Bayan kwanaki 55 a tsare, ‘Yan bindiga sun saki daliban makarantar Afaka, Kaduna

Bayan kwanaki 55 a tsare, 'Yan bindiga sun saki daliban makarantar Afaka, Kaduna

‘Yan bindigan da suka sace daliban makarantar koyon aikin gona da gandun daji da ke Afaka, Kaduna sun sake su.

Wani babban Jami’in gwamnatin jihar Kaduna ya tabbatar wa AREWANMU cewa maharan sun sako daliban.

Daliban makarantar sun shafe kwanaki 55 tsare a hannun yan bindigan bayan gaza biyan su kudin fansa da gwamnatin jiha da na tarayya suka yi.

Maharan sun bukaci a biya su naira miliyan 500 kudin fansa.

Sai dai kuma gwamnatin Kaduna ta bayyana cewa ba za ta biya kudin fansa ga kowani dan bindiga ba.

Shugaban Kotun CCT, ya bayyana gaban Majalisar Dattawa, bayan maigadin da ya kifa wa mari ya kai mata karar sa

Hakan ya sa iyayen yaran sun rika yin zanga-zanga domin jawo hankalin gwamnati su tausaya wa yayan su a samu a sake su.

Idan ba a manta ba, an sako dalibai 10 a kwanakin baya, yau kuma an saki sauran 27 da ke tsare a hannun yan bindigan.

Shugaban kungiyar iyayen daliban, Abdullahi Usman ya shaida wa Channels TV cewa an saki daliban da misalin Karfe 4 na yamma.

About Daniel olakunle 97 Articles
Am the pioneer of this web. Am smart, vibrant, and I love to keep the readers informed, and Blogging is my profession and wining is my satisfaction.

Be the first to comment

We Love Comments