Babban dalilin da yasa maharan ‘yan bindiga suke kaiwa farmaki wasu garuruwa 2 a jihar Katsina

A binciken da akayi ya bayyana dalilin da yasa maharan ‘yan bindiga suka addabi gurare 2 a jihar Katsina, an gano cewa farmakin da suka kai ya biyo bayan kashe wasu fulani da ‘yan sa kai suke yi, a ranar Talatar data gabata sai da ‘yan bindigar suka kashe mutane 10 a Batsari.

Premium Tiame ta ruwaito yadda yadda maharan ‘yan bindigar suka kashe mutane 10 a garin Yasore dake Batsari a daren ranar Talata, jama’ar garin da dama sun raunata sannan kuma ‘yan bindigar sun kone musu gidajen su da shaguna.

Babban dalilin da yasa maharan ‘yan bindiga suke kaiwa farmaki wasu garuruwa 2 a jihar Katsina

A yayin da aka tattauna da manema labarai a jihar Katsina, kakakin rundunar ‘yan sandan jihat Gambo isa yace, ‘yan bindigar suna mayar da martani ne, kamar yadda ya bayyana a bida ruwayar Premium Time.

READ:   Manoman dawa a Najeriya sun fito da dabarun rage dibga asara bayan sun yi girbi

Binciken mu ya tabbatar da cewa ‘yan bindigar suna kawo hari ne a matsayin martanin halaka fulani da wasu ‘yan sa kai suka dinga yi, wadannan ‘yan sa kan sunyi ta hallaka fulani ba tare da wani laifi ba.

Kakakin rundunar ‘yan sandan yace suna ta bincike kan kashe mutane da ake yawan yi a Daudawa dake karamar hukumar Faskari, baya ga Yasore.

Kamar yadda ya bayyana: A Daudawa a kwai batun mayar da martane da basuji dasu gani ba da ‘yan sa kai sukeyi, amma tun a makon daya gabata muke ta bincike kan al’amarin, wasu matasa ‘yan sa kai suna ta daukar doka a hannun su mun tattaro bayanai kan ta’addanci a kananun hukumomi kamar Bakori, Batsati, Funtua da dai sauran su kan kashewa fulani.

READ:   Yadda Naziru Sarkin Waka Yake Cigaba Da Rikita Yan Matan Arewa

Karamar hukumar Faskari da kuma Batsari suma suna cikin kananun hukumomin da suke fuskantar ta’addanci, an katse dukkan nin wasu hanyoyin sadarwa da kasuwanci mako a yankunan domin kawo karshen ta’addancin.

About Arewanmu 609 Articles
24/7 Hausa Hip Hop Music, Music Videos, Wakokin Hausa, Labarai, Kannywood, Naija Music, Addini, Fadakarwa, Wasanni, in indigenous language✅✅✅

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*