayi sannan ta tashi ta buɗe frich ta kawowa Barrister Umar ruwa ta shige ɗaki tana murmurshi ganin har Barrister ya kauda ɓacin ran Indo, shima dubanta yayi yace.

” Ehh ke kyakkyawa ce ta ajin farko duk inda ake neman kyau to idan akazo aka sameki ayi fatiha a tashi domin an gama samun kyakkyawa.”

Sosai Indo take dariya cikin mintuna ƙalilan Indo ta saba sosai da Barrister, har takai ga sunyi exchange ɗin numbern waya, amma Barrister bai sanar da ita cewa yana sonta ba, har ya tafi a cewar sa sai sun shaƙu sosai kafin ya sanar da ita.

A cikin kwanaki kaɗan shaƙuwa mai tsanani ya shiga tsakanin Indo da Barrister Umar inda ko yaushe suna cikin chart ko waya amma duk wannan shaƙuwar Indo bata taɓa ɗaukar sa da sunan soyayya ba, mutunci kawai take ɗaukar sa, haka kuwa Habeeb domin kuwa Indo tafi kowa shaƙuwa dashi, duk randa bata ji muryar sa ba takan shiga cikin damuwa wanda hakan yakan hanata sukuni har sai ya kirata ko ta kirasa tukunna ta samu walwala, Mustafa kuwa har yanzu rashin jituwa yana nan tsakanin sa da Indo, idan baya kusa da ita yakan ji wani irin yanayi haka zai kasance yana tunanin ta, soyayyar ta kuwa kullum ƙara ƙarfi take cikin zuciyarsa, amma da zarar sun haɗu kuma sai faɗa ne zai biyo baya, haka kuma a wajen Indo duk sanda ta haɗa ido da Mustafa takan jin gabanta ya faɗi ko da kuskure ya riƙe hanunta sai taji wani shirking a jikinta.

🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌

Yau ta kasance juma’a haji babbar rana, Mustafa da Habeeb daga masallaci gidan su suka wuce kasancewar yau ne ranar da zasuyi Family meeting, sun sami kowa ya hallara wajen har Daddy da su RAUDA Hasina Sharifa hatta autan momy ba’a barsu a baya ba, Indo KUWA tana maƙale gefen Aunty Hindu, bayan gaisuwa Daddy yasa Mustafa ya buɗe taron da addu’a kafin Daddy Yayi gyaran murya tare da cewa.

“Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah daya tara waje ɗaya, dukanku nan kunsan wacce ta tara mu a wajen nan, sai dai babu wanda yasan dalilin ta na haɗamu wannan waje, Hindatu muna sauraronki ki sanar damu dalilin ki na haɗamu a wajen nan”

Gyaran murya Aunty Hindu tayi kafin ta fara magana.

” Yaya ba wani abu yasa nace a haɗa wannan family waje ɗaya ba, sai dan wata alfarma da muke nema gareku, nida mijina mun zauna mun tattauna akan wannan baiwar Allah wato Indo, SAKAMAKON komawar mu Egypt daya taso yasa muka yanke shawarar cewa mai zai hana a bamu Indo mu tafi da ita idan yaso sai mu jona mata University ɗin ta acan ta cigaba, tunda kaga yanzu babu kowa gaban mu, zamuji daɗi idan muna kallonta gaban mu.”

Shuru Daddy Yayi yana tunanin wannan alfarmar Aunty Hindu, domin kuwa shi yafi so Indo ta zauna a ƙasar ta haihuwa, kuma gabansa ko yanzu ma daya bari Indo take Zaune gaban Aunty Hindu Saboda cika wasiyyar Inna na cewa abar Indo ta zauna gaban Hindu har lokacin da zafin mutuwar ta ya kau mata, ɗago kansa Daddy Yayi ya dubi Aunty Hindu Yace.

” Shikenan maganar koko akwai wata idan akwai wata ki faɗa kafin na amsa miki su duka.”

Tunda aka fara maganar Dukansu suka nutsu suna sauraron Aunty Hindu da Daddy, duk da shi Mustafa bai ji daɗin maganar Aunty Hindu na cewa zata koma da Indo Egypt, Yayi shuru ne kawai yana jiran yaji amsar da Daddy zai bata, Aunty Hindu ce tace.

” Magana ta biyu itace akan *BARRISTER UMAR JIJJI* Yaya mun tattauna da Barrister sosai ga lamarin Indo a Inda yake sanar dani cewa yana sonta, zai kuma nemi Soyayyar ta, idan harta amince masa, zai turo iyayen sa su nema masa aurenta, kuma gaskiya yaya naji daɗin hakan domin kuwa Barrister Umar mutumin kirki ne kuma ina da kyau tabbacin cewa idan har Indo ta auresa zataji daɗi ta kuma samu nutsuwa, sai dai na sanar dashi cewa ya turo iyayan nasa kawai gareka domin na fiskanci akwai Soyayya tsakanin su idan ka nutsu kayi duba ga shaƙuwar da take tsakanin su, kaga idan an basa zata cigaba da karatun ta harta gama kafin ayi Maganar Aure Allah yasa banyi kuskure ba”

Gabaki ɗayan su ukun a firgice suka juyo suke kallon Aunty Hindu, mussaman Indo da bata san wata soyayya dake tsakanin ta da BARRISTER UMAR ba da har ake mata Maganar Aure, Habeeb kuwa wani irin maƙoƙon ɗaci ya haɗiye cikin wuyansa yana jin wata munguwar tsanar Barrister Umar, Mustafa Sarkin rashin haƙuri, tashi yayi tsaye idanunsa rufe domin kuwa baya kallon gabansa Magana ya fara cikin ɓacin rai da kaushin murya.

