Dr Ibrahim Jalo Jalingo Yayi Martani Mai Zafi Kan Wannan Fitsara

Dr ibrahim jalo jalingo yayi martani mai zafi wanda dole saboda irin wannan abubuwan suna jawo fushin ubangiji.

Inda ya wallafa a shafinsa kamar haka

1. Lalle irin yadda amare ‘ya’yan musulmi suke yin shiga ta nuna tsiraici a mahangar Musulunci sannan kuma su dauki hotunansu cikin wannan shiga ta fitsara su watsa wa Duniya, abin takaici ne matuka. Kuma abu ne da zai iya jawo hushin Allah a kan al’ummar Kasa.

Subhannallah Kalli Video Yadda Yar Madigo Take Rokon Yar Uwar Lalatarta Da Ta Tuba Ta Daina

2. Lalle mun ga irin wannan fitsara, da saba Shari’ah, a ‘yan shekaru kadan da suka wuce daga wata ‘yar shugaban kasa, muka kuma sake ganin irinta daga wata ‘yar gwamna, ga shi a yau kuma muna ganin ta daga wata ‘yar babban sarki!!

3. Muna rokon Allah Madaukakin Sarki cewa kada Ya kama mu da laifin da wawayen cikinmu suke aikatawa. Ameen.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here