Alluran kara kaifin rigakafin COVID-19 wato “booster jabs” a turance na kara ciwo, alluran rigakafin ba su aiki da sauran za

Alluran kara kaifin rigakafin COVID-19 wato “booster jabs” a turance na kara ciwo, alluran rigakafin ba su aiki da sauran za

Bayan da aka gano nau’in Omicron na COVID-19, an shiga wani sabon yanayi na damuwa dangane da ko alluran rigakafin da aka riga aka sarrafa za su iya kasancewa garkuwa daga kamuwa da sabon nau’in, abin da kuma ya kara sa mutane jan-kafa wajen karbar allurar.

Kwanan nan wani sakon da aka tura a WhatsApp ya yi zarge-zarge da dama dangane da allurar rigakafin da wadanda suka karba da wadanda ba su karba ba.

A cewar wannan sakon, wadanda suka karba alluaran biyu za su kasance barazana ga jama’a lokacin hunturu don haka dole a killace su, yayin da wani zargin kuma ke cewa alluran ma ba su aiki.

Sakon ya kuma kara da zargin cewa alluran da ake so a kara dan inganta kaifin maganin wato boosters sukan ta’azara ciwon a jikin wanda ya riga ya kamu da COVID-19 sa’annan kuma wadanda ba su yi allura ba ko daya sub a hadari ba ne ga al’umma.

Tantancewa
Ganin cewa zarge-zarge na da yawa, Dubawa ta gano kowanne zargi ta tantance su daban dadan

download

Zargin farko: Dole a kebe wadanda suka yi allura lokacin hunturu don za su kasance barazana
Sakon na WhatsApp na zargin wai dole a killaci wadanda suka yi allurar rigakafin COVID-19 a watannin sanyi na hunturu idan ba haka ba akwai hadarin za su yada cututtuka masu tsananin gaske.

Ana dangantaka wannan zargin da Christuan Perronne wani tsohon mataimakin shugaban kungiyar masu bayar da shawara ga Turai, kuma kwararru kan allurar rigakafi na Hukumar Lafiya ta Duniya WHO.

“Tsohon mataimakin shugaban kungiyar masu bayar da shawara kuma kwararru kan alluran rigakafi na Hukumar Lafiya ta Duniya, Farfesa Christain Perrone jiya ya ce dole a kebe duk wadanda suka riga suka yi allurar da zarar aka shiga watannin hunturu idan ba haka ba akwai hadarin cututtuka masu tsanani”

Da muka yi binciken mahimman kalmomi, binciken mu ya kai mu shafin Dr. Jesse Livermire LL.M, PH-D (@jessielivermore) a shafin Tiwita inda a ranar 20 ga watan Satumba 2021 shi ma ya yi zargi makamancin wannan. Sai dai a na shi zargin ya ce kamfanin Pfizer ta ce wadanda suka yi allura za su iya kasancewa hadari ka wadanda ba su yi ba.

Wannan labarin an wallafa tare da adireshin wani shafin da ke dauke da labarin da aka yi a wantan Mayu 2021 inda ake zargi wai Pfizer ta bayar da tabbacin cewa wadanda suka yi allura suna zubar da daya daga cikin sinadiran da ake noticed a a allurar mai suna “Spike protein” a turance wanda kuma ke da hadari ga wadanda ba su yi allurar ba.

Hukumar Lafiya ta Duniya wato WHO ta amince da alluran rigakafi guda 8 dan COVID-19 bayan da ta gama tabbatar da karfin aiki da amincin shi. A cewar Bloomberg, a yanzu haka an riga an yi amfani da allurai na COVID-19 biliyan 8.23 a kasashe 184.

Wadanda suka karbi alluran biyu kuma a cewar CDC zai yi wahala cutar da yi tsanani a jikinsu ko da solar kamu da ita. Sa’anan allurar rigakafi ba ta barin jikin mutu ta zube kamar yadda suke zargi sai dai idan an yi amfani da kwayar cutar da ba shi da karfi sosai ne wajen yin allurar kuma ba haka ba ne idan aka yi maganar allurar rigakafin COVID-19

Sinadiran na Spike Porteins (Wanda shi ma akan samu a kwayoyin cutar da ke kawo COVID-19) wanda ake samu a allurar rigakafin Pfizer da Moderna, wadanda suke da fasahar mRNA akan similar su ne bayan allurar ya tura sako zuwa kwayoyin jikin mutun, sai su da kan su su fitar da sinadarin na Spike Proteins.