” AUNTY Hindu Babu soyayya tsakanin UMAR JIJJI da Indo ki sanar dashi cewa ya fita rayuwarta domin kuwa bata dace dashi ba, kuma nima zan sanar dashi, idan kuma yaƙi ta lallami to kuwa zaiji ta tsiya wlh.”

Gabaki ɗayan su wajen tsayawa sukayi suna kallon Mustafa cikin mamakin kalaman sa, Aunty Hindu ce tace.

” Meye ya haramta Soyayya tsakanin Umar JIJJI abokin ka da Indo, tunda bata dace dashi ba, dawa ta *DACE* sanar dani?

Babu shakka cikin Zuciyar Mustafa domin kuwa a yanzu ya shirya bayyana sirrin Zuciyar sa, Saboda yaga wankin hula na ƙoƙarin kaisa dare gara kawai ya faɗa a wuce wajen.

” *Nine Wanda na dace da Indo ba Umar ba, nine Wanda na juma ina ajiyar Soyayyar ta cikin zuciyata tun kafin takai ga wannan matakin, Aunty Hindu SHATUU BUGUN NUMFASHI NANE INA SONTA FIYE DA YANDA NAKE SON KAINA HAKA KUMA INA DA TABBACIN CEWA ITAMA TANA SONA TUN ƘARAMAR TA* wannan shine hujja ta.”

A matukar razane Habeeb ya miƙe Indo RAUDA suna masa wani irin kallo na ka haukace ne, RAUDA kuwa wani jirine yake neman yardar ita, saurin komawa tayi ta dafe kanta, jan hanun Indo Habeeb yayi har gaban Mustafa yace.

” Kasan me kake cewa kuwa, ko ka manta waye kake zancen cewa kana so, *INDO CE FA WANNAN ƘAZAMAR ƘAUYEN WACCE KAKE KIRA DA ALJANA WACCE KAKE CEWA ALLAH YA SAUWAƘE KA SOTA, WACCE KAKE ƘYAMAR TA, ITACE YANZU ZAKA DAWO KACE KANA SO*……..

MURYAR Momy Habeeb yaji ta katse sa ta hanyar cewa.

” Ka rufe Min baki haka Babu wata Soyayyar tsakanin *GUDAN JININA DA WANNAN TAMBAƊAƊƊIYAR ƘAUYEN WACCE TA FITINI GARIN SU TA FITINI IYAYEN TA, TA GAGARESU SUKA HAƊO MU DA ITA BABU JININI BABU ITA,* koda wasa Mustafa karna ƙara ji ka ambaci kalmar soyayya tsakanin da wannan abar ƙyamar.” Ta ƙarasa maganar tana huci.

Runtse idonsa Mustafa Yayi yana jin zafin kalaman Momy, amma sai dai duk abunda zai faru bazai taɓa rabuwa da Indo ba komai tsanani komai wahala, duban Momy Habeeb yayi tare da cewa.

” Momy ba cewa zakiyi Babu junin ki babu Indo cewa zakiyi babu Mustafa babu Indo domin kuwa shi Mustafa yana Auren ƴar gwal ɗinki bazaki so a mata kishiya ba, Momy jininki yana tare da Indo kuma bana tunanin zai iya rayuwa ba tare da ita ba, ki janye kalamanki Momy pls.”

INDO dake sandare tana sauraron sune ta juya a guje ta fice daga gidan cikin matsanancin kuka, Daddy kuwa gyaran murya yayi tare da cewa kowa ya shiga hankalinsa ya nemi waje ya zauna.

________________________________________

Kash mai karatu anan na kawo ƙarshen wannan littafin kashi na farko, sai mu tara daku a kashi na biyu mai taken *SO BAI SAN JINI BA* cigaban *INDO A BIRNI* domin jin yanda zata kasance nanda wasu ƴan kwanaki, akwai tambayoyi kashi kashi da kuke buƙatar amsar su, wanda dole sai kun kasance dani cikin *SO BAI SAN JINI BA* anan ne zaku samu amsar ku.

1 shin Indo zata so Mustafa kuwa harta yarda ta auresa, duk da ɓakar ƙiyayyar daya nuna mata a baya?

2 shin Habeeb yana nasarar samun soyayyar Indo kuwa, gashi dai ya mata Hallaci cikin Rayuwar ta, shin zata duba wannan hallacin ta amshi soyayyar sa?

3 shin Indo zata amince da Soyayyar Barrister Umar kuwa idan har ta amince da Soyayyar sa ya Rayuwar Mustafa da Habeeb zata kasance?

4 gefe ɗaya kuma ga Momy, shin Momy zata yarda ɗanta ya auri Indo KUWA?

6 shin Daddy zai amince da komawar Indo Egypt kuwa idan ya amince ya rayuwarta zata kasance a Egypt?

Shin wake nasarar samun Indo?

Kudai ku biyoni cikin BOOK 2 SO BAI SAN JINI BA CIGABAN INDO A BIRNI DOMIN JIN YADDA ZATA KASANCE. Duk wanda yaji ance SO BAI SAN JINI BA yasan dole Akwai gurmi.

Kafin na shiga BOOK 2 ina son ku sanar dani me kuka fahimta game da wannan littafin, wani irin saƙone yake ciki, jin ra’ayin ku shine zaisa na samu ƙarfin gwiwwar cigaba da Wannan book ɗin sai naji daga gare ku.

Karku manta taken sa *SO BAI SAN JINI BA*

*Vote*

*Share*

*And*

*Comment*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah ce)*

About Arewanmu 1238 Articles
24/7 Hausa Hip Hop Music, Music Videos, Wakokin Hausa, Labarai, Kannywood, Naija Music, Addini, Fadakarwa, Wasanni, in indigenous language✅✅✅

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*