Kwayoyin jikinmu ne ke yin sinadarin wanda garkuwan jikinmu ke ma sa kallon bako sai ya mayar da martani ta fitar da wadansu kwayoyi wadanda za su ingata garkuwar jikin mutun ya yaki cutar.

Wadannan sinadaran na spike proteins ba su da wani lahani, ba su janyo ciwo kuma bas u dadewa a jikin mutum. Dan haka wannan zargin karya ne.

Wane ne Christian Perrone?

Christian Perronne farfesa ne na cututtuka masu saurin yaduwa da wadanda ke yankunan da ke da zafi a jami’ar Versailles-St Quentin, Paris-Saclay, Faransa. Sai dai an san shi a matsayin likita mai rigima da son jayayya wanda ya yi suna saboda yadda ya ke sukan manufofin lafiyar da aka dauka don yaki da COVID-19.

Binciken da muka yi kan Kungiyar shawarar ta WHO sai ta kai mu shafin wata kungiyar mai suna SAGE ita ma kan allurar rigakafi ta ke a karkashin Hukumar Lafiya ta Duniyar. Wannan ya nuna mana cewa sunan Christian Peronne ba ya cikin jerin sunayen mambobi na baya da na yanzu. Shugaban kungiyar SAGE yanzu shi ne Dr. Alejandro Cravioto.

Zargi na biyu: Wadanda ba su yi alluran rigakafi ba ba su da hadari

MUTAN ZAMFARA SUN BANI: ‘Yan bindiga sun aika wasiku kauyuka 9 su biya Harajin miliyoyin naira ko su kwankwadi ruwan azaba

Wadanda ba su yi allurar rigakafi ba su na da hadari ga wadanda ke kewaye da su musamman ma ga wadanda garkuwar jikin su ba ta karfi sakamakon wata lalurar da suke dauke da shi ko kuma dai tsufa. Christopher Martin wani farfesa kan kiwon lafiyar jama’a da ke jami’ar West Virginia ne aka rawaito yana cewa wadanda ba su yi allurar rigakafib be su ke bai wa kwayar cutar damar rikida zuwa nau’o’i daban-daban kamar yadda ake gani yanzu.

“Kasancewar mutane da yawa wadanda ba su yi allurar rigakafi ba ke kara yiwuwar samun sabbin nau’o’in cutar. Idan har aka yi kuskuren da ya kara wa kwayar cutar karfi kamar saukin kamuwa da ita yadda aka gani a nau’in delta wannan nau’in na iya kasancewa mafi rinjaye a al’umma,” y ace.

Duk da cewa an sami nassarori kan cutar a wadanda suka yi allura, yawanci wadanda aka kwantar a asibiti da ma wadanda aka kwantar a sashen masu bukatar kulawa maia tsanani ko kuma ICU duk wadanda ba su karbi allura ba ne.
Ghazala Sharieff, babban likita na kulawa mai zurfi ya ce “Abin da ya fi mahimmanci shi ne allurar rigakafin COVID-19 na da kaifi wahen kare mutane daga kamuwa da cutan da ma mutuwa a dalilin cutar.

Zargi na uku: Kashi 95 cikin 100 na duk wadanda aka yi wa allurar na fama da matsanancin ciwo

Sakon ya kuma kara da cewa wani likita dan Isra’ila, Kobi Havi, y ace kashi 95 cikin 100 na wadanda ke ciwo solar karbi alluran rigakafin biyu.
“Kashi 95 cikin 100 na masu ciwo solar yi allura. Wadanda suka karbi alluran biyu su ne kashi 85 – 90 na wadanda suke kwanciya a asibiti

Wane ne Kobi Haviv?

Daga bayanan tarihin sa da muka gano a shafin shi da ke manhajan LinkedIn mun ga cewa Hobi Haviv jagora ne a masana’antar sarrafa magunguna na Teva da ke Isra’ila. Wani shafin kuma ya ce shi jagora ne a wani kamfani mai suna Elbit Land Methods da ke Elbit Methods Ltd

Wani rahoton da aka wallafa a shafin haaretz.com, Dr Kobi Haviv shi ne shudaban asibitin jinya na Kudus.

Mun kuma gano wata hirar bidiyo da Dr Haviv a UGETube da wannan zargin a taken.

“Dr Kobi Haviv, yau a tashar 13 labaran Israila 13,” kashi 95 cikin 100 na wadanda ke fama da matsanancin ciwo solar yi allurar rigakafi,” in ji taken.

Duk da cewa hirar ba a turanci ba ne, an rubuta fassarar abun da suke fada a jikin bidiyon hirar.

Dr Haviv ya ce “yawancin mutane solar yi rigakafi, kuma kashi 90… kashi 85 zuwa 90 cikin 100 na wadanda ke kwanciya a asibiti solar yi duka alluran biyu. Eh abin takaici allurar kamar yadda ake fada karfin shin a raguwa. Barkewar cutar a asibiti, idan mutun daya ya sanyawa mutane da yawa, ba nan ba can….” Wasu bangarorin fassarar suka fada.

A cewar kamfanin dillancin labaran Reuters kusan rabin marasa lafiya 600 da ke kwance a asibiti da matsanancin ciwon COVID-19 solar yi rigakafi da allurar Pfizer duk guda biyun. Sai dai ya bayyana cewa wannan akasi ne cikin kusan mutane milliyan 5.4 da suka yi allurar.

Mafi yawan marasa lafiyan da suka karbi allurar watanni biyar da suka gabata solar wuce shekaru 60 na haihuwa kuma suna da cututtukan yau da kullun irinsu ciwon suga, ciwon zuciya na huhu da sauransu, wadanda da ma an san su kan ta’azara cutar coronavirus.

Haka nan kuma a cewar rahoton wani binciken da aka wallaga a watan Oktoba cikin kasidar likitoci na New England, an sami ma’aikatan lafiya da suka kamu da cutar bayan akalla makonni biyu da karbar allurar rigakafin.

“Daga cikin ma’aikatan lafiya 11,453 da suja yi allura, 1467 (kashi 13.1 cikin 100) solar yi gwajin RT-PCR – mai nuna sakamakon gwajin nan take – lokacin da ake gudanar da bincike. Daga adadin da suka yi gwajin 39 solar kamu da cutar,” wani bangaren binciken ya bayyana.

Duk da cewa ana iya samun irin wannan akasin na wanda ya yi rigakafi ya kamu da cutar yawan da ake amfani da shi a matsayin hujja ba gaskiya ba ne dan haka yaudara ce.

Zargi na hudu: Kaifin allurar na raguwa ko bacewa

Gaskiya ne wai garkuwan da ake samu daga sadda aka yi allurar farko yak an ragu, wanda shi ne dalilin da ya sa ake sake bayar da wani allurar wanda zai inganta kaifin maganin. To amma wannan bay a nufin wai karfin allurar na raguwa ko yana bacewa.

Kaifin aikin allurar ya banbanta daga allura zuwa allura, amma duk wadanda mahukunta a fanin lafiyar suka amince da su suna da karfin kare mutun daga kamuwa da cutar ko ma mutuwa daga shi.

Bayanan Hukumar Dakatar da Yaduwar Cututtuka, CDC solar nuna cewa Johnson and Johnson na da kaifin kashi 71 cikin 100 na kare mutun daga zuwa asibiti dan COVID-19 a manya wadanda ba su da wata cuta, a yayinda Moderna ke da kashi 93 cikin 100 ita kuma kashi 88 cikin 100.

Zargi na biyar: Alluran booster suna kara ciwo a jikin wadanda suka riga suka kamu da cutar

A halin yanzu an amince da alluran booster ma manya a Amurka kuma duk wanda ke da shekaru 18 na haihuwa ko fiye wanda kuma ya yi allurar Moderna ko Pfizer sa’anan ya cika watanni 6 da yi ko kuma ya yi allurar Johnson and Johnson watanni biyun da suka wuce, zai iya zuwa a yi mi shi karin allurar.

Hukumar kula da Abinci da Magunguna a Amurka wato FDA tana ba da shawarar karbar allurar watanni 6 bayan daya daga cikin alluran da ake kira mRNA wato Pfizer da Moderna domin bayanan da aka samu dangane da aikin su ya nuna cewa bayan wani dan lokaci garkuwar da suke bayarwa na raguwa.

A waje guda kuma allurar Johnson & Johnson ana bayar da shawarar yin allurar watanni biyu bayan allurar farko tunda bayanan karfin aikinta a cikin jama’a ya nuna cewa karfin aikin ta kashi 71 cikin 100 wanda ya nuna cewa Pfizer da Moderna solar tsere mata.

Zargi na shida: Allurar rigakafin ba ta aiki

Allurar rigakafi na aiki, shi ya sa hukumar FDA ta amince a yi amfani da su a kan jama’a

About NgArewa 2782 Articles
Am the pioneer of this web. Am smart, vibrant, and I love to keep the readers informed, and Blogging is my profession and wining is my satisfaction.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